Showing 63001 words to 66000 words out of 275313 words

Chapter 22 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

Mumy xa su koma station, kaka ta dauko Hijab ta bi bayansu, Mami na kallonta tace "Kaka kiyi tsayawarki ki k'arya mana...." Kaka tace "Ce maki nayi yunwa nake ji, a fara abu da ni kuma sai a ki karewa da ni" Mami bata kuma ce mata komai ba ta bi bayan 'yan sandan suka fita, Kaka na biye da su da sauri. Hajiya Sadiya ta rike ha6a tana kallon Mumy da tayi tagumi tace "Ikon Allah, wllh wanda ya dauketa a gidan yake, bbu shakka ya gano komai ne yyi hakan, kuma ba kowa nake xargi ba illa Shuraim" Mumy ta dago da sauri tace "Shuraim?? Shuraim dai, A'a Shuraim baya ma gidan hakan ya faru, yana can asibiti" Hajiya Sadiya tayi wani dariya tace "Dai dai ma kenan tunda baya gidan, wato shine ya bi dare ya sadado ya dauketa...." Mumy ta mike tace "Haba Shuraim baxai ta6a yin haka ba, Bai san ma komai kan wannan plan din namu ba, to idan ma ya sani Allah na tuba meye hikimar dauketa balle bai sani ba, he has nothing to do with the blind girl a gidan, ko kallonta ma shi bai yi, Yan gidan ma yaushe ya samu lkcn yi masu magana balle makauniyar? Bai ta6a kallon inda take ba ma" Hajiya Sadiya tace "Wllh ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba Shuraim ne ya dauke yarinyar nan, idan ma xaki yarda ki yarda, wnn d'an naki baki san kyar yake kallon ki ba ko? to wai idan ba shi ba Aljanine xai shigo ya dauketa? Ke ki duba lamarin nan fa, sannan kince a bude kika ga gate din bayan gidan ba wai 6allawa aka yi ba, waye yasan wani inda makulli yake?? Gwara ki ajiye wnn batun na cewa Shuraim baya kula kowa a gidan, Kuma in har yaron nan naki na gidan nan bbu abinda xa a yi ma wannan yarinyar...." Mumy dake tsaye ta kasa cewa komai tace "Shuraim Kuma, Shuraim????" Hajiya Sadiya ta ja tsaki tace "Ai sai ki yi kuma, kema kinsan duk shirunsa shegen wayo ne da shi snn kinsan he is never in support of anything bad.... Tsaf shi xai dauketa sannan ya maidota bayan yaga duk an watse a gidan" Mumy dake xufa ciki da waje tace "To kuwa xan ci ubansa la'ada waje, xan ji ko shi ya haifeni ko ni na haifesa" Hajiya Sadiya tace "Atoh wnn dama dai ta wuce kuma, sai mu tari gaba, ga asara, ga xargin ki da kowa ke yi a gidan, ga kuma 'yan sanda na nemanki..." Mumy ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni wllh da ma ni na dauketa ko a jikina, amma bani bace sannan gashi kowa kallon ni na dauketa yake min, ga dai ta nan na hadu da ita a gate da xan fito amma sbda tashin hankali ko tunanin cutarta ban yi ba, kai a lkcn ji nayi na fi kowa farin ciki da dawowarta don wnn ba karamin case bane gashi kaka ta ga shigowana daga waje, da dai kattin sun shigo sun bubbuge kowa ne sun dauke yarinyar da Rabi'ah kamar yanda muka shirya daga baya sai su sako Rabi'ar ai kinga bbu shegen da xai xargeni, to ba a kai ga hakan ba aka nemeta aka rasa, Amma wllh idan har da gaske Shuraim na da sa hannu a dauke yarinyar nan sai na nuna masa ni na haifesa..... Sai ya yaba ma aya xakinta" Hajiya Sadiya tace "Ni duk ba wnn ba Maryam, yanxu dai daga nan har xuwa wata biyu ko daya da rabi babu ruwanki da yarinyar nan, tsakanin ki da ita ido, ko magana ba dole kiyi mata ba, sai mun bari kowa ya sakankance sannan sai a shammace su...." Mumy na share idonta tace "Tunanin da nayi kenan nima, shi kuma Shuraim don ubansa dama masters din nan dai da baya son yyi yanxu shi xai tafi yyi, ga Sudais har ya kusa gamawa, to dolensa sai ya tafi shima yyi, ko ya ki ko ya so wllh tllh sai ya tafi...." Hajiya Sadiya tace "Shkkn wllh, kinyi maganinsa cikin sauki" Mumy ta nemi waje ta xauna tace "Ita kuma wnn karuwar yanxu nake da lkcnta a gidan nan, na amince xan banxatar da batun makauniyar har na yan watanni ita kuma yanxu xa mu fara gogawa da ita" Hajiya Sadiya tayi dariya tace "Ki goga da wa? Matar da in ta fita tun safe sai yamma, ai bata da wnn lkcn sai dai makauniyar" Kiran Abba ne ya shigo wayar Mumy ta gyara xama da sauri ta daga ta kai kunne cikin sanyin murya tace "My Barrister"





Heedayah isn't free, you read for free πŸ€·πŸ»β€β™€οΈπŸ€·πŸ»β€β™€οΈ

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....

