Showing 66001 words to 69000 words out of 275313 words

Chapter 23 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

wllh, ni dama ko tsinke shegen bai kawo min ba, shi kuma Junaidu daxu ya kirani wai nan da sati xai dawo har yace in bata suka dade kuwa suna waya, ko kanwarsa bai ce in ba ma ba, ita kuma Khadijah daxu...." Shuraim ya dakatar da ita yace "Ina tsaraban??" Kaka tace "Ae baxa su dauku ba Shureen" yace "Suna ina?" Mikewa Heedayah tayi a hankali tana laluba hanya xata fita kaka tace "Ji algunguma, Ina kuma xaki, kinji nace xan dau kayanki ne da xaki wani mike xaki fita??" Shuraim dai sae kallon dakin yake yana neman kayan.....


Am so exhausted yau, let it not just be as if I didn't type🥺


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Ta gefen ido Shuraim ya dinga kallon Heedayah dake kokarin fita ya ga ko xata ta6a sa, she was so careful ko kusa da shi bata bi ba har ta fita dakin, kaka tace "Ni sae nake ga kamar karyar makanta take yi, ynxu a hka fa sai ta fita har tsakar gida" Shuraim yace "Ina kayan?" Kaka tace "Naga jaraba, Ina ruwanka da kaya Shureen? Tun daxu ka isheni ina kaya to kai aka kawo ma kayan? Kayan me xaka dameni haka, Komai fa na da sirri, ba ruwana ni ba 'yar cin amana bace, Bai ce in nuna ma kowa ba har Amadun balle kai karan kada miya...." Wani kallo yyi mata ya juya ya fice daga dakin.... Turuss Khadijah tayi rike da bucket din ruwan kumfa a hannunta, ya kalli direction din da take kokarin xuwa da sauri, Heedayah ce har sannan bata isa bangaren Mami ba tana tafiya a hankali kuma very careful, ya kalli Khadijah da tayi wuri wuri da ido, da sauri ta juya xata koma Inda ta fito, ya bi bayanta tana ganin haka ta sake bucket din hannunta a rikice, ya ja baya da sauri ganin ruwan kumfan ya malale kasan tiles bai ankara ba sai gani yyi tayi sama sannan aka nanota kasa da karfi, wani ihu tayi can kasa makoshi, ya ma rasa ko dariya xai yi ko d'aga ta xai je yyi, ta kwalo ma Mumy kira tana cewa Wayyo bayanta, yana jin hka ya kalli Heedayah da har ta kai kofar parlon Mami ta tsaya, Farida ma ta fito da sauri don ganin me ya faru, Shuraim na jin Mumy ta bude kofarta xata fito tun bata karaso ba tana tambayar lafiya me ya faru, yyi saurin shigewa dakin kaka ya rufe kofar. Farida ta ja Heedayah suka shige ciki ta kulle kofa. Bayan isha Farida na parlon Mami da Heedayah, Mami kuma ta je kai ma Abba abinci aka bude kofa Sudais ya shigo da sallama, daga kai Heedayah tayi tana kallon ta Inda ta ji muryar sa, da farko Farida ta xata Shuraim ne sai kuma ta ga wannan ya fi Shuraim haske, Ta gaishesa ya amsa yana murmushi yace "Ya kike?" Tace "Lafiya lau" ya xauna yana facing din su idonsa a kan Heedayah yace "Ba gaisuwa Deedayan kaka" Heedayah ta jinginar da kanta da kujera tace "Ni ba Deedayah bace" yace "To ya sunan?" Ta langwabar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Cutie, ya karatun kuna ta yi koh? And kina ganewa?" Ta gyada masa kai, ya kalli Farida yace "Ya sunan ki 'yan mata?" tace "Farida" yace "Ban ta6a ganin ki nan ba Farida, though Naga kuna kama da Junaid" Farida tayi murmushi tace "Ehh na xo hutu ne kawai" yace "Wani makarantar kike?" Tace "Nigerian Turkish...." Yace "Boarding?" Ta gyada masa kai, yace "Maa sha Allah" Heedayah tace "Yayana baxa ka sake komawa UK ba koh?" Yace "Idan ma xan koma tare xa mu koma ae" Ta wara ido tace "Da gaske?" Yace "Ehh mana sai in gaya ma su Abba da Kaka su bani ke, kowa ya shaida sannan mu wuce" Murmushi tayi tace "To kayi masu magana plss" yace "Da gaske dai xa ki bi ni? Xamu dade fa bamu dawo ba" tace "Allah xan bi ka" yana murmushi yace "Toh shkkn" Bude kofa aka yi Rabi'ah ta leko fuska daure tace "Ya Sudais kaka na kiran ka" ya kalleta kafin yace komai tayi banging kofar ta wuce, Farida tayi kwafa can kasa