Showing 213001 words to 216000 words out of 275313 words
Chapter 72 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
na dauke wata yar babban mutum kai ne kuma xaka dauko ta mun fi wata hudu muna targeting mun kasa dauketa, sharadin karshe kuma baxaka sake gigin bijire umarnin mu ba, idan kuma sharadin sun maka tsauri cikin mintuna kalilan xan aika matar barxahu, snn in sa a dauko min 'yarta ma in kasheta, idan kuma ka kwafsa gaban matar wllh wllh a gabanka xan harbeta kaji har na rantse maka" Banda xufa bbu abinda Khaleel ke yi yana kallon Arne don ko wani kalma da ya fada hakan yake, baya xance biyu, snn ko dot din tausayi baya da shi a ransa, he can even do more than what he said.... Arne ya ciro masa bindigar aljihunsa ya mika masa yana kallonsa da jajayen idanuwansa yace "Mu tafi saman" Khaleel ya lumshe ido ya bude snn ya amsa bindigar a sanyaye ya shiga gaba Arne na biye da shi da nasa bindigar bayan ya rufe fuskarsa da Mask, Fago ne ya bude masu kofar dakin da Mami ke ciki da Ashnaah, Khaleel dake tsaye bakin kofar ya kallesa sannan ya shiga dakin, daga kai Mami tayi suka yi ido hudu da shi ta dinga kallonsa with so much shock ko kiftawa bata yi, Tunda Khaleel yake bai ta6a jin weakness irin na wnn lkcn ba, he felt like collapsing kawai, he wish this isn't happening, Arne dai sai kallonsa yake da mayun idanuwansa yana pointing Mami da bindiga alamar yana kwafasawa xai yi harbi, Cikin rawar murya Mami tace "Khaleel???" Kallonta kawai Khaleel keyi ya kasa cewa komai, Arne na nunata da bindiga cikin tsawa yace "Kar ki sake kiran oganmu kai tsaye...." Khaleel ya jefa mata wayarsa ba tare da ya yrda sun sake hada ido ba yace "Ki saka number da xa a kira a bada kudin fansa" Kuka kawai Mami take sosai ta ma rasa abinda xata ce gaba daya ta shiga wani irin shock ne me iya ba mutum attack, kasa ci gaba da tsayuwa a dakin Khaleel yyi ya juya yace "A kawo min number idan ta saka" daga haka ya fita daga dakin, Arne yyi wani murmushi ta cikin mask dinsa, yyi ma Mami wani firgitattcen tsawa yana nuna ma Ashnaah dake bacci a hannunta bindigarsa yace "Baxa ki sa number ba sai na harbe wnn yarinyar dake kafarki" Jin abinda yace kuma bbu alamar joke tare da shi Mami ta dau wayar ta shiga dialing number Junaid tana kuka sosai, ya kwace wayar a hannunta snn ya fice daga dakin Fago ya kulle kofar da makulli ta waje. That same time Abba da Doctor da Baffan Junaid na tsaye parlon Mami ko wannensu is just short of words, gaba daya kukan kaka ya cika ma kowa kunne a parlon, Farida da Heedayah ma kukan suke cikin tashin hankali kamar ransu xai fita, Yakumbo dai banda xare ido bbu abinda take daga wajen da take xaune, ta kalli wnn ta kalli wancan kamar mara gaskiya, Junaid dai na tsaye ya jingina da bango a parlon yana kallon sama, duk dakiyarsa tashin hankalin dake tare da shi bai boyu ba, Ammi kam na xaune parlon bata cewa komai sai tagumi da tayi, Hajiya Zuwaira da kanwarta na gefen Ammi su ma, kowa dai ka gani a parlon hankalinsa a tashe yake sosai, cikin kuka kaka tace "Toh kai da ka hango motarta ta window me yasa baka fito da sauri ba Amadu, ko ofishin naku bashi da taga ne da