Showing 174001 words to 177000 words out of 275313 words
Chapter 59 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
ta leka cikin motar tana kallon Heedayah, Dafa ta Alhaji Ahmad yyi xai janyeta daga motar ta fixge hannunta da sauri, ta fi minti daya tana kallon Heedayah da idanuwanta kamar xa su fito, can ta xaga daya side din motar da sauri har tana neman faduwa, da mamaki ta sa sojoji da Zayyad da suke tsaye wajen ke kallonta, ta bude motar tana sake kallon Heedayah kirjinta na Heaving, har wani rawa hannunta yake ta kamo hannun Heedayah na dama ta daga rigar Abayarta tana duba hannun, ta kara xaro ido sosai snn ta juya wuyar Heedayah nan ma ta ga black dot din da take son gani, wani kara me karfi tayi da ya farkar da Heedayah daga nan kuma ta sulale wajen, Heedayah ta kara lumshe idonta sbda har sannan maganin bai saketa ba nan ta kuma komawa duniyar bacci, da sauri Mai gidan ya xaga xuwa inda matarsa ta fadi sojojin ma duk suka bi sa da Mai gadi, Zayyad dai was extra confuse, ga wayarsa dake ta vibrate a aljihunsa ya san kuma Khaleel ne ke kiransa, Mum Islam da ta ji karan uwargidan nata ta fito da sauri daga bangarenta, Tuni Mai gadi kuma ya tafi dauko ruwa daga dakinsa da gudu, Daya sojan sai fifita yake ma Madam din Mai gidan nasu da hularsa, Alhaji Ahmad dai ya dago matar tasa yana kiranta amma ta suma, a rikice mum Islam tace "Abiey lafiya?? what happened, jikin nata ne ya tashi?" Ta amshe ta hannunsa ita ma tana mata fiffita da gefen dankwalinta tace "Asibiti xa mu tafi yanxu" ganin hawaye fuskan mijin nasu ya sa Mum Islam tayi still tana kallonsa, a hankali tace "Subhanallah is everything alright Abiey, wani abu ya faru ne ta fadi" Daukar matar tasa kawai yyi yana kallon Zayyad yace "Bring the girl in" daga haka ya wuce ciki yana rike da wife din tasa, duk sai mum Islam ta ji ba ddi tayi jigum tana bin su da kallo bata mike daga durkushen da take ba, Zayyad ya fiddo Heedayah daga cikin motar, da ido Mum Islam ta bi Heedayah da kallo tace "Wacece wnn kuma?" Sai kuma ta wani xaro ido ganin kamar da Heedayah ke yi da co wife dinta, lkci daya ta mike ita ma jikinta ya dau tsuma tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Ta furta haka ya fi a kirga, sai kuma ta bi bayan Zayyad da yabi bayan Mai gidan nasu da sauri, Mai gadin ya girgixa kai shi ma dai har da hawayensa yana kallon sojojin that all look confused yace "Sai gashi har gida an dawo mata da 'yar ta da ta bace yau shekara kusan biyar kenan, bbu tantama wnn yarinyar 'yar uwar gidansa ce" Zayyad ya kwantar da Heedayah nan tsakiyar lallausan carpet dake parlon, Alhaji Ahmad kuma ya kwantar da matarsa saman kujera wanda a nan take ta bude idonta, ta mike xaune weakly, da kyar ta fashe masa da kuka tana rike da hannunsa tace "Wllh Heedayah na gani Ahmad, wllh Heedayah ce, daughter na ce, tana Ina yanxu? Ina ku ka bar ta" Alhaji Ahmad ya koma gefenta yanda xata ga Heedayah dake kwance parlon, Kukan da Mum Islam take kai kace ta ta6a ganin Heedayah ko ta ta6a saninta, Kuma har xuciyarta take farin cikin bayyanar 'yar kishiyar tata bayan an fidda rai da dadewa, Kuka sosai Mahaifiyar Heedayah take tace "Ahmad idan mafarki ne wnn Allah ubangiji kada ya bani ikon farkawa, idan na farka naga mafarki nake nasan kilan karshen rayuwata ne ya xo coz I won't be able to stand it, let it not be a dream plsss, baxan iya ci gaba da rayuwa ba idan na farka naga mafarki ne" Mum Islam ta durkusa kusa da ita ta rikota tace "You are not Dreaming Mum twins.... We all are not Dreaming, Heedayah ce ba mafarki bane" Zayyad was so emotional at that time, ga confusion da ya dabaibayesa ta ko ina, but Khaleel yace masa a jiya ya dauketa daga gida, then why are they acting kamar sun yi shekara da shekaru rabonsu da ita, and wnn ai shine Mutumin da suka so kidnapping shekaranjiya, shine Alhaji Ahmad dake neman takarar gwamna how is this girl his daughter..... Mahaifiyar Heedayah ta rungume kishiyartata tana kuka sosai tana cewa bata son