Showing 120001 words to 123000 words out of 275313 words
Chapter 41 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
abu na kullum" Mami bata kuma cewa komai ba har suka isa makarantar, a nan kofar makarantar suka tadda Junaid yana jiransu, a ranan aka yi enrolling din Heedayah a Nigerian Turkish, aka sata a Jss2, har hostel dinsu kaka da Mami suka shiga, kasancewar hostels din na sama classes dinsu kuma na kasa, Mami dai da taga Kaka xata xabga shiriritan ta sai tayi saurin dakatar da ita ta kwaba mata, a haka har suka bar makarantar wajajen la'asar, Kaka har da kwallarta wai an raba ta da Deedayah, duk yanda Mami ta so convincing din kaka su koma gida tare kin amincewa tayi tace ita dai a sauketa a gidan d'an albarka Umaru. Mami tayi parking a parking space ta sauka ganin babu motar Abba ta gane ya fita gidan kenan, ciki ta shiga ta tadda Mumy xaune parlor da Hajiya Sadiya da Hajiya Baturiya ga abinci iri iri an baxa a parlon sai shewa suke ana hira kamar wa enda aka yi ma bushara da gidan aljanna, Mami tayi masu sannu amma bbu wanda ya tankata cikinsu ta wuce bangarenta, ga mamakinta a bude ta ga parlon nata bayan ta rufe da xata fita daxu, duk gidan ta san Barrister kadai ke da spare key din bangaren nata, ta dai shiga ciki tana bin parlon da kallo, farar takarda ta ga saman kujera a linke, ta dau takardan tana jujjuyawa, can ta warware takardan tana duba rubutun ciki....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Murmushi kawai Mami tayi bayan ta gama karanta content din takardan ta linke a hankali ta wuce daki da shi ta saka a jakarta. Mami na idar da la'asar ta dau wayarta ta kira Hajiya Zuwaira, bayan Hajiya Zuwaira ta daga suka gaisa Mami tace "Su Nafisah sun wuce makarantar yau kuwa?" Hajiya Zuwaira tace "Aa sai gobe in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai mu, don Allah Hajiya, Shafa'atu nake son ki turo min nan gida ynxu idan bata maki komai, xata min wani aiki ne" Hajiya Zuwaira tace "Toh shkkn babu matsala xan turo ta, Allah dai ya sa ta gane gidan" Mami tace "Toh Ameen" da haka suka yi sallama, Mami na ta xaune saman darduma har Shafa'atu me aikin Hajiya Zuwaira ta iso, Mami tayi welcoming dinta tace "Wani d'an aiki nake so ki taya ni amma ba a nan ba, bari in shirya mu je ko" Shafa'atu tace "Toh Hajiya" Mikewa Mami tayi ta wuce daki, ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motarta da handbag tace "Mu je" Shafa'atu ta tashi ta bi bayan Mami suka fita parlon, Mami bata kulle bangaren nata ba ta bar sa haka a bude, har sannan Mumy na parlon da tawagarta da suka karu a kan daxu, Suna ganin Mami suka tuntsire da dariya, Mami dai ko kallon Inda suke bata yi ba har suka fita compound da Shafa'atu, motarta ta nufa suka shiga suka bar gidan, can gidanta ta tafi, bayan sun gaisa da Mai gadi ya bude masu gate suka shiga babban compound din gidan, Mami na shiga parlor ta kalli Shafa'atu tace "Gyaran gidan nan nake so kiyi min shafa, har sama duk xa ki gyara min, labulayen nan ki cire xan baki wasu ki canxa, kitchen ma Ina son a gyara, But anya xa ki iya ke kadai, naga aikin ya maki yawa koh?" Shafa'atu tace "Aa xan iya