Showing 147001 words to 150000 words out of 275313 words

Chapter 50 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

dariya...." Heedayah ta jingina da cabinet din kitchen din ta langwabar da kai tana kallonta so amazed, sae kuma ta fashe da dariya tana tafe hannu tace "Tell me something, really??? But ai in dai kina son uniform din da gaske to son wanda ke cikin uniform din ba abu bane me wahala, Kinga perfect match kawai, bari ki ga inda xa ki kai sa idan kun tsaya yin pre wedding...." Ganin Farida na kokarin ajiye tray din hannunta Heedayah ta fice da gudu tana kyalkyala dariya ta wuce sama, Shuraim ya bi ta da ido.




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Farida ta fito ta ajiye masa abincin ita ma ta wuce sama, da ido ya bi ta, can ya kalli agogon wrist din sa ya ga bakwai da rabi, ya dau bottle water da ke saman tray din kawai ya mike, fita gidan yyi, yyi wucewarsa. Washegari Tuesday da sassafe wajen shidda da rabi Mami na kitchen tare da Farida da Heedayah suna hada breakfast, Zainab Mai aiki kuma na gyaran gida ta gama shara tana mopping aka bubbuga kofar parlor, Zainab ta ajiye mopping stick din tafi ta bude kofar, kaka ce tsaye da katon jakarta a sakale a hannu, Zainab ta duka ta gaida kaka, kaka ta amsa tana kokarin shigowa parlon tace "Ina Rakiyar, duk tsiyarta dai na san bata fita opis ba yanxu" Zainab tace "Tana kitchen" Kaka ta ajiye jakar hannunta ta wuce kitchen din, Washe baki tayi bayan ta shiga tace "Ina kwana Rakiya" Mami na kallonta da mamaki tace "Aa, daga ina da sassafe haka kaka?" Kaka tace "Gidan Umaru mana, ai bani da wani gun bayan nan" Mami tace "Ikon Allah, amma kawo ki aka yi dai ko" Kaka ta marairaice tace "Wa na ajiye xai kawo ni Rakiya?? Kamar dai suna tsorona, d'an adaidaita na samu ya kawo ni har nan, na basa nera dari don ya mun mutunci, kuma kinsan na samu kudi sosai da bikin nan shine ma na xo nuna maki kudin ko xa ki bani shawara in siya fili" Mami tace "Aa gaskiya kam gwara ki siya fili in dai kudin na da yawa Kaka" Kaka tace "Yawa kai, ya kusa dubu talatin da biyar fa, don ma ina xara kadan kadan" Mami ta dauke kai tana ci gaba da yanka green pepper da take yi tace "Ehh kam da yawa gaskiya, sai ki ba ko Baffa ko Barrister wani ya samar maki fili a anguwa me kyau" Kaka tace "Shkkn kuwa, shi yasa na fi son inyi shawara da ke a kan kowa, baki da kyashi, kinga idan da canji ma sai su maido min kayana don ba basu xan yi ba, ynxu dai xuwa nayi in maki bangajiya duk da dai a gantale muka dinga ganin ki gidan bikin, daga nan kuma bayan na karya sai wnn yara su rakani gidan Amadu inje can shima inyi masa ban gajiya, miliyan daya ya bada tasa gudunmawar wllh, in gaya maki gadaje bibbiyu aka yi ma yaran, shi dai Amadu yace bashi da kudi ynxu... amma ga miliyan daya ayi duk abinda xa ayi, ke kuma naji labarin kin basu dubu dari ko? Kawun Junaidu bai bada ko sisi ba duk kudinsa" Mami tace "Aa dubu dari biyu ya saka ma Junaid ya kai masu" Kaka tace "Abu ya lalace, ya cinye kenan wllh don kwandala bai kawo masu ba" Mami tace "Aa ya kai masu Ina gidan ma ya