farkawa daga wnn mafarkin da take yi don tasan ba gaskiya bane, she is just dreaming, meeting with her daughter can't be just like a film to her. Khaleel ya kira Zayyad ya fi a kirga no response, hankalinsa ya tashi ba kadan ba, ya ma rasa tunanin da xai yi, gidan ne bai kai ta ba deceiving dinsa yyi duk da yasan Zayyad just can't do that, ko kuma ya kai ta aka kamasa, he don't know which to keep in mind, he don't know which to imagine, gashi ya ki komawa gida duk da ciwon da yake ji a xuciyarsa yana dai ta xaune inda suka yi xa su hadu idan Zayyad ya ajiyeta a address din da ya basa, ganin this is almost an hour hakurin Khaleel ya kare gaba daya, da kafa ya koma har layin, sai dai he is really not fine, at anytime he can fall sick ya sani, tafiyar ma daurewa kawai yake yi, yana isowa dai dai gate din gidan Deenar ya tsaya thinking of what next to do, gaba daya bbu alamar motar Zayyad a layin sai dai ga wata bakar mota a dai dai kofar gidan Dinar din, ya sake ciro wayarsa ya kira layin Zayyad for the countless time no answer, har ya kai hannu xai buga gate din dai dai nan aka bude, At first baya Khaleel ya koma da sauri ba tare da ya bari ya ga ko waye ba, bayan few seconds ya dago kansa ya ga ana pointing dinsa da bindiga, kallon Shuraim kawai Khaleel ke yi, da mamaki Abba ya kalli Shuraim yace "Hey, What's that u are doing Shuraim, I told u bana son kana bi na da bindiga, meye hakan...." Asp na Yan sanda dake wajen shi ma don duk tare suka fito Calmly yace "Drop that Shuraim, sure everybody is a suspect now, but...." Shuraim yyi wani murmushi yana kallon Khaleel da kyau yace "Shine saurayin da ya tafi da ita, he is the main suspect" yana fadin haka ya isa dai dai gaban Khaleel ya mayar da bindigan aljihunsa yana kallonsa fiercely nan take yyi masa naushi har biyu a ciki, lkci daya idanuwansa suka sauya kamanninsu just as the soldier he is yace "Ina ka kai Heedayah???" Junaid was just still a bakin gate din yana kallon Khaleel, Asp ya kwace Khaleel daga damkar da Shuraim yyi masa, da ido Khaleel ya bi Shuraim da kallo ko kiftawa bbu, Asp ya xaro handcuff din aljihunsa yana kallon Khaleel yace "You are under arrest"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Abba ya dafa Asp a hankali yace "Sir, isn't it good mu fara jin abinda ke tafe da shi tukun..." Asp ya girgixa kai strictly yace "That will be at the station not here, a suspect??? Noo" Handcuffing din hannun Khaleel dake ta kallon Shuraim ta gefen ido yyi in both hands, yana pointing dinsa da pistol din hannunsa Incase he should make any attempt of wanting to escape, ba musu Khaleel ya nufi motar da Asp din ke nuna masa yana biye da shi bayansa, nan yyi instructing din Shuraim ya biyo su, Khaleel ya sake kallon Shuraim kafin ya shiga motar da Asp ya bude masa, kawai he just don't want to escape ne banda haka pistol din Asp bai bashi tsoro ba, minti nawa ne xai yi guduwan sa kuma bullet dinsu baxai ta6a shi ba, but he can't just run without knowing if Heedayah is home or not, ynxu bai san ko Zayyad ya kawota gidan ko bai kawota ba, Junaid dai har sannan yana tsaye bakin gate tare da Abba, Abba ya dafasa yace "Let me go with them, Kai kuma ku taho station din tare da Barrister yanxu...." Junaid ya gyada masa kai snn ya juya ya koma cikin gidan. Khaleel na xaune yana facing wani d'an sanda dake masa tambayoyi yana rubutu a report book dinsu, su kadai ne xaune wajen, Shuraim na daga bakin kofa a tsaye looking directly at Khaleel dake magana calmly without any fear, he felt like shooting Khaleel ko xai ji saukin abinda xuciyarsa ke yi masa, bai ta6a jin he wants to use his gun on someone ba irin Khaleel, Mami dai na xaune ita ma a sanyaye tana kallon Khaleel, gaba daya ta dawo kamar warce ta tashi ciwo sbda damuwa, wnn dalilin yasa Abba bai bata fault ko kadan ba duk da without knowledge dinsa Heedayah ta taho Abuja which isn't right but he never blamed her even for a second, Abban ma dai da Junaid na xaune wajen, sai Mijin