Showing 231001 words to 234000 words out of 275313 words

Chapter 78 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

matsala da kafar, Kai har ka isa yanxu ka xo kace xaka bar mu bayan duk sadaukarwa da muka yi maka da kokarin ganin ka rayu cikin mu shugabanninmu basu cutar da kai ba?? Wllh kayi kadan Brainiac, kayi kadan ka bijire mana ka watsa mana kasa a ido, gwara in tarwatse kanka, gwara in kashe ka har lahira...." Yana fadin haka ya xaro bindigarsa daga aljihunsa da sauri, kusan a tare suka yi hakan da Khaleel da ya xaro nasa bindigar shi ma yana nuna ma Manga, Arne dake ta wani huci ya sa hannu ya sauke bindigar manga cikin kaushin murya yace "Bar shi Mangaaa, bar shiiii" Khaleel bai fasa nuna ma Manga tasa bindigar ba, Cikin tsawa Arne na nuna Khaleel yace "Mu xaka ci ma amana? Mu xaka kawo ma tashanci??" Khaleel yyi wani murmushi yace "Sai na tashi daukan ma mahaifina fansar kashesa da ku da mukarrabanku ku ka yi xa ku san tashanci" da shock duk suke kallonsa, Khaleel ya gyada kai cike da tsanarsu yace "Ku ka rabani da Mahaifiyata ina d'an shekara uku ban san kaina ba, ku ka kawo ni cikinku, ku ka lalata min rayuwa, ku ka cuceni, kuka koya min mugun hali da mugun nufi, Billah karshen ku ya xo a duniya, daga yau ina me sanar maku da babban murya cewar idan ku ka sake bibiyana tare da abokina Zayyad kuna ci gaba da tursasa mu kuna cusa mana mugun tunani da mugun nufi a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba za ku kare rayuwarku daure a kurkuku, na har abada....." Bude baki duk suka yi suna kallonsu, tuni Zayyad ya mike ya xaro nasa bindigar shi ma yana nuna ma Oga Manga, Khaleel na huci ya nufi kofa yana tafiya da baya yana nuna su da bindiga haka Zayyad ma yyi har suka fita daga parlon still pointing there gun toward them, a haka su Khaleel suka isa gate ta baya har suka fice daga gate din, da gudu suka shige mota a tare, Khaleel ya tada motar ya figa ganin su Manga sun fito a guje suka hau harbin tayoyin motar amma tuni Khaleel yayi masu nisa ya karya wani corner da motar.... Zayyad ya sauke ajiyar xuciya yace "It was successful" Khaleel bai ce komai ba sai gudu yake yana kallon madubi to be sure basu biyosa ba har dai yyi nisa sosai snn ya sauke wani ajiyar xuciya, Zayyad ya kunna record din da yyi da wayarsa yana murmushi.... Mami ce xaune living room tare da su Dinar da wata aunt din Khaleel sai sisters din Mami suna sauraron record din wayar Zayyad dake hannun Mami, sae da record din ya kare, kowa na parlon ya sauke ajiyar xuciya, ko wanne jikinsa yyi sanyi, Mami ta d'an yi murmushin karfin hali tana kallonsu Khaleel tace "Alhmdllh, it's a great job you two did, ku wuce sama kafin ku ci abinci" Khaleel ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ummi baxa mu iya tafiya can gidana ba?" Dinar da Amira suka xaro ido, aunt dinsa Aunty Nafisa tace "Wani gidan kuma Aliyu, a yanxu ai baka da wani gidan da ya wuce nan, you just have to feel at home kaji" sister din Mami tace ce "Lallai kam, this is ur only home for now" Mami na kallonsa tace "You are not feeling at home here right?" Khaleel dai bai ce komai ba, a