Showing 168001 words to 171000 words out of 275313 words

Chapter 57 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

gwara ta tafi kawai kafin ya dawo ya ka ita gida. Murda kofar tayi ta ji a rufe, kamar xata yi kuka ta dinga kallon kofar, ta sake murdawa bai buduwa ba, a hankali ta juya ta koma sama duk jikinta a sanyaye ta dau abubuwan da ya ajiye mata saman gado ta shiga bandakin, ko da ya dawo bata fito ba ya ajiye mata ledan hannunsa kan gadon sannan ya fita dakin ya wuce nasa, har ya sakko wajen karfe goma bayan yyi wanka ya shirya Heedayah bata sakko ba, sai kallon agogo yake don ya kagu ya ga ya mayar da ita gida, daga karshe ya mike ya wuce saman, karo suka kusa ci xata sakko ya koma baya yana kallonta, sosai bakin abayar yyi mata kyau kamar ya aunata kafin ya siyo, ya sakar mata murmushi yace "U look cute" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Taho kiyi breakfast lkci na wucewa" bin bayansa tayi suka koma kasa, ya hada mata shayi ya bata fried Irish with egg and ketchup da ya siyo, yace "Do you take bread?" Ta girgixa masa kai, shayin ta fara shanyewa gaba daya, ya buda ido yana kallonta yace "Why?" Tace "Haka nake yi" yace "You need more?" Ta girgixa masa kai, jawo plate din Irish din tayi ta fara ci a hankali, ya d'an yi murmushi ya hada shayinsa da iyakarsa bai kai rabin cup ba ya fara sha, yace "Ina xa ki ce ma Guardians dinki kin tafi idan na mayar da ke yanxu Heedayah?" Ta kallesa bata ce komai ba, lkci daya ta kasa ci gaba da cin dankalin, ganin hakan yace "Why are you not eating" bata ce masa komai ba ta ci gaba da ci without appetite, har cikin ranta bata son xancen gida, daga karshe ta tura Irish din ganin ya fice a ranta gaba daya, ta koma saman kujera ta xauna ta jinginar da kanta da kujeran, da ido ya bi ta yace "What's wrong Heedayah?" Ta girgixa masa kai tace "Nothing na koshi" Kafin yace komai tayi saurin cewa "Wannan shayin ne xai isheka?" Yace "Baxan ma shanye ba" Tayi shiru tana kallonsa bata ce komai ba, a hankali kuma tace "I saw u with gun yesterday, waye ya baka" kallonta yyi da sauri coz her question came unaware, sai kuma ya sauke idonsa kasa cikin cool voice dinsa yace "My father, you know.... he is a soldier, da naji barayin sun shigo shine na tafi dakinsa na dauko bindigar" Yana iya ganin tsoron da ya bayyana fuskarta lkci daya, ya ajiye sauran shayin da ya rage ya mike yace "I need to get u back home Heedayah, nasan hankalin kowa ya tashi yanxu, ki saka kayan ki da kika cire a leda ki sakko da shi mu tafi" Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa babu, gabanta na faduwa kuma sosai, ganin jiranta yake tace "Na saka a leda...." yace "To dauko su" tayi narai narai da ido cikin tsigar shagwaba tace "Ni baxan iya xuwa sama ba kuma, my legs a paining me, ka dauko min" ya kai minti daya yana kallonta can yyi murmushi ya wuce saman ta bi sa da kallo har ta daina hangosa, mikewa tayi da sauri ta tafi ta saka takalminta ta fice daga parlon da ya bari a bude bayan shigowarsa daxu, kusan da gudu ta isa gate shi ma lock kawai ta bude ta fice daga gidan gaba daya, mota ce tayi parking dai dai gate din gidan, tana kallo har wanda ke cikin motar ya sakko, kallonta ya dinga yi, taki yarda su hada ido ta nufi hanyar da take tunanin xai fitar da ita daga anguwan da sauri, da ido ya bi ta har tayi nisa snn ya shiga gidan, ya bude parlon ya shiga, daga kitchen Khaleel ya fito yana neman Heedayah, ya tsaya kallon wanda ya shigo parlon, Zayyad yyi masa wani shegen kallo sai kuma ya kyalkyale da dariya yace "I am happy for you frnd, ko ba komai kai ma xaka bada labarin wacece mace tunda ka kwana gida daya da mace yau, sai dai you are in great risk Brainiac, Mu ma ba wai bama harka da mata ba, but we still concentrate on our goals, kai kuma da yake sabon shiga ne, it's causing you much distraction, ga mata iri ri sai warce ka xaba ka darje a gari, don't be afraid of loosing this one....." Wani kallo Khaleel ya jefa masa xai koma sama neman Heedayah and idan ma ya ganta baxai bari ta fito ba har Zayyad ya wuce, Zayyad yace "Na samu labarin artabun da kayi da su Oga daren jiya, you chop liver Genius... and probably my text message helped, yanxu dai tunda har gari ya waye har kuma yarinyar ta kama gabanta sai mu je ka bada hakuri, I don't want to imagine anything happening to you Brainiac..... But isn't that girl I saw too young for u, anyway sweet sixteen, and she is damnnn pretty with the perfect curves...." Har Khaleel ya fara hawa stairs ya dakata ya juyo da sauri fuska daure yace "And where did u see her??" Zayyad yace "Mun hadu bakin gate xata wuce yanxu" Wani tsalle Khaleel yyi ya duro maimakon sakkowa few stairs din da ya hau yace "Ta tafi Ina?????" Zayyad ya tsaya kallonsa, Khaleel ya nufesa da sauri yace "Answer me plss Zayyad, Ina ta tafi" Zayyad yace "Wahala be like bicycle, I just met with her outside ynxu da xan shigo and tayi hanyar titi how will I know inda xa ta" Khaleel yace "Nooo, why did u let her" Zayyad ya saki baki yana kallonsa yace "Ikon Allah to nasan inda xa ta ko nasan me ya fito da ita" Khaleel ya warce car key din hannunsa ya fita waje da sauri almost running, Zayyad ya bi bayansa with much surprise.