Dinar da ya dawo a ranan shi ma yana gun a xaune, Dpo na xaune shima yana ta rubuce rubucensa shi ma a gurin, police officer din na kallon Khaleel yace "Bayan ka tafi da ita sai aka yi yaya?" Khaleel yace "A jiyan nace xan dawo da ita gida tace baxata dawo ba..." Police officer din yace "A daren still?" Khaleel yace "Eh" Police officern na gyada kai bayan ya gama rubutu yace "To sai aka yi yaya?" A takaice Khaleel yace "Sai na wuce da ita gidana" Hawaye ya shiga sakkowa Mami uncontrollably, Shuraim ya dauke kansa daga kallon Khaleel jin wani abu da ya tokaresa a kirji, Abba dai ya sauke kansa kasa, Junaid ya shafa kansa ya nemi waje ya xauna daga tsayen da yyi a wajen, Police officern yace "A gidan naka ta kwana kenan?" Khaleel yace "Ehh" police officern yace "Go on, sai aka yi yaya" Khaleel yace "Da safe after breakfast nace xan mayar da ita gida, tace min she isn't going back home, I insisted and she ran away without me knowing" Police officern yace "She ran away from ur house?" Khaleel yace "Yes, but after 4 hours ta dawo gidan nawa, bana gidan ma lkcn da koma coz I was looking for her from the moment I noticed ta bar gidan, na dawo da yamma na ganta kwance parlor tana bacci, I have to make plans with my frnd kafin in basa ita ya mayar da ita gidan da na daukota" Dpo ya daga kai yana kallonsa yace "Wani plan kenan?" Khaleel yace "Na sa mata pill din bacci a lemo, bayan tayi bacci sai muka tafi da ita da abokina na nuna masa layin, na kuma gaya masa house number din snn na sauka motar nace ya karasa da ita" Dpo yace "Me yasa kai baka kai ta ba?" Khaleel yace "Because I remain a suspect a gidan, duk da I didn't take her to my house intentionally, na tambayeta ko anyi mata wani abu a gidan ne da tace she isn't going back, tace min nothing, she only want to stay with me" Kallonsa kowa na wajen yake yi, Mami dai sai kuka take don tasan ba training din da tayi ma Heedayah bane, something might be wrong somewhere" Dpo din yace "Toh abokinka bai kai ta gidan ba, and now tell us more about him, and where he stays...." Khaleel yace "I've been calling him but no response, shine ma yasa na tafi gidan to check if she is home..." Dpo din yace "Ya sunan frnd din naka?" Shiru Khaleel yyi, Dpo ya masa wani kallo yace "You Answer me...." Khaleel yyi kasa da idanuwansa yace "Zayyad" Dpo yace "Full name?" Khaleel yace "Zayyad Idris" Dpo yace "A ina yake xaune" Khaleel ya shafa kansa bai ce komai ba, dai dai nan wayarsa ya fara ring a pocket dinsa, xai ciro officern dake facing dinsa ya dakatar da shi ya mike ya ciro wayar da kansa, ya kalli screen din snn ya nuna ma Khaleel yace "Waye yake kiran ka?" Khaleel yace "Zayyad, shine ke kiran" Officer din ya daga ya sa handsfree snn ya mika ma Khaleel, lkci daya Khaleel ya ji gabansa ya fadi ganin handsfree d'an sandan ya sa wayar, daga Mami, Abba, Junaid da mijin Dinar duk kallon Khaleel suke, don Shuraim tun da ya fita bai sake dawowa ba, Daga daya bangaren Zayyad yace "Tell me Brainiac wacece wnn yarinyar da ka bani kace in mayar gida, for how long take wajen ka??" Khaleel yace "Why were you not picking my call?" Zayyad yace "No tell me yaushe ka fara rayuwa da yarinyar, how long??? coz ni na kawota gidan da kace and ban gane drama din da mutanen gidan suka yi displaying ba after seeing her, shekaranku nawa tare da yarinyar ni ban sani ba" Khaleel yace "Wani gidan ka kai ta??" Zayyad yace "Gidan da kace mana, I am even still at the house now, her father ya ki bari in tafi, it seems the girl have been away from home for long faaa" Gaba daya occupant din office din kallon wayar Khaleel suke listening to what Zayyad was saying, Khaleel yace "Are you sure layin da muka tsaya ka shiga?" Zayyad yace "Haba, shine wllh, and you know what Khaleel????" Khaleel yyi shiru, Zayyad yyi kasa da murya yace "Gidan Alhaji Ahmad ne, shine Mahaifin yarinyar, ka gane wani Alhaji Ahmad din?" Kittt Khaleel ya katse wayar, Officern dake kallonsa yace "Hey, Why did u cut the