kawo, ki tambayi shi Baffan" Kaka tace "Atoh da kyau... Toh duk Allah ya saka, Allah ya nuna mana na 'yan baya, yanxu sai ayi harin na Farida nan da yan watanni ko?" Mami bata kuma ce mata komai ba, Farida da Heedayah suka gaida kaka, kaka ta amsa tace "Toh kuyi maxa mu karya mu wuce gidan Amadu shi ma kafin ya fice" daga haka ta juya ta fita kitchen din tana cewa "Ita wancan xalben ma ban ganta gidan yinin ba, tana fama da tsayi kamar daren sllh" Sai da kaka ta ci tayi nak sannan ta kishingida a parlor tana jiransu Farida su shirya su wuce gidan Abba, Mami ta shigo parlon tace "Kaka ko xa ku tafi da Farida kawai, don Heedayah bata wani jin dadi, kafin in tafi aiki xan fara ajiyeta a asibiti" Kaka ta mike xaune da sauri tace "Aa Rakiya ki rufa min asiri don Allah, ga dai likita Shureen a can gidan na samu labarin yana nan da safe yawanci, ba sai kawai ya dubata ba, amma ni dai dole da ita xan tafi, yaushe rabon ta je gaida uban rikon nata?? Ki dinga abu sbda Allah mana Rakiya" Komawa tayi ta kishingida bata kuma cewa Mami komai ba, Har ta fara gyangyadi ta bude ido da sauri jin ana gaisheta, Junaid ta gani xaune yana kallonta, tace "Kana gidan dama Junaidu?" Yace "Ehh nan na kwana" Kaka tace "Shikenan ya xo gidan sauki bbu ni bbu fada da masu adaidaita sai ka ajiyeni gidan Amadu kawai" ya kalli agogo yace "Toh amma yanxu xa mu tafi sbda aiki xan wuce" Kaka ta mike da sauri tace "Toh me nake jira, wa encan rubabbun ne idan basu gama ba muyi wucewarmu kawai ban iya wahala" daga haka ta dau jakarta ta nufi kofa, bin ta yyi da kallo snn yyi murmushi ya mike ya bi bayanta. Bata yadda sun tafi ba duk da Junaidu yyi kokarin convincing dinta don baya son Heedayah taje gidan amma kaka tace sai dai ya sauketa ita baxata iya wahalansa ba, sai da Farida da Heedayah suka fito snn hankalinta ya kwanta, Farida ta bude front seat ta shiga, Heedayah ta xauna tare da kaka a baya, kaka tace "Wnn ai walakanci ne kawai daga ku yi wanka ku sa kaya sai ku bar mu a walakance a mota muna jiran ku, ko ita Rakiyar ce tace ku dade??" Ganin Mami kaka tayi shiru, Mami ta karaso gun motar tace "Toh Allah ya tsare kaka, mun gode" Kaka tace "Yauwa Rakiya Allah yayi maki albarka, in sha Allahu anjima xan dawo maki da su ni ma ban fiye son xama gidan mutane ba ai kin sani, ko da azahar ne Shureen sai ya dawo da mu gaba daya mu ajiye su ni kuma ya maida ni gidan Umaru tunda can nafi wayo" Mami tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye" daga haka ta koma ciki, Kaka tace "Toh Ameen dai" Junaid ya ja motar suka bar compound din don Mai gadi ya riga ya bude masu gate, Farida na kallonsa tace "Ina kwana Yaya?" Yace "Lafiya lau" Heedayah ma tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" kaka ta tabe baki tace "Abun bai yi ba oo, dama baku san yana gidan bane? Tun wayewar gari sai ynxu xaku ce Ina kwana" Junaid yace "Duk sun shiga daki kafin na dawo jiya, so basu san ina gidan ba ma" Kaka tace "Ni duk sai na ganka wani iri Junaidu, ko baka da lafiya ne" yace "Lafiyata qlau" kaka tace "Toh ku ma dai ku yi kuyi ku fiddo da