ka yrda wnn abu ya faru? Kai ma fa sai Allah ya kamaka wllh" Abba dai bai bata amsa ba kansa na kasa, Kaka ta kara rushewa da wani kukan tace "Yau naga abinda ya isheni ni Patuu, gandareriyar mata haka ace mana an dauke ta a mota, ni dai wllh ban yarda ba baxan kuma yrda da wnn karyar ba, ta ya xata amince ta bisu kamar wata shashasha" a hankali Yakumbo tace "Kun dai tabbatar kun duba motar da kyau bbu Ashnaah" ita ma bbu wanda ya tanka ta a parlon, lkci daya ta rushe da matsanancin kuka ita ma tace "Bbu yanda Ashnaah bata yi xata bi ni gidan dubiya ba nace baxan je da ita ba, yau ga inda son gantalinta ya kai ta, ita yar uwar bbu ruwanta da biye biyen mutane wllh" Mumy ce ta shigo parlon da sallama a rikice bayan many interrogations tun farkon shigowarta layin domin kuwa tun daga farko har karshen layin sojoji ne da yan sanda har cikin compound din Mami, Mumy ta fashe da kuka sosai sai dai ba hawaye ta shigo parlon ta xauna ta saki salati tace "Ikon Allah ya fi da haka, ynxu abinda ya faru kenan ni Maryam, to Allah ya kubutar da Rahinah daga hannunsu alfarman annabi, Allah ka dubemu a sako ta cikin aminci, wnn duniya Ina xa ya da mu..." Yakumbo tace "Ae har da Ashnaah...." Wayar Junaid dake hannunsa ne ya fara ring duk aka juya ana kallonsa a parlon, Junaid na kallon Screen din wayar ganin bakon number ne ya daga ya sa handsfree, bbu ko sallama aka fara magana kamar haka "Anyi garkuwa da Mahaifiyarku ana kuma bukatar ransom na miliyan hamsin daga yanxu xuwa gobe da karfe sha biyu dot.... failure to comply xa ku tadda gawarta nan bakin layinku gobe da yamma, ur Mother's life or 50 million, more details to be pass to you later...." Kasa motsi Junaid yyi inda yake tsaye yana sauraron mutumin, kaka ta mike da sauri ta nufo Junaid cikin daga murya tana nuna wayar tace "Allah ya tsine maka, Allah yyi daidai da kai, don uwarka ajiya ka bamu.... shege kawai haihuwar rage jini haihuwar asara, ubanka ne ya bamu miliyan hamsin din ko uwarka, to wllh jikana soja ne sai yyi gunduwa gunduwa da rubabben namanka an jefa ma kifaye a ruwa, d'an Iska kawai munafuki....." Yakumbo na tuntube ta taso ita ma tana kunduma nata xagin tana cewa "Idan ka isa ka xo ni ka daukeni d'an kaza kazan ka, dangin uwa ko na uba xa mu baka miliyan hamsin, ko wiwi ka narka kafin ka kira..." Abba ya nufosu da sauri yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, meye haka ku ke yi fisabilillahi" Yakumbo tace "Allah ya tsine masu muka ce, me xasu mana da Allah bai mana ba, idan sun isa su fadi inda suke yanxun nan in tafi in samesu mana, mutane matsiyata marasu tsoron Allah kawai" Barin wajen junaid yyi don ba ta su yake ba maganganun wanda ya kirasa ne ke dawo masa, don takaici Abba bai sake tanka su ba suka fita parlon tare da Dr da Baffan junaid don sanar ma yan sanda kidnappers din sun kira, Heedayah dai tun bayan da taji abinda aka ce ma Junaid a waya ta kasa kwakkwaran motsi inda take xaune, tunani iri iri ne ke kai komo a xuciyarta, A hankali ta juya ta kalli Farida, lkci daya ta tashi da sauri ta wuce sama xuciyarta na bugawa tana shiga daki ta kulle kofa a hankali tace "Khaleel???" Wani ihu ta fasa da ya ja attention din mutanen dake parlor....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