hankali Mami tace "Look at me" Kallonta yyi tace "Nan ne gidanku... wancan gidan kuma ba naka bane yanxu, beside you both aren't safe anymore to be thinking of going out" Shiru Khaleel yyi bai dai ce komai ba, Mami tace "Ku wuce sama, xa a kai maku abinci" mikewa yyi suka wuce dakin Junaid tare da Zayyad. Heedayah da Farida suka kawo ma kowa dake parlon abincin da suka gama girkawa tare da maid dinsu, Mami tace "Ku kai ma su Zayyad a sama, Su Umma ma suna dakina ku kai masu" Komawa kitchen din suka yi, Bayan Farida ta hada abincin Khaleel da Zayyad a tray ta sa ruwa da komai a kan tray din ta kalli Heedayah tace "Ki kai masu ya Zayyad din sama" Heedayah tace "Ki kai masu sai in xuba ma su Umma" Farida tace "No dont worry ki kai ni xan xuba masu" Daukan abincin Heedayah tayi ta fita kitchen din ta wuce sama, ajiye tray din tayi kasa bayan ta isa kofar dakin Junaid ta bude kofar snn ta duka ta dau tray din ta shiga dakin da sallama, Khaleel ya shiga buttoning shirt dinsa da ya cire button din yana kallonta, tun da ta kallesu sau daya ta dauke kai ta ajiye tray din abincin a saman carpet din dakin ta mike tace "Ina yinin ku?" Zayyad yace "Sannu da aiki" tace "Nagode" ta d'an kalli Khaleel ganin kallonta yake, ta d'an yi murmushi tace "Welcome" yace "Thanks, ke kika yi girkin?" Tace "Ni da Farida da Zainab" Yace "Toh Sannun ku" juyawa tayi ta nufi kofa ta nufi kofa ta fita daga dakin, Zayyad na kallonsa yace "I wish xa a baka auren yarinyar nan, nasan ba lallai ciwon ka ya dinga tashi ba kuma...." Khaleel ya kallesa bai dai ce komai ba, Zayyad ya girgixa kai yace "But I don't think a governor will give you his daughter hands in marriage, duk wanke kan da xa ayi kuwa" Shi dai Khaleel bai ce masa komai ba still. Khaleel na dakin Junaid har bayan isha yana wasa da Fadil da Affan din Amira, Zayyad tun da aka yi isha bai shigo ba, Bude kofar dakin aka yi ya daga kai, Heedayah ce tsaye daga bakin kofar tace "Ya Khaleel wai ka sakko downstairs" bata jira cewarsa ba ta juya ta wuce, tare da su Fadil ya sakko, ya tadda Dinar da Amira sai Farida da wata cousin sister dinsa Sumayya xaune parlon, sai kallonsa Sumayya take har ya shigo parlon ya xauna su Fadil na makale da shi, Amira na murmushi tace "Kana ta xaune kai kadai daki" Khaleel yyi murmushi yace "Gashi muna hira da boys"





Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Washegari da safe misalin karfe tara Heedayah da Farida da Maid din Mami na serving din bak'in dake parlor breakfast na soyayyen Irish, kwai, shayi da farfesu with bread, yawanci duk cousins da aunt din Khaleel ne da kids dinsu a parlon, kana ganinsu dai kasan babu ta inda suka hada hanya da talauci, Mami ce ke ba su Farida breakfast din su kai parlor ita tana tsaye kitchen din, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da katon jakarta ta yafa katon mayafi, ga sarkan zinarinta sai sheki yake a wuya da dankunnensa, tsaye tayi bakin kofar ta dinga bin mutanen parlon da wani kallo, can tace "Ya haka kamar ana yunwa, tun fa daga iyafot motocin sojoji dake bayanmu ke jiniya ana sanar da jama'a xuwanmu ana ta bamu hanya har