Showing 171001 words to 174000 words out of 275313 words
Chapter 58 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
kashi, sai dai a nemi Salima a rasa ba Deedayah ba, a xo ma a kai ni gidan Rakiyar kwana biyu ban ga Deedayar ba, jiya Ina jin ma kamar nayi mafarkinta, Amadun ma a xo a kira min shi ban ji dadin wnn mugun alkaba'in na Maryam ba" Karfe uku ya wuce Khaleel ya iso gida tare da Zayyad a motar Zayyad din, Zayyad yace "Why don't you just go to where u picked her from kaji ko ta koma gida Khaleel" Khaleel da gaba daya ya koma kamar wani mara lafiya ya juya yana kallon Zayyad, Zayyad yace "Yess, she can decide to just go back home at last, ka daina ba kan ka wahala haka, beside you need rest, don't stress ur self much, u know ur condition Khaleel" Khaleel ya jinginar da kansa da kujeran motar yace "What will I say idan naje gidansu, and wnn sojan nan dama I've made a vow, it's either I or him, nasan xai yi xargina idan na je gidan, contact dina da shi baxai yi kyau ba" Zayyad yace "Toh ni ka bani address din gidan, xan je, xan san kuma abinda xan yi, but I am exhausted sai na d'an watsa ruwa na ci abinci snn in tafi" Khaleel that have no other choice yyi accepting din abinda Zayyad yace, coz he trust him, 100% trust, Zayyad ya sauka motar ya bude gate din da suka bari a bude tun safe da suka fita, Khaleel ya shiga gidan da motar yyi parking, Zayyad ya nufesa bayan ya kulle gate din gidan yace "Mun yi asaran jam'i, ko in ce kayi asaran jam'i" Khaleel bai ce komai ba ya nufi entrance din shiga gidan, he feels like he is going to fall sick at anytime, yasan he is harming himself stressing din xuciyarsa da yake yi, Zayyad ya bi bayansa yana tausayin abokin nasa, dafa sa yyi yace "You know what Khaleel, ka kwantar da hankalin ka plss, in sha Allah I will try my best xa mu ga yarinyar nan, ynxu ka yi sllh ka ci abinci ka sha drugs dinka and rest..." Khaleel yace "Alright" Bude kofar parlon da shi ma din suka bari a bude tun safe yyi, tsaye yyi bakin kofar bai shiga parlon ba, Zayyad dake bayansa yace "What happen? Why are u still?" Khaleel ya kasa cewa komai, Zayyad ya bi gefensa ya leka parlon, kwance take saman dogon kujera tana bacci peacefully, daga kasa kusa da kujeran kuma darduma ne da tayi sllh a shimfide da Hijab din da ya bata da asuba, Khaleel ya karasa cikin parlon walking tiredly yana kallonta, kujeran ya nufa ya duka a hankali yace "Heedayah" Lkci daya ta bude ido ta mike xaune da sauri tana kallonsa, shiru yyi yana kallonta shi ma, Zayyad dai yyi wucewarsa sama yana imagining irin wahalan da suka sha kan yarinyar nan tun safe ashe gata nan tana ta baccinta hankali kwance, tana mitsika idonta a hankali tana kallon Khaleel tace "I am hungry" Yace "Ina kika tafi?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Talk to me, yaushe kika dawo?" Tayi kasa da idonta tace "Tun daxu" xaunawa yyi saman kujeran da take xaune kai, ya jinginar da kansa da kujeran ya lumshe idonsa a hankali yace "You suffered me Heedayah, why did you leave, don't you know...." sai kuma yyi shiru, ya bude idanuwansa yace "But tell me, me yasa baki son komawa gidan ku, sun maki wani abun ne da baki son gaya min??" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai baxan koma ba...." Yace "To Ina kike son in kai ki yanxu?" Tayi shiru tana kallonsa, can tace "Ina son in xauna a nan, da kai" Da mamaki ya xauna da kyau yana kallonta, ya girgixa kai yace "Noo Heedayah, it can't be, idan baki son xama nan gidan da ku ka sauka ne sai in mayar da ke Kaduna" tace "Kadunan ma bana son xuwa" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, tace "Idan baxan xauna nan ba sai in tafi wani wajen" Da sauri yace "Aa xa ki xauna nan mana, kar ki tafi ko ina plss, kin ji" Jinginar da kanta tayi da kujeran bata ce masa komai ba, Yace "Me xa