*What is _funnying_ me is the way free readers are taking this book for head like gala, sun fi kowa xakewa fahh, ku ji da hakkin dari uku mana banda abin ku* 🤔
Kuka kawai Heedayah take ta kasa cewa komai duk da hayaniyar da kaka da Yakumbo ke mata suna tsaye a kanta, Farida dai na rakube gefe banda kuka bbu abinda take, DCP dake tsaye kusa da Baffan Junaid ya kwantar da murya yana kallon Heedayah yace "Xa ki gane gidan nasa na Abuja yanxu?" Heedayah ta girgixa masa kai kawai, yace "Da yaushe ya gaya maki su suka ta6a dauke ki?" Heedayah ta harari Farida amma taki cewa komai, DCP yace "Talk to me young lady, da yaushe ku ka yi xancen da shi?" K'in cewa komai Heedayah tayi still, Ammi ta sauke mata wani mari a fusace tace "Baxa ki bude baki kiyi ma mutane magana ba" Heedayah ta rufe fuskarta tana kuka sosai tace "Ni ba shi ne ya daukeni ba fahh" Mumy dake tsaye ita ma parlon tace "Haba Hajiya ai bin ta xa ayi a hankali, duka ba shine mafita ba a yanxu, idan aka lallabata duk sai ta buda mana abubuwan da Faridar ta fada yanxu" Abba na kallon Heedayah yace "Tashi xaune" Mikewa xaune tayi a hankali hawaye na sakkowa idonta, yace "Da yaushe ku ka yi magana da shi yace maki shi ya dauke ki years back" A hankali ta girgixa masa kai tace "Ni ba shine ya daukeni ba Abba" DCP yace "To wa ya dauke ki" Cikin rawar murya tace "Wasu mutane ne ba shi ba" Ya daure fuska yace "Amma yar uwarki ta ce kince mata shi ne ya ajiye ki gefen hanya bayan ya daukeki daga wajensu" Heedayah ta girgixa kai tace "She's not saying the truth, ni ba haka nace mata ba" cikin kuka Farida tace "Karya take sir, ce min tayi yace mata shi kidnaper ne" Heedayah ta jefa mata wani kallo tace "He is not!!! Ni bance maki haka ba" DCP ya xauna yana facing dinta da kyau yace "You are not saying the truth young lady, baki son a ceto Mum din ki ne??" Heedayah ta fashe da kuka sosai gaba daya she look confused, Farida tace "Sir she's lying, ya sanar mata shi kidnaper ne, da bakinta ta fada min haka wllh" Kuka sosai Farida take, Heedayah dai hawaye sai sakko mata yake taki cewa komai, DCP yace "Xaki xama suspect dinmu kenan, and we have no choice then to go with u to the station...." Abba yayi kasa da murya yace "She's only confused sir, a bata sometimes xata yi magana idan Allah ya yrda" Junaid dake xaune ya sauke ajiyar xuciya yace "Lkcn da aka kwantar da shi a asibitin Abuja, the phone call his frnd is always making is highly suspicious, bbu gaskiya a kiraye kirayen sa, and idan yyi noticing dina a waje baya sakewa yyi magana, tun a lkcn na fara xarginsa amma ban kawo wani abu a kan shi Khaleel din ba" Baffansa yace "Abokin barawo ai barawo ne" Junaid yace "Ban yi tunanin Mami xata sake da shi Khaleel din har nan Kaduna ba, I once told her wnn mutumin stranger ne bai kamata tana jawosa jiki haka ba tunda ba saninsa tayi ba, she don't know him but Mami didn't listen to me, Dinar ma tayi mata magana bata saurareta ba..." Kaka na Shessheka tace "Mu dai daga ita har Heedayar sun kai mu sun baro mu muna xaman xamanmu