matar nan dai a maku aure ku bar yawo a titi bakwa wancan gida bakwa wannan gida, auren shi ya fi maku daga kai har Shureen, don shi Sudais naji uwar na cewa cikin shekaran nan ne idan Allah ya kai mu, dama shi me yan mata ne iri iri, xaba kawai xai yi ya darje" Murmushi kawai junaid yyi, Kaka tace "Ba abun murmushi bane, har da rashin auren ke damun ka kai da Shureen, Kai kuma naga ai wayayye ne a kan Shureen da yake nan dunkum, Kai baxa ka rasa yan matan ba ynxu hka, shi kuwa Shureen da kyar idan ba hadin gida xa ayi masa ba, idan ba haka ba kuwa sai yyi shekara hamsin bbu aure, duk da dai shi da maganarsa da wata yarinya a kasa don har naje na nemi alfarman a bamu ita gidan iyayen yarinyar kuma sun amince, sa rana kawai ya rage idan yarinyar ta gama karatun sakandari, ta ma kusa gamawa" daga Farida har Heedayah kallon kaka suke, Junaid ya kalleta ta madubi kawai yyi murmushi bai dai ce komai ba, Heedayah tace "Da gaske kaka?" Kaka tace "Wllh, ai maganan ya fi shekara uku ynxu..." Heedayah tace "Kuma ya san maganan?" Kaka tace "Haba wane mutum, ai baxa a bar sa ya san da maganan ba, ni dai ai ban biye ta rashin kunyar da yake min ba nayi masa gata a matsayin warce ta haifi ubansa, Amadun ma yasan da wnn xancen kuma" Heedayah ta kyalkyale da wani dariya tace "Allah ya sa kwanan nan xa ayi" kaka tace "Aa baxai dau lkci ba dama" Farida tace "Toh auren dole xa ayi masa kenan" Kaka tace "Kaji gantalalliya, auren dole ai tun xamaninmu aka daina, ai baxai ki yarinyar ba tunda tana da kyau kamar uwarta, Allah na tuba me xai nuna mata banda matsayinsa na soja, ai son kowa ce k'in wanda ya rasa" Heedayah ta kara kyalkyalewa da dariya, Kaka tace "Ke ma auren xa a maki kwanan nan ai" Ta dakatar da dariyar da sauri, Junaid dai sai kallonsu yake, ta turo baki tace "Yar yarinya da ni" Kaka tace "Wace yarinya, bayan naji labari a wajen Rakiya kin fara al'ada" Farida ta kauda kai tana dariya kasa kasa, Heedayah tayi shiru bata kuma cewa komai ba, kaka ma tayi shiru jin kowa yyi shiru. Suna isa gidan Abba Junaid yyi parking a waje, kaka tace "Toh Alhamdulillahi Allah ya maka albarka Junaidu, Allah ya nuna min bikin ka" Daga haka ta sauka motar Heedayah ma ta sauka Farida ma ta sauka, Farida ta daga masa hannu tace "Allah ya kiyaye" Heedayah ta kallesa tace "Sai anjima" ya gyada mata kai ta bi bayan kaka da har ta shiga compound din. Hamdala kaka tayi ganin motar Abba da na Shuraim, ta wuce ciki tana cewa "Allah ya so ni, idan Amadu ya fita ai xuwan banxa nayi kenan" Abba ya fito parlonsa cikin shigar fita office tare da Shuraim dake rike da brief case dinsa kenan kaka ta shigo parlon Heedayah na biye da ita, Kaka ta washe baki tace "Sannu Amadu Ina ta sauri kar ka fita, Allah ya so ni...." Kallon Heedayah kawai Abba yake, hakan ya sa ta karasa inda yake tsaye ta rungume sa cikin sanyin murya tace "Abba..." Kaka tace "Atoh, ai Rakiya ta shiga uku ta lalace, ta tarwatsa xumunci" Abba ya d'an yi murmushi ya maida Heedayah gefensa yana kallonta yace "How are you" tace "I'm fine good morning" Yace "Ya karatu" tace "Alhamdulillah" Farida