*pls I am begging some people that don't use to reason in the mighty name of God to stop disturbing my peace, ni Khaleesat bana son sharhi daga wanda bai biya kudin karatun littafin nan ba, littafin Heedayah is not free but they are reading for free and they will just comfortably come to u with their bend bend opinion as if it's normal, ko kunya bbu fa, to plss ku ji da hakkin mutum dake kanku ma kadai, swallow ur sharhi, allow those that subscribed to dagger it with me shè oti gbo?* _urs faithfully Khaleesat Haiydar_✍🏻


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Tafiya kawai Khaleel ke yi for almost 20mins kenan a motar Zayyad not knowing the particular direction he is heading to, he just can't believe Heedayah is gone, ya ji hankalinsa yyi matukar tashi, bbu inda ta sani a Abuja snn ba hanyar gida ta sani ba balle yyi assuring kansa gidan ta koma duk da ya san he is just assuming don ba gidan xata ba tunda a dalilin yace xai kai ta gida ta gudu, but is she even alright, ba ayi mata komai ba tace baxata koma gida ba, who does that.... Parking yyi daga karshe ganin ko alamarta bbu, ya jingina da kujeran motar yana kiran Allah a xuciyarsa, yanxu a ina xai nemo yarinyar nan, where is he to start from.... Abba na office kiran Shuraim ya shigo wayarsa, ya dau wayar bayan ya daga ya kai kunne yace "How are you Shuraim" yace "Alhmdllh" Abba yace "Baka dawo Abujan ba har ynxu?" Yace "Eh" Jin yanayin muryar sa Abba yace "Are you alright?" Shuraim ya d'an yi shiru, Abba yace "Hello, are you there" Shuraim yace "I'm fine" Abba bai ce masa komai ba bayan few seconds yace "Ohk then..." Shuraim yace "I called to announce to you that Heedayah is missing" Abba ya ajiye takardan hannunsa after digesting the information yace "Ban gane ba, wace Heedayah?" Shuraim yyi shiru, Abba ya daka masa tsawa yace "Will you enlighten me more" Shuraim yace "She got missing yesterday at Abuja" lkci daya Abba ya mike yace "Me ta je yi a Abuja??" Shuraim yace "Sun yi tafiya da Farida xuwa gun yayar Faridar..... She is still yet to be found tun daren jiya" katse wayar Abba yyi ya koma ya xauna yana jin xufa all over him, can ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyu, bai san lkcn da ya furta "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Heedayah missing??" ya sake mikewa ya dau makullin motarsa ya fita office din. Mumy na xaune main parlor tare da Sadiya kasancewar bbu kowa gidan, su Rabi'ah da Khadijah na can gidan Baffa tunda ba a koma makaranta ba, Hajiya Sadiya tace "Ni wllh shi sa bana son harka s?dake don kin fiye gajen hakuri Maryam...." Mumy tace "Uhm uhm ba gajen hakuri bane Sadiya dubu dari da hamsin fa a wnn marran, ai ko dole in damu, ance idan na barbada maganin a abinci kuma na tabbatar ta ci in koma in sanar, to na koma an bukaci uban kudin nan na bayar to har yau shiru kke ji kamar malam ya ci shirwa, ai dole in damu da zinarin xobe na siya da ba yanxu ina kallonsa a yatsa na ba" Hajiya Sadiya tace "Kai.... wllh wani sae yyi tunanin kudin ya kai wata biyu da kika kai, nan kuma ko kwana biyar ba a yi ba, amma har kin xaku, ke dai kawai idan an maki aiki lkci daya ki ga ya ci kamar yankan wuka, to ance maki haka ake yi? Su ma ba sai sunyi duk abinda ya kamata na kafin aikin yaci, Komai ba d'an hakuri bane dama, ni dai idan kina haka sacce min gwiwa kawai kike wllh sae kace ba musulma ba sbda rashin hakuri" Mumy tayi tagumi tace "Ae baki sani ba Sadiya, wllh tun da na kyalla ido na