kasa, mikewa yayi yace "I'm coming back...." A hankali Heedayah tace "No chocolates?" Ya kalleta yyi murmushi yace "Sai na dawo" daga haka ya fita, Farida tace "Ke da kike cewa xa ki bisa ke matarsa ce?" Heedayah tace "To ba Yayana bane" Sudais na tsaye yana sauraron abinda kaka ke cewa, can yace "Toh yanxu me kike nufi?" Tace "Ina nufin in har baka bani nawa tsaraban ba wllh baxan bata ba, gwara in kwashi tarkacen da ka kawo in kai kasuwar 'yan koli in siyar, haka kawai daga ganin sarkin pawa sai miya tayi xaki, uwar me ma ka hada da ita bani da labari, duk wahalan da nayi da kai kana karami ka dawo daga kasashen turai ko abun sakace hakuri baka kawo min ba sai yar tsintuwa" dai dai nan Shuraim ya shigo dakin da ledan fruits da Abba ya sa ya siyo mata, Sudais ya kallesa sannan ya ci gaba da sauraron kaka, Shuraim na ajiye ledan tace "Shureen tunda muke da kai ka ta6a fita kasar waje ka dawo baka min tsaraba ba, ko nan nan da Zaria idan kaje ai kana siyo min 'yar lemon nan" Shuraim na kallonta ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihu, kaka tace "Toh don me Sudess xai fita ya dawo min haka sai wata can wai Deedayah xai kwaso ma kaya iri iri kamar kanwar ubansa" Sudais yace "Saboda ta fiye min ke" shiru kaka tayi tana kallonsa a bit shock, yace "Kuma ki fito da kayan in kai mata yanxu" Kaka tace "Al-qur'an kasuwan 'yan koli xan kai su gobe da sassafe, idan na baka in tafi a karkace, Deedayar kanwar ubanka ce ko ta uwarka?? Waye kuma Deedayah? Me na hada da ita banda dai d'a na ya tsinto mana ita" Sai kuma ta xauna ta fashe da kuka tace "Ehh lallai karshen duniya ta kankama" Juyawa Sudais yyi ya fita daga dakin, Kaka ta kalli Shuraim tana matsar kwalla tace "Ka dai ga ko Shureen?? Hakan da Sudess ya min ya kyauta" Yace "Ni baxan ce komai ba sai na ga kayan" Babu wata wata Kaka ta dauko makulli da sauri ta bude gun ajiye kayanta ta fiddo akwatunan har biyu da karamin jaka, kallonsu kawai Shuraim yake, ta xuge jakar ta shiga fiddo abubuwan ciki, cikin lkci kadan ta fiddo komai ta bajesa a gaban Shuraim tana kallonsa, Kallon kayan kawai Shuraim yake, beautiful English wears, teddie bears, biscuits, dolls, chocolates, sweets, shoes, har da jewelries, Shuraim ya dauke idonsa daga kan kayan, kaka na matsar kwalla tace "Ka dai gani ko, ni fa na haifi ubansa Umaru" Mikewa Shuraim yyi bai ce mata komai ba ya fice daga dakin... Ta bi sa da kallo baki bude sai kuma tace "Toh Allah ya isa" Sudais na komawa parlon Mami, Mami dake xaune parlor tace "Mutan UK, sai yau muka hadu" Ya gaisheta yana murmushi yace "Jiya da na xo kina gun aiki" Mami tace "Ehh ina can, ya karatun kun gama kuwa?" Yace "A'a saura kadan" Mami tace "Maa sha Allah, Allah ya sa a gama a sa'a, ya su Hajiyar ku?" Yace "Suna lafiya gaba daya" Tace "To maa sha Allah, a xubo abinci?" Yace "A'a na ci" ta mike tace "To yayi kyau" bedroom dinta ta shiga ya kalli Heedayah ya koma kusa da ita yace "Ina kawar ki Farida?" Tace "Ta tafi wanke wanke a kitchen" Sudais yace "Masu aiki fa?" Heedayah tace "Mami ce tace taje ta yi" Yace "Ohkk" ta matso kusa da shi a hankali ta laluba hannunsa tace "Yaya kasan me?" Ya kalli kofar dakin Mami sannan ya hade forehead dinsa da nata yace "No..." Tace "Yau ina son in sha ice cream" yace "Ice cream?