Showing 111001 words to 114000 words out of 275313 words

Chapter 38 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

na fi kowa sanin halin d'an nan naka Shureen, kwanaki kana ji cewa yyi xai kwakule idon Deedayah ya kai kungiyar su amma ko mataki baka dauka ba, ni dai ina ta xuba ido in ji tace idonta na ciwo ko wani abu wllh a nan xan rufe ido mu tafi gidan yan sanda in gaya masu abinda Shureen yace" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Mumy dai ta cika kiris ya rage ta fashe sai dai bata tanka kaka tun asali dama, Abba ya sauke ajiyar xuciya ya girgixa kai shi ma bai ce komai ba... Yau Heedayah tana xaune dakin kaka tana kallon cartoon ta cikin glasses dinta dake mata kyau sosai kullum baya rabo da idonta, kaka ta yi mata maganan ta miko mata darduman kusa da ita yyi sau uku amma bata san tana yi ba, gaba daya hankalinta na kan kallon da take, aka bude kofar dakin Shuraim ya shigo, rufe ido tayi da sauri xuciyarta na bugawa, Kaka tace "Algungumar yarinya kawai sai wahala take bani Shureen, tun daxu fa nake mata magana tayi min banxa ta saka kallon jaraba da baxae mata gafara ba a gaba, ni dai wllh na gaji da yarinyar nan, ba ta da aiki fa sai kallon robobin nan da an mayar min tashar wa'axi sai ya canjo min na aljanu, gashi kaf gidan nn bbu wanda ta raina sama da ni, ynxu kuma daga ganinka ta runtse ido ba tsoron Allah, shi boding din har ynxu basu koma bane, naji labarin Farida sun yi hutu wajen Junaidu fa, kawai dai Uwar bata bari ta xo mana nan bane..." Bude kofar dakin aka yi sai ga Farida ta shigo tana kalle kallen Inda xata ga Heedayah, she looks so happy, ganin Heedayah ta saki jakar hannunta ta tafi da gudu ta tsallake Shuraim cike da murna ta rungume Heedayah gam tace "Didi na dawo, Didi I am happy you can see me...."





Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍


Heedayah ta bude ido a hankali tana kallon fuskar Farida, murmushi tayi ta rungumeta ita ma tace "Farida" sai kuma ta saketa tana kallon fuskarta, ta wara manyan idonta ta kai hannu dimples dinta tace "Kamar na Yaya" Dariya Farida tayi tana kallonta, she is so happy seeing Heedayah, Kaka ta nemi waje ta xauna tace "Allah sarki, jininsu ya hadu wllh, su Rabi'ah da Khadijah dama bakin hali baxae bar su suyi hka ba, uwar tayi kane kane ta hanasu, ko kulata ma basa yi a gidan, ita ma Deedayar ta kanta take" Farida dake murmushi har sannan ta xamo kasa tace "Ina yini kaka?" Kaka tace "Lfya lau Farida, ya karatu? Sae yau shi Honorable din ya ga daman sako ki kixo gun uwarki knn" Farida tace "Aa naje gidan wani kawun mu ne fa kaka ba gidan Baffa nake ba" Kaka tace "Toh baku gaisa da Shuraim ba, ko baki gansa ba" Juyawa Farida tayi ta d'an kallesa, ya ki juyowa fuskarsa bbu yabo bbu fallasa, ta kyabe baki tace "Ina wuni" still bai juyo ba yace "Lfya" Heedayah sae satan kallonsa take, Kaka tace "Tunda uban ya samar masa Soja yake amsa gaisuwan kowa cikin isa da gadara, mu dai bamu kulasa ba balle ayi tashin hankali da shi...." Farida ta mike ta daga Heedayah tace "Ki rakani in je in gaida Mamina" Kaka tace "Aa je ki gaisheta ki dawo, baki ga ni daya bace parlon, ae ita ke taya ni xama" Farida ta sake hannun Heedayah tace "Toh" daga hka ta fita dakin, Heedayah na kallon kaka kamar xata yi kuka tace "Kaka don Allah in bi ta, ae xan dawo..." Kaka tace "Toh kya ci kanki, bi ta ku je, dama amfanin me kike min bnda kallo" Da sauri Heedayah ta juya xata fita parlon tayi tuntube da kafar Shuraim ji kke tim ta fadi kasa, A tsorace ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace "Wayyo kayi hkuri..." Ya janye kafarsa bai kalleta ba, kaka tace "Yau naga jaraba, Allah ne shi da xa ki basa hkuri bayan tika ki da katon kafarsa yyi da kasa, Shureen fa ba Mala'ika bane da