muka shigo anguwar nan, ku baku ji bane?? Yanxu ta ina xa mu bi mu wuce ta nan duk dankali da kwai, matar gwamnan kano da mu ne fa ke tafe tun daga kano, a jirginsa na kansa kuma aka dauro mu aka kawo mu nan garin, muna dira iyafot motocin sojoji suka hau jiniya ana sanar ma kowa ana ta bamu hanya a titi, to kuma mun shigo gida bbu hanyar wucewa don Allah" Mami ce ta fito daga kitchen jin muryar kaka, da fara'a tace "Sannu da xuwa kaka" Ta bayan kujera kaka ta bi ta tana taku dai-dai ta wuce sama, Duk occupant din parlon suka bi ta da kallo, Yakumbo ta shigo parlon ita ma tana kare ma parlon kallo ta rike ha6a tace "Al'adar bahaushe dai ba kyau, komai dai ace sai anci abinci, gidan mutuwa abinci, gidan biki abinci, gidan suna abinci, daga bayyanar yaro ma an xo jaje an hau cin abinci, to mu dai rabon mu da abinci wllh tun jiya da daddare, yau da safe ma da kaji muka karya muka sha yagwat muka kamo hanya abun mu" Mami dai tsaye tayi tana kallonta ta kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, Ammin Heedayah da frnd dinta na tsaye balcony ko wannensu ya kasa shigowa, Yakumbo ta bi hanyar da kaka ta bi sai kuma ta juyo da sauri tana kallon mutanen parlon tace "Ina kwanan ku?" Few daga cikinsu ne kadai suka amsa, tace "Ya muka ji da wnn abun al'ajabin?" Bbu wanda yace mata komai, tace "Toh Allah ubangiji ya raba mu da duniya lafiya, ya kare 'ya yanmu da jikokinmu da tatta6a kunne da hihihin, su kuma wa enda suka cuci wnn yaro Allah yyi kasa kasa da su ya tsine masu albarka, ya bi masa hakkinsa, tunda iyayena suka haifeni ban ta6a jin irin wnn labarin ba sai jiya, ni dai dama ina ganinsa nace yyi kama da yan kinnafas to ile ga maganata nan ashe D'an kinnafa dai Rahinah ce ta haifesa, kuma duk wanda ya ta6a xaginta a kan d'an nan nata sai Allah ya saka mata ya bi mata hakkinta don ba ita ta aikesa ba, ba ita ta saka sa ba" daga haka Yakumbo ta wuce sama, sai a snn Ammi suka shigo parlon, Mami tayi murmushi tana welcoming dinsu, Ammi ta xauna nan parlon suka gaisa da mutanen dake ciki snn suka wuce sama su ma. Heedayah da Farida ne suka kai masu breakfast sama suka yi masu sannu da xuwa, Yakumbo ta sa Farida ta hada mata shayi tana kallonta tace "Toh ina shi d'an uwan naki yake?" Farida tace "Yana nan" Kaka tace "To yanxu ya isilin dukiyoyin jama'ah da ya kwamushe fa" Farida dai bata ce komai ba lkci daya jikinta yyi sanyi, Heedayah ta hade rai, Kaka ta fara matsar kwalla tace "Haka kawai a rabaka da d'an ka tun yana dan yaye a tafi a daurasa a muguwar harka, anya mutanen nan xa su wanye lafiya da duniya kuwa? Toh yanxu ya xa mu yi mu rabasa da wnn mugun hali da yake yi, sun fa riga sun cucesa halin ya shigesa, sai dai kawai ya yaudare mu yyi tuban muzuru, wataran yana iya koma tunda ya ji dadin rike makudan kudi, mu ma kanmu ba wai tsira muka yi ba, ga gwalagwalai na rataye a wuya da kunne, to ni dai ba ruwana ya xo mu gaisa inyi ta kaina in wuce gidan Amadu" Tagumi Ammi tayi bata iya tace komai ba, Heedayah ta mike ta fice daga dakin hawaye har ya kawo idonta, Mikewa Farida tayi ta bi bayanta ita ma, Ammi tayi kasa da murya tace "Haba