Showing 126001 words to 129000 words out of 275313 words
Chapter 43 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
amsa yana kallonta suka shiga back seat gaba daya, ya shiga motar suka wuce gida. Farida ta gama hada ma mai aiki kayansu gaba daya da na Heedayah tace "Idan ma baxa ki iya gugan ba idan kin wanke ki bari xan saka Yusuf yyi mana, pls ki wanke mana da kyau sis Zainab" Muryar Mami suka ji daga sama tace "Zainab bar masu kayansu, idan baxa su wanke ba su bar shi, kada kiyi ma ko wani yaro wanki a gidan nan" Farida ta juya tana kallon Mami kamar xata yi kuka tace "Mami jiya fa muka dawo ko hutawa ba mu gama yi ba, sannan I have a lot to read for my coming waec" Mami tace "Kar ma kiyi karatun mana, na dai gaya maki Zainab, kuma kada ku sake ku dawo min da kayan wanki sama, daga nan parlor ku yi waje da shi" daga haka tayi komawarta daki, Zainab dai na tsaye bata ce komai ba, Farida ta tabe baki ta kwashe kayan a fusace tana kallon Heedayah da ta kwanta saman dogon kujera jin abinda Mami tace, tace "Toh baxa ki tashi mu je mu yi ba" Heedayah ta marairaice tace "Farida wllh I am not feeling well kema kin sani" Farida tace "Yes I know but ki taso sai ki dinga dauraya ni sai inyi shanya, if not ni dai baxan maki wanki ba" Turo baki Heedayah tayi Farida ta fita can compound da kayan, Mikewa Heedayah tayi ta dau hularta ta saka don doguwar riga ce har kasa jikinta ta bi bayan Farida xuwa waje, Farida har ta tara buckets din a tap dake tsakar gidan xata fara wankin, Heedayah ta xauna saman Plastic chair, Wanki Farida ta fara yi duk rai ba dadi, ganin ta wanke yafi biyar Heedayah ko motsawa bata yi daga xaunen da take ba, ta fara ware kayan tana maida na Heedayah gefe daya, dariya Heedayah tayi ta sakko tace "Toh yi hakuri Faree" Kamar warce bata da laka ta dinga shafa kayan wai tana daurayewa, ta marairaice fuska, sun yi nisa a wankin aka bude gate duk suka juya, sosai gaban Heedayah ya fadi bayan sun hada ido, Farida ta dauke kai ta ci gaba da wankin da take yi, slowly yake tahowa sanye da kananun kaya, ya sa face cap, camouflage na Soja" Heedayah ta saci kallonsa ganin ya kusa inda suke suka kara hada ido don kallonta yake, sunkuyar da kanta tayi, Farida tace "Good evening" Yace "Evening, Mami na ciki?" Farida tace "Ehh" murya can kasa Heedayah tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" daga haka yyi wucewarsa ciki. Mikewa Heedayah tayi bayan wasu mintuna ta xauna tana girgixa kai tace "Wllh Farida cikina ciwo yake min" Farida tace "Dama fa babu abinda kike min a nan Didi, you can go in and stop pretending pls" Heedayah bata ce mata komai ba, ta rike cikinta da ta ji yana murda mata, Farida tace "Nace ki wuce ciki kawai, don't worry by the time na yi waec next month xan ga wanda xai dinga maki wanki a schl" Mikewa Heedayah tayi tsaye da kyar ta nufi cikin gida tana cewa "And don't forget also ss2 xan yi waec" Farida bata tanka ta ba, tana duddukawa ta shiga parlor ,Mami na xaune parlorn tare da Shuraim, "Jiya na dawo" Cewarsa kenan yana duban Mami, Mami tace "Amma kaka tace min kana nan mun yi waya da ita few days back" Yace "Aa, Ina Abuja and