ki ci?" Tace "Rice and stew" yace "Ohk bari in yi sllh in tafi in siyo maki" Tv ya kunna mata ya kulle kofar da makulli don gani yake tana iya guduwa kuma, ya wuce sama yana waigota, sai da yyi wanka ya sauya kaya snn yyi sllh, yana xaune saman darduma yana kallon Zayyad dake kokarin kunna Cigarette yace "Hey pls not here Zayyad" Zayyad yace "Sbda budurwar ka na gidan?" Yace "No kawai kasan dai bana so" Zayyad ya saka a aljihu ya mike xai fita, Khaleel yace "Plss will you mind getting us food" Zayyad yace "Ohk" daga haka ya fita dakin, Khaleel ya mike ya bi bayansa, har sannan Heedayah na xaune parlon tana kallo, Zayyad yyi mata kallo daya ya nufi kofa, ita ko idonta na kan TV, Khaleel na daga stairs a tsaye yace "The keys" Juyowa Zayyad yyi, Khaleel ya jefa masa makullin kofar parlon ya cafke snn ya bude kofar ya fita, Khaleel ya karaso parlon ya xauna kujeran dake facing dinta yace "Wa ya dawo da ke nan gidan" Tace "Da kafa na dawo" yace "Ta ya kika gane?" Tace "kawai na gane" Yyi shiru yana kallonta bai ce komai ba. Flight Abba ya biyo xuwa Abuja coz baxai iya driving din ba kuma ba train, Mami dai a parlon Dinar ta yini, tayi kuka har ta gaji yau kam, abu uku kenan a rayuwarta da ya sa ta shiga tashin hankali da shock sosai, na farko kashe mijinta na farko a gabanta wanda shekaransu hudu da aure aka tafi da 3 years old son dinta wanda sai tashin labari, na biyu kuma rasuwan Mahaifinsu junaid, sae ynxu da aka nemi Heedayah ko sama ko kasa tun jiya, ita kanta ta rasa irin soyayyar da take ma Heedayah, tashin hankalin da ta shiga ko 'yar cikinta sai haka, Junaid yyi kokarin danne nasa damuwar sosai ba kadan ba ganin halin da Mahaifiyarsa ta shiga, ya dinga kwantar mata da hankali with assurance na cewar xa a ga Heedayah idan Allah ya yrda, ganin Shuraim yana kan komai ya sa Junaid ya tsaya tare da Maminsa kawai, duk wani information da Shuraim ya so samu ko kadan ne a kan Khaleel bai samu ba, don Farida dai bbu abinda ta sani a kansa, ko sama ko kasa kuma ta duba wayar da ya ba Heedayah bata gani ba, wanda hakan ke nuni da cewar da shi ta fita, broadcast kawai Shuraim ya bada a duk gidajen Radio da ma talabijin, sai ma da yyi hakan snn ya kira Abbansa ya sanar masa abinda ake ciki. Abba bai iya ce ma Mami komai ba bayan Shuraim ya kai sa har gidan, don yana sauka Airport Shuraim ya daukesa suka wuce, Abba na kallon Dinar dake xaune kasa da Hijab dinta har kasa ita babban abinda ke daga mata hankali yake sa ta kuka sosai sai cewa da mutane xa su dinga yi ai a gidanta abun ya faru, "Tun karfe nawa ta fita a jiyan?" Cewar Abba kenan yana kallon Dinar, tana share hawayenta a hankali tace "Ba ayi isha ba, duk muna nan parlor a xaune ta shiga kitchen, ni ina ce abinci ma ko wani abu xata dauka, ashe bude kofar kitchen din da ke nan nafi shekara ban bude ba tayi ta fita, shi kuma me gadi be sani ba ya bude mata gate...." Tana kai wa nan ta kuma rushewa da kuka, Abba yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Mami dai bata cewa komai sai hawayen da take gogewa, Shuraim dai na tsaye bakin kofar parlon yana rungume da hannunsa, tun safe ko ruwa shi kam bai sha ba dama, Abba na kallon Farida yace "Ke kinsan inda ta san shi mutumin da ya bata waya" Cikin sanyin murya Farida ta sauke idonta kasa ganin no need of hiding anything again, ta shiga yi ma Abba bayani tace "Ranan mun je shopping Mutumin ya tare mu a hanya muna dawowa...." Shuraim ya sauke hannunsa yana sauraronta keenly haka ma kowa na parlon, nan ta bada labarin yanda Heedayah ta fara haduwa da Khaleel, ta kuma ce daga nan bata sake sanin suna haduwa ba har ya bata waya sai just of recent lkcn bikinsu Aunty Jamila, shi ma din Heedayah bata bari ta sani ba, Abba dake ta kallonta yace "Ya sunan hotel din da ku ka fara ganinsa" Nan Farida ta gaya masa, Abba yace "Xa