ana shirye shiryen tafiya Gwamnet house, yanxu gidan ubanwa xa a samo wani shegen dubu miliyan hamsin idan ba Heedayar xa a kai kasuwa ba, ko ubanta dake da mukamin gwamna ynxu bashi da dubu miliyan hamsin balle mu karere, ni ban ta6a ganin yaron ba da sai na gane barawo ne tun kan aje ko ina wllh" Cikin rawar murya Heedayah tace "Ba barawo bane" wani Marin Ammi ta kara sauke mata, Abba yace "Subhanallah kar ki sake Hajiya" DCP da Baffan Junaid ma duk suka yi ma Ammi magana, Yakumbo ta fashe da kuka tace "Idan nayi magana sai a dinga min kallon me ta6in hankali, ranan farko da na fara ganin mutumin nan sai da nace ban yarda da shi ba yyi kalan yan satan mutane, amma bbu wanda ya dau maganata da muhimmanci, to yau ga dai abinda na fada ya fito, yanxu ya xa muyi fisabilillahi ga yar yarinya ko abinci nasan bata ci ba har ynxu, wani kai rahotu gidan radio da talabijin da gidan yan sanda duk ba shi bane wllh, fatana su fito cikin aminci, Ashnaah bata minti ashirin bata sha yagwat ba, to uban wa xai bata a can, Amadi daga komawarsa kujeransa yau sai yaji wnn mummunan labari mai cike da tashin hankali, don ma gwamnan kaduna bai bar maganar a haka ba shi ma yana bakin kokarinsa, ai wllh kashin yan kinnafas din nan ya bushe, xa su san har da 'yar gwamna suka dauke, don nasan da sun san yar gwamna ce Ashnaah baxa suyi gigin ta6a ta ba, dama an hada da Heedayar an tafi wllh da hankalina bai tashi haka ba tunda ita sun saba dauketa dama, ynxu banda xuciyar musulunci kina tunanin Junaidu xai yarda ya aureki bayan kwamushe uwarsa da aka yi ta dalilin ki, don ubanki gwamna ne ai ba ke bace gwamnan da xaki ja ma mata fitina tana xaman xaman ta..." Mumy sai da taji gabanta yace rasss jin abinda Yakumbo tace kan Junaid sai ya fasa auren Heedayah, Ammi dai ko kallon Yakumbo bata yi ba, Abba na rike da wayar Junaid yana ta kiran layin da aka kira da shi amma a kashe, Dr ya sauke ajiyar xuciya yace "Xa su kira Barrister, we have to calm down" Oga Arne na xaune parlor kan kujerarsa ya gama zuke zukensa Salim ya mika masa wayar da aka yi amfani da shi wajen kiran Junaid daxu, canxa layi yyi ya kunna wayar ya sake dialing Number Junaid, yana fara ringing Abba ya daga daya bangaren ganin bakon layi, Arne yace "Na kira in sanar maku inda xa ku kai mana kudin ku ajiye...." Abba yace "Yallabai ba mu da miliyan hamsin ynxu haka, ku fadi abinda xa mu iya baku domin Allah" Arne yace "Motar hawanta kadai ma xai yi miliyan 12, kada ku raina mana hankali, da alamar kun gaji da rayuwarta a doron kasa, xuwa karfe sha biyu gobe sae dai a dinga wani labarin ba wnn ba" Abba yace "Ka saurareni" katse wayar Arne yyi ya kashe gaba daya ya jefa ma Salim, Khaleel dake tsaye for almost an hour jikin pillar din dinning area din parlon ya rasa me ke masa ddi ya daga jajayen idanuwansa yana kallon Arne, wani dariya Arne yyi, Khaleel ya karaso cikin parlon yana dubansa sosai yace "A janye maganar kudin fansar ni xan baku...." Arne yace "Kana da wani alaka da ita ne da xaka bada kudin fansan?" Khaleel yace "Xan bada saboda a ta dalilina ku ka dauketa, snn they can't afford that amount" Arne ya mike yace "Naga alama after