bata sani ba" Mami tace "Can kake aikin?" Yace "Aa nan Kaduna, Ina 44, mun je aiki ne Abuja..." Mami tace "Maa sha Allah, it's been long Shuraim" Ya cire face cap dinsa ya d'an yi murmushi yace "Haka ne" Heedayah ce ta shigo parlon, Mami tace "Meye haka? Me ya faru" Da kyar tace "Mami cikina" Mami tace "Me ya sami cikin?" Ta nufi sama tace "Ciwo yake min" Mami ta bi ta da kallo har ta wuce sama sannan ta dawo da dubanta kan Shuraim, ya sauke idonsa daga kallon da ya bi Heedayah dashi shi ma, Mami ta kwalo ma Zainab kira, ta fito daga dakinta, Mami tace "Ki kawo ruwa" Shuraim yace "Noo I am okay..." Mami tace "Ki xubo har da abinci" Tana fadin haka ta mike ta wuce sama xuwa gun Heedayah, dakinsu ta shiga ta ganta durkushe a kasa ta rike cikin tana hawaye, Mami tace "What did you eat?" Cikin kuka tace "Nothing, tun a schl yake min ciwo wani lkcin" Mami tace "Toh kwanta in samo maki magani yanxu" Kwanciya tayi saman gadon tana goge idonta, Mami ta dawo parlor ta dau wayarta xata yi kira, Shuraim yace "Is she okay?" Mami tace "No Ciwon ciki take tun a schl, so ina son in aiki driver ya karbo mata magani a pharmacy..." Tana magana ta nufi kofa, Shuraim ya bi ta da kallo yace "But Mami asibiti xai fi ai" Mami ta dawo tace "Au, ai na mance you are also a Dr, kayi mata prescribing maganin mana yaje ya amso mata" Shuraim yace "Ban san wani irin ciwon ciki bane" Mami tace "To mu je ka tambayeta" tashi yyi ya bi bayan Mami xuwa dakinsu, Kuka Heedayah ke yi sosai saman gadon, Mami na shigowa dakin tace "Wayyo Mami it's paining me ni baxan iya ba" hankalin Mami ya fara tashi tace "Toh ko dai mu tafi asibiti" Karasowa dakin Shuraim yyi yana kallon Heedayah, Mami tace "Bari kawai mu tafi asibiti Shuraim, let me get my Hijab" daga haka ta fita, Da sauri Heedayah ta sauka saman gadon ta toshe bakinta ta shiga bathroom ta hau kwarara amai, Shuraim ya dinga kallon saman xanin gadon da ta tashi, can ya juya ya fita daga dakin, ko da Mami ta dawo dakin Heedayah bata fito bandaki ba, Mami har xata shiga bandakin jin amai take idonta ya sauka saman gadon, ta kalli kofa da sauri ta karasa ta cire xanin gadon, ta wuce bandakin, Durkushe ta sameta a ciki, Mami ta ajiye xanin gadon hannunta kan washing machine ta dagota tace "Sannu Daughter" Da kyar tace "Mami xan kwanta" Mami tace "No, u are stained" Heedayah ta kalli jikinta da sauri, a hankali Mami tace "Kin ta6a yi a schl ne?" Heedayah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Mami tace "Talk to me dear, kin ta6a yi?" Girgixa mata kai Heedayah tayi ba tare da ta dago ba, Mami tace "Ohk this is ur first time?" nan ma ta gyada kai kawai, Mami tace "But you know what it is right?" Nan ma dai Heedayah kanta a kasa tace "Uhn" Mami tace "Toh ina xuwa" Mami na fita Heedayah ta sake kallon jikinta sannan ta kalli xanin gadon da Mami ta kawo bandakin, Shuraim ne ya fado mata ta hadiye abu da kyar, duk da axaban da take ji fata take he didn't see anything, a haka Mami ta dawo bandakin rike da pad da pant, Mami tace "Kiyi wanka tukun, hope kin iya sa pad din?" Heedayah ta sunkuyar da kai tace "Uhn" Mami tace "Toh yi wankan ki gama" fita