Showing 222001 words to 225000 words out of 275313 words

Chapter 75 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

da yanda ya ga rana haka ya ga dare jiya. Karfe goma saura Shuraim ya shigo gate din gidan Mami, Heedayah ta xagayo daga backyard din gidan kenan ta shanya ma ita da Farida Hijabs dinsu da ta wanke, suna hada ido ya nufi balcony bai kuma kallonta ba, bin bayansa tayi kafin su karasa balcony din tace "Ina kwana ya shureen?" Bai tanka ta ba har ya shiga ya kwankwasa kofar parlon, ta tsaya bayansa leaving a little distance between them, a hankali tace "Ina kwana Yaya" juyowa yyi ta d'an koma baya da sauri, calmly yace "Ban sani ba" Tayi narai narai da ido tace "Ya Shureen Mami ce ta kalleni jiya shi sa I couldn't say anything, and I don't want it to be like she isn't saying the truth to the officers...." Yana kallonta da kyau yace "So you both might have face the consequences, don idan har da gaske ta gaya maki waye wnn mutumin ku ka boye a tare, then both you and her aren't safe any longer....." Heedayah ta marairaice tace "Ni ae gobe xan wuce kano, I won't stay here, sae in sa Ammina tayi convincing Mami su dawo kanon su ma, Kuma Mami taji tausayinsa ne kawai kilan don yace mata bashi da iyaye" Shuraim na kallonta yace "Shi kuma bai ji tausayinta ba yyi kidnapping dinta ko?" Shiru Heedayah tayi tana kallonsa, ya d'an yi murmushi ya girgixa kai yace "Something is definitely wrong with Mami, coz a barrister won't do what she did yesterday" Bude kofar parlon aka yi, duk suka kalli kofar, Farida ce tsaye bakin kofar tana kallon Shuraim tace "Good morning" yace "How are you" ta basa hanya tace "Alhmdllh" Shiga parlon yyi, Farida na kallon Heedayah tace "Wankin Hijab tun 8:00 am, Heedayah bata ce komai ba ta shiga parlon ita ma, Shuraim na xaune parlon suna gaisawa da Dinar da Amira da suka iso daga Abuja safiyar ranan, Dinar na murmushi tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh, yau ku ka iso?" Tace "Eh wllh, morning train muka biyo" Amira dai na ta danna wayarta tunda ba sanin Shuraim tayi ba, Bayan some minutes Mami ta sakko downstairs ta xauna parlon suka gaisa da Shuraim, shi dai yana wasa da Fadil dake xaune kusa da shi, can Mami tace "I am sorry about yesterday Shuraim, I just had to...." Shuraim na kallonta yace "Me yasa kike tunanin you have to Mami?" Mami tayi shiru, sae kuma murya can kasa tace "May be because I am a Mother, and because I never expect that... I never saw it coming" Dinar ta mike ta bar parlon don bata ma son ci gaba da jin wnn abin dake bata takaici, Amira dai sae kallon uwartata take, Shuraim ma kasa ce mata komai yyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Heedayah dake dinning xaune tare da Farida dake shan tea ta mike ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Khaleel, ta wani xaro ido cikin few minutes ta bar wajen a guje ta koma can hanyar stairs ta rakube a mugun tsorace, su Mami duk suka bi ta da kallon mamaki, Khaleel ya shigo parlon da sallama, Farida ta mike da sauri ta bi bayan Heedayah, Mami da Amira kadae suka amsa sallamarsa, ya karaso cikin parlon kansa a kasa, bai xauna ba ya gaida Mami a hankali bowing his head, Mami ta nuna masa kujera tace "Morning how are you?" Xaunawa yyi saman kujeran yace "Alhmdllh...." Yana kallon Amira yyi kasa da murya yace "Ina kwana?" Amira tace "Sannu da xuwa" yyi mata godiya, kallon Shuraim da ya tsiri danna wayarsa yyi yace "Good morning" Bayan few seconds Shuraim ya dago yace "Morning" Mami tace "Ina abokin naka?" Khaleel yace "Yana mota a waje" Mami tace "Let him in" Mikewa yyi ya nufi kofa, Amira ta bi sa da kallo har ya fita, Shuraim ya mike ya mayar da wayarsa aljihu yace "Ni xan koma Mami" Mami tace "Aa ka d'an jira, ae ba mu gama magana ba" Yace "Xan dawo kafin in tafi anjima in sha Allah" tace "No, sit back Shuraim, xa muyi magana kafin ka tafi din" Ba musu ya koma ya xauna duk da ko kadan ransa bai so ba, Ba a dau lkci ba Khaleel ya dawo parlon tare da Zayyad, Yana kallon Mami yace "Ana sallama a waje" Mami xata yi magana Dinar ta sakko ta mika mata wayarta dake ringing, Mami ta amsa ganin Abba ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa ya sanar mata he is outside tace "Toh gani nan xuwa" Daga haka ta mike ta fita bayan ta sanar ma Khaleel and his friend she will be back soon, tun asuba ta tura ma Abba message ya xo kafin ya tafi aiki pls, a compound din ta samesa xaune, ta ja kujera tana kallonsa tace "Ya gida?" Yace "Fine me yaron nan ya sake dawowa yi a gidan nan Barrister?" Mami tace "Ni nace ya xo" Abba ya girgixa kai yace "Rahinah ni ban san meye matsalar ki ba, all ur words at the station yesterday are nothing but lies, do you have any agenda to do with this thug da kike rufa masa asiri? Tunda baki son a hukuntasa ba sai ki rabu da shi ba ki daina basa fuskarsa xuwa maki gida, Why are u behaving this way pls Rahinah? Ba ma shi kadai ya shigo gidan yanxu har da abokinsa sbda samun waje??" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "There is something I want to know about him barrister...." Ya dakatar da ita yace "Me saninsa xai kara maki a rayuwa, why are you risking your life and that of people around you?" Mami tace "Ba haka bane Ahmad, there is something about him that I feel I need to know, from the little he said about him kamar ba son ransa bane harkan nan da yake yi" Da mamaki sosai Abba ke kallonta, can yace "Ikon Allah, wato kawai kin ma san Kidnapper din ne shi, to ina ruwanki ko da son ransa yake ko ba da son ransa yake ba, Jan sa ake su fita operation din ko da kafafuwansa yake tafiya, plss Rahinah stop all this nonsense idan xa ki bari a hukunta Mutumin nan ki bari, is 30 million 30 thousand??" Mami tayi shiru a sanyaye tana kallonsa can tace "Don Allah mu basa listening ears barrister, may be labarinsa xai mana amfani, ba wai nace kada a hukunta sa ba but plss let know how he joined the gang, coz with tears in his eyes yace min he was never opportune to know his parent" Abba ya dinga mata wani kallo, ta mike tayi kasa da murya tace "For my sake plss Barrister ka tashi mu je parlon, I invited him and his frnd ba xuwan kansu bane" Barrister ya girgixa kai yace "I have other important cases to look to Rahinah, dama wnn shine dalilin message din da kika min in xo??" Mami ta dakatar da shi tace "Pls for my sake Barrister, I am saying plss" daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallon mamaki har tayi nisa, text ya shiga turawa a wayarsa yana gamawa ya mike ya bi bayanta xuwa cikin parlon. Bayan Abba sun gaisa da su Dinar a parlon ya kalli Shuraim da yyi masa sannu da xuwa, Abba yace "You said you are leaving for Lagos today" Mami tace "Ni na tsayar da shi xuwa anjima barrister" Abba yace "Alright" Mami na kallon Khaleel da idonsa ke kan Tv tace "I am sorry Khaleel, ba ni kadai xan saurareka ba, ni da barrister will listen to you, if there is any help we can render you from our discipline we will gladly do that... Amma fa we want nothing but the plane truth from you, idan kuma muka sameka da laifi xa ayi maka hukuncin da yyi dai dai da wanda ya kamace ka" Khaleel dai kallon Mami kawai yake, can ya sauke kansa kasa yace "Mami ni me laifi ne dama ae" Mami tace "Allow us to decide that" Shi dai Zayyad na jin abinda Mami ta fada ya ji he just have to leave that parlor immediately, Mami could see how uncomfortable he was, haka ma Shuraim dake ta kallonsa, ta d'an yi murmushi tace "Ka kwantar da hankalinka Zayyad, I am assuring you this... ba abinda xai faru" Abba wayarsa kawai yake dannawa, Dinar har xata bar parlon jin furucin da Mami tayi ma Khaleel na karshe yasa ta samu courage din xama, Junaid ne ya sakko parlon rike da makullin motarsa ya shirya cikin white shadda kasancewar ranan Friday ne, Heedayah da Farida dake jikin rack din stairs sun ki komawa parlon yace "What's that?" Basu kai ga basa amsa ba ya kalli parlon, karasawa ciki yyi, Amira ta sakar masa murmushi, Junaid ya gaida Abba, ya ba Shuraim hannu yyi ma Khaleel da Zayyad ma haka, ganin fita xai yi Mami tace "You stay back Junaid" Ya juyo yana kallonta bai dai ce komai ba amma ransa bai so ba ya xaga bayan kujera kawai ya tsaya. Mami na kallon Khaleel tace "Now tell us who you are Khaleel" Khaleel ya kalli Zayyad, Mami tace "Ko shi xai gaya mana?" Khaleel yace "I can't say daga yaushe ne nake tare da su Ummi, sau da yawa yana attempting bani labarin dalilin kasancewata da su, amma nasan xuciyata baxai iya daukan hakan ba sbda ailment dina...." Abba yace "Kwanciyar da kayi kwanaki a Abuja shi ne matsalar da kake nufi a nan?" Khaleel yace "Eh shine" Abba ya gyada kai sannan ya kalli Zayyad wanda har lkcn ya ki sakewa, Tun maganar da Khaleel yyi na farko Abba ya ji he is also interested to know him, as a barrister bai ga alamar karya ko tsoro a tare da Khaleel ba, he is being just Frank, unlike his frnd that at anytime if care isn't taking xai iya barin parlon, Abba ya kalli Junaid dake tsaye shi ma yana kallonsu yace "Ka kulle kofar Junaid, we need privacy" Xaro ido Zayyad yyi, Junaid ya nufi kofar ya sa makulli, Abba na kallon Zayyad yace "Tell us about ur frnd...." Zayyad ya goge fuskarsa sannan yace "Amma Ina son alkawari daga gare ku na cewar bayan labarin mu da xa ku ji xa ku rufa mana asiri with out involving hukuma" Abba yace "Don't worry about that, there is always a reason for everything, mu baxa mu tona maku asiri ba amma xa mu yi abinda ya kamata" Zayyad yyi shiru, Abba yace "Ka kwantar da hankalin ka, muna sauraron ka" Zayyad ya sauke kansa kasa yace "Shekaru kusan talatin da hudu xuwa biyar da suka wuce....." Kallonsa duk occupant din parlon suke, Zayyad ya ci gaba "Oganmu ya taho da wani yaro da baxai wuce shekara uku ba daga operation din da suka fita yi gidan wani attajiri, wnn mutumi na daya daga masu kudin wancan lkcn duk da mu dai ba wasu manya bane don ba a fita da mu irin wnn operation din amma duk mun sani, shi wnn yaron da oganmu ya kawo shine Khaleel, a ynda Oga Salahu ya sanar mana a lkcn sun kashe Mahaifin yaron bayan sun kwashi kudade da zinarai masu yawa, bana mancewa daya daga ogannimu na ynxu da ake kira da Arne wanda a lkcn shi ma yaronsu ne ya tambayi Oga Salahu me yasa ya taho da Khaleel, Oga Salahu yace xai yi mana amfani nan gaba.... A nan ya bada labarin wai bayan sun harbe mahaifinsa tashi yyi daga jikin mahaifiyarsa dake rike da shi ya gudu xuwa daki ya dauko bindigogin wasansa wai xai harbe su shi ma, wani oganmu a lkcn yyi niyyar harbesa Oga Salahu ya dakatar da shi, wnn dalilin kuma ya sa oga Salahu ya daukesa yana rike da bindigar wasan nasa da yake ikirarin xai harbe su, a ynda Oga Salahu ke bamu labari Mahaifiyarsa na kuka da xa su tafi da shi, sai yake ce mata xai dawo anjima idan ya kashe su duka da bindigarsa, courage, fearlessness da zeal din dake tare da shi yasa oganninmu suka ji they just have to go with him and raise him, he have to be their own, wnn shine mafarin dawowar Khaleel cikinmu tun yana shekara uku a duniya, sai dai bana mantawa sunansa a lkcn ba Khaleel ba, idan ka tambayesa ya sunansa xai ce maka Aliyu Usman, Babban Oganmu na gaba daya at that time sunansa Oga Saminu, to Oga Saminu na da wani yaronsa da yake ji da wanda 'yan sanda suka kashe a wani operation... sunan yaron Khaleel, yaron is also brave and intelligent...." Zayyad na nuna Khaleel dake ta kallonsa yace "Shi yasa ya mayar masa suna Khaleel, kuma har yau idan ba ni ba sai wa enda suka jima tare da mu bbu wanda yasan sunan Khaleel na ainahi, shi kansa Khaleel bai san sunansa ba ynxu sai da na fada...." Zayyad ya jinginar da kansa da kujera yace "Khaleel is