wllh Hajiya, ai k'ura ne kawai ba wai wani datti ke gare gidan ba" Mami tace "Toh shkkn, xan je in dawo in sha Allah" Shafa'atu tace "Toh sai kin dawo" har Mami ta nufi kofa sai kuma ta juyo tace "Kin dai ci abinci ko?" shafa tace "Ehh na ci Hajiya" Mami tace "Toh shkkn" daga haka Mami ta fita gidan, sai bayan isha Mami ta sake dawowa gidan, Mai gadi ya shigo mata da boxes din kayanta da na Heedayah daga cikin booth xuwa parlor, tsinkenta ko na Heedayah bata bari gidan Barrister ba, Shafa'atu ta kwashi kayan gaba daya ta kai su sama tace "Xa a jera maki su ne a siff Hajiya?" Mami tace "Aa, mu tafi kawai in maida ke gida kin ji, nagode kwarai" A bakin gate din gidan kawunsu Junaid Mami ta yi parking ta bude jakarta ta fiddo dubu uku ta mike ma Shafa tace "Ga wnn shafa, naji dadin aikin da kika min nagode" Shafa tace "Aa wllh Hajiya nagode...." Mami tace "Ki amsa ai ni na baki, amsa" Shafa ta karbi kudin da ladabi tace "Toh Allah ya saka da alkhairi ya kara girma Hajiya" Mami tace "Ameen ki ce da Hajiya Zuwaira ina gaisheta" Shafa tace "Toh in sha Allah" Da haka ta sauka motar ta rufe ta wuce ciki, Mami tayi reverse ta bar layin ta dau hanyar gidanta. Mami na gama parking sai ga kiran Hajiya Zuwaira, ta kashe motar ta daga, Hajiya Zuwaira tace "Barrister yanxu na fito bangarena naga Shafa'atu ta dawo shine take nuna min kudin da kika bata wai kun je can gidanki ta gyara maki, lafiya dai koh?" Mami tace "Lafiya lau Hajiya" Hajiya Zuwaira tace "Toh gyaran na menene ke da ba a gidan kike ba" Mami tace "Ina son in koma can ne in d'an kwana biyu tunda Heedayah kinga yau aka kai ta makaranta" Da mamaki Hajiya Zuwaira tace "Toh xaman Heedayah kike a gidan dama??" Mami tayi murmushi tace "Not at all wllh, kawai dai ina bukatar hutu ne, Kinga nan bbu kowa, bbu wani hayani, sannan ina da cases da yawa to attend to, shi sa na dawo nan sbda privacy" Hajiya Zuwaira tace "Toh Allah ya taimaka" nan suka yi sallama Mami ta ajiye wayarta. Mumy ce xaune da Hajiya Sadiya a wani d'an akurkin daki, Mumy ta gama kirga damin kudin hannunta 'yan dari biyar biyar da ya kama dubu dari da ashirin ta mika ma gabjejen mutumi me gemu dake xaune gabansu, ya amsa kudin yana dariya me sauti ya ajiye a gefensa, Mumy na murmushi tana gyara yafin mayafinta tace "Toh saura na ita yarinyar, sai dai kace ba yanxu xa a bada kudin ba ko?" Yana kallonta da jajayen idonsa ya girgixa kai yace "Aa, kamar yanda sai da kika ga aiki da cikawa kika kawo min kudin wannan aikin, to shi ma wnn sai kinga aiki yayi, mu bama amsan kudi sai bukata ta biya...." Cikin gamsuwa Mumy tace "Gaskiya ne, na kuwa ga aiki da cikawa wllh, ban ta6a tunanin haka aikin ka yake ba...." Yayi dariya yace "Toh ya kika ce xa ayi da ita yarinyar?" Mumy ta gyara xama da kyau tace "Ranka shi dade ni dai kawai ta walakanta, kmr ynda tasa na sha walakanci na wani d'an lkci, in son samu ne ma ta xamo abar kyama cikin jama'ah, wanda har ita uwar rikon tata xata sallamata taji ta fita ranta, sannan ka rabata da mijina wato tayi nisa sosai da inda muke ta je can ta karata, kada ta sake shigowa rayuwar mu" cikin katon murya mutumin yace "Toh an gama, xa a jefa rayuwarta cikin garari a takaice...." Mumy tace "Yauwa Ranka shi dade, ta xamo abar kyankyami cikin al'umma" Yana gyada kai yace "An gama" Junaid ne xaune bedroom din Mami dake harhada wasu files nata xata fita aiki, bin ta kawai yake da kallo har ta gama abinda take ta dau hand bag dinta tace "Kana nan ai..." Ya girgixa kai a hankali yace "Aa xan fita" Tace "Toh mu je ka ajiye ni kawai ba sai na fita da mota ba, I don't feel like driving, anjima when I am done with whatever I am doing xan kiraka ka mai da ni gida" Bai ce komai ba, ta dau takardan da ta basa da ya ajiye gefensa bayan ya gama dubawa, ta linke ta mayar da takardan jakarta, cikin sanyin murya yace "But Mami...." Mami ta dakatar da shi tace "But nothing Ahmad Junaid, tashi mu je ka ajiye ni" tana fadin haka ta fita dakin, mikewa yyi ya bi bayanta fuskarsa dauke da damuwa. Da yammacin ranan Mami na parlor tana jiran isowar mai aikin da ta bukaci a sama mata, aka danna bell, mikewa tayi ta isa kofan ta bude, Shuraim ne tsaye bakin kofar, da mamaki tace "Shuraim.... come in" shigowa parlon yayi, Mami ta koma ta xauna, ya kulle kofar ya karasa shi ma ya xauna yace "Ina yini?" Da murmushi tace "Lafiya lau, baka koma Zarian ba...." Yace "Ban tafi ba" tace "Ohk sae yaushe?" Yace "Next week in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen" Mami tace "Ya mutanen gidan" daga kai yyi ya kalleta yace "Alhmdllh, but why did you leave Mami" Tace "Nothing Shuraim, I only need rest and enough privacy" kallonta kawai yake yi bai ce komai ba, can dai yace "Wani abun ya faru ne?" Mami ta kallesa tace "Aa bbu wani abinda ya faru Shuraim..." Ya girgixa kai yace "Idan ma wani abun ya faru kiyi hakuri" D'an murmushi tayi tace "No bbu abinda ya faru, let me get you something to eat" Yace "Alhmdllh, will be on my way now" tace "Toh bari in kawo maka ruwa" fridge ta tafi ta dauko masa drink da goran ruwa daya da cup, ta ajiye masa, ya dau bottle water din ya mike yace "Xan wuce" Mami tace "So soon, toh nagode, Allah ya kiyaye hanya...." ya amsa da "Ameeen" ya nufi kofa ya fita. Da sallama kaka ta shigo gidan rike da katon handbag dinta, Khadijah da Rabi'ah ne parlon sanye da school uniform suna yin breakfast, Mumy kuma na kitchen da talatu sai fada take tana tsine ma Talatu ta cika man gyada a suyan kwai, Rabi'ah da Khadijah suka yi ma Kaka sannu da xuwa suka gaisheta, Kaka da ke ta kallon kitchen tace "Ita kuma wancan ita da waye kamar karya da sassafen nan, tun bakin get nake jin muryar ta" daga Rabi'ah har Khadijah bbu wanda yace mata komai sai shayinsu suke sha, Kaka ta tabe tace "Wajen Rakiya na xo kafin ta fita, yau sati daya tun da muka kai wannan yarinya Deedayah makaranta ban ganta ba, ita ma lalacewa tayi taki xuwa gaisheni ko ko?" Mumy ta leko kitchen jin kamar muryar kaka, wani shegen kallo ta shiga yi mata suka hada ido, da sauri Mumy ta sake fuska da fara'a tace "Lahh kamar kaka, wata sabon gani, sannu da xuwa kaka...." Kaka tace "Ina ruwana da sannu da xuwan ki Maryam, wajen Rakiya na xo ba gun wani gantalalle ba a gidan nan...." Mumy ta karasa fitowa kitchen din tace "Ohh wai Rahinah? Ai yau