kike gigicewa ki tsorata idan kin gansa, ko meye gamin ki da shi banda Ubansa da yayi sanadin xuwan ki gidan nan??" Mikewa Heedayah tayi ta fita da sauri, duk gaba daya a tsorace take, kaka tace "Ni dai ba ruwana, kai kuma Shureen ya wnn yarinya Farida na gaishe ka kana amsa mata a walakance kamar an maka dole? Ba fa yar banxa bace da ka ganta nan, da gatan ta wllh, kuma da kyar idan ubanta bai fi naka kudi ba duk da ya rasu, snn ga kawunta shi ma gidansa gari guda yyi gaba daya anguwar nan, bbu abinda bbu a gidan, to a kan me kuma kake amsa mata gaisuwa can ciki ciki? Ka fita kyau ne ko gayu aka ce maka? kai da ko manyan kaya baka sakawa sae na tsigalallu" Ya juya yana kallon kaka yace "Na hada wani abun ne da ita? Kin ga ki daina min shisshigi a lamarina, bbu ruwanki da harkata, dole aka ce maki sae na amsa gaisuwarta ko ina da wani alaka da ita ne??" Bai jira cewarta ba ya mike ya fice daga dakin, kaka ta nemi kujera ta xauna a hankali tace "Ikon Allah, Amadu dai ya ja mana bala'i, muna xaman xaman mu yace xai kai sa Soja gashi tun ba a je ko ina ba ya fara kilewa.... To banda bala'i yaushe har Shureen ya fara magana da har xae xageni ya fita, dama haka sojojin suke bani da labari??" Washegari Monday da safe Mami ta koma bakin aikinta, Farida ta gama duk abinda xa su yi da Heedayah a bangaren Mami suka fito, Heedayah na sanye da wando da riga sai hula da ke kanta, sosai kayan suka yi mata kyau kamar yar turawa ga gashinta da ta baxo ta cikin hular, Farida kuma Abaya ta saka da veil dinsa, ta kulle bangaren Mami suka wuce gaida Kaka a dakinta, Kaka tace "To ita Deedayah me yasa Rakiya bata siya mata irin wnn kayan na jikin ki ba, ko don ba ita ta haifeta ba sai tayi ta sa mata kayan anna??" Farida dai bata ce komai ba, haka ma Heedayah, Farida ta mike tace "Kaka xa muje tsakar gida mu dawo" Daga haka Farida ta kama hannun Heedayah suka fita dakin, Kaka ta kyabe baki tace "Wnn faridan ta fiye rawan kai da iyayi kamar dai uwarta, ba don wannan halin nata ba dai Shureen xai aureta, banda dai kowa na son inda nasa xai huta ai wnn rawan kan nata ya fi karfin Shureen" Garden din cikin gidan Farida suka tafi da Heedayah, suka xauna kan kujeran dake garden din Farida na kallonta tace "Toh ko na nuna maki yanda ake operating wayar ai ba siya maki Mami xata yi ba, nima fa Baffanmu ne ya siya min, kuma da kyar ta bar ni na rike..." Heedayah ta langwabar da kai tace "Ae Yaya xan ce ya siya min ko Yaya Sudais" Farida tayi dariya tace "Toh shkkn, nasan Yaya xai iya siya maki, shi kinsan babu ruwansa" Tsakaninta da Allah ta shiga nuna ma Heedayah ynda ake amfani da waya da abubuwan dake cikin waya tun daga lock button, Heedayah ta maida hankali kai kace karatu take dauka... Tun da suka shigo garden din Shuraim dake xaune sama yana karatu a laptop dinsa ya mayar da laptop din gefe yake kallonsu, su kam ko lura da shi basu yi ba, can ya mike ya bar wajen, Farida ce ta fara hangosa yana tahowa toward them bayan ya sakko downstairs, tayi kasa da murya tace "Wannan Yaya Shuraim din is coming" Sosai Heedayah ta rikice a gun, ta dinga cewa "Farida tashi mu tafi yana yi ma mutane duka wllh, ki tashi mu tafi...." Farida ta hade rai tace "Toh ba sai ya doke mu ba" Har dai ya iso kansu, yana kallon Farida yace "Me ku ke yi a nan?" Farida ta d'an kallesa tace "kawai labarin mu muke" yace "You are showing her how to operate phone right?" Tace "Yea.... sannan muna hiran makaranta" ya mika mata hannu yace "Bani wayar" Mayar da wayar Farida tayi bayanta ta hade rai tace "As in how?" Yace "Baxa ki bani ba" A takaice tace "Gaskiya...." Mikewa Heedayah tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba xata bar wajen yace "Kina kara step daya sai na 6allaki" Tsayawa tayi, tayi narai narai