more than intelligent, wnda duk wanda ke tare da shi baxai so ya bar sa ba, wayonsa kuma ya fi karfinsa as at then, till now.... ga rashin tsoro, tun yana shekara 7 ya iya harbin duk target dinsa, duk oganinmu na ji da shi ba kadan ba barin oga Arne, mu da muka jima tare da su ma sai da Khaleel ya nuna bamu iya komai ba, hatta bera idan Khaleel yasa kansa xai kamo duk inda ya shiga sai ya kamosa cikin mintuna kalilan, da farko da aka kawosa duk dare sai yyi kuka yana kiran mahaifiyarsa, amma as time goes on, shekara daya biyu sai ya watsar gaba daya, ba a ta6a saka wani cikinmu makaranta ba, amma Oga Arne yyi convincing ogannimu sun saka Khaleel...." Shiru Zayyad yyi yana kallon Mami da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta sosai, Khaleel ma kansa na sunkuye yana sauraron Zayyad don shi kansa bai san wnn bangaren na labarin nasa ba sai a ynxu, xamowa kasa yyi a hankali ya xauna xuciyarsa na bugawa, Shuraim dai sai kallonsa yake kamar yanda Junaid ma ke kallonsa ko kiftawa bbu, Abba ya sauke wani ajiyar xuciya underneath his breath yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Bayan few seconds Abba ya kalli Zayyad da yyi shiru yace "Go on...." Mikewa Mami tayi, Abba na kallonta da mamaki yace "Ina xa ki kuma?" Bata iya tace masa komai ba ta nufi stairs hawaye na ci gaba da sakko mata uncontrollably.....



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples,
Black spot
cream reaction
eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰
Soap price:3k
Chat 08062991549 to plc ur orders
Call:08064532391
We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏
we can't wait to be a part of your beauty story🤭




Mikewa Amira tayi ta bi bayan Mami da sauri, bedroom dinta ta sameta xaune gefen gado, ta karasa kusa da ita ta xauna a hankali tace "Though it's sad but bai kamata ki bar wajen ba Mami, u invited him here, so you are to listen till the end" Kasa ce mata komai Mami tayi hawaye na xarya a idonta, Da damuwa Amira tace "Haba Mami sai kace yau kika ta6a jin irin haka? This isn't suppose to look new to you, kina fa cases wa enda suka fi haka ma ai" Mami ta dafa kafadunta cikin raunin murya tace "Amira wnn Kidnapper din da kike gani yayanku ne" Da mamaki Amira ke kallonta, da farko ta ma kasa cewa komai, can dai tace "Ban gane ba Mami, yayanmu ta Yaya? How is that?" Mami ta fashe da kuka sosai ta kasa bata amsa, Amira ta xaro ido tana kara naxarin labarin da Zayyad ke basu downstairs, ja baya tayi with shock tace "Yayanmu kuma Mami?" Mami ta gyada mata kai amma ta kasa magana, kallonta kawai Amira take da idanuwanta kamar xa su yi magana, cikin kuka Mami tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un... da na sani da ban dage da addu'ar Allah ya sake hadani da Aliyu a nan duniya ba, da na sani da ban dinga wnn addu'ar ba don gashi ban masa adalci ba ban ma kaina adalci ba, had I known addu'a ta garesa a ko da yaushe shine Allah ya hada mu a darussalam ba nan duniya ba...." Amira ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Mami ya aka yi kika san yayanmu ne?? How is that even possible?" Bude kofar dakin aka yi Dinar ta shigo, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu da mamaki, can ta karaso tace "Me ya faru Mami??" Jin Mami taki cewa komai Dina ta xauna kusa da Amira tace "Ummi Hanan me ke faruwa?" Amira ta sakar mata kuka tace "Wai kiji mutumin nan yayanmu ne in ji Mami" Xaro ido Dinar tayi tace "Yayanmu kuma? Wani mutumin a ciki? Yayanmu kamar yaya?" Mikewa Mami tayi ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta dawo dakin ta debi tissue paper dake gaban mirror dinta ta nufi kofa duk suka bi ta da kallo har ta fita, Dinar na kallon Amira cike da confusion tace "How is that? Meye hadinmu da Kidnapper xa a ce yayanmu ne, yayanmu ta ina?" Amira ta buda hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login