kwana takwas bata gidan nan kaka" Kaka ta xaro ido tace "Ina ta je?" Mumy tayi fuskar tausayi ta nemi waje ta xauna tace "Tohh, ni dai ban san me ke faruwa ba, amma lahadin da ta gabata ba na jiya ba, naji suna ta tashin hankali da Barrister wai sai ya bata takardan ta, ta dai daga masa hankali sosai, kinsan Barrister ba me magana bane sannan shi baya son duk wani abun tashin hankali, matar nan sai da ta san yanda tayi ta kure sa, xagi kam bbu wanda bai sha ba, daga karshe dai na shiga tsakanin su ina ta bakin kokarina na sasanci amma abun ya ci tura...." Kaka da ta gwalo gaba daya idonta tana kallon Mumy tace "Sai aka yi uban ya??" Mumy tayi kasa da murya a hankali tace "Daga karshe dai sai da aka rabun" Kaka ta saki wani rikitaccen salati ta nemi kasan tiles ta xauna tace "Ya saketa?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace "Wllh kuwa, yau kwananta takwas rabonta da gidan nan duk ta kwashe komai nata" kaka ta kuma sakin salati, sai kuma ta fashe da kuka tace "Yanxu ta6arewar Amadu ya kai haka nake xaune ban nemi taimakon Allah ba?? Ashe budirinsa na rashin mutunci kawai yake yi ba kama kafar yaro, yau fa kwanansa takwas bai taka ya je inda nake ba, har wayar ma ya ki yi min yace min ci kanki..." Mumy ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Mu ma nan duk hakuri muke da shi, fadan yanxu daban na anjima daban... Da yake ni na saba da halinsa shekara talatin da uku ba wasa ba gashi har yau ai ba a ji kan mu ba" Kaka ta share idonta tace "Ina Amadun yake yanxu?" Mumy ta saci kallon hanyar parlon Abba dake cikin dakinsa yana bacci tace "Yau kwana biyu yace min ya tafi Abuja, yana can" Kaka tace "Ko bayan duniya ya tafi ai xai dawo, Ina Shureen?" Mumy ta d'an 6ata fuska tace "Shi ai yana Zaria" Jakarta ta bude ta ciro wayarta ta mika ma Khadijah tace "Nemo min Junaidu a wayan nan" Ido Mumy ta dinga yi mata kar ta kira, ai ko Khadijah ta gama latse latsen wayar tace "Babu lambar Junaid a nan" Kaka ta fixge wayar tace "Dakikiya kawai, ana ta dai asaran kudin makaranta a banxa" Daga haka ta nufi kofa kamar xata tashi sama, Mumy ta bi ta da harara har ta fita parlon sannan ta tabe baki tana tafe hannu. Mai adaidaita kaka ta tsayar a titi tace "Kai yaro kayi boko?" Yace "Nayi mama" Kaka tace "Toh ka shiga wayar nan ka nemo min wata lamba, Junaidu xaka ga an rubuta ka kira min shi" Bayan wani lkci ya mika ma kaka wayar yace "Yana yi" kaka ta amsa tace "Yauwa" ta kai wayar kunne, sai da ya kusa katsewa Junaid ya daga, Kaka tace "Junaidu kana ina yanxu?" Junaid ya mike xaune daga kwancen da yake yana bacci yace "Ina kwana kaka" Tace "Lafiya lau, a ina xan sameka?" Yace "Ina gida" tace "Ina ne gidan?" Rasa abinda xai ce mata yayi baya son cewa nan gidansu cos he knows Mami won't take it likely with him, yace "Gidanmu a Abuja" Kaka ta saki salati a gigice tace "Har ita Rakiyar?" Yace "Ehh" Kuka ta sakar masa tace "Toh yanxu ni ya xa ayi da ni ina son ganinta, ka rufa min asiri ka kai mata wayar yanxu inyi mata magana" Yace "Toh" Tace "Toh Ina jira don Allah" katse wayar yayi, tana kallon Mai adaidaitan dake tunanin shiga xata yi su wuce, tayi shigewarta