I am just super amazed at the well wishes from different angles, I really appreciate my lovely fans, Allah ya bar min ku, nagode kwarai da birthday wishes, Allah yayi mana albarka gaba daya, Ameeen.πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜πŸ’–
Those that didn't wish me kuma should come and patronize meee ejoo, shi ma love neπŸ₯Ί




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable....😍



3months later....


Kaka ce tsaye kan Khadijah inda take shiga ba nan take fita ba, Khadijah sai turo baki take tana yatsina fuska, Haka Rabi'ah dake tsaye bakin kofar parlon Mumy, Kaka tace "Yar banxa kawai me bakar fuska kazama, mummuna, ni dai wllh da ba don ina asibitin aka haife ki ba ma cewa xanyi ke ba 'yar Amadu bace canje aka masa, dama hutun da suka baku a makarantar cewa suka yi ku dawo gida ku dinga yi ma babban ku rashin kunya ban sani ba?" A fusace Khadijah tace "To wai ni kaka me nayi maki ne, ni kadai ne kika gani a parlon nan...." Kaka tace "Wllh Sudess xan kira yanxun nan ya casa min ke idan kika kara xagina, kawai don yarinya Allah ya yo ta makauniya sai ki juye mata shayin da take sha ki dura ruwa a kofin saboda bakin hali ko me? Sannan wannan yarinya Farida ta maki magana xaki hau ta da dambe kamar 'yar da6a? To bari yanxun nan xa a kira min Sudess, Allah ya rufa min asiri ya dawo shekaranjiya ai da lalacewa ta sameni" Khadijah ta fashe da kuka tace "To ita faridar Ina ruwanta da ni xata tsoma min baki?" Kaka tace "Aa wllh da ruwanta, bayan ni da uwarta Rakiya akwai me son Deedayah ne a gidan nan, to sai kilan Amadu duk da bamu san xuciyarsa ba, nan nan nan uwarki ta cakali Rakiya da fitina jiya Rakiya ta ki kulata, Farida kuma duk da dai agola ce a gidan bata fiye min ku ba sau dubu, Aa wllh ta fiye min ku, Maryam dai jaraba kawai ta haifa matsayin 'ya ya, idan ma bakin ciki kike faridar ta fi ki kyau ne ai sai ki fito ki fada in sa Amadu ya samar maki ko 'yar man kanti ne ki shafa kiyi hasken" Khadijah ta mike fuuu tayi wucewarta bangaren Mumy tana cewa "Gobe ta sake saka baki a harkana wllh wllh sai na mata dukan tsiya na farfasa mata baki" Farida dake tsaye bakin kofar Mami tare da Heedayah da ta rike rigar faridan, ta tabe baki tace "Toh ba sai ki dokeni ba, wllh karya ki xan yi...." A fusace Khadijah ta nufo Farida gadan gadan, kaka ta shiga kwala ba isiya kira da karfi, dai dai shigowar Shuraim parlon, Kaka ta fashe da kuka sosai tace "Shkkn kuma ni don mijina ya mutu ya barni bani da gata sai a ajiyeni a gida daga safe har dare ina ra6on katti yara fada, shi Amadu ya fita neman na xuba ma bakin salati, ita kuma wnn kinibabbiyar xabiyar ta bi sa ita ma aikin, uwarka kuma gantalalliya suna fita ta tafi gantali ita ma, wllh tun fitan iyayen suke dambe kamar raguna har an ji ma TVn Amadu, yanxu da baka dawo daga Zaria ba ya xanyi da raina yau, da gangan malam suka basu hutu don su kashe ni...." Shuraim ya kalli Farida da ta wani turo baki, ya kalli Khadijah da ta koma kofar parlon Mumy da gudu, ya karaso cikin parlon yace "Ku dawo nan gaba dayan ku" ko rufe baki bai yi ba Farida ta ja Heedayah suka shige parlon Mami ta sa makulli, Khadijah ta marairaice sanin in har ta shiga ya bi ta to mai kwatar ta sai Allah, Rabi'ah dake makale kofar ita ma tace "Allah ya so ni dai..." Kaka tace "Wa??? Ai kece katuwar munafukar ke ke sa Khadijah tayi komai, duk bakin ki daya" Rabi'ah ta fashe da kuka sosai tana kallon kaka, Shuraim ya hade rai yace "Baxa ku dawo nan ba nace" Khadijah ta Rabi'ah suka fito main parlon suna matsar kwalla, Cikin rawar murya Khadijah tace "To ita Farida fa Yaya" buge bakinta yyi, kaka tace "Ai ba kyaleta xa ayi ba, abinda ba tsoron ta yake ba" Da wayar rechargeable ya xane su a tafin hannunsu gaba daya, yayi wucewarsa dakinsa, Kaka da tayi tagumi tace "Dama dai neman wanda xai duka yake tun daga Zaria, Banda haka ga dai katti sa'anninsa a titi ya baro ya shigo gida ya ci xali, ku dai kuyi hakuri ku bar sa da Allah kawai" Rabi'ah da ke kuka sosai ta dinga hararan kaka, Khadijah na Shessheka tace "To mu kadai xai doka, ita faridan fa" kaka tace "Waye ubanta da baxa a doketa ba tunda aka doke ku, ai yanda yyi maku haka xai mