Showing 135001 words to 138000 words out of 275313 words
Chapter 46 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
d'an buda ido coz basu ma san yana gidan ba, ta karasa kitchen ta rufe a hankali sannan ta fara aikin da xata yi. Bude kofar kitchen din aka Heedayah tayi still, sai kuma ta juyo tana kallonsa, ya jingina da kofa ya rungume hannunsa yana kallonta da lumsassun idonsa, ta dauke kai tana ci gaba da wanke wanken da take tace "Ina kwana Yaya" Jin bai amsa ba ta juya tana kallonsa, calmly yace "Lafiya lau, yau ma xa ku fita kenan?" Ta gyada masa kai tace "Xa mu je gidansu ya Sudais" yace "Me ake yi yau din?" Tace "Mothers day" shiru yyi yana kallonta, can yace "Why not stay back home ke da Farida, ai ba sai kun je ba, mother's day ai ba ladies day bane, ko kun fi son ayi ta ganinku..." Heedayah tace "Ae Mami ce tace mu je, tare da ita ma xa mu je" Bai kuma cewa komai ba ya juya ya bar bakin kofar, Heedayah ta turo baki ta ci gaba da wanke wankenta.
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Bayan Azahar Mami ta gama shirin xuwa can gidan biki, tana xaune parlor tana jiransu farida dake sama suna shiryawa, sanin they need time to prepare ya sa bata takura su ba take xaune parlor patiently waiting for them, Farida ce kadai ke kwalliya ita Heedayah ta gama saka kayanta tunda ba kwalliya take ba dama, ta dai shafa powder da man baki, atamfa ce iri daya yau ma suka sa da Farida, sosai kayan yyi masu kyau ba kadan ba, tun safe Farida taki wani kulata ko magana a takaice take amsa mata, ita ma Heedayah bata sake ce mata komai ba har ynxu da suke shiryawa, tuni Heedayah ta maida wayar Khaleel jakar da xa ta fita da shi tana rungume da abarta, yau ma da safe sai da ta ga miss call dinsa hakan yasa ma ta cire wayar a total silent ta bar sa a vibration but very low with the help of side buttons din, vibration din wayar ta ji yanxu ma, da sauri ta kalli Farida dake ta kwalliyarta, can dai ta mike a hankali ta nufi bandaki ta shiga bandakin ta kulle, fiddo wayar tayi tana kallon screen din sannan ta daga ta kai kunne kafin ya katse, yyi mata sallama, murya can kasa ta amsa, sai da ya d'an yi shiru sannan yace "Me yasa baki daukan waya idan an kira ki?" Tace "Saboda ba yawo nake da wayar ba, kuma gidanmu bama rike waya, I am not allowed to do so" yace "Gidanku?" Tace "Ehh" yace "Ohk... I tot ba a gidanku kike ba" Shiru tayi tana naxarin abinda yace mata, sai kuma tace "How did you know that?" Yace "I only guessed, and lkcn da na san ki kamar.... you were unsighted...." kamar me counting words din yyi maganan, gaban Heedayah ya dinga faduwa tana sauraronsa, can ta marairaice tace "Plss a ina ka san ni ka gaya min don Allah, I can't remember where I knew ur voice...only knew it sounds familiar" yyi murmushi da take iya ji, sannan yace "Na sanki Heedayah" Kamar xata yi kuka tace "To a ina?" Yyi kasa da murya yace "Wani waje mana" Turo baki tayi tace "Bana so" yace "Toh gaya min inda xa mu hadu sai in gaya maki inda na sanki" ta d'an yi shiru sannan tace "Mami will punish me, ba a barin mu fito..." Yace "Yes... not at home...." Tace "To a ina?" Yace "Anywhere, duk inda kike so you tell me" ta buda ido sosai tace "Nace maka ba a barin mu fita ai a gida" yace "To ranan da na ganku Ina xa ku? And who was the lady you were together with" Tace "Mun je supermarket ne, she is my sister" Yace "A gidansu dai kike" ta d'an yi masa shiru sannan tace "Gidanmu ne nima" yace "Noo ba gidanku bane wllh" Cikin sanyin murya tace "To a ina gidanmu yake?" Bai ce komai ba haka yasa tace "Ka gaya min" yace "Wani makaranta kike?" Tace "Nigerian Turkish" yace "Why are you not in schl now?" Tace "Hutu" ya d'an yi shiru sannan yace "So bbu ranan da xa ki samu ki fito??" Tace "Ehh, but