da ido, sai dai taki yarda ta juyo ta kallesa, Farida ta mike xata bar wajen ya riketa ya kwace wayar a hannunta, tsaye tayi tana kallonsa tana huci, yace "Daga yau.... Ina nufin daga wannan moment din ko by mistake kika sake xaunar da ita kina nuna mata waya sai kin sha mamaki a gidan nan" Farida tace "Toh ai wayana na nuna mata ai ko? Kuma ni ka bani wayata...." Ya mata wani kallo ce "Ki kwata mana" Kallon Heedayah yyi ya kara daure fuska yace "Uban me xa kiyi da waya da kika xauna tana nuna maki ynda ake amfani da shi" Heedayah ta girgixa kai bata ce komai ba, strictly yace "Juyo Ina maka maki magana" A hankali ta juyo tana facing dinsa idonta har ya kawo ruwa, ya kara shan kunu yace "Ke kika ce ta nuna maki waya ko?" Ta girgixa kai bata ce komai ba, yace "Toh na sake ganin ki xaune ana nuna maki waya sai na xane ki a gidan nan, daina kallona" Ta sauke idonta kasa hawayen ciki ya xubo, a fusace Farida ta bar wajen kamar xata tashi sama, Shuraim ya bi ta da wani kallo har tayi corner, yana kallon Heedayah yace "Start going" juyawa tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya har suka shiga cikin parlor sannan ta juya suka hada ido, daure fuska yyi ta nufi dakin Kaka tana goge idonta, Kaka dake ta sauraron Farida ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Toh, a gaskiya ni dai baxan iya tunkaran Shureen ba ynxu don ya xama abinda ya xama, rashin kunya yake ma kowa gadan gadan, Kuma ni ban san ko har sojojin sun basa bindiga ba inje in ja ma kai na, yo in ja ma kaina mana, yanxu sai ki tashi mu tafi bangaren uwarsa nasan tana can tana baccin asara kin san me xaman banxa, nasan ita idan tayi masa magana xai ji" Heedayah na shigowa dakin kaka ta fashe da kuka ta fada kan gado har da Shessheka, kaka ta mike da sauri tace "Lafiya, me ya faru, ni dai na shiga uku, kukan me kike" Kuka kawai Heedayah take, Farida tace "Shine ya doketa kila" Kaka tace "Ya doke ki???" Da sauri Heedayah ta mike xaune tace "Aa bai dokeni ba fa" Kaka tace "To kukan me kike" ta girgixa mata kai kawai, Kaka tace "Oho ni ban iya wahala, tashi mu je gun uwar tasa Farida, dabanci kawai Shureen ke ji a gidan nan kwanan nan" Tare Farida suka fita da kaka xuwa bangaren Mumy, Khadijah na xaune parlor tana kallo, kaka tace "Gantalalliya abinda kika iya kenan, Ina Rabi'ar?" Khadijah ta wani daure fuska tace "Ta tafi gidan Aunty Asma'u" Kaka tace "Ta tafi gidan Asma'u? Shine bata sallameni ba? Wai me yasa Amadu ke min haka ne a gidan nan kamar ba uwarsa ba, ynxu fa a kullum da kyar ku ke shigo min bangarena sau daya, Mata duk ta kanainaye ku bata son ku ra6i kowa na gidan nan kullum kuna kunshe a daki?? Toh bari ya dawo shi Amadun" Mumy na daki duk tana jin kaka, kafin ta karasa cikin dakin tayi saurin fitowa, Kaka na ganinta tace "To Shureen ne ya kwace wayar Farida, kuma dubu dari biyu aka ce an siya wayar, to siyarwa yake da niyyar xuwa yyi shine ban gane ba" Mumy tace "Ni kuma ina naga Shuraim da safen nan kaka?" Kaka tace "Aa ba ruwana ki fita ki nemosa duk inda yake ya maido ma yar mutane wayarta kafin ya tafi chechenia da shi a shiga uku" Mumy ta kalli Farida daga sama har kasa, Farida tace "Ina kwana" a walakance Mumy tace "Lafiya" Kaka tace "Yar gidan Rakiya ce fa, daga makarantar kwana suka yi hutu ta xo mana shine har xai saka mata ido a gidan ya kwace mata waya to ina ruwansa da ita idan ba neman fitina ba, daga ance an samar masa Soja sai ya xame mana ibilisu a gida??" Mumy tana wani kyabe baki tace "Toh ni ban san inda Shuraim yyi ba tun asuba da ya shigo ya gaisheni ban sake ganinsa ba wllh" kaka tace "Toh ai nemosa nace xa kiyi idan ba haka ba wllh sai in ja ta mu tafi gidan yan sanda su san abinda ake ciki, muka san ko sojojin kwacen wayar mutane suka sa shi" Tana