gan Yarinyar nan gidan bikin su Jamila nake samun sleepless night, duk yarinya ta bi ta xama mace ta ko ina, wnn ai idan ba ayi hankali ba ma 'ya 'yan masu kudi ne xa su dinga tururuwa a kanta, wani d'an me kudin kawai ya aureta, ni kuma haka baxai min ddi ba ai, ta ma ci riban rayuwa da mu bayan tarwatsa nawa rayuwar da tayi knn, auren ne ni bana son tayi kwata kwata gwara ace ta kare a iskanci ma kawai, har yau fa Barrister fitowa fili ne kawai baxai yi ya gaya min ba haushi na yake ji tunda amaryarsa ta ki dawowa, don ma ban barsa haka ba, komai dai na tambayesa xai min kuma ko xan kwana ina masa bala'i baya tankawa, amma ba shi da walwala irin rayuwar mu ta da, shi dai gashi nan ne kawai, ke ni akwai ranan da na dau wayarsa na duba kusan kullum ashe sai yyi ma Rahinar text message, sae dai kawai ni banga tana reply ba, to kin ga kuwa ai bani da babban makiyiya kamar Heedayah" Shiru Mumy tayi da mugun mamaki bayan an bude kofa Abba ya shigo da sallama, Hajiya Sadiya ta amsa sallaman tana masa sannu da xuwa tana sissinne kai kamar munafuka, ya nufi parlonsa bayan ya amsa, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya tace "Ko lafiya ya dawo da wuri haka yau, Allah ya sa kofa dai a rufe yake da na shiga uku, bari in je in ji ko lafiya" mikewa tayi ta wuce parlon Abba, Mumy na kallonsa a bedroom dinsa tace "Lafiya barrister?" Ba tare da ya juyo ba yace "Lafiya lau" tace "Ina kuma xaka haka?" Yace "I will be going to Abuja now" Tace "Ohk aiki?" Yace "Noo, ynxu aka kirani ba a ga Heedayah ba" Still Mumy tayi tana kallonsa da mugun mamaki, lkci daya tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ba a ganta ba kuma? Kamar Yaya? Ina ta je? Kuma me xaka je yi a Abuja ance ba a ga Heedayah ba a nan" Abba bai kuma ce mata komai ba ya dau abinda xai dauka ya fita dakin, Da sauri Mumy ma ta fito amma tuni har ya fita parlon, ganin Hajiya Sadiya bata parlon Mumy ta wuce nata parlon da sauri sanin cewar can ta tafi, kulle kofar parlon Mumy tayi tana kallon Hajiya Sadiya idanuwanta kamar xa su fito tace "Sadiya wai kinji ba a ga Heedayah ba" Sadiya ta mike tsaye tace "Ba a ganta a ina ba?" Mumy tace "Oho ynxu Barrister ke gaya min, ya kuma kiyi min gamsasshen bayani wai yanxu Abuja xai wuce, bari dai in kira Shuraim nasan kila uban ya kirasa" Gaba daya farin cikin Mumy a fili yake, tana neman wayarta tace "Allah ubangiji yasa guduwan tayi da gaske, kuma ta bar gida kenan har abada taje can tayi duniyanci, to ko dai a Abujan ta gudu Barrister xai je, to me ya kai ta Abuja kuwa" Dialing number Shuraim tayi bayan ta ga wayar, har ya katse bai dauka ba, ta kira ya kusa sau hudu snn ya daga, tace "Gidan uwar wa ka shiga nake ta kiranka no answer?" Gaisheta yyi ta amsa ta marairaice murya tace "Yanxu Barrister ke min bayanin da ban fahimta ba shine nace bari in kiraka nasan baxa ka rasa labari ba, Wai yanxu yake ce min ba a gaya Heedayah ba, wace Heedayar tukunna?" Shuraim yyi shiru har sai da tace "Hello" yace "Ehh ba a ganta ba" Mumy ta saki salati da karfi tana girgixa kai tace "Garin Yaya Shuraim, barin gidan tayi haka kawai ko guduwa tayi, innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Yace "Nima ban sani ba" tace "A gidan Rahinar aka nemeta aka rasa" Yace "I don't know Mumy, Abba ke gaya min nima" Tace "Toh Allah ya kyauta, bari in shirya in tafi gidan Rahinar, ba a ga Heedayah ba kuma sai kace allura, yaran yanxu kawai ka haifesu baka haifi halinsu ba, to ina xata ni Maryam?? Ohhh" Shi