all this baxa ka rabu da mutanen nan ba, I think the best thing is just to send her to her early grave snn mu bi duk wani nata mu kashe, hakan kadai xai sa hankalin ka ya dawo jikin ka, amsan kudin fansa da 6ata maka suna a wajensu duk ba shi bane, xaka iya yin komai don ganin ka koma garesu, I mean xaka yi brain washing dinsu su kuma su kara amsar ka, kasheta shine kadai mafita a yanxu....." Khaleel da xuciyarsa yyi masa nauyi ya duka nan kasa da kyar yace "Kada ka kasheta Oga, don't forget she is a barrister idan nace xan koma gun daughter dinta xata yi exposing dina a idon duniya, xata tona min asiri, Kar ka manta bbu uwa ta gari da xata so tarayyar 'yar ta da hoodlum, ni kuma hoodlum ne, don haka kun riga da kun rabani da su don't go further then this plss, kar ku kasheta...." Arne dake ta sauraronsa yace "Toh idan ka kuskura ka sake cewa xaka bada kudin fansa sai na aika wnn yar yarinyar dake tare da ita lahira" Khaleel ya sauke kansa kasa hawaye na sauka idonsa bai ce komai ba, Arne ya koma ya xauna yana huci, Khaleel ya daga kai bayan few seconds yana kallonsa da kyar yace "To a taimaka a basu wani abun su ci ko su sha...." Arne ya mike yana masa wani kallo yace "You cannot break our rule all of a sudden Brainiac...." Mikewa Khaleel yyi a hankali ya koma inda yake tsaye ya jingina da pillar din ya runtse idonsa. Karfe sha biyu na dare Arne ya sake kiran Abba, nan Abba ya nemi alfarman su bar kudin miliyan talatin, da kyar da kyar Arne ya amince bayan cin mutunci iri iri a waya snn ya bukaci Motorcycle guda biyu sababbi dal a hada da kudin, nan ya sanar masu inda xa su tafi su ajiye masu kudin da safe. Washegari da sassafe Junaid ya tafi tare da Abba da Baffansa sai DCP a cikin motar Abba kai kudin inda Arne yace su kai a wani kauye cikin garin kano, wata motar kaya ce a bayansu dauke da Motorcycle guda biyu, a cikin motar motorcycle din kuma Yan sanda ne gudu hudu duk sanye da mofti, banda motar dake bayan motar Motorcycle din dake cike da sojoji, wayar Junaid dake hannun Abba ne ya fara ring ganin sabon Number ya daga ya sa handsfree, muryar Manga ne ya cika motar yace "Kai ku koma da kudin ku, snn karfe hudu na yamma ku duba can karshen layin gidanku xa mu ajiye maku gawarsu a can, sbda raini xaku kawo kudi sai kun yi xuga har da motoci uku, mu xa ayi ma wasa da hankali, mu xa a raina ma wayo, to wllh wllh kasheta xa mu yi idan mutum daya baxai taho da kudin ba" DCP sai kalle kallen hanya yake don ko Zaria basu karasa ba kuma motoci dai dai ne a hanyar ke tafiya, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujeran motar hankalinsa a tashe, Parking Abba ya samu gefe yyi sauran motocin bayansa ma duk suka tsaya ganin haka, DCP yace "Mu je kawai Barrister kyale yan Iska suna biye da mu ne...." Baffan Junaid yace "Aa kamar dai yanda yace Sbda lafiyar Rahinah da yarinyar wajenta mutum daya kawai ya kai kudin yallabai, further investigations should follow forth, yanxu dai the life of Rahinah and the little girl matters first, ba imani ne da su ba xa su iya aikata abinda suke fada" Abba yace "Haka ne, ni xan tafi in kai masu kudin, kamar yanda Alhaji Imran ya