xa mu je biki yanxu" Kofa ta ji an bude a can daki da sauri tace "I need to hang up now...." Yace "Wait... to yaushe xa mu sake magana...." tace "Anjima" daga haka ta katse wayar ta saka shi jaka xuciyarta na bugawa, Mami ce ta shigo dakin tana kallon Farida dake makale bakin kofar bandaki wanda tana ganin Mamin ta bar wajen da sauri tana dube dube kamar tana neman wani abu a kasa, Mami tace "Meye hakan?" Farida tace "Aa barima na nake nema ya fadi ban san inda ya shiga ba" Mami tace "Ina Heedayar?" Farida tace "Ta shiga bandaki ne, ita nake jiran ta fito" Mami tace "To ni xan yi wucewata tunda abun naku walakanci ne idan kun gama sai ku samu adaidaita ya kawo ku, for almost an hour ina jiranku kamar masu shirin jaraba" Farida tace "Aa Mami wllh ni na gama, ita nake jira" Mami bata kuma ce mata komai ba ta nufi kofa ta fita dakin, Farida ta sake kallon kofar bandakin sannan ta dau jakarta ta bi bayan Mami, a hankali Heedayah ta bude kofar bandakin ta fito tana kalle kalle, ganin bbu kowa dakin ta fita xuwa downstairs da sauri. Back seat farida ta xauna, hakan ya sa ta bude gaba ta shiga, Mai gadi ya bude gate suka fita gidan. Sosai jama'ah suka cika gidan biki ana ta shagalulluka a katon tsakar gidan, lallai taron ya amsa sunansa na Mother's day, don iyaye ne mata sun yi shiga ta kece raini, can Heedayah ta hango kaka cikin jama'ah yanda ta kankance ido ya isa kasan cewar ba maganar arxiki take masu ba a can don wasu sai tabe baki suke, Heedayah ta bi bayan Mami da Farida da suka shiga parlon, Hajiya Hauwa na welcoming dinsu, kiris ya rage ta ci karo da Mumy da ta mike xata bar parlon cike da isa don bai ma Mami access din ganin kwalliyarta da gwalagwalanta da kyau, Heedayah ta koma baya tayi kasa da kai ta bata hanya tace "Ina yini" Ko kallonta Mumy bata yi ba ta wani daure fuska ta fita parlon Heedayah ta shiga a sanyaye, da fara'a Step mum din Sudais ta amsa gaisuwan Farida da Heedayah sannan tace "Ga can Sudais xai ajiye su Zainab saloon ku bi su ku ma kuyi gyaran gashi" da sauri Heedayah tace "Aa gashin mu a gyara yake ai" Mami ta juya tana kallonta, Farida tace "Toh bari mu je Mama" Hajiya Hauwa tace "Su Zainab din na daki ku tafi ku samesu sai ku wuce tare" Farida ta tafi inda Hajiya Hauwa ke nuna mata, Heedayah ta turo baki ta bi bayanta ranta bai so ba, Zainab 'yar Hajiya Hauwa ce, sai Jamila daya daga amaren, Daya Amaryar Safiyya dakinsu daya da Sudais sai Nafisa da Aisha, Zainab da Rabi'ah da Khadijah kadai xa su tafi saloon din don sauran sun je jiya tare da amaren, sae ynxu da Heedayah da Farida xa su bi su, Zainab na ganin su Heedayah tayi welcoming dinsu da fara'a tana masa sannu da xuwa, Aisha ma dai tayi masu sannu da xuwa sama sama, amma Nafisa tayi kamar bata gansu ba ballantana Rabi'ah da Khadijah, a haka dai har Sudais ya kira Zainab yace yana jiransu a waje, Zainab ta mike tana kallonsu Farida tace "Mu je yana jiranmu a waje" har ta fita ganin Rabi'ah da Khadijah basu fito ba ta dawo tace "Yana fa jiran mu a waje" Khadijah ta wani yatsine fuska tace "Ku je ku, anjima xa mu je wani saloon din" Zainab bata ce komai ba ta fita, a parlor Hajiya Hauwa tace "Ina sauran fa" Zainab tace "Wai baxa su ba" Mumy da shigowarta parlon kenan ta xo debar ma bakinta lemo tace "A kan me baxa su je ba??" Zainab tace "nima ban sani ba" da haka ta fita Farida da Heedayah na biye da ita, Mumy ta wuce sama fuskarta a tamke tana cewa "Bari in kira driver na ya xo ya kai su saloon din, ai ba dole dama su bi ku ba, ko wani saloon din ne sai ya kai su yanxu" Hajiya Hauwa dai bata ce komai ba balle Mami dake parlon. Zainab ta shiga front seat Heedayah da Farida suka shiga baya, Sudais ya amsa gaisuwarsu gaba daya yana kallonsu ta madubi yace "Yaushe ku ka xo?" Farida