napep din tace "Sanyi ya dameni, ka jira in gama wayata a tsanake sai kayi wucewar ka Allah yayi maka albarka" juyowa yyi da sauri yana kallonta, ta rafka uban tagumi tace "D'a na ne yyi ta'asa ya saki matar arxiki matar kirki bani da labari" Junaid na kwankwasa kofar bedroom din Mami tayi masa izinin shigowa, Vid call take yi da Second daughter dinta dake aure Abuja, hannu junaid ya daga ma kanwar tasa dake masa murmushi ganinsa, ya tafi gefen makeken gadon dakin ya xauna, Mami ta juya tana kallonsa tace "Ya aka yi?" Yace "Aa ki gama" Jin abinda yace kanwarsa Deenar tace "Mami we will talk later a ji da Yaya" Mami tace "Alright" daga haka ta katse kiran ta juya tana kallon Junaid tace "Har ka tashi?" Yace "Eh na tashi, Ina kwana" tace "Lafiya lau" Yace "Mami yanxu kaka ta kirani" Mami tace "Ohk ya aka yi?" Yyi kasa da murya yace "She said she wants to speak with you" Mami ta d'an yi shiru kafin tace "Ohk kirata" Dialing number xai yi sai ga kiran kaka ya mike ya kai ma Mami bayan yyi picking, Mami ta kai kunne hade da sallama, kaka ta fashe da kuka tace "Yanxu Rakiya ashe abinda ke faruwa kenan sbda ba ni na haifeki ba kika ki gaya min, shi Amadun ne yyi maki haka don ya sameki a banxa?" Mami ta d'an yi murmushi tace "Aa kaka kiyi hakuri, ba wani abu...." Kaka ta dakatar da ita tace "Ke dakata ba ruwana da kame kamen ki, kina ina yanxu?" Mami tace "Ina gidana" Kaka tace "A ina?" Mami tace "Unguwar Dosa" Kaka tace "Ahhh lalacewa ta same Junaidu kenan, da girmata xai gilla min karya? To ai kuma ya xama abun tsoro in haka ne, dama bakin ciki yake da sanin ki da nayi ban sani ba, to aniyarsa ta bi sa..." Murmushi kawai Mami take, Junaid ya xaro ido yana sauraron kaka don muryarta xaki xakwai a wayar, Kaka tace "Ga d'an sahu nan kiyi masa kwatance ya kawo ni yanxun nan" daga haka ta mika ma Me adaidaitan waya Mami ta basa address din anguwar yace ya gane ya katse wayar ya mika ma kaka, kaka ta jefa jaka murya can kasa tace "Naira hamsin ai xai kai mu ko kuma arba'in" Mami ce ta fito bakin gate bayan me adaidaitan ya kira yace suna layin, Junaid dama bedroom dinsa ya shige ya kulle, Mami tayi murmushi bayan adaidaitan ya tsaya kaka ta sakko tace "Sannu da xuwa kaka" Kaka na bincika jakarta ta ciro naira hamsin tace "Yauwa Rakiya" Mika ma me adaidaitan hamsin din tayi, yyi kasake yana kallonta, Mami da dama ta fito da kudi ta mika masa dubu dayan hannunta tace "Mun gode malam...." Ya amsa kaka tace "Ga dai canji a hannuna kuma kya basa uban kudin nan a ina xai samo canji dari tara da hamsin Rakiya" Mami tace "Mu je ciki don Allah kaka, ai gidan da nisa" Godiya me adaidaita yayi ma Mami ya ja adaidaitansa, kaka ta bi sa da cewa barawo a fusace, Mami ta yi shigewarta ciki, Kaka ta bi bayanta tana cewa "Duk 'yan fashi ne a da, alqunut da ake ta jifansu da shi ya sa suka koma kabu kabun adaidaita, Banda haka meye xa a bashi dubu daya ya falla a guje da mashin kamar barawo" Suna shigowa parlor kaka na bin ko ina da kallo tace "Nan ne gidan naki Rakiya?" Mami tayi murmushi tace "Aa gidan Mahaifin su Junaid ne, ba nawa bane wannan" Kaka ta marairaice ta xauna sai kuma ta fara kuka