Showing 255001 words to 258000 words out of 275313 words

Chapter 86 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

aka kai ni dakina, kinga ke ai an maki gata sosai har sati hudu" Heedayah ta share hawayen idonta a hankali, Mom Islam tace "Ki kwantar da hankalin ki kin ji my daughter, ba dai kina son mijin ki ba" Heedayah ta gyada mata kai, sai kuma a hankali tace "Amma ni tsoronsa nake" Dariya sosai Mum Islam tayi tace "Tsoron me?" Heedayah dai bata ce komai ba, Mom Islam tace "Shi yasa jiya kika ki dadewa da kika fita wajensa?" Heedayah ta turo baki tace "Aa shine yace min yana jin bacci" Mom Islam tace "Ayya, ya koma Kadunan shi?" Heedayah ta gyada mata kai, Mom Islam tace "Allah sarki, ni dai nutsuwarsa na burgeni kuma naji dadi da ba a samu matsala shari'ar da aka yi ba, Allah ya dubesa da yake xaluntarsa aka yi" Heedayah dai bata ce komai ba, Mom Islam ta ci gaba da kwantar mata da hankali har suka gama tsifan ta hau sharce mata dogon gashin nata kafin ta wanke. Sai bayan awa kusan biyu Heedayah ta koma bangaren Amminta bayan Step mum dinta ta gama gyara mata gashinta, Amminta ta bi ta da wani kallo tace "Kumbure kumburen uban me kike?" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba komai" Ammi ta ci gaba da abinda take, juyawa Heedayah tayi ta fita ta koma bangarenta. Mumy ce xaune parlon Hajiya Sadiya hawaye na sauka idonta tace "Ni shkkn dai a tutar bbu na tashi wllh...." Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Hajiya Sadiya dai ta ma rasa abun cewa, cikin rawar Mumy tace "Dama nace asirin nan bai ci Shuraim ba ku ka ce ina na fito, Salima ta sa ina ta kashe kudi a Iska, ga dai yarinya yau an sa mata rana da d'an gidan Rahinah, kamar fa almara labarin ya xo min, ban ta6a kawowa hakan xai faru ba, kuma tunda na ji kullum sai Shuraim yaje government house na xata saboda ita yake xuwa ina ta murna sun shaku yanxu ashe ashe ba haka bane, Wai ina kwance Barrister ya shigo ya sanar min xa su kai kudi da safe...." wani sabon kuka ne ya kubce mata, a hankali Hajiya Sadiya tace "Shuraim yana da tsari duk ynda aka yi, tunda bake kadai Mutumin nan ya ma aiki ba, ni da mutumin ya min aiki kan surajo ba gashi yayi ba, ko sati ba ayi ba ya saki matar saki uku ya auri warce nake so....." Mumy na share hawayenta tace "Kuma haka ne wllh, yanda dai kika fada haka ne Shuraim na da tsari, kinsan Kakar ma ba wai barin su haka tayi ba" Hajiya Sadiya tace "Toh wata nawa aka saka ranan yanxu?" Da damuwa Mumy tace "Wata daya kacal Sadiya" Hajiya Sadiya ta bude baki tace "Toh sai dai in Heedayar xa a asirce tace ta fasa kawai ko?" Hawaye na taruwa idon Mumy tace "Ta yaya? Shi wnn mutumi sai yace a barbada a abinci ko abun sha, to ina xa mu ga wata Heedayah tana gidan iyayenta, Kadunan ma ko ta xo kwana biyu take yi ta koma, balle ma tunda aka sa mata rana ma shkkn ba lallai ta xo kwana kusa ba sai bayan bikin" Sadiya tace "Wai tsaya ba d'an fashin nan bane d'an Rahinar da aka sa mata rana da?" Mumy tace "Shine dai wllh, in gaya maki sun shiga sun fita sai da suka tabbatar sun wankesa tass, su kuma abokan huldarsa duk an masu daurin rai da rai a gidan yari haka naji, lkcn shari'ar kuwa ko baccin kirki Barrister baya yi, su kusan biyar suka hada kai aka wanke Mutumin nan me laifi kiri kiri gashi a bayyane, kuma wllh gagarumin d'an Kidnapping ne fa aka ce" Sadiya da ta saki baki tace "Ikon Allah, to ya aka yi da dukiyoyin jama'ah da ya tara da mutanen da ya kashe???" Mumy tace "A karyansu wai bai ta6a kisa ba, dukiyoyin jama'ah kuma an kai gidan Marayu, ke kiji daure ma karya...." Sadiya tace "Lallai yana da masu tsaya masa ne" Mumy tace "Da fa, ance kanin ubansa wani babba ne a Gombe, snn autarsu ubansa ma wani babba take aure a gomben, snn ga danginsu Junaid su ma kinsan an sansu, uwa uba ga gwamnan kano dake tunanin xai xama surkinsa, kinga kuwa ai ba karamin wanki xa ayi masa ba" Sadiya ta rike ha6a tace "Ikon Allah" Mumy tace "Ni dai mu koma abinda ya dameni, yanxu Sadiya ya xan yi??" Sadiya tace "Asiri kawai xa mu je ayi ma Heedayar idan ma magani ya bada wanda ake son ta ci sai ki wanke kafa ki tafi government house ai bbu wanda xai ce maki don me, bbu wanda xai koreki, da ba don mijinki ba da yanxu kilan bbu Heedayah a doron kasa, kina sauka kano sai Shuraim ya shigar da ke government house din kawai" A hankali Mumy tace "Toh hakan xa ayi, tunda da sauran lkci tashi mu tafi gun Mutumin Sadiya" Kallon Mumy kawai Abba ke yi har ta gama maganan da take sannan yace "Ki dai gaya min me xa ki je yi a kano Maryam" Tayi masa wani kallo tace "Me xanje yi kamar Yaya? Kana nufin karya nayi maka kenan ko me? Nace xanje gaida kaka kace min me xanje yi a kano" Abba yace "Sati me xuwa kaka xata dawo ba sai kin je ba, bbu inda xaki je" Mumy tace "Toh wllh wllh sai naje ko da gobe xata dawo kuwa" bata jira me xai ce ba ta fice daga dakinsa xata je hada kayanta ya bi ta da kallo keenly. A ranan da safe Heedayah na babban parlon Abbanta xata yi masa sallama, ya gama wayar da yake yana kallonta yace "Kwana nawa Ammin ki tace kiyi?" A hankali Heedayah tace "Biyu" Abba yace "Toh Allah ya kiyaye hanya, xa ku je tare da Shuraim...." Heedayah tace "Ammi ta gaya min" mikewa tayi ta fita daga parlon, step mum dinta ce ta rakota gun wata rantsantsiyar mota ta shiga baya ita kadai sai driver dake gaba, step mum dinta na kallonta a hankali tace "Ki kula da kanki kinji daughter?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Toh Aunty" Mom Islam ta daga mata hannu Heedayah ta daga mata ita ma, Kalle kallen wajen Mom islam ke yi tace "Toh ina Shuraim din" Heedayah ta bude hannu alamar bata sani ba, can Mom Islam ta hangosa cikin daya daga motar da xasu yi masu escort, Mom Islam na tsaye har motocin suka fara fita.....