ta karasa ita ma ta gaida Abba da ladabi, ya amsa da murmushi yace "How are you Farida" tace "I'm fine sir" Abba yace "That's good" Kaka ta tafi parlor ta xauna tana cire hijab din jikinta tana kara gode ma Allah ta samu Abba, Abba ya karasa ya xauna ya gaisheta tace "Lafiya lau Amadu ya taro? Fatan duk kun watsa su lafiya" Yace "Alhmdllh" kaka tace "Toh Allah ya maku albarka ya mayar maku da dubun abinda ku ka kashe, saura na wnn yaron naka Shureen kuma" Shuraim dake ta tsaye ya kalleta ta gefen ido, Abba dai yyi murmushi ya mike yace "Na makara Baaba, kuna nan har in dawo ai" Kaka tace "To ina xa ni? Ai ina nan in sha Allahu har ka dawo, yi tafiyar ka Allah ya tsare" Yace "Ameen" hannun Shureen ya amshi briefcase dinsa yace "You didn't greet her" Shureen ya karasa parlon yana kallonta yace "Ina kwana" kaka tace "Lafiya lau, jiya ka kai ma Rakiya su dubulan da alkaki da cincin din kuwa, naje gidan na manta ban tambayeta ba wllh" Wani kallo ya mata bai ce komai ba, Abba na kallon Heedayah yace "Sai na dawo" Tace "Allah ya tsare Abba" ya amsa da "Ameen" Farida tayi masa Allah ya tsare ita na snn ya fita parlon, Farida da Heedayah suka dawo parlon suka xauna, kaka tace "To ita Maryam din bin ta xa mu yi parlonta kenan, toh ai bbu komai ku tashi mu je, mu ba bakin xafi bane, baxan biyeta ba, amma kuma ban ji kun gaida Shureen ba" Farida ta mike ganin kaka ta mike, tace "Ina kwana" Heedayah ma ta tashi tace masa "Ina kwana" Duk bai amsa masu ba, Suka bi bayan kaka xuwa parlon Mumy, Mumy ta fito bedroom dinta kenan ganin kaka ta d'an canxa fuska tace "Kaka ce..." Kaka tace "Wllh ni ce, ina ta sallama shiru, ashe kina can ciki" Mumy juya xata rufe kofar dakinta tana yatsine yatsine tace "Ehh ina ciki" Heedayah ce karshen shigowa parlon, Farida ta xauna kusa da kaka, Heedayah ta xauna gefenta duk suka gaida Mumy, lkci daya fara'a ya bayyana fuskar Mumy ganinsu tace "Aa ashe baki muka yi hka, to sannun ku da xuwa" Kaka tace "Ehh cewa suka yi sai sun xo sun gaishe ki, su Rabi'ah kuma can na barosu gidan Umaru basu ma san xan yo nan ba" Mumy na washe baki tace "Allah sarki, Sannun ku da xuwa, bari a kawo maku breakfast" Kaka tace "Aa ni kwai kawai xa a soya min, idan akwai d'an farfesu a hada min da shi, kwanan nan ba wani cin abinci nake ba" Daga Farida har Heedayah suka kalleta, Mumy tace "Toh su kuma 'yan matan fa" Kaka tace "Su ma soya masu kwan kawai a hado masu da d'an dankali" Farida tace "Aa mu mun koshi" Kaka tace "Da yake sun karya su" Mumy bata ce komai ba har ta fita parlon sai kuma ta dawo ta shiga bedroom dinta tace "Bari in maida wayata caji" rufe kofar dakin tayi ta nemo wani karamin purse dinta da ta adana sosai ta bude ciki ta dau wani kullin xani, ta fi minti daya tana kallon kullin da xai yi shekara uku a ajiye cikin jakar, "Ko nan da shekara goma ne bbu abinda xai hanasa aiki" murya wanda ya bata ne ke dawo mata, tayi wani murmushi ta kunce habar xaninta ta kulle kullin maganin a jiki snn ta daura xanin ta fito parlor tace "Sannu kaka, bari in je inyi masa in soya maki" kaka tace "To