ki iya tuna date, day, da time din da ku ka gansu bakin hotel din" Farida tayi shiru tana naxari, Abba yace "Relax and think calmly dear, the date, time and day...." Mami dai sai kallonsu take gaba daya. Khaleel na kallon Heedayah ta gama cin abincin gabanta ta matsar da plate din, yace "Kin koshi?" Ta gyada masa kai tana kallonsa tace "Why is ur frnd smoking?" Ya d'an bude ido yace "Where did you see him smoke?" Tace "Naji warin cigarette sae na leka window na gansa parking space smoking..." Shiru tayi ganin Zayyad na sakkowa kasa, Khaleel ya bi sa da kallo ganin ya nufi kofa, Zayyad yace "I'm leaving, enjoy ur self Kayy" Khaleel ya mike yana kallon Heedayah yace "Let me see him off" ta gyada masa kai, daga haka ya bi bayansa, Heedayah ta bi su da kallo har suka fita, Zayyad ya bude gate ya fitar da motarsa waje, Khaleel ya tsaya kusa da motar yana kallonsa kafin yace komai Zayyad yyi masa wani murmushi yace "But tell me, how was ur experience yesterday night, nasan baka ta6a ba" Khaleel yace "What experience?" Zayyad ya kashe masa ido yace "Sai na tona" kallonsa kawai Khaleel ke yi, Zayyad ya fashe da wani dariya, sae a snn Khaleel ya gane inda Zayyad ya dosa ya dinga masa wani kallo, Zayyad yace "Don't bother her much, she is too young" Khaleel yyi ignoring din xancen yace "Plss I need a favor" Zayyad yace "All ears" Khaleel yace "Ko da yake mu yi waya kawai" daga haka ya juya ya koma cikin gidan ya kulle gate dinsa. Tun da aka yi Magrib Khaleel na masallaci har sai da Zayyad ya kirasa snn ya fito, Zayyad ya sakko daga motarsa rike da ledan fresh milk ganin Khaleel, yace "A ina ka bar visitor din taka?" Khaleel yace "Tana ciki" bude gate din yyi suka shiga ciki tare, Khaleel na kallonsa yace "Did u get d pill??" Zayyad yace "Sure..." A aljihu ya ciro pills din ya basa, Khaleel ya amsa yasa a nasa aljihun, snn suka shiga Parlorn, xaune suka Heedayah tana shan pineapple tana kallo, Khaleel ya amshi ledan hannun Zayyad, Zayyad ya wuce sama shi kuma ya wuce kitchen, glass cup ya dauka ya xuba milk din ciki snn ya ciro pill din 6alli daya ya saka, ya sa cokali sae da ya tabbatar ya narke snn ya fito parlor, xaunawa yyi kusa da ita ya mika mata, tace "What's that?" Yace "Milk" tace "Na koshi" yace "Noo ki sha kadan mana, sai in shanye sauran" amsa tayi ta sha kusan rabi snn ta mika masa, ya sakar mata murmushi ya amsa ya ajiye, ta maida dubanta kan tv, yana ta xaune kusa da ita har ya ga ta fara hamma, ya kalleta yace "What?" Kanta ta daura kan kujeran a hankali tace "Bacci" ya mike yace "To kwanta" Ba musu ta kwanta ta lumshe ido, ya koma wani kujeran yana kallon kyakkyawan fuskarta ko kiftawa bbu, bayan kusan minti goma ya mike ya tafi sama sai gashi sun sakko da Zayyad, Zayyad yace "Toh wai idan mun je can din sai in ce me tukun?" Khaleel yace "You just explain ka ganta ne a bakin hanya, kawai dai kayi composing duk abinda xaka ce I trust you, I'm really disturbed Zayyad, nasan ynxu her guardians are very worried, ita kuma naga alamar she is serious ba komawa xata yi ba, I don't know what came over her all of a sudden" Khaleel ya nufi Heedayah dake ta bacci, dukawa yyi yana kallonta ya dauketa a hankali kamar wata yar tsana ya nufi kofa ya fita Zayyad ya bi bayansa ya kulle gidan, a bayan motar Zayyad ya kwantar da ita still looking at her, Zayyad ya shiga maxaunin driver, Khaleel ya rufe motar daga karshe ya koma front seat, Zayyad ya tada motar suka bar layin, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka isa street din su Dinar, Khaleel yace "Drop me here, gida na daya, na biyu na uku.... I think na biyar shine gidan da take, you just step down and knock the gate" Zayyad yace "Ohk" sauka Khaleel yyi da face cap dinsa da ya kafa a kansa ya rufe kusan rabin fuskarsa yyi wucewarsa walking calmly ya bar area din.
