Showing 177001 words to 180000 words out of 275313 words
Chapter 60 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
Heedayah da ta fara gani a parlon da sauri ba tare da ta bi ta kan mutanen dake parlon ba ta durkusa kusa da ita ta fara kiranta tana girgixa ta, a rikice tana kallon likitan tace "Me ya sameta Dr??? what's wrong with her" Mikewa Mum Islam tayi tana kallon Mami da mamaki bata son tabbatar da cewa Ita ce yarinyar da ake ta nema tun jiya a makotansu, Junaid dai na tsaye bakin kofar parlon sai kallon Mahaifiyar Heedayah yake, same goes to Khaleel that is shocked at the resemblance, Mami dai hankalinta gaba daya na kan Heedayah da take tadawa, Asp da Abba, da Alhaji Ahmad sai Mijin Dinar kadai ne waje basu shigo parlon ba har sannan, Heedayah ta bude ido a hankali, kana ganin yanda take bude idonsa kasan sun mata nauyi, murya can kasa tace "Mami" Rungumeta Mami tayi hawaye na sakkowa idonta tace "Ina kika tafi Heedayah, me yasa kika fita gida da daddare?? Where did you go to" A hankali Heedayah tace "I just felt like going Mami, Mami don Allah kiyi hakuri baxan sake ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai, Mikewa Mahaifiyar Heedayah tayi daga inda take xaune hawaye na sakko mata ta wuce dakinta, Mami ta goge ma Heedayah idonta tace "It's okay daughter, we are going back to Kaduna now, in sha Allah..." Heedayah ta d'an yi shiru, sai kuma da sauri tace "Mami where is he?" Mami tace "Who" Heedayah tace "Ya Khaleel, shi ya dawo dani gida ko?" Mami bata saurareta ba tace "I don't know, we are going home now" Mami na fadin haka ta tashi tana dago Heedayah, Heedayah ta xame hannunta tace "Mami Ya Khaleel din fa? Da ya kawo ni wucewa yyi?" Sai a snn Mami ta juya ta kalli Khaleel bayan ta fahimci shi Heedayah ke tambaya, sosai gabanta ya fadi da suka hada ido da shi, don har sai da ta koma ta duka kasa, Heedayah ta shiga bin mutanen dake parlon da kallo, idonta ya fara sauka kan Zayyad, tashi tayi ta tafi gunsa da sauri tace "Ina ya Khaleel din, did he leave after bringing me home?" Zayyad ya nuna mata Khaleel da ke tsaye yana kallonta, kallon handcuffed hands dinsa ta dinga yi sai kuma ta tafi gunsa almost running tace "What's this, waye yyi arresting din ka?" Komawa gun Mami tayi hawaye cike idonta tace "Mami wllh nice na bi sa ba shi ya tafi da ni ba, shi ba ruwansa, he only helped me, he is innocent, tell them not to arrest him plsss" Dai dai shigowar Asp tare da su Abba da Mahaifin Heedayah, Asp ya karasa gun Khaleel da makullin handcuff din ya bude ya cire handcuff din daga hannunsa, Heedayah ta tafi gunsa tana kallon wrist dinsa cikin sanyi tace "I am sorry I caused you everything" Mami ta nufeta ta dafata tana kallon Khaleel da ya sunkuyar da kai bayan ya hada ido da ita, ta kama hannunta za su fita parlon, Asp yana kallon Mami yace "Ku dakata Hajiya...." Kallonsa Mami tayi da sauran mutanen parlon, Asp ya kamo hannun Abba dake tsaye gefensa yace "Barrister Ahmad d'an uwan abokina ne da muka yi karatu tare, and we are still family frnds till date, 5 years ago Barrister ya xo station dinmu da wata yarinya da baxata wuce shekara 12 ba, a blind girl, lkcn Ina kano ba ayi transferring dina xuwa Abuja ba...." Very briefly Asp Usman ya bada wnn takaitattcen tarihin, Asp ya ci gaba yace "Shekarun baya, like 2 to 3 years back mu kan yi waya da shi in tambayesa how is this little girl kafin daga bisanni na watsar sanin baxai cuceta ba don a lkcn yace min har tayi regaining sight dinta, don har lkcn mu ba mu samu wani labarin iyayenta ba, but I must confess it's a case we never took serious, ganin makauniya ce ita wnn yarinya kuma gata yar karama, nafi xaton daga less privileged home ya fito, ni Allah ya ga xuciyata kusan gata nayi mata na son in ga ta xauna gun shi wnn bawan Allah, nasan shi da iyalansa baxa su cuceta ba, xa kuma ta samu gatan karatu..." Yana nuna Heedayah yace "As at the time this lady got missing yesterday evening, d'an barrister ya kai