Showing 252001 words to 255000 words out of 275313 words

Chapter 85 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

tafiya, taji ya kamo hannunta a hankali, ta kallesa bata dai ce komai ba har suka isa gate din, tsayawa yyi yana facing dinta, ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "Thanks for ur care sweetheart" Bata ce komai ba ya kai hannunta bakinsa yyi pecking, sosai gabanta ya fadi, ta ki yarda su hada ido, ya saketa cikin sanyin murya yace "Sleep tight dear" Ta gyada masa kai kawai ya fita gate din ta juya ta koma building din gidansu tana tafiya a hankali..... Tun daga nisa take kallon Shuraim dake tahowa, sai kuma ta tsaya har ya iso inda take tace "Why didn't u pick my call" Yace "When did you call?" Tace "To ka duba wayar" Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga call log, kafin yace komai ta amshi wayar tana kallon call log din, taga bayan miss call dinta ya daga kira har uku, ta kallesa tace "Kace baka gani ba" Yace "Ohk na gani, ban ga damar dauka bane" Ta tabe baki tace "Toh ai nima ba da kai xan yi magana ba, dama naga ya Sudais bai dawo bane shi sa na ke son in tambayeka ko ya wuce ne, da ina da number sa ma baxan kira ka ba" Tana fadin haka ta mika masa wayarta tace "Sa min number sa" shafa kansa yyi a hankali yana kallon wayar da take mika masa, can ya sa hannu ya amsa, tafiya ta ga ya fara yi, ta xaro ido tace "Ina kuma xaka da wayata" Bai juyo ba balle ya bata amsa, ta bi sa da sauri tace "Ya Shureen ina xaka tafi da wayata, number ya Sudais nace ka sa min fa" ganin ya ki tsayawa kuma ya ki ce mata komai ta riko hannunsa kamar xata yi kuka tace "Ni dai ka bani wayata, ba kawai sai kace min baxa ka bada ba...." Warce wayar tayi lkci daya ya xamo daga hannunsa ya fadi kasa screen din ya tarwatse, still tayi tana kallon wayar kamar yanda shi ma yake kallon wayar, lkci daya ta fashe da kuka ta juya xata koma cikin gida ya rikota, kwace kanta take son yi tana kuka sosai yace "Ke fa kika fasa kayan ki kuma kike kuka" kin ce masa komai tayi, ganin ba saketa xai yi ba ta tsaya tana kukanta a hankali, Jan ta yyi xuwa gun da ta xauna daxu da Khaleel ya xaunar da ita ya xauna gefenta yace "Toh yi hakuri, xan kawo maki wani gobe" Rufe fuskarta tayi da hijab dinta tana shessheka, Yana kallonta yace "To baxa ki daina kukan ba?" Cikin rawar murya tace "Bayan ka fasa min sabuwar wayata" Murmushi yyi ya mika mata nasa yace "Toh ga nawa idan na kawo maki sabo gobe sai ki bani" Ta d'an kallesa ta turo baki a hankali tace "Toh sim dina fa?" Yace "Sai a mayar maki nawa wayar" Tace "Toh" amsar wayar tasa tayi tace "Da me xa a bude wajen sim din?" Yace "Ke xan tambaya" Ta bata fuska tace "Toh bani da pin" yace "Likewise me" shiru tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Ohk, let me see ur earring" Cire hannun Hijab din tayi ta bude hijab din tana nuna masa dankunnenta, ya kai hannunsa ya cire earring din daya snn ya bude wayarsa ya cire sim cards dinsa, ya bude nata ya ciro sim dinta ya maida wayarsa, nasa kuma ya saka a wayarta, daukan wayar tasa tayi ta kunna ta mika masa tace "Ka cire lock din" amsa yyi, yayi yanda tace, yana kallonta yace "Shkkn?" Ta juya masa gefenta tace "Ka maida min dankunne na" Daukan dankunnen yyi ya shiga sa mata yana kallon gefen fuskarta, ta juyo suka hada ido, sauke idonsa yyi kasa ya mike yana rike da wayarta yace "Sai da safe" Tace "Kace xaka kawo min sabo gobe" yace "Ehh" tace "Toh wani kuma nake so ba wnn ba" Yace "Sai mu je tare ki xaba" tace "Toh xan gaya ma Ammina" Bai ce mata komai ba ya fara tafiya, ta bi sa da kallo har yyi nisa, snn ta mike ta wuce cikin gida. Abban Heedayah na xaune parlonsa tare da Yakumbo dake xaune ita ma duk a firgice, Cike da damuwa tana kalle kalle tace "Amadi ni dai Allah ya gani muna cikin hatsari a gidan nan tun xuwan yaron nan, garin yaya aka barsa ya shigo mana har nan, me ya kawosa, ai shkkn duk rayuwar mu a hatsari yake ko da kuwa bariki goma xa a xube mana a nan, Mutumin da yyi shekara talatin yana abu daya ai bbu abinda baxai aikata ba, har bam sai ya iya dasa mana a nan, snn ni abinda nake son sani shine me ya kawo sa gidan ma, wajen wa ya xo, wllh na shiga bandaki yyi sau ashirin tun barin sa parlona...." Abban Heedayah dake ta sauraronta yace "Haba Yakumbo ki dinga kyakkyawan xato mana, ko don uwarsa ai ya kamata a raga masa balle tasa kaddarar ce ta xo a haka" Yakumbo ta marairaice tace "Toh ni me nace? Ka ji na xagesa ne?" Abba yace "Aa ki daina maganar nan da kike don Allah" Yakumbo tace "Toh ni dai gaskiya nayi kewar inda na fito, Ina son komawa tunda na xo na maku kusan shekara a nan, idan an sa bikin Heedayah sai in dawo bbu ruwana" Abban Heedayah yace "Ai bikin ko xa a sa baxai wuce wata uku ba" Yakumbo tace "Toh naga ai iyayen Junaidun basu xo ba har yanxu, ba sai sun xo xa a sa bikin ba? Balle ma ni duk a tsorace nake da su gaba daya ma ynxu" Abba ya d'an yi shiru kafin yace "Ba da Junaid xa ayi ba kuma" Yakumbo ta gyara xama tace "Toh Alhmdllh, ko don rikon da uwarsu tayi ma Heedayah kamar ita ta haifeta bai kamata ace da aure ma tsakaninsu ba, duk da dai na ya6a da hankalin yaron wllh, amma ni kawai abun ya fitar min a kai ne, yanxu aure ma ba tasa bace kamata yyi ya xauna yyi ta nusar da yayansa da Allah ya kubutar kwanan nan" Kallonta kawai Abban Heedayah ke yi, kafin yace "Toh da yayansa xa ayi, don ita Heedayah tace shi take so, kuma bana tunanin akwai abinda dangin Hajiya Rahinah ko Barrister Ahmad xasu bukata daga bangarena in hana ko da abun yafi karfina xan yi iya bakin kokarina in ga na kwatanta masu...." Yakumbo kallonsa take kamar bata fahimci abinda yace ba, can dai tace "Wani ne a dangin nasu yace yana son Heedayar kake nufi ko me, ni ban gane ba" Abba yace "Shi dai Khaleel din ke sonta da aure, ita ma kuma ta shaida min shi take so, Barrister ya kirani mun yi magana, Yan uwan mahaifinsa ma sun kirani munyi magana jiya, kanin mahaifinsa ma na da wani mukami a nan gombe, gidansu ba kananun mutane bane, gida ne me tarihi me kyau da usuli, ynxu xa mu jira ne a gama shari'ar da ake a kotu snn a sa rana wanda baxa a ja lkci ba idan Allah ya yrda, ni na yrda da kaddara, me kyau ko akasin haka, kaddarar Khaleel ne sai yyi rayuwa cikin gurbatattun mutane, kaddarasa ce sai sun gurbata masa rayuwa, amma ynxu Alhmdllh da Allah ya maidosa hanya madaidaiciya ya shiryesa, ni baxan kyamacesa ba kamar yanda Uwarsa bata kyamaci tawa 'yar ba, snn bana fatan wani nawa ya kyamacesa, ba laifinsa bane don ya tsinci kansa a rayuwar da yyi a baya.... In dai aurensa da Heedayah alkhairi ne garemu baki daya Allah ya tabbatar" Yakumbo ta fashe da wani kuka tace "Ba ruwana da surutunka mara kan gado wllh Amadi, idan kotu ta yanke hukuncin xa a ratayesa ko xa a dauwamar da shi a gidan yari na har abada sai ayi yaya kenan?" Abba ya girgixa kai yace "Dangin ubansa baxa su ta6a barin hakan ya faru ba, haka zalika mahaifiyarsa da ta kasance babban lawyer, snn ga mijinta da shi ma babban lawyern ne, idan kuma an ajiye batunsu... laifin Khaleel ba mai yawa bane tunda bai ta6a kisa ba" Yakumbo ta kara rushewa da kuka tace "Katon mutumi ya xauna ya giggilla maku karya yace bai ta6a kisa ba ku yrda, dama an ta6a d'an ta'adda da bai ta6a kisa ba? To wllh ni dai da ya auri Heedayah gwara kawai a kasheni" Tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Abba ya girgixa kai don darun Yakumbo ba matsala bace a wajensa, shi dai yasan bbu abinda xai hanasa bai ma Khaleel auren 'yar sa, sai in shi ya fito da kansa yace ya fasa. Heedayah ta gama saka kayan baccinta kenan taji ringing wayar Shuraim dake kan gadonta, karasawa tayi tana kallon screen din wayar taga number ne kawai, bata dauka ba ta karasa shiryawa ta kwanta kan gado ta dau wayar, WhatsApp dinsa ta bude ta shiga, messages sun kusa dari uku ta gani da ba ayi replying ba, bin messages din ta shiga yi tana dubawa, duk yawanci taga na mata ne, call ne ya shigo wayar ta ga still number daxu ne, dagawa tayi ta kai kunnenta taji ance "Isn't the number saved?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Ehh no name" yace "Toh wani labarin ku ka yi da saurayin naki yau?" Tace "Me yasa kake tambayata?" Yace "In kara maki experience" bata san lkcn da tayi dariya ba tace "Wanda baya soyayya ne xai bani experience, ashe xaka korar min saurayi"





Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Murmushi Shuraim yyi yace "Toh sae da safe" Heedayah tace "Ko kana yi?" Yace "Mene?" Tace "Soyayyan mana" ya girgixa kai yace "Aa sai ke" Tace "Tohm byee" katse wayar ta ji yyi, ta kalla sannan ta ajiye a hankali ta juya ta kwanta. Washegari da safe Heedayah ta samu Mami a parlon Amminta, bayan ta gaisheta a hankali tace "Mami don Allah ina son in bi ku...." Mami tace "Ki bi mu ina?" Heedayah tace "Kaduna" Mami tace "Yaushe kika xo xaki ce xaki koma Kaduna?" Shiru Heedayah tayi, Mami tace "Look Heedayah gidan ku ne nan idan xaki saki jiki ki saki jiki, bana son gulma" Ita dai Heedayah bata ce komai ba, Shigowar Ammi ya sa ta mike ta fita, a ranan karfe goma da rabi Heedayah na tsaye sai kallon Khaleel dake xaune gaban motar da xai kai su Kaduna take, Mami ta shiga bayan motar bayan ta gama sallama da Ammi da Mom Islam, a hankali Heedayah ta daga mata hannu, Sannan ta daga ma Khaleel ma, murmushi ya sakar mata ta juya ta koma ciki kar hawayen dake makale idonta ya gangaro. maid dinsu Amina ce ta kwankwasa dakinta bayan Magrib, Heedayah dake xaune saman darduma ta mike ta bude kofar tana kallonta, Amina tace "Baaba Yakumbo na kiran ki" Heedayah bata ce mata komai ba Maid din ta juya ta bar wajen, Heedayah ta koma ta dau wayarta ta fita dakin, gaba daya a sanyaye take, sosai take jin tana missing din Khaleel, a hankali ta bude kofar parlon Yakumbo bayan ta isa, Yakumbo ce xaune parlon da kaka da tayi tagumi, Shuraim ma na xaune parlorn, ta karasa ta durkusa saman lallausan carpet dake parlon ta kalli Shuraim tace "Ina yini Ya Shureen" Yace "Lafiya" Ta kalli su kaka ma ta gaishesu, bbu wanda ya amsa mata cikinsu, Bayan few seconds tace "Gani" Kaka ta saki kuka tace "Yanxu fisabilillahi Deedayah ki rasa wanda xaki ce ma iyayenki kina so sai d'an kinnafin? Ke ko me ya sameki haka kika xabar ma kanki mutumin nan ni Patuu??" Tuni Heedayah ta hade rai tace "Shi ba Kidnapper bane" Kaka tace "Aa toh wllh kin karyata ubanki, Mutumin da tun kina ficiciyar ki ya daukeki ya raba ki da iyayenki, sbda addu'ar da ake jefa sa da shi ya rasa sukuni ya fito dake daga garkensu ya yasar dake gefen titi shine xaki bude baki kice mana ba kinnafa bane???" Hawaye ya kawo idon Heedayah tace "Ni dai ba Kidnapper bane, ku daina kiransa haka" Yakumbo na kallonta da kyau tace "Toh bari kiji wllh indai da raina bbu wanda ya isa ya nuna ni yace ga surkar kinnafa, tun wuri kiyi maxa ki sauya shegen tunanin ki, kaf xuri'ar mu bbu me abun fadi da ya bar ma jika, don haka baxa ki bar mana abun fade ba, har gobe mutumin nan kinnafa ne a idona, ba komai bane mu ma ya kwamushe mu wataran" Kaka tace "Toh da fa?? Ai ynxu da kyar idan bai lallabo ya dawo nan ba yyi abinda xuciyarsa ke raya masa, ni ban yrda ya wani koma kaduna ba, yana nan makale a kano xai dawo tsakar dare, sannan wlh banda ina kunyar uwarsa ni rufe ido xanyi in gaya masa abinda ke raina, to meye hadina da shi??" Heedayah ta fashe da kuka sosai tace "Ni dai ba Kidnapper bane...." Yakumbo ta dau pillon da ke gefenta ta jefa mata a fusace tace "Kin karyata uwarki, wllh in dai ina numfashi baxa ki auri katon D'an ta'addan nan ba" Kaka ta kalli Shuraim dake danna wayarsa tace "Kai kuma an kiraka ka xo ka yi mana shari'a kayi shiru kana kallonta tana mana fitsara" Ya dago kai yace "Toh Kaka ku xa ku xauna mata da shi?" Bude baki Yakumbo tayi tana kallonsa, yace "Ita xata xauna da abun ta, kuma Kidnapper da ku ke ce masa ya ta6a kidnapping din ku ne?" Yakumbo tace "Naga abinda ya isheni...." Kaka tace "Toh tashi ka fita, na mance halinka ne ya sa na kiraka, Allah yayi maka yanda kayi mana yanxu" mikewa yyi ya maida wayarsa aljihu ya nufi kofa, Yakumbo tace "Kai xaka yrda kanwarka ta auri tatattcen tsohon d'an kinnafin idan ba mugunta ba, ashe haka xuciyarka take ban sani ba, toh aniyarka ta bika wllh" Kaka tace "Gantalalle ne fa, ni ba na mance waye shi ba na gayyatosa, ai fadan gaskiya karara sai Sudess Dan arxiki" Mikewa Heedayah tayi ta fita tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, tsaye ta ga Shuraim bakin stairs, ta fashe da wani sabon kukan, yana kallonta yace "Toh meye na kuka? Ba dai Abbanki ya amince ba haka ma Amminki?" Ta hade kanta da bango tana kuka sosai tace "Toh shine xa a dinga ce masa Kidnapper bayan ya daina???" Yace "Haka yace maki?" Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, yace "Suna nufin idan ku ka yi aure da shi, ce maki xa a dinga yi matar tsohon Kidnapper" Tace "Ehh na yarda" daga haka ta bi gefensa xata wuce ya riko hannunta, kin juyowa tayi hawaye na sauka idonta, ya juyo da ita yace "Toh kiyi hakuri idan ma sun kiraki kar ki sake xuwa" ita dai bata ce komai ba, yace "Mu je ki amshi wayarki ki bani nawa" Ba musu ta bi sa downstairs. Mami ce xaune bedroom dinta tare da Junaid dake sauraron abinda xata fada masa don kiransa tayi a waya, Mami na kallonsa tace "Da farko na so ka da Shaheedah ka kawo excuses which I had no option then to let you stick to ur choice, kace kai Heedayah kake so, fine ka je gun iyayenta without me even knowing kuma sun nuna sun baka ita, weeks back ana da intention din kai kudi gidansu, sai abubuwa suka faru wanda ya sa aka daga, to har yanxu naji kayi shiru kan xancen baka cewa komai ba, da akwai wani abun a ranka ne??" Tunda Mami ta fara magana Junaid ke kallonta, can ya sauke idonsa kasa yace "Na hakura da ita ne kawai Mami" Mami na kallonsa tace "Ko saboda me?" Yace "Saboda yayana, I will welcome anything that will make him happy, he deserves to be happy bayan duk abubuwan da yyi passing a rayuwa, I over heard conversation dinku the other night, a wannan daren kuma na cire Heedayah a raina, bbu aure tsakanina da ita, na bar ma Ya Khaleel, Allah ubangiji ya sa rabonsa ce ita" Mami ta kasa cewa komai don tunda Khaleel ya gaya mata Heedayah yake so bata da wani kwanciyar hankali, har ranta take son duk abinda xai faranta ma first son din nata, amma kuma bata sanar ma Junaid xancen ba sbda bata son ya ga kamar ta fifita Khaleel a kansa, amma furucin Junaid yau ya sa taji hankalinta ya kwanta, Rasa ma abinda xata ce masa tayi, Junaid ya mike ya fita daga dakin.

3 months later....
Heedayah na parlon Stepmum dinta dake tsefe mata kitson da tayi mata duk da satin kitson daya bbu abinda yyi, Mom Islam ce ke ta surutun ta ita kadai Heedayah bata cewa komai, can Mom Islam tace "Are you okay Heedayah?" Da sauri Heedayah ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, Mom Islam tace "Tunanin me kike?" shiru Heedayah tayi, Mom Islam tace "Talk to me" A hankali Heedayah tace "Nothing aunt" Murmushi Mom Islam tayi tace "Sa ranan da aka maki yau ne ya sa kike ta tunani tun daxu" Lkci daya hawaye ya kawo idonta amma bata ce komai ba, Mom Islam tace "Toh ki kwantar da hankalin ki dear, kowa ma haka ya ji yanda kike ji, amma naki shirun yyi yawa, you are suppose to be happy...." Heedayah tace "I am not sad" Mom Islam tace "Ko ranan da aka sa yayi maki kusa?" Heedayah ta dago ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Ehh" Mom Islam tayi murmushi tace "Wata dayan ne yyi kusa?" Hawaye na sauka idonta tace "Aunty just four week fa, yar karamar yarinya da ni?" Dariya sosai stepmom dinta tayi tace "Ehh lallai kam yar karamar yarinya, to ni a ranan da Abbanki ya kai kudi ranan ma aka daura auren, kinsan Ammin ki ce ta hada mu dama" Heedayah dai tayi shiru bata ce komai ba, Mom Islam tace "Washegari kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login