dai Shuraim bai ce komai ba, ta katse wayar.... ta saki wani shewa da kabbara tana kallon Sadiya baki har kunne tace "Ta shiga duniya Sadiya, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah na gode maka, Allah nagode maka, bari in shirya in je gidan kar a xargi komai Sadiya, tashi mu je" A nan take Mumy ta bar gidan tare da Hajiya Sadiya a motarta xuwa gidan Mami, banda shewa bbu abinda suke cikin mota Mumy ta cika wakar gwanja suna bi a motar, kai kana ganinsu kasan duniya ta masu dadi, Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace "Kai dole ki kara ma wnn mutumi kudi Maryam, yanda kika san yankan wuka haka fa aikinsa yake" Mumy tace "Ai ko na kara masa ban yi asara ba wllh, to ni ko me kudi Heedayah ta aura yarana basu samu haka ba duk da na rabata da barrister ai ci baya ne gareni hakan, amma kinga duk kyan mace tana duniyanci uban wa xai dubeta, ba ga Salima ba dai" Hajiya Sadiya tace "Wnn gaskiya ne aminiya" Mumy na parking ta sauka tare da Sadiya, nan me gadi ya sanar masu ai Mami na Abuja, cike da damuwa Mumy tace "Kawai sai aka nemi yarinya aka rasa, wai garin yaya hakan ta faru" Mai gadin yace "Wace yarinya Hajiya" Nan Mumy ta gane bashi da labari ta ja kawarta suka bar sa tsaye wajen, sai da suka hau saman titi Mumy tace "Bari mu je gidan Dakta nasan baxa a rasa labari a can ba, xa mu ji yanda komai ya faru in sha Allah" haka aka yi suka tafi gidan Baffa, Ko bangaren su Umma Mumy bata shiga ba ta wuce gun kaka, Kaka na wankin bandaki suka nemi waje suka xauna, ta leko jin alamar an shigo mata daki, ganin Mumy ta ajiye roban ruwan hannunta ta fito da sauri tace "Maryam dama turo Rabi'ah da kika yi gidan nan cewa kika yi ta xo ta dinga min rashin kunya tana xagin iyayena?" Mumy tace "Xagin iyaye kuma?" Kaka tace "Wllh kuwa, ni dai nayi mata koran kare nace ta tafi tunda ba ita ta haifa min Umarun ba, yanxu ma sauri nake in tafi in ga ko ta tafi din don wllh baxata kwana gidan d'a na yau ba, tana raina uwarsa uban me xata tsaya yi masa a gida banda ita shashasha ce, ke dai baki iya haihuwa ba, yara duk munana sai baki kamar hancin saniya, shi dai Shuraim Allah ya rufa masa asiri ya yo sa kyakkyawa sam6alele" Mumy da ba abinda ya kawota ba kenan ta dakatar da xancen kaka ta hanyar cewa "Ya muka ji da abinda ke faruwa kaka??" Kaka tayi shiru tana kallonta, can ta nemi kujera ta xauna tace "Me ke faruwa??" Mumy tace "Au wai baki sani ba dama?" Kaka da ta rikice tace "Wllh bani da labarin komai Maryam, me ke faruwa" Mumy ta mike tace "Atoh ba kya ji a bakina ba kaka, tashi mu je Sadiya, na xata ai kin sani ne muka xo jaje" kaka ta rushe da kuka tace "Ni dama ae ba bakin komai ba nake a gidan nan ba, bbu wanda yace min komai, asara aka yi ne bani da labari?" Mumy tace "Aa jita jita ake wai ba a ga Heedayah ba tun jiya da safe, na xata an sanar maki shi sa ma na xo ai" Mumy bata jira cewar Kaka ba ta ja Sadiya suka fita parlon, Kaka ta bi su da kallo kamar warce aka dasa a wajen, can a hankali tace "Wacece Heedayah kuma?" Shiru ta kuma yi na kusan minti daya, sai kuma kamar warce aka tsikara ta rafka wani uban salati tace "Ba a ga wace Deedayar ba kuma? Amma Maryam anyi matsiyaciya, fatan bata take ma yarinyar xata ce ana jita jitan ba a ganta ba, ke ba gidan Rakiya kike xuwa ba, ke bbu hadin ki da yarinyar nan, to meye na xuwa ki gilla karya kice ba a ganta ba kamar wata sakakkiyar akuya, to bakin ki ya sari danyen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login