tace "Ba dadewa" yace "I see, ku ma xa ku yi gayun kenan" dariya kawai Farida tayi, ya kalli Heedayah da tayi shiru yace "Cutie kema gyaran gashin?" Murmushi tayi ta sauke idonta kasa tace "Uhn" yace "Toh idan kun dawo anjima sae a nuna min gashin in gani" Nan ma bata ce komai ba sai murmushi, sai da suka yi nisa Sudais ya d'an kalli Zainab yace "Wai su Rabi'ah sun fasa xuwa ne" Zainab tace "Ehh wai anjima xa su taho" yace "Ohk then" yana ajiye su saloon din ya ba Zainab kudin gyaran gashin nasu da kudin adaidaita da xai maida su gida sannan ya wuce. Sai kusan Magrib su Heedayah suka dawo gida, basu tadda Mami a gidan ba, Heedayah na kallon Farida da ta amshi gugan tiles din da kaka ke yi a dakinta tace "Toh mu wa xai kai mu gida?" Kaka ta juya da sauri tana kallonta tace "Wa xai kai ku gida kuma? Ba lafiya, Nan ba gida bane? To nice nan nace Rakiya tayi wucewarta kuna nan har bayan biki tunda ita baxa ta tsaya ba, idan ma ita faridar taga baxata xauna ba to ke kina nan, nan ne dolenki" Heedayah ta xauna saman kujera kaman xa ta yi kuka, Farida dai bata ce komai ba. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh taji vibration din wayarta dake kusa da ita, bin dakin tayi da kallo, Farida da Zainab ne xaune dakin suna hira, sai wata yar uwar Umma dake dakin tana waya. Heedayah ta saka jakar cikin hijab dinta cikin dubara ta mike ta ta shiga toilet, ciro wayar tayi ta dauka kafin ya katse, sallama yyi mata ta amsa yace "Kince anjima xa mu yi magana kuma nake ta kiranki baki dauka ba" ta wani turo baki tace "Toh ni ai bana nan mun fita, kuma the phone isn't ringing" Yace "Ina kika je?" Tace "Saloon" yace "Why didn't you tell me?" Tace "How will I tell you?" yace "Call me" tace "A rufe wayar yake, you didn't tell me the password" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "I remember, so where are you now?" Tace "Gidan yayan Abbanmu" yace "A ina?" Tace "Unguwar rimi" yace "Wani layi?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Toh ki tambaya" a hankali tace "Toh" yace "I will call back in few minutes" tace "Tell me the password" yace "Sai na xo...." daga haka ya katse wayar, fita tayi bandakin ta xauna gefen gado, Farida dai ta kalleta bata ce komai ba suna ci gaba da labarinsu da Zainab, Bayan kusan minti biyar Heedaya ta kwanta tana kallon Zainab tace "Ya ma sunan layin nan sis" Zainab ta kalleta tace "Wai anguwar nan?" Heedayah tace "Ehh" Zainab ta gaya mata sunan anguwar, Heedayah tace "Ohk" bata kuma cewa komai ba tana ta kwance, sai taji wayar na vibrate, mikewa tayi tace "Bari in je in amso abinci am hungry" daga haka ta fita, can bayan gidan ta xaga bayan ta fita, ta daga kiran having making sure that bbu kowa wajen, nan ta gaya masa sunan layin yace "Ohk I am on my way" komawa tayi cikin gidan bayan ta mayar da wayar jaka, ta ki komawa bangaren kaka ta xauna parlor duk da akwai mutane, wasu na yanke yanken kayan ganye, kowa dai da abinda yake yi, bayan kusan minti sha biyar sai ga kiransa, da sauri ta fita ta daga kiran, yace "I am outside" sosai ta ji gabanta ya fadi, a hankali tace "Toh amma idan aka gan ni fa?" Yace "Babu wanda xai gan ki, ki fito" A hankali ta katse wayar ta mayar cikin jakar dake cikin hijab din jikinta sannan ta nufi gate tana yi tana waige waige har ta isa gate din xata fita, tana dube duben inda xata gansa, karo suka kusa ci da Shuraim da xuwansa gidan kenan, Suna hada ido ta koma baya a tsorace tana xare ido, juyawa yyi yana bin layin da kallo as if wanting to figure out something, suka hada ido da Khaleel da yyi parking daga daya side din kafin a iso dai dai gate din gidan, Khaleel ya fiddo wayarsa ya fara danne danne ya kai kunne, magana ya fara yi a wayar yana driving a hankali, har ya iso dai dai