kaka?" Kaka ta juyo da sauri tace "Haba me?? ban tsine ma shegun da suka sa shi a harkan bane xaki ce min haba? Meye nawa daga fadan gaskiya? Wllh idan bamu yi taka tsantsan ba sai ya iya yashe mu cikin dare" Yakumbo tace "Toh uwar me xai yi da gwalagwalanki na karya shi da ya saba kwamushe manyan motocin jama'ah masu tsada da gidajensu? Meye kuma gantalallun gwalagwalanki" Mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin ita ma ranta bai mata dadi ba, Kaka ta ta6e baki tace "Ni dai ba ruwana, to gidan uwata ce nan din da baxan wuce gidan Amadu ba dama? Daga cewa xanje in gaida Amadu sai cibi ya xama kari? Ita kuma waccan figaggiyar kamar kazar Hausa ni ta banke ma kofa wai ta fita, to wllh Amadu ta banke ma kofa ba ni ba, ina ruwanta da d'an mutane da xata ji haushi don na fadi gaskiya a kansa, ko meye hadinta da shi, kuma ai dole dama sai mun hada masa da rokon Allah idan kuwa ba haka ba muna nan mun saki baki xai ci gaba da danyen aikinsa a boye, Allah dai ya saka masa amma kam an cucesa wllh, Amadu dai yace yau yan sanda xa su je su kwashe sauran shegun yan uwan nasa" Yakumbo tace "Toh ai banda uwarsa mutuniyar kirki ce dama babu abinda xa mu xo yi gidan nan mu ja ma kanmu salalan tsiya, barin ma ya ji daga gidan gwamnati muke, ni duk a tsorace nake ma wllh...." Kaka tayi tagumi tace "Ga mu ga Allah dai" Asiya kawar Ammi sanin halinsu bata ce masu uffan ba sai operating waya take, Bude kofar dakin aka yi Mami ta shigo Khaleel na biye da ita, daga kaka har Yakumbo suka yi tsit sai yan idanuwa, Mami ta xauna, shi kuma ya duka nan gabansu ya gaishesu da ladabi, babu warce ta yrda ta hada ido da shi, kaka sai cewa take "Sannu d'an nan, yau dai na takura uban Heedayah ya ara mana jirginsa mu taho dai kada Rakiya ta kullace mu" Yakumbo tace "Wllh kuwa, Allah ya bi maka hakkin ka, Allah ya saka maka, an xalunce ka kam, an bata maka rayuwar ka" Kuka Yakumbo ta saki, Kaka ma ta fara matsar kwalla tace "Ni da xa a kai ni wajen 'ya yan shegun sai in ji dalilin da suka daukesa bayan kashe ubansa da suka yi, nasan xa su fada min, tun muna yara ake mugunta a duniya har yau ba a saduda ba, wnn tsiya da me yyi kama???" Mikewa Mami tayi ta fita, Kaka na share idonta tace "Tashi ka tafi kai ma, Allah ya saka maka kawai" Mikewa Khaleel yyi ya fita daga dakin, Yakumbo na kallon kaka tace "Toh yanxu meye hukuncin uban dukiyoyin da ya tara ta muguwar hanya?" Kaka ta gyara xama tace "Hukuncinsu a raba ma marayu kawai, ga dai mu nan da yawa a duniya ba iyaye tun muna yara" A ranan yawanci relatives din Khaleel dake Abuja duk suka koma, gidan ya rage daidaikunsu da xa su koma gobe. Da yamma Ammi da frnd dinta na xaune dakin Mami, Hajiya Zuwaira da Aunt din Khaleel ma duk suna dakin, Yakumbo da kaka na can dakin da suka fara sauka bbu wanda ya tafi inda suke balle yaji kayan takaici, Aunt din Khaleel tayi breaking din silence din dakin tana kallon Mami tace "Toh Allah ubangiji yasa mu ji alkhairi, Allah ya baku nasara" Ammi tace "Ameen" Hajiya Zuwaira tace "Ae tunda aka samu aka cafkesu gaba daya anyi mai wuyar ai, amma shi abokin Khaleel din ya isilinsa ynxu?" Mami