Mami tayi ta bar bandakin, A parlor ta tadda Shuraim, Ta xauna tace "Heedayah ta fiye raki ne, idan cikin bai lafa mata ba sai mu tafi asibitin, na bata wani magani ynxu" Shuraim yace "Allah ya sauwake" Mami tace "Ameen" Mami tace "Ka ci abincin mana" Yace "I am full" Bude kofar parlor aka yi Junaid ya shigo, Sau daya ya kalli Shuraim ya kauda kai, ya gaida Mami xai wuce sama Mami tace "Baka ga Shuraim bane Junaid" Junaid ya juyo ya kallesa, kamar sannan ya fara ganinsa yace "Ohh I didn't notice" karasawa yyi ya basa hannu suka gaisa briefly Junaid ya wuce sama Shuraim ya bi sa da kallo, Can kuma ya kalli Mami yace "Tayi bacci ne?" Mami tace "Ohk let me check" Tashi Mami tayi ta bi bayan Junaid, bakin kofar dakinsu Farida ta gansa a tsaye, kafin ya bude kofar tace "Kayi ajiya ne a ciki??" juyowa yyi da sauri ya fara kame kame yace "Noo, emm dama xan amshi wayata ne" Mami na kallonsa da kyau tace "Nace bana son kana shigar masu daki haka, I have warned u severally Junaid" Bai ce komai ba ya juya ya wuce dakinsa, Mami ta karasa ta bude kofar ta shiga, a gaban madubi taga Heedayah daure da towel ta duka, Mami tace "Sannu, ki saka kaya in baki magani" Heedayah ta dago a hankali tace "Mami ciwo yake min sosai" Mami tace "Xai daina in sha Allah" Mami ta fiddo mata kayan da kanta ta ajiye mata sannan ta tafi dauko mata pain relieve, Kwanciya tayi saman gado bayan ta saka kayan, Mami ta dawo dakin da maganin da bottle water ta bata ta sha tace "Tashi in shimfida maku wani bedsheet" Heedayah ta sauka ta durkusa a kasa, Mami ta shimfida xanin gadon sannan ta sa ta kwanta. Karfe Takwas na dare Mami ta sa Farida ta tafi ta kira Heedayah ta xo ta ci abinci, tun yamma tana daki, gani take kamar Shuraim na nan har lkcn, ba komai ke damunta ba sai xanin gadon da take tunanin kila ya gani, Farida tace "Ya jikin Didi?" Heedayah ta langwabar da kai a hankali tace "Da sauki" Farida tace "Allah ya sauwake, Mami tace ki sakko ki ci abinci" Heedayah tace "I am not hungry Farida" Farida tace "Toh mu je ki gaya mata ni ba ruwana, she said I should call you" Heedayah ta d'an yi shiru, can tace "Is Shureen still around" Farida tayi dariya tace "He is Shuraim not Shureen, baya nan ya wuce tun daxu" Heedayah ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, sakkowa tayi daga kan gadon tana kallon xanin gadon da jikinta, Farida ta kara fashewa da dariya tace "Toh ai idan kina haka xa ki sa a gane, just pretend, it's nothing, sannan ai kin canxa pad ko?" Heedayah ta gyada kai, Farida tace "Toh mu je" Bin bayanta tayi suka fita, gaba daya a tsarge take da kanta, Junaid na xaune parlor yana shan fruit salad suka shigo, Mami tace "Ga abinci Heedayah, if you want fruit sai Farida ta yanka maki" Heedayah dai bata ce komai ba ta xauna saman carpet a hankali tace "Ina yini Yaya" Junaid dake ta kallonta yace "Lafiya lau, u slept all day" Ita dai bata ce komai ba, Farida ta debar mata abincin ta ajiye gabanta, Junaid da sai kallonta yake ya kalli Mami yace "Mami is she sick" Mami tace "No, just slight headache magani ta sha shine take ta bacci" Yace "Ohk" Mami ta ci gaba da danne dannen laptop dinta, A