report police station dinmu, but bana office then, sai daxu da rana abokina Dr Umar wato yayan shi barrister din ya kirani ya sanar min halin da ake ciki, and I immediately reported to office to see the needful we can do about the case.... Sai dai cikin hukuncin ubangiji bamu ga yarinyar nan a ko ina ba sai gidan biological parent dinta yanxu, and yanda ni nayi tunanin iyayen nata ba haka bane, sannan ba ayi masu adalci ba kwarai da gaske...." Asp ya nuna Alhaji Ahmad that is also by his side trying all possible mean to control his tears yace "Mahaifin yarinyar nan kenan, Honorable Ahmad, we saw pictures, resemblance, and concrete proofs, that's just it, nan din gidan iyayen wannan yarinya ne" Heedayah ta juya tana kallon wanda Asp ke nunawa matsayin Mahaifinta, Khaleel couldn't stop looking at him also, Abba ya karasa gun Heedayah yana kallonta ya kamo hannunta gently yace "That's ur father Heedayah, I am sorry I never made any effort to take you back to them, I am sorry daughter" Rungume Abba tayi ta fashe da kuka sosai, almost whispering into his ears tace "You are always my father Abba, you remain my father" Mami taji ta kasa ci gaba da tsayuwa ta nemi waje ta xauna hawaye na sakko mata sosai, junaid dai ya dafe kansa kawai daga inda yake xaune, sai duk suke jin abun kamar a film, Mum Islam ta nufi Mami ganin yanda take kuka ta duka kusa da ita, ita ma tana share hawayen dake sakko mata tace "Mami nasan Dinar tun dawowarsu anguwar nan, mun shaku da ita sosai, har gaisawa mu kan yi da ke a waya in dai ta kira ki ina gidan ko kin kirata, amma duk bamu san ke ke rike da 'yar Mai gidana da ta bace shekaru biyar kenan ba, wanda har yau duk muna rayuwa ne da ita a ran mu, ba tare da sanin ko tana raye ko ta mutu ba, Heedayah 'yar kishiyata ce ta fari, wanda saboda bacewarta har yau ba a gane kan mahaifiyarta ba, but How can we pay for this great deed Mami? A blind little girl got lost, but we are seeing a sighted teenager now, baxa mu ta6a iya biyanku ba koda duk dukiyar Mahaifinta xa a baku" Mami bata iya ta ce komai ba sai share hawayen da ya ki tsaya mata take, sai take jin abun kamar a mafarki, so she is leaving Heedayah with them kenan yanxu, Abba dai na tsaye still holding on to Heedayah dake kuka sosai ita ma, shi kuma nan gani yake bai mata adalci ba bai ma iyayenta adalci ba, shi dai yasan ba da nufin komai ya banxantar da batun iyayenta ba, Abba ya kalli Alhaji Ahmad da ke ta kallon 'yar tasa shi ma yana tunanin how is he going to pay barrister Ahmad and Barrister Rahinah, Abba yace "Ina mahaifiyar ta?" Alhaji Ahmad bai ce komai ba, can ya nufi dakin matar tasa, kwance ya sameta ta takure waje daya, ya xauna gefenta ya dagota yace "Aisha ur Daughter Heedayah is back home, my assurance to you always, didn't go in vain, na sha gaya maki idan Allah ya amince Heedayah xata dawo garemu, and here she is today" Ta kamo hannunsa hawaye na bin fuskarta tace "Noo Ahmad kullum irin mafarkin nan nake, daga karshe sai kuma in tashi da wani ciwon, why is this dream taking long, don Allah ka tasheni daga wnn baccin, ni nasan ba gaskiya bane, irin mafarkin da nake yi kenan a ko da yaushe.... Daga karshe na tashi naga ba Heedayata, beside my Heedayah I know is blind...." kuka sosai take yi tana kallonsa, ya dagata suka fita dakin, suna fitowa parlor tayi ido hudu da Heedayah, kallonta kawai Heedayah ke yi, lkci daya ta xame hannunta daga na Abba, ta tafi da gudu ya rungume uwarta ta fashe da kuka, sai a snn mahaifiyarta ta tabbatar ba mafarki take ba, Heedayar tace ta dawo, but not blind Heedayah, ba mafarki bane, Cikin kuka tace "Heedayah" Heedayah bata mance muryar mahaifiyarta ba, har cikin ranta ta ji murya ta rungumeta sosai tace "Ammi I have missed you a lot, nayi missing din ki, you've always been in my thought, nayi missing din ki" Uwar ta kasa cewa komai sai hawaye, lkci daya Heedayah ta xame jikinta ta juya tana kallon Khaleel dake kallonsu, Bata san lkcn da ta nufesa da gudu ba