call??" Khaleel yace "Layin xa mu je da yace ya kai ta, sai a dubata a nan" daga Mami har Abba kallonsa suke keenly, Abba yace "But y did you end the conversation that way, when he is talking?" Khaleel ya kallesa bai ce komai ba, Abba ya kalli Dpo dake office din yace "I think ya kamata su gama maganan, he should call him back" officern na kallon Khaleel yace "sake kiransa" Mami ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Da dai mu fara xuwa mu ga halin da yarinyata ke ciki don Allah dpo, Ko xan samu nutsuwa" Dpo yace "Their conversation will take just few minutes Madam kiyi hakuri, xa mu je can din yanxu, ka sake kiransa" Dpo ya fadi haka yana kallon Khaleel, Khaleel ya sauke idanuwansa kan wayarsa ya sake dialing Number Zayyad, Zayyad na dagawa Khaleel yace "Be brave Zayyad.... where are you at now?" Wani kallo Dpo ya jefa ma Khaleel, ya tashi da kansa ya katse wayar yace "Maganar da yake maka daxu xaka ce ya ci gaba.... Keep on to that conversation" Khaleel yace "Ohhh, ohk" Daga haka ya sake kiran Zayyad, Zayyad na dagawa yace "Yauwa, Brave you, kace gidan wa kake?" Zayyad ya d'an yi shiru snn yace "Gidan Baban yarinyar..." Khaleel yace "Maintain... So waye baban yarinyar?" Zayyad yace "Uhn sure..., I just learnt that Alhaji Ahmad ne, wanda ke neman takarar gwamna na jihar kano, so I was surprise, ashe babanta babba ne... That's all abinda xan fada maka, sai kuma ince why did she decide to leave home" murmushi kawai Abba yyi, Mami dai sai kallon Khaleel take, police officer ya katse wayar, Dpo ya mike yace "Xa ku tafi can anguwar tare da Asp Ina jin" motar yan sanda daya suka shiga, wanda Khaleel ne ciki da two police men, sai Shuraim dake motar shi ma, Mami da Junaid suka shiga mota daya, Abba da Mijin Dinar su ma mota daya suka hau suka bar police station din. Officer daya ya sa Khaleel ya sake kiran Zayyad ya tambayesa gida na nawa ne, Zayyad yace "Gida na biyar...." dai dai gidan Alhaji Ahmad duk motocin suka tsaya suka sakko, mijin Dinar yace "Wnn ai gidan makocina ne Honorable...." Asp ya bubbuga gate din, Yan sanda biyu na tsaye tare da khaleel, ba a dau lkci ba aka bude gate din, Dpo ya gaisa da sojan da ya bude gate din Snn ya nuna masa ID dinsa yace "Muna son ganin me gidan nan ne...." Sojan yace "Alright, bari ayi alerting dinsa" kulle gate din yyi ya koma, Jikin flowers Shuraim ya tsaya fuskarsa bbu walwala, ya ki yrda ma ya kalli direction din Khaleel kar xuciyarsa yyi explode, gaba daya he is just restless da bayanin da Khaleel yyi a station, su Mami da Abba duk suna tsaye bakin gate din, ita dai Mami fatan ta a ga daughter dinta kuma ko kwana ta dau ma kanta alkawarin baxa su yi a Abuja ba xata dauketa su koma gida, da ta tuna wai gidan namiji ta kwana jiya sai taji hawaye na mata xarya, bayan wani lkci Alhaji Ahmad ya bude gate din da kansa, da kallo ya bi dukansu snn suka gaisa da Asp dake kallonsa shi ma, Asp na murmushi yace "Sorry for the disturbance Honorable, amma daxu an shigo da yarinya gidan nan kuwa.... They mistook here for the girls home" Alhaji Ahmad ya d'an yi shiru duk yana kallonsu, can ya gyada kai cikin sanyi yace "Kwarai an kawo yarinya gidan nan daxu" Asp yace "Fatan tana nan gidan har yanxu?" Alhaji Ahmad yace "Sure, tana nan" Asp yace "To Alhmdllh, xa mu shiga mu tafi da ita ynxu" Mami bata san lkcn da ta sauke wani bayyanannen ajiyar xuciya ba, taji wani farin ciki ya lullubeta, Alhaji Ahmad dai bai ce komai ba ya basu hanya duk suka shiga gidan, k'in shiga Shuraim yyi ya nufi titi walking like the soldier he is, Khaleel dai sai kallon Alhaji Ahmad yake bayan sun shiga gidan, har suka isa building din Uwar gidan Alhaji Ahmad, Har sannan Heedayah na kwance parlon still sleeping heavily, Zayyad kuma na xaune saman kujera, Mum Islam na kusa da Heedayah da family Doctor dinsu da ya gama dubata, Mahaifiyar Heedayah kuma na xaune ta takure waje daya sai kallon Heedayah take ita a dole she is dreaming and can wake up anytime, Mami ta karasa gun