fadin haka ta kama hannun Farida suka fita, Mumy ta bi su da wani irin kallo. Har Mami ta dawo da yamma Shuraim bai ba Farida wayarta ba, barin gidan ma yayi gaba daya, Mami ta tabe baki bayan ta gama sauraron farida tace "To uban wa xa kiyi ma kuka?" Farida ta kara rushewa da kuka tace "Wllh Mami bbu abinda muka yi masa kawai ya amshe wayata" Mami tace "Me kike yi da wayar ya amsa?" Cikin kuka tace "Babu komai wllh" Mami tace "Toh ai shkkn, dama nima na gaji da shegen wayar da kike rikewa" Tana fadin haka ta shiga daki, Heedayah dai na xaune parlon tayi shiru, can ta mike ta isa gun Farida tace "I am sorry I caused you all this Farida, da bance ki nuna min ba baxai amsa ba" Farida tace "Ai wllh sai ya bani wayata, you caused me nothing" Kaka ce xaune parlon Abba da Farida, Heedayah ma na xaune kusa da kaka, Abba yyi shiru yana sauraron kaka, kaka tace "Toh a gaskiya bbu ruwana kar ya ja mana fitina muna xaman xaman mu, a nemo sa duk inda ya shiga ya ba yar mutane wayarta" Abba na kallon farida yace "Me kike yi da wayar ya amsa?" Ta girgixa kai a hankali tace "Babu abinda nake yi Abba, ni da Heedayah ce ma a xaune lkcn" Kaka tace "To me xata yi da wayar banda karatu kaji ka da wata magana, bbu abinda suke yi vanda karatu" Abba yace "Toh shkkn xan nemi Shuraim din" mikewa kaka tayi ta nufi kofa tace "Ku taso mu je, shi da ya sa shi a sojan su karata can" Mikewa Farida da Heedayah suka yi suka bi bayan kaka. Shuraim na tsaye dakin Mumy dake ta masa fada kamar xata ari baki, shi dai bai ce mata komai ba, tace "Banda ka haifi yaro baka haifi halinsa ba ina ruwanka da lamarin su a gidan nan? Ka hada wani abu ne da yarinyar da xaka amshe mata waya da sunan discipline? Ina ruwanka da ita nace" ya shafa kansa still bai ce komai ba, tace "Toh wllh ka kiyayeni a gidan nan, banda baka kishina kai ko kallon yar nan xaka yi balle ka amshi wayarta Aliyu" Wayarsa dake hannunsa ne ya fara ring, Mumy tayi shiru tana kallonsa, yace "Abba na kirana" Mumy tace "Wannan damuwarka ce, ni dai idan har baxaka fita hanyar makiyana a gidan nan ba to wllh sai dai ka canxa wata uwar ba ni ba" juyawa yayi ya nufi kofa ya fita, a main parlor ya tadda kaka tana dube dube kamar munafuka, tana ganinsa ta hade rai ta hau kakkabe kujerun parlon tana cewa "Mata duk kazamai kawai" yayi wucewarsa bangaren Abba, tana ganin haka ta nufi dakinsa da sauri ta shiga tana kalle kalle, saman madubi ta ga wayoyi har biyu a ajiye da dubu biyar ta kwashe duka ta fice. Shuraim yace "Abba Heedayah take koya ma ynda ake operating waya shi yasa na amshe" Abba yyi shiru yana kallonsa haka ma Mami dake parlon tana xuba ma Abba abinci, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, can Abba yace "A ina ka gan su?" Shuraim yace "Can baya" Abba yace "That's wrong, and you did the right thing collecting the phone, ka rike wayar wajen ka nan da kwana biyu sai ka bata" Shuraim ya dago kansa yace "Ita ma bai kamata ta rike waya ynxu ba, she still in Jss2 I think" Abba yace "Haka ne but assuming a gidan nan take ni baxan bari ta rike waya ba, but tunda ba a nan take ba we have no say, ka maida mata wayarta after two days..." Shuraim yace "Idan xata koma makaranta xan bata amma ba ynxu ba" Abba ya kalli Mami da bata kalli Inda suke ba yace "Ur opinion Rahinah" Mami ta kallesa tace "Duk ynda kayi dai dai ne barrister" Abba yace "Alright, ka bar wayan gun ka Shuraim" Shuraim yace "Toh shkkn" daga haka ya mike ya fita parlon. Karfe tara da rabi kaka na xaune dakinta ta daura kafa daya kan daya ta gama cinye kazar da Junaid ya kawo mata tana sakace hakori Shuraim ya shigo, tana ganinsa ta ci gaba da sakace sakacenta tana lumshe ido, ya bi dakin da kallo sannan ya juya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login