hankali Heedayah ke cin abincin, da ta daga kai sai ta ga Junaid na kallonta, duk sai ta takura, ta gama cakalkala abincin ta mike ta wuce kitchen, satan kallon Mami da hankalinta ke kan abinda take yyi, ya mike a hankali ya dau Glass bowl din da ya ci fruit salad, Farida dai na kwance saman three seater tana danna wayarta, Kitchen ya nufa ya bude kofar ya shiga ya rufe, Heedayah ta juya da sauri, ya karasa inda take tsaye xata hada shayi ya tsaya bayanta yace "What wrong Heedayah?" Kasa cewa komai tayi tana girgixa masa kai, ya kamo hannunta yace "Talk to me plss are you sick" Kamar xata yi kuka tace "Yaya... Mami fa fada xata min, ka tafi plss, she can come in now" Juyo da ita yyi suna facing juna still holding her hands yace "Ki gaya min kukan me kika yi..." Ta xaro ido tana kara kallon kofar kitchen din tace "Aa ban yi kuka ba" Yace "Ur eyes are swollen" Tace "Baccin da nayi ne, Yaya don Allah ka fita Mami xata min fada sosai" Bude kofa aka yi, ya saketa ta juya da sauri har wani rawa hannunta yake, Farida ce tsaye bakin kofar kitchen din tace "Heedayah Mami na kiran ki" Heedayah tace "Toh" bata bi ta kan shayin ba ta bi bayan Farida da sauri, Junaid ya bi ta da ido har ta fita sannan ya ci gaba da hada mata shayin, Suna shigowa parlor Mami ta dinga yi ma Heedayah wani kallo, Heedayah ta sunkuyar da kanta tace "Na kai plate ne kitchen" Mami tace "So? sai aka ce ki dau ages kafin ki fito kitchen din?" Ta girgixa kai kawai ta xauna kasan carpet, fitowa Junaid yyi da cup din shayin, ko kallonsa Mami bata yi ba, ya iso cikin parlon ya mika ma Heedayah cup din, Mami tace "Wani ya sa ka hada mata shayi?" Yace "No ta fara hadawa ne ta fita shine na karasa mata" Heedayah ta amshi shayin tace "Nagode" Mikewa tayi tace "Mami sai da safe" Mami tace "Ki sha magani kafin ki kwanta" ta amsa da "to" sannan ta wuce sama. Har karfe sha daya Heedayah bata yi bacci ba cikin na damunta sosai, Farida tuni tayi bacci bayan ta gama phone call, Heedayah ta mike xaune ta sauke kafarta daga kan gadon ta goge guntun hawayen idonta, tashi tayi ta nufi kofa sbda wani shayin da take so ta sha, ta bude kofa a hankali ta fita don in Mami taji fitowarta baxata yrda ta hada wani shayin ba, sauka tayi downstairs, ta shiga kitchen ta kulle kofan, daxu ruwan flask din ba shi da yawa sai ta daura wani a gas, ta kunna gas ta sa ruwa kadan aka bude kitchen din, a tsorace ta juya, junaid ta gani, ya shigo kitchen din ya kulle, tace "Yaya baka yi bacci ba" Yace "Yea, another tea?" Ta kirkiri murmushi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita yana kallon lashes dinta da ya d'an jike da hawaye, da damuwa yace "Ki gaya min me ke damun ki Heedayah" Tace "Ba komai Yaya, amma kar Mami fa ta shigo nan yanxu" Yace "Ga hawaye idonki kice min ba komai" Matsawa xata yi daga kusa da shi ya rikota, kamar xata yi kuka tace "Yaya ka bari pls" Yace "Toh gaya min kukan me kike" Tace "Cikina ke ciwo" ya xaro ido yace "Cikin ki kuma? Tun yaushe? And did you take drug?" Kafin ta ce komai ya kai hannu cikin nata, ta xaro ido xata durkusa ya rikota, ta hade rai tace "Yaya bana son haka" yace "Tun yaushe cikin ke maki ciwo?" Tace "Da safe" yace "Kin sha magani?" Tace "Mami ta bani" Cike da tausayinta yace "Sorry Lolly" ta xuba mashi ido kawai, yace "Har yanxu yana ciwon kuma" hawaye ya kawo idonta ta gyada masa kai, yace "Toh ya yake maki?" Tace "I don't understand the pain too" kashe gas din yyi sbda ruwan ya tafasa, ya hada mata shayin da kansa yace "Toh mu je ki sha shayin sai in baki magani" ba musu ta shiga gaba ya bi ta da kallo, doguwar riga ne fari irin na bacci jikinta sai hulan dake kanta, ya dinga kallonta ganin xata juyo ya kauda kai ya tafi switch din wutan kitchen din xai kashe, xaune ya sameta parlor tana fiffita shayin da spoon, ya karasa Inda take ya xaune gefenta yyi kasa da murya yace "You know what?" Ta girgixa masa kai, yace "Kawo in fifita maki shayin ki tafi daki ki canxa kayanki ki dawo" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi, da kyar tace "Me ya samu kayana?" Yyi kasa da murya yace "You are stained" still tayi tana kallonsa da idanuwanta kamar xa su yi magana, yace "Tashi ki tafi" Ta sauke kanta kasa, ba karamin courage tayi gathering ba sannan ta mike ta wuce sama da sauri ya bi ta da kallo, tana shiga daki bayan ta gyara jikinta ta kashe wuta tayi Kwanciyarta. Washegari bata yadda sun hada ido da junaid ba da ya hade rai yana bin ta da kallo a parlor, Atamfa ne jikinta riga da skirt ta yafa dankwalin a kanta, ban da Mami da ta aika Farida kiranta in d'an ta ita ne ma baxata sakko ba yau baccin kirki bata yi ba jiya sbda stain din da Junaid yace tayi, ji tayi gaba daya kunyarsa ma take, shayi ta hada ta xauna nan parlor tana sha a hankali da dankali, Farida da Zainab na kitchen suna gyare gyare, Mami kuma na xaune parlon tana waya, Mami na gama wayar tace "Heedayah anjima sai ki raka Farida supermarket ku siyo mana spices, bana son kwanciyan nan da kike yi, ku je a Napep idan xa ku dawo ku yi strolling you will feel strong" a hankali Heedayah tace "Toh Mami" Mikewa Junaid yyi ya wuce sama, Mami ta bi sa da harara don tana lura da kallon da yake ma Heedayah. Hijab har kasa Heedayah ta saka don gani take ko jingina tayi by mistake da abu sai tayi staining mutane sun gani, Farida dai ta saka abayarta da veil ta dau karamar jakarta suka fita, adaidaita sahu suka samu xuwa shopping mall din bayan duk sun gama siyayyar su, har da guzurin turare duk cikin kudin Mami suka fito shopping mall din, da kafa suke tafiya kamar yanda Mami ta umarce su, Heedayah dai sai yatsina fuska take don gaba daya bata son tafiyar.....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Tsaye suke su biyu jikin mota a bakin wani katon hotel, alamar dai wani suke jira, wanda ba shi da tsayi sosai ya ta6a me tsayin gefensa dake waya yana sanar ma wanda suke jira a hotel din xa su wuce idan baxai fito ba, Juyowa yyi yana kallonsa da alamar tambaya amma bai ce komai ba, Mutumin yyi kasa da murya yace "Babaa kaga wasu fine chicks kuwa, dogaye farare....." Tsaki yyi ya ci gaba da wayarsa ba tare da ya kalli direction din da abokin tsayuwar nasa ke nuna masa ba, Gajeran ya kara tabosa ganin su Farida sun kusa inda suke yace "Dallah ka sallami idanuwanka malam, just