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk bari Farida ta gama wanke wanke sai mu je gaba daya" Tayi murmushi tace "Nagode" Farida na shigowa yace "Farida tell Mami xa mu je siyo abu yanxu, with you and Heedayah" tace "Ohkk" daga haka ta shiga bedroom din Mami, ba a dau lkci ba ta fito da Hijab dinta da na Heedayah tace "Mami tace alright" sosai Heedayah ta ji dadi, ya amshi Hijab din ya sa mata sannan ya daga ta holding her hands suka fita parlon tare da Farida, Shuraim na xaune parlor shi kadai, tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai har suka fita parlon.... Wani wajen shan ice cream Sudais ya kai su, yyi parking ya sauka motar, ya bude ma Heedayah back seat yana rike da hannunta ta sauka, Farida ma ta fito daga front seat da ta xauna, Sudais na rike da hannun Heedayah da ta makalesa suka shiga ice cream parlor din, Ya duka dai dai kunnenta yace "Wani irin ice cream kike so?" Tace "Vanilla" ya kalli Farida dake kallonsu yace "Ke fa Aunty Farida?" Tayi 'yar dariya tace "Irinsa nima" Wani mutumi ne xaune wajen da roban ice cream a gabansa, su uku ne xaune a round table din, all wearing glasses, tun da suka shigo yake kallonsu ta bak'in glass din idonsa, Sudais ya biya kudin ice cream da ya siya masu yana rike da hannun Heedayah ya nufi kofar fita Farida na biye da shi, mikewa Mutumin yyi ya dau makullin motarsa, wanda ke kusa da shi ya kamo hannunsa murya can kasa yace "Hey... ina kuma xaka? Ynxu fa xa su gama su fita..." Ba tare da Mutumin ya kallesa ba yace "Ina xuwa ynxu" daya Mutumin yace "Noo this is our only chance...." Ya fixge hannunsa ya fita da sauri, Sudais ya kulle motarsa kenan bayan ya sa Heedayah ciki ya bude maxaunin driver ya shiga yana kallon Farida dake gaban motar yace "Did you need anything again Farida?" Tace "Aa mun gode" tada motar yyi yayi reverse, Mutumin da tuni shi ma ya shiga motarsa ya bi bayansa, mota daya ne interval tsakaninsu, Mutumin ya dinga kokarin ganin yyi over taking motar har suka kusa traffic, Sudais na tsallaka wajen traffic din ya nuna red, hakan ya sa motar dake bayansa ya tsaya, Mutumin ya jinginar da kansa da kujera ganin motar Sudais yyi nisa sosai... Sudais na parking a kofar gida ya bude ma Heedayah back seat ya sakko da ita, Farida na rike da ledan ice cream din suka wuce ciki, har sannan Shuraim na xaune main parlor, wannan karan kallon gefen ido yyi masu, Sudais ya duka kusa da Heedayah yace "Sai da safe, I am going home now" tace "Xaka xo gobe?" Yace "In sha Allah" tace "Haka kace jiya kuma baka xo ba" yace "Ba gashi na xo yau ba" tace "Toh byee" ya ja hancinta a hankali yace "Bye" Farida ma tayi masa sai da safe tana rike da hannun Heedayah suka wuce bangaren Mami, Sudais na kallon Shuraim yace "Sai da safe bokan turai" Shuraim na danna wayarsa yace "Allah ya tashe mu lfya" Sudais ya juya ya fita parlon... Washegari karfe tara saura Hajiya Amina mahaifiyar Sudais ta shigo gidan, Khadijah na xaune dinning suna breakfast da Rabi'ah, duk suka gaisheta suna mata sannu da xuwa, ta nufi dining din tana kallonsu murya can kasa tace "Abba na nan??" Rabi'ah tace "Aa ya fita" Umma tace "Hajiya Maryam fa?" Khadijah tace "tana daki" Umma ya nufi bangaren Mumy ta bude kofar ta shiga, bbu kowa parlon haka yasa ta wuce daki, Mumy ta katse wayar da take yi da sauri tana cewa "Waye??" Umma tace "Ni ce Maryam" Mumy tace "Aa Amina, daga ina da safe haka?" Umma tace "Daga gida..." Mumy tace "Allah ya sa lafiya dai, ko munafukar ta sake hada ki da Dakta?" Umma tace "Ba gwara a hada ni da Dakta ba a kan wnn takaicin...." Mumy ta gyara xama tace "Me ke faruwa?" Umma tace "Uban kayan da Sudais ya kawo ma makauniyar nan na xo amsa tunda ba ubanta bne ya basa kudin banxa" Da mamaki Mumy tace "Kaya kuma, wllh bani da labari Amina, ta Ina aka shigo da kayan gidan ban sani ba?" A fusace Umma tace "ni kai na da na haifesa a jaka daya ya kawo min tsaraba, kanninsa kuwa dama tsaraban baya wuce chocolate da biscuits..." Mumy tace "To wai kayan me ya kawo mata?" Umma tace "Wllh tsaraba ya yo mata niki niki, iri iri kuwa, bai san xancen xai dawo kunne na ba, har manyan akwatuna biyu da jaka fa Maryam, abinda hakan ke nufi shine na kasa ganewa" Mumy ta gwalo ido tace "Sudais din?? Jiya na ji ance ya xo dama amma ko shigowa ya gaisheni bai yi ba, kinsan fa har