ta rungumesa sosai, cikin kuka tace "You promised to take me to my parent, and u fulfilled ur promised, I love you dearly, and I will forever be grateful" Junaid ya sauke idonsa kasa daga kallonsu da yake, shi dai Khaleel na tsaye yana jinta har cikin ransa, but he is weak and breaking down, Baya yyi a hankali, ganin haka Heedayah ta sakesa tana kallonsa, ya dafe kirjinsa ganin xai kai kasa ta saki wani kara, tuni Zayyad ya mike ya nufo sa, haka ma Junaid da Abban Heedayah da Abba, with Asp, Mami ma ta mike tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Mami na xaune tare da Heedayah kan kujerun dake jere a dogon corridor din 4 wards dake wani bangare na hospital din, sai Abba da Alhaji Ahmad dake tsaye wajen su ma tare da Zayyad da Junaid, kusan awansu daya kenan a asibitin, Babban asibiti ne sosai me kuma tsada don a ward din da ake admitting authoritative patient ma aka kwantar da Khaleel, ba kowa ake admitting a wnn bangaren na Babban hospital din ba sai wanda ya isa, but being that Honorable Ahmad ne ya taho da Khaleel hospital din, nan aka kwantar da shi, Likitoci biyu ne suka fito babban ward din da ko kadan bai wani yi kama da dakin asibiti ba, dayan yyi wucewarsa, sai daya da ya tsaya yana kallon su Abba snn ya kalli Mami da gaba daya ta kasa samun natsuwa, smiling to give her assurance yace "His mother?" Mami ta d'an yi shiru sai kuma ta girgixa kanta tace "No" Zayyad ya karaso gun likitan gently yace "Ni abokinsa ne..." Likitan ya kalli Zayyad yace "Ohk, kai abokinsa ne, to iyayensa fa??" Alhaji Ahmad ya karaso gun likitan yace "If there is anything ka sanar min, we brought him to the hospital..." Likitan yace "Ohk sir, mu tafi office" Bin bayansa Alhaji Ahmad yyi xuwa office dinsa, Zayyad ya bude kofar ward din, politely wani likitan dake ciki yyi masa alamar da he should stay behind plss, rufe kofar yyi ya tafi ya xauna, gaba daya tausayin abokin nasa yake sosai don yasan wahalan da yake duk sanda ya samu attack, shi yasa tun safe yake ta kokarin ganin bai wahalar da kansa ba considering his condition but all in vain. Alhaji Ahmad na kallon Likitan yace "MI? Is that a disease?" Likitan yace "Yes, Myocardial infarction... Damage or expiry of any area of the heart muscle.... And this is as a result of lack of flow of blood to the area" Alhaji Ahmad yyi shiru, can yace "Was he born with that?" Likitan yace "I don't know, I can't tell, amma in sha Allah he will be fine, he just had an attack, amma kasan iyayensa? I mean are frnds with the parent?" Alhaji Ahmad yace "Not at all..." Likitan yace "Ohk then, but sbda condition dinsa yana da kyau ya dinga nesa da duk wani abu da xae daga masa hankali ko makamancin haka, I mean slightest of it, ya daina damun kansa a kan komai, kaga nasa kalan Heart attack din is very dangerous, a likitance ana kiran da wnn Heart attack din STEMI... Kuma alamu sun nuna ya dde da ciwon, he just need to learn how to live properly with it, in some cases ana surgery but I can't say tukunna, mun dai daura sa under medication ynxu, kuma in sha Allah xae samu sauki, in sha Allah" Alhaji Ahmad yace "Toh Allah ya basa lafiya, ya yaye masa" Likitan yace "Ameen honorable, that's just it, Allah ya kara mana lafiya baki daya" Alhaji Ahmad ya amsa da Ameen snn ya mike suka yi sallama da likitan ya fita. Alhaji Ahmad yyi ma Abba bayanin da likitan yyi masa, Mami dai na xaune daga inda take tana sauraronsu, sosai taji tausayin Khaleel jikinta yyi sanyi, Abba yace "To Allah ubangiji ya basa lafiya, Allah ya tashi kafadunsa" Alhaji Ahmad ya amsa da "Ameen" Alhaji Ahmad na kallon Mami yace "Hajiya I think ya kamata mu tafi yanxu it's getting late" Abba yace "Sure, abokinsa with Junaid can stay with him...." Junaid ya kalli Abba bai dai ce komai ba, Heedayah na kallon Mami a hankali tace "Mami pls can I go in and see him before we leave?" Mami tace "No Dr yace kar a shiga, gobe da safe xaki duba sa" Likitan da ke cikin ward din ne ya fito, Heedayah ta bi