saitin Shuraim sannan yace "Ohhh ba nan bane? But I am seeing no. 28 here, ohk sorry 38, but wait.... can you plss come out ka daina bani wahala??" Sai kuma ya ja tsaki yace "kasan ba karamin aiki na bane in koma gida ko" yana magana yana tuki slowly har ya wuce Shuraim, Heedayah dake xare ido cikin rawar murya tace "Inn... Innaa yini" ya hade rai sosai yace "Ina xa ki?" Bakinta na rawa tace "Ruwa xan siya...." Yana mata wani kallo yace "Bbu ruwa a duk gidan sai kin fito siya?" Kamar xata yi kuka ta gyada masa kai kamar kadangariya, yace "Go back inside now" juyawa tayi da sauri ta wuce ciki tana hade hanya, ya juya ya sake kallon motar ya gansa can tsaye 4 houses away, can wanda ke cikin motar ya sauka ya nufi me gadi dake xaune bakin gate din, sai kuma mai gadi ya bude masa gate ya shiga cikin gidan, Shuraim ya dauke kai ya shiga gida shi ma snn ya rufe gate din. Farida na balcony tana danne dannen wayar hannunta Heedayah ta wuceta sai a sannan ta bi ta da kallo, Shuraim ma ya wuce bata ce masa ba bai ce mata ba, mikewa tayi ta bi bayansu, Dakin kaka Heedayah ta shiga ta rakube can karshen gado har lkcn gabanta bai daina faduwa ba, kaka tace "Ga abinci ki diba ki ci, ni na rasa gane ko Rakiya bata baki abincin kirki ne, wnn sirancin haka ai yyi yawa kamar bafillatanar da shanu ya kare ma" Heedayah ta turo baki bata ce komai ba, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo, kaka ta dauke kai kamar bata gansa ba, dubu ashirin ya ciro aljihunsa ya mika mata yace "Abba yace a kawo maki" Kaka ta amsa ta kirga gaba daya sannan ta yashe kudin gefen gado tace "Ni dai na shiga uku, meye dubu ashirin kuma Allah na tuba, wnn ai baxai isa liki ba wllh, snn duk a ciki in ba bakina da suka xo kudin mota me yasa Amadu ke min haka ne ni" Shuraim dai sai kallon Heedayah ta gefen ido yake yi, don kai kana ganinta kasan bata da gaskiya sai wani kokarin boye jaka take a cikin Hijab nan kuwa vibrating wayar yake, Suna hada ido da shi ta daburce, can ta mike ta nufi kofa ta fita da sauri, kaka tace "Ni kawai a kira min Junaidu bani da kowa sai shi, shi daya xai fitar da ni kunyar likin nan da xan ma yara, da tsofaffin nan da suka xo min" Heedayah na fita dakin su Zainab ta wuce da sauri ta shige bandaki ta kulle, tunanin inda xata boye wayar jakarta take, ta fiddo wayar tana kalle kallen bandakin, window ta bude ta jefa wayar ta waje sannan ta fito bandakin.
_I want to alert those that didn't patronize the book Heedayah, pls and plss don girman Allah su rike sharhinsu su bar wa enda suka siya littafi su yi, baki siya littafi ba baxa ki xo kina gaya min abinda ya kamata inyi da abinda bae kamata inyi ba, littafin nan dai ba kyauta bane amma wasu a kyauta suke karanta shi comfortable hankali kwance, to su ji da wannan kawai ma mana_
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....
Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍
Zainab ta mike jin ana knocking din kofarsu ta bude, ganin Shuraim tsaye bakin kofar tace "Ina yini Ya Shuraim" Aisha da Nafisa duk suka kame kansu a dakin kuma bbu wanda ya kallesa cikinsu, cikin few seconds ya gama bin dakin da kallo snn ya amsa gaisuwar Zainab yace "Lafiya" Heedayah dai na kwance saman gado tayi backing din kofar gabanta sai faduwa yake, karasawa cikin dakin yyi cike da kasaita ya nufeta yace "Bani jakar ki" kamar jira take ta mike xaune da sauri ta dau jakar ta mika masa, ya amsa ya bude ciki, bbu komai sai kudi da awarwaro with different chocolate, tunda ta mika masa jakar bata yrda ta kallesa ba, xuciyarta kamar xai fito don tsoro, ya jefar da jakar saman gado ya juya ya fita, Zainab ta xauna gefen Heedayah tace "What is he looking for?" Heedayah tayi tagumi tace "Ohon masa" Zainab ta tabe baki bata ce komai ba ta