wani xumunci ya kulla da kishiya ta" Umma ta mike tace "Ina xuwa, ba dai Barrister baya nan ba, yau xa ayi ta ta kare" bata jira cewar Mumy ba ta fita. Bangaren Mami Umma ta nufa ta bude kofar hade da sallama bbu yabo bbu fallasa, Mami na tsaye parlonta tana sa wrist watch ta gama shirin fita, su Farida na parlon, a takaice Umma tace "Ina kwanan mu" Mami na kallonta tace "Same to you" Umma tace "Kayan da Sudais ya kawo gidan nan na taho a miko min..." Mami tace "Kaya? Kayan me kenan?" Umma tace "Ai kin fini sanin ko kayan menene tunda kece kika amshi kayan, to ba duniya na haifar ma shi ba, ayi hakuri a fito da kayan a bani in kama gabana" Mumy dake ta leko parlon tana tsaye daga bakin kofa tace "Atohhh, gwara dai ki sanar masu ba duniya kika haifar ma shi ba" Mami bata sake kula su ba, ta gama saka agogonta ta dau handbag dinta da veil tana kallon Farida da Heedayah tace "Farida bring hijab for the both of you sai in ajiye ku gidan Hasinah" Farida ta mike ta wuce daki, Umma tace "Ni fa ba Maryam bace da xaki wani dinga sha ma kamshi bbu hadina dake, kayan da d'a na ya kawo maki nace ki fito min da su yanxu, ko alkali ce ke ni baxan fasa amsan abinda na xo amsa ba baxan kuma fasa gaya maki abinda ke raina ba....." Farida ta fito da hijab Mami ta amsa ta sa ma Heedayah, Farida ta ajiye mata takalminta ta a gabanta, Mami tace "Ki je ku sallami Kaka, sai ku sameni a mota" Umma ta bude baki tana kallon Mami ganin har sannan ta ma ki kallon inda take, Mami ta nufi kofar sai a nan ta kalli Umma tace "Malama xan wuce, bani hanya" Umma tace "Hanyar ya ci kaza kazan sa, kayan da aka kawo maki nace ki fito min da su yanxu kada abu ya 6aci tsakaninmu, ni fa ba Maryam bace wllh" Kaka ce ta taho wajen da sauri tana cewa "Muryar waye nake ji wnn kamar na Amina, me ke faruwa hka?" Umma ta juya tana kallon kaka fuska daure tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Lafiya kike hayaniya haka a kofar mutane Amina, me ya faru??" Mumy tace "Wllh kaya wai Sudais ya kawo gidan nan ba mu da labari, kaya wai me yawa..." Kaka tace "Kayan me??" Mumy tace "Ni kaina bansani ba, ance dai kayan na nan bangaren" Kaka tace "Au, wai tsaraban da yayo ma Deedayah?" Mumy tace "Toh shi din kenan" Kaka tace "To sai aka yi yaya? Ai kaya basa wajen Rakiya suna wajena, waye ya xo amsa?" Umma da ta daure fuska tace "Ni na xo amsa" Kaka ta kalleta daga sama har kasa tace "Haba, to sannu da xuwa Amina, bakin cikin ne ya motsa kenan yau, to bari kiji ko Umaru yyi kadan ya amshe ma Deedayah kayan da Sudess ya siyo mata balle ke, kuma in sha Allahu yau xata fara saka kayan sai in ga ta tsiya, ke kuma Maryam har kin mance hijaran da kika yi na kwana biyar a gidan nan bayan kin sa an sace Deedayah kin maido ta, kin manta yanda kika dawo duk a lalace shine xaki sake shiga wani kess din da sassafe koh, to wllh Rakiya kiris take jiran ki ko bata fada ba ni na sani, haka kawai duk kun bi kun sa ma makauniya ido, to wllh karyan ku, tunda ina sonta Rakiya na sonta Sudess na sonta, Junaidu na sonta shi Amadu ba wai mun gama sanin xuciyarsa bane, to kowa ma ya ki ya indai mu muna sonta" Umma ta fiddo wayarta tayi dialing number Sudais yana fara ringing ya daga, strictly tace "Kana ji na Aliyu??" Sudais yace "Ina ji Umma" tace "Wannan kayan da ka kawo gidan Barrister da sunan kayi ma makauniya tsaraba maxa maxa ka xo ka amshe su ka kawo min dakina, idan kuwa ba haka ba wllh wllh ka canxa wata uwar...."



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍




Kaka dake ta kallon Umma baki bude ta saki salati tana tafe hannu, ganin Umma ta yanke wayar bayan ta gama magana kaka tace "Toh yanxu dai kafin ince komai so nake a fara gaya min munafukin da ya kai maki xancen nan, idan kuma baxa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login