yi maxa" daga hka ta fita parlon, tsaye ta ga Shuraim har sannan a Main parlor, Tace "Aliyu tun da sai yamma xaka fita bari in baka sako ka kai ma Hajiya Sadiya yanxu..." Ya kalleta yace "Akwai aikin da nake yi ban gama ba, ki bada sakon idan na fita anjima sai in kai mata" Ta wani hade rai tace "Toh ni yanxu nake son ka kai mata ba sai anjima ba" Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, sauke ajiyar xuciya yyi ya xauna saman kujera, Mumy na tsaye kitchen ta sa mai aiki ta soya lafiyayyen kwai da ya ji albasa da tsire a ciki na kaka, sauran tsiren kuma ta saka a plate daban daban guda biyu, tana kallon Mai aikin tace "Duba min Shuraim na parlor ne" Mai aikin ta fita ta dawo tace "Aa baya nan" Mumy ta dau plate din kwan kaka ta mika mata tace "Ki kai ma kaka, idan tace wa ya soya kice ni ce.... Sai ki tafi ki ce ma driver yyi wucewarsa nayi baki sannan ki dawo ki kai ma yan matan nan tsire" Mai aikin tace "Toh Hajiya" daga haka ta nufi kofa ta fita, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofar, kallon window din kitchen din tayi snn ta kai hannu gefen xaninta, cikin few minutes ta gama abinda xata yi ta barbada ma naman yaji snn ta dau plate din biyu ta fita xuwa parlonta, ta ajiye daya gaban Farida, na hannun hagunta ta ajiye ma Heedayah tace "Naji kaka tace kun karya wnn kuma ai abun marmari ne, da asuba nayi ma Barrister ashe baxai ci ba, wnn nawa ne da na Shuraim, shi ma nasan ba lallai ya ci ba" Kaka tace "Atoh, rabonsu ne, ku yi maxa ku ci"





Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Mumy ta nemi kujera ta xauna tana murmushi, labarin biki da abubuwan da suka faru suka dinga yi da kaka, kaka ta saki baki sai xuba take, Mumy tace "Ai ni kin kyauta min da kika ce a sauke canopy din nan, mutane basu da hankali wllh" Kaka tayi fuska kamar 'yar yarinya tace "Lallai, haka kawai a lalata min motocin yaro, uban waye ya siya masa, kiris ya rage wnn suntumemen ya gogi motar da karfen fa, ba ruwana ni dai na koresu, wanda suka kafa a bakin titi bai isa ba sai an shigo mana gida da katon lema a kakkafa" Mumy tayi 'yar dariya, sai kuma ta kalli su farida tace "Ku ci mana kar ya huce da xafinsa kuwa" Farida ta ajiye wayarta da take dannawa tace "Na koshi ni" Mumy ta hade rai tace "Kin koshi kamar Yaya, hanaki cin abinci aka yi a nan din idan kun xo" Kaka tace "Aa babu wanda xai hanata, da yake kinsan sun karya kafin mu fito" Mumy tace "Aa to gaskiya baxan ji dadi idan basu ci ba tunda da kai na na kawo masu" Kaka ta kalli farida tace "Ko kwara daya ne ki ci kar taga kamar an hanaki, nasan a koshe ku ke" Mumy na kallon Heedayah tace "Ita idan ta ki ci ai ke bakya ki ci ba, dau plate din ki ci abun ki" Heedayah tace "Ahh haba wnn ai Mayyar nama ce xata ci nasani" Heedayah ta kalleta bata dai ce komai ba, Mumy tayi dariyar da bai kai ciki ba tace "Dauka ki ci Heedayah" Heedayah ta sauke idonta tana kallon naman tace "Mumy na koshi, mun yi breakfast a gida kafin mu fiti" Mumy ta d'an hade rai tace "Nama abinci ne? Bana son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login