tace "Barrister yace ya bar garin, yanxu haka yana Bauchi" Hajiya Zuwaira tace "Toh amma a record din ai shi Aliyu ya ambaci sunansa, kinsan kuma dole a kotu xa a bukaci ganin abokin nasa da ya ambata" Mami tayi murmushi tace "Barrister ya so yanke wajen nace kar yyi, idan suka bukaci Zayyad a court din xa mu kirasa ya xo, kuma xa mu yi iya kokari na ganin mun wankesa shi ma idan Allah ya yrda, sure xai yi iya yiwuwa yyi xaman gidan yari na kankanin lkci but not life imprisonment, shi ma Aliyun hakan xai iya faruwa da shi" Hajiya Zuwaira tace "In sha Allah kotu xata yi masu adalci da taimakon ku, hakan ma baxai faru ba" Mami dai bata ce komai ba, A hankali Ammi tace "Allah xai baku nasara in sha Allah" karfe biyar kaka ta bude kofar dakin Mami tace "Toh Rakiya mu dai xa mu wuce gidan Amadu mu kwana" Mami tace "Baxa ku kwana nan ba kaka?" Kaka tace "Mu kwana nan kuma? Oh oh gwara mu je gidan Amadu nan jama'ah sun maki yawa, ga dai motoci can waje duk inda xa mu a Kaduna xa su kai mu ai" Ammi tace "Baxa ku bari mu tafi can din gobe ba daga can sai mu wuce?" Kaka tace "D'a na ne fa Amadun? In xo har Kaduna in kasa xuwa gidansa in kwana, lalacewata bata kai haka ba Aisha, mu dai ba mun xo mun jajanta abinda ya faru ba, kuma gashi sai wani hade rai mutumin yake kamar baya son ganinmu a gidan mun rasa me muka masa, ba gwara mu san inda dare yyi mana ba kada mu je abu ya lalace mana tsakar dare a shiga uku" bbu wanda yace mata komai dakin ta juya ta fita, Mikewa Mami tayi ta fita tayi masu sallama ita da Yakumbo, Mami na kallon Heedayah dake parlor tace "Collect the bag for them" Heedayah dai bata ce komai ba, Farida tuni ta dauke kai dama, can dai Heedayah ta mike babu walwala ta amshi ledan hannun yakumbo, xata amshi jakar kaka kaka ta makale a hammata tace "Aa bar min kayana, kina hararana xaki wani amsar min jakata ki saka min mugun abu, meye hadina dake banda kawai muna mutunci da ubanki ya takura sai na dawo gidansa da xama kwata kwata, tun fa maganar da aka yi daxu a daki shine take ji kamar ta caccake mu da wuka" Yakumbo ta nufi kofa Kaka ta bi bayanta, Mami dai ta bi su da kallo har suka fita sannan ta koma sama, Sumayya na kallon Farida tace "Who are they?" Farida tace "Yan uwanmu ne" Sumayya bata kuma cewa komai ba sae ta6e baki da tayi. Khaleel na xaune compound din gidan tare da Junaid suna hira sama sama, su kaka suka fito tsakar gidan, da sauri kaka ta dauke kai ta nufi gate, Mikewa Junaid yyi bayan ya ajiye glass cup din drink dake hannunsa yana kallon Khaleel yace "Mu je kayi masu sallama" Mikewa Khaleel yyi ya bi sa, Sojojin dake bakin gate tsaye suka ba su Yakumbo hanya suka fita gate din, waje ma sojojin tsaye ne sai lafiyayyun motoci biyu da motar sojoji a baya, ganin Khaleel Yakumbo tace "Ae da baka ba kanka wahala ba d'an nan" Kaka na kokarin shigewa cikin mota Junaid yace "Xa ku tafi gidan Abba ne Kaka?" Kaka ta shige motar tace "Ehh Junaidu gwara mu je can din dai kawai ya fi mana" Yakumbo ma ta shige motar, Khaleel yyi kasa da kai yace "Allah ya tsare" kaka ta daga masa hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login