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Basu yi awa daya suna tafiya ba motar da Heedayah ke ciki ya gangara daga tsakiyar motocin da yake yyi parking gefen titi, hakan yasa duk sauran motocin har da na gabansa suka yi parking, Heedayah ta bude motar ta sauka ta tafi gefen ciyayi ta durkusa, Shuraim ya sakko daga motar da yake ciki ya nufeta yana kallonta, sojojin ma duk suka sakko daga mota, lkci daya Heedayah ta mike da kyar tana kallonsa tace "Ya Shureen amai nake ji" Tsayawa yyi ya jingina da motar ya rungume hannunsa yace "Toh kiyi" ta koma ta durkusa sai kuma ta dago kamar xata yi kuka tace "Ya ki xuwa" gaba daya she's restless alamar aman na damunta, bai ankara ba sai gani yyi ta duka da sauri ta fara kwararo amai a kan ciyayi, ya tsaya yana kallonta, can ya bude motar ya fiddo bottle water dake ajiye kan kujera ya bude ruwan, sai da ta gama sannan ya karasa ya mika mata, ta amsa da kyar ta wanke fuskarta ta mike tana maida numfashi, ya bude mata motar yana kallonta, shiga tayi ta jinginar da kanta da kujera xai rufe motar a hankali tace "Don Allah ka shigo nan Ya Shureen, ni kadai ce" yace "In shigo in maki me?" Da damuwa tace "Ka xauna, kuma kace ma driver ya rage Ac din sanyi nake ji" Da kamar baxai shiga ba, sai kuma dai ya shiga motar ya rufe, sauran sojojin suka koma motarsu, Shuraim ya umarce driver da ya rage sanyin Ac, drivern yyi haka nan suka ci gaba da tafiya. Lumshe ido tayi daga haka bacci ya dauketa, sai da suka iso Zaria ta bude idonta a hankali, daga kai tayi ta kalli Shuraim dake danna wayarsa, ta kalli shoulder dinsa da ta daura kanta, gyara xamanta tayi tace "Ba mu kai ba?" Bai ce mata komai ba, ta karbi wayar hannunsa ya kalleta, tace "I am asking ko mun kai" yace "Ehh har mun juyo" Yana fadin haka ya kwace wayarsa, ta turo baki ta koma can nesa da shi ta xauna, d'an murmushi yyi ya ci gaba da abinda yake yi a wayarsa, bude handbag dinta dake hannunta tayi ta fiddo wayarta dake vibrate, ganin Khaleel ke kiranta sai da gabanta ya fadi, ta dai daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yyi sallama, ta amsa, yace "How are you?" Tace "I am fine" yace "Kun taso?" Tace "Ehh mun taso" yace "Okay, ya hanya?" Tace "Alhmdllh" Yace "Ke da waye?" Ta d'an kalli Shuraim snn tace "Ba kowa, ni da driver ne" Yace "Ohk, Allah ya kawo ku lafiya" A hankali tace "Ameen" snn ta katse wayar, satan kallon Shuraim tayi suka hada ido don shi ma kallo ta yyi, ta dauke kanta ta gyara xamanta, har suka shigo kd wajejen karfe sha biyu. A hankali Heedayah ta bude motar ta sauka bayan driver yyi parking compound din Mami, Farida ce ta fito ganin Heedayah ta taho da sauri ta rungumeta, Kankameta Heedayah tayi tace "I missed you Farida" Farida tace "I missed you more Didi ya su Ammi?" Daga kai Farida tayi suka yi ido hudu da Shuraim, yace "Ya kike?" Farida tace "I am fine" juyawa yyi ya nufi gate ya ciro wayarsa dake ring a aljihunsa, Heedayah ta bi sa da kallo tace "Ain't you coming in ya Shureen?" Ba tare da ya juyo ba yace "Xan dawo" Daga wayar yyi ya kai kunne ganin Mumy ce ke kiransa, Ya gaisheta tace "Shuraim ga ni a kano ka xo ka shigar da ni government house, ina nan kofar Nasarawa gidan 'yar uwar Sadiya" Shuraim dake sauraronta yace "Bana kano, Ina Kaduna ynxu" Da wani irin shock Mumy tace "Kaduna