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Driving Zayyad yake yi carefully yana kirga manyan gidajen da yake wucewa a layin, har ya tsaya a dai dai gida na biyar kamar yanda Khaleel yace masa, a hankali ya bude motar ya sauka ya nufi gate din yana kare ma gidan kallo, da zoben hannunsa ya kwankwasa gate din, bayan few seconds ya kuma kwankwasawa, dai dai nan aka bude gate din, wani ne sanye da khaki hannunsa rike da bindiga ya gani, sai ga Mai gadin gidan ma ya taho da sauri, Zayyad ya d'an sosa kansa yace "Erm don Allah tambaya nake" Me sanye da khaki na kallonsa fuska a murtuke yace "Go on..." Zayyad yace "Na xo wucewa ne daxu na hadu da wata yarinya bakin hanya, she was almost unconscious, so being the good Samaritan that I am na nemi gefe nayi parking na sauka coz she looks responsible, nan kuma na tambayeta abinda take yi bakin hanya da daren nan, I have to listen with both my heart kafin in fahimce me take ce min, that dumping dinta wai wasu suka yi a wajen suka wuce, I asked her wani anguwa take, and she mentioned here with both the address, daga haka kuma she passed out, wato ta suma, I hate police cases snn ni matafiyi ne ba d'an Abuja ba, bana son kuma duk wani abu da xai hadani da Yan sanda su bata min lkci, to tunda dai ta bani address din inda take shine na dai sakata a mota na kawota nan din da tace min gidansu ne, ina kuma fatan shine gidan nasu" daga Mai gadi har masu khaki biyu dake tsaye bakin gate din kallon Zayyad that is speaking confidently suke suna sauraronsa da kyau, daya daga me khakin sojan ya fita xuwa gun motar Zayyad holding on to his gun, ya leka cikin motar yana kallon Heedayah dake bacci gently, komawa yyi yana duban Zayyad yace "I think it's better ka kai ta police station din for police report ba yar gidan nan bane, kuma shi xai fi maka sauki" Mai gidan ne da matarsa ke tahowa xuwa parking space alamar xa su fita don makullin mota na hannunsa, kuma dama jiransa sojojin suke ya fito kasancewar su excort dinsa na nan garin, ganinsu tsaye bakin gate din gidan har yana hango Zayyad yasa Mai gidan yace "Allow him, if he wants to see me, let him plss" Sojan ya koma gefe Zayyad ya shigo compound din yana kallon Mai gidan almost shocked, walking calmly Mai gidan ya iso har gabansa ya tsaya ya basa hannu with smile a fuskarsa suka yi musabaha, Mai gidan yace "Kana son ganina ne gentleman, kaga kuma xan fita yanxu but in sha Allah ka dawo gobe da safe xan ganka" Zayyad dake ta kallonsa ya fara kame kame yace "Noo, A'a dama yarinya na kawo, i was thinking gidansu ne nan, tace min nan ne gidansu, Kuma address din nan ta bani, I saw her almost unconscious a hanya and decided to help her" da mamaki Mai gidan yace "Yarinya? Ina yarinyar take yanxu?" Zayyad yace "Tana cikin motana" gaba daya Zayyad a daburce yake ya ma ki yarda su hada ido da Mai gidan, Mai gidan yace "To shigo da motar taka" Zayyad ya juya da sauri xai fita and dama yyi niyya idan ya samu ya fita to fecewa kawai xai yi abunsa, daya daga sojan ya dakatar da shi, snn shi sojan ya fita kamar yasan abinda ke ransa, Mai gadi ya bude gate din gidan sojan ya shiga motar Zayyad snn ya shigo da motar cikin compound din, matar da suka fito tare da Mai gidan ta karaso gun me gidan nata tace "Abiey Ina jin yarinyar da Mum Islam tace ake nema a gidan makotan mu ce fa, kilan bai gane kwatancan nata bane, nan makotan mu ya kamata ya kai ta" Zayyad dai sai keto masa xufa yake yana sharewa with swag, Mai gidan ya nufi motar da sojan yyi parking a tsakar compound yana duba cikin motar, Tana kwance har snn sai da kusan rabin fuskarta rufe yake da mayafin abayarta kamar yanda Khaleel yayi mata tun daxu da ya kwantar da ita a motar, sojan ya bude motar ya yaye mayafin daga fuskarta bayan ya kunna wutan motar, kallonta kawai Mai gidan ke yi without blinking, ita dai matar na tsaye taki leko cikin motar tace "Ko a kira Mum Islam nasan baxata rasa sanin yarinyar ba tunda tana shiga gidan sosai" Sojan dake tsaye bakin motar shi dai ya kalli Heedayah snn ya sake kallon matar Mai gidan nan, yyi hakan yyi sau uku, Jin shirun da Mai gidan nata yyi, matar tace "Abiey Ina magana, nace should they call Mum Islam ayi alerting din neighbors din namu" Can dai ta gaji da magana ganin mijin nata ya ki cewa komai, ita ma