sa da kallo, Mami ta mike ta nufi Junaid, ganin haka Heedayah ta mike da sauri ta bi bayan likitan, a hankali Mami na kallon Junaid tace "I know baka son xaman hospital but kayi hakuri just for today" Ya gyada mata kai kawai, Heedayah na shiga office din likitan bayan ya shiga ya juya yana kallonta, a hankali tace "Good evening sir" yace "Evening dear how are you?" Ta marairaice tace "Pls I'm begging you can I go in to check on him?" Likitan yyi murmushi yace "He is asleep young lady, Gobe idan kin xo da safe xa ki gansa" Kamar xata yi kuka tace "Ae ba tashinsa xan yi ba kawai ganinsa xan yi" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Ohk, but don't go hear him ki tsaya daga middle of the room check on him and leave, promise?" Ta gyada masa kai da sauri tace "I promise" yace "Good, you can go in" Tana murmushi tace "Thank you sir" daga haka ta fita da sauri, Mami har ta fara nemanta a asibitin don su Abba da Alhaji Ahmad sun fita haraban hospital din, Junaid na xaune corridor din tare da Zayyad Heedayah ta dawo, bude kofar ward din xata yi Zayyad yace "Noo, it's not allowed" ta kallesa tace "I asked for permission" daga haka ta shige ciki, Junaid ya bi ta da ido har ta kulle kofar, kwance ta gansa saman gadon dake babban dakin wanda kamar ba a Nigeria ba tsabar haduwar ward din, ta tsaya dai dai inda likitan yace ta tsaya tana kallonsa yana bacci breathing dinsa very slowly, bata san lkcn da tayi breaking din promise din da tayi ma likitan ba ta karasa kusa da gadon da sauri, lkci daya ta ji hawaye ya kawo idonta, ta durkusa kusa da shi a hankali ta kamo hannunsa tace "Are you alright?" Bayan few seconds ya bude idanuwansa a hankali sai kuma ya sake kullewa, cikin sanyin murya tace "Are you feeling better now?" Ba tare da ya bude idonsa ba, murya can kasa yace "Sure" tace "Magani suka baka?" Ya girgixa mata kai, tayi shiru tana kallonsa don har sannan ya ki bude idon, murya can kasa yace "Injections" Hawayen dake makale idonta ya sauko tace "Allah ya baka lafiya" Ya gyada mata kai, ta kafesa da ido tana ta kallonsa, a hankali ya bude idonsa jin shirun yyi yawa, suna hada ido ya mayar ya rufe idon nasa, har sannan tana rike da hannunsa da yyi xafi tace "Ina yake maka ciwo" ya daga daya hannunsa da kyar ya nuna mata kirjinsa, ya mayar da hannun bayansa, sannan ya dafe forehead dinsa, wasu hawayen suka sake xubo mata cikin sanyin murya tace "In sha Allah xa su daina ka ji, you will be fine in sha Allah" ya gyada mata kai, ta xame hannunta daga nasa tace "We are going home now, get well before tomorrow plsss" Sae a snn ya sake bude jajayen idonsa murya can kasa yace "Thanks Heedayah!!" ta gyada masa kai sannan ta mike ta juya ta nufi kofa ta fita ta kulle, Mami na tsaye bakin ward din, da sauri ta sunkuyar da kanta, Mami tace "To mu tafi gida tunda ke baki jin magana" Mami ta yi wucewarta daga wajen bayan Zayyad yyi mata sae da safe, Heedayah ta daga ma Junaid da ya bi ta da ido hannu ta bi bayan Mami da sauri. A Motar Alhaji Ahmad Mami da Heedayah suka dawo gida tare da excort dinsa dake biye da su a baya, bbu ynda Alhaji Ahmad bai yi da Abba su taho nan gidan nasa tare ba Abba yyi declining yace xai tafi hotel din da yyi lodge, haka Alhaji Ahmad ya hakura ya kyalesa kawai, ganin Alhaji Ahmad xae shiga ciki da motarsa bayan masu gadi sun bude gate Mami tace "Xan sauka ba sai ka shiga ciki ba Alhaji" Alhaji Ahmad yace "No Barrister, you can spend the night here" Mami tayi murmushi tace "Thanks sir, xan shiga gidan Daughter na, will spend the night there in sha Allah" ita ma bbu ynda bai yi da ita ba ta kafe a kan gidan Dinar xata shiga hakan yasa ya hakura, ta bude motar ta sauka tana kallon Heedayah dake ta kallonta, Heedayah ta sauke idonta sai kuma ta bi ta xaya sakko Mami tace "Noo dear, go in with ur Abba" Alhaji Ahmad yace "Aa.... go with ur daughter barrister" Mami tace "Yau dai ta kwana tare da Ummanta, it's been long" Bata jira Abban Heedayah ya ce komai ba ta rufe