kuma? Me kaje yi Kaduna, kuma wa ka gaya ma xaka je kaduna? To ni yanxu wa xai shigar da ni government house din?" Shuraim yace "Ki kira kaka ta sanar masu xa ki shiga" A fusace Mumy tace "To wai ma uban me kaje yi Kadunan ne baka gaya min ba?" A hankali yace "Aiki Mum" Mumy tayi tsaki tace "Toh kawai ka turo min number Maman Heedayah, kaka mutum ce da xa a kira, ni ka ji da ni ina jira" Yace "To" daga haka ta katse wayar, ya tura mata number Ammi da ta ce. Heedayah ta ja hannun Farida da ta bi Shuraim da kallo suka wuce cikin parlor, har bedroom din Mami Heedayah ta shiga ta tafi da sauri ta rungume Mami cike da murnan ganinta tace "Mami good afternoon...." Mami na kallonta tana murmushi tace "Afternoon My Daughter ya hanya?" Heedayah tace "Alhmdllh, su Ammi da Aunty sun ce a gaisheki" Mami tace "Maa sha Allah ina amsawa hope baki yi amai a hanya ba" Heedayah ta boye fuskarta jikinta tace "Nayi sau daya Mami" Mami tace "Allah ya yaye maki, ya Abban ki da su Yakumbo??" Heedayah tace "They are all fine, they sent their regards, kaka ma next week xata dawo tace amma kwana biyu kawai xata yi ta koma" Mami tace "To maa sha Allah, Allah ya kawota lfya" Heedayah tace "Mami Ya junaid fa?" Mami tace "Yana gidan Baffansa, anjima xai shigo in sha Allah" Heedayah tace "Allah ya dawo da shi lfya" daga haka ta mike tana kallon Mami tace "Xan yi sllh Mami" Mami tace "Toh kiyi wanka gaba daya, idan kinyi sllhn sai ki ci abinci" Heedayah tace "Toh Mami" daga haka ta nufi kofa ta fita ta kulle ma Mami kofarta, Tsaye ta tadda Khaleel bakin kofar bedroom dinsa yana sanye da kananun kaya ya rungume hannunsa yana kallonta, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ina yini" murya can kasa yace "Lafiya, why did you lie to me?" Ta kallesa da sauri tace "Na me?" Shiru yyi yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "What did i lie about?" Yace "Kince ke kadai kika taho" da sauri tace "Ehh with... with Escort" Ya gyada kai yace "Good, Sannun ku da xuwa to" Downstairs ya fara sauka ta bi sa da kallo, snn ta turo baki ta shiga dakin Farida ta kulle kofar, sai bayan da Heedayah tayi wanka ta canxa kaya tayi sllh snn ta fito dakin ta sauka downstairs, Khaleel na xaune parlon da Farida dake kusa da shi yana nuna mata abu cikin laptop, tsaye tayi bakin stairs tana kallonsu, ko lura da ita basu yi ba a wajen, Farida ta wara ido tace "Waow yaya, you are an expert, ni ma ka koya min" ya kyabe baki yace "Xaki shekara goma baki iya ba" Bata rai tayi tana kallonsa, dai dai nan ta ga Heedayah dake tsaye har lkcn, ta sakar mata murmushi tace "Ga abincin ki can dinning na ajiye maki" Heedayah bata ce komai ba ta nufi dinning din, can Khaleel ya dauke laptop din kafarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya bi bayanta. Mumy na xaune parlon Yakumbo tare da Ammi da Mom Islam bayan an gama gaggaisawa, Kaka na kallonta da kyau tace "Toh me ya kawo ki Maryam??" Mumy ta yi yake tace "Aa biki muka yi, shine nace bari in karaso in kawo ziyara inyi xumunci snn inyi Allah sanya alkhairi ranan da aka sa ma Heedayah tunda har na shigo kanon" Kaka ta rike ha6a tace "Su xumunci manya, to amma kina da wasu yan uwa ne a kano wanda bani da labari Maryam?" Mumy ta sunkuyar da kanta tace "A'a yar uwar Sadiya ce aka yi bikinta" Kaka ta kyabe baki tace "Toh sannu da xuwa, gwara kema ki xo ki d'ana arxiki kar ayi ba ki" Yakumbo ta kyabe baki, Ammi ta mike tana kallon Mumy tace "Mu je can bangaren Hajiya" Mumy ta mike tana murmushin karfin hali ta bi bayanta suka fita parlon kaka ta bi ta da kallo tace "Kiri kiri ta ki rike Heedayah bbu irin walakancin da ba mu gani ba daga wajen matar nan, kawai dai a bar kaza cikin gashinta" Yakumbo tace "Toh ba kanta tayi ma ba, yau ba arxikin Heedayar ta ci ta shigo gidan nan ba, Banda haka meye hadin mu da ita??" Kaka tace "Kul.... Uwargidan Amadu ce, uwar Shuraim, da ba don Amadu ba kuma Heedayah kilan sai dai kullum a dinga mata addu'ar gafara gun ubangiji, Kinga kuwa ai ba laifi don ta shigo Gwamnet house" Ammi na komawa bangarenta da Mumy ta sa masu aiki suka kawo mata kayan ciye ciye da ruwa da abinci, Mumy sai kalle kalle take tana duba inda xata ga Heedayah ta billo, duk wnn abun da aka cika mata a gabanta ba shine damuwarta ba, can dai ta kalli Ammi murmushi dauke fuskarta tace "To ina Heedayar ta shiga ban ganta ba" Ammi tace "Ayya ai yau suka wuce kaduna" Mumy ta gwalo ido da sauri tace "Da wa?" Ammi tace "Ita da Shuraim suka tafi, taje yi ma iyayenta na can sallama, tunda bikin ba wani lkci me tsayi aka sa ba" Mumy taji xufa ya karyo mata tace "Yaushe xata dawo kenan?" Ammi tace "Baxa dai ta wuce kwana uku ba ina jin, duk dai yanda Abbanta na Kaduna yace" Mumy tayi wani murmushin karfin hali tace "Toh maa sha Allah, Allah ya dawo da su lafiya, nima din dai yau xan koma dama" Da mamaki Ammi tace "Yau kuma Hajiya, ai yamma yyi, ki bari gobe" Mumy tace "Aa ba mu yi da barrister xan kwana ba, in sha Allah yanxu xan wuce, dama kawai nace in xo inyi Allah ya sanya alkhairi ne" Ammi tace "Da dai kin hakura gobe Hajiya, hanyar nan bai fiye kyau ba" Mumy ta sauko kasa ta dau snacks daya tace "Aa Hajiya yanxun nan ma kuwa xan wuce, bari in d'an ta6a abincin" ko minti ashirin Mumy bata kara a government house ba ta dau hanyar park wajajen karfe uku na yamma. Shuraim na xaune parlon Abbansa yana sauraron maganan da Abba ke masa, Jin ya ki cewa komai Abba yace "Ka min shiru" Shuraim ya daga kai ya kallesa yace "Abba ni fa ban san komai kan xancen nan ba" Abba yace "Kwana biyu da suka wuce kaka ta kirani a kan batun, na kuma yi tunanin kai kayi mata maganan" Shuraim yace "Aa ni ba mu yi wata magana da ita ba" Abba ya girgixa kai yace "Toh bayan bikin Heedayah ina son inji kace min ga gidan da xa mu tafi nema maka aure, naga kamar baka san a sa maka ido ba" Shuraim dai bai ce komai ba, bayan few seconds Abba yace "Snn akan batun mahaifiyarka...." Daga kai Shuraim yyi yana kallonsa, Abba yace "Wannan karan xan dau mataki me tsananin gaske a kanta, tunda har na hanata fita gidan nan tayi disobeying dina tayi ficewarta, to ta tabbatar ba gidan nan xata dawo ba" Wayarsa ne ya fara ring, ganin number isn't saved ya dauke kai, Shuraim dai bai iya yace komai ba, Abba yace "Ina raga ma Maryam wasu abubuwan sbda ku amma bata gani, duk ina sane da abubuwa da yawa da Maryam ke yi ba wai bana sane ba, Maryam bata san annabi ya kafu ba, I am overlooking so many things a da, but today I am done...." Abba ya kalli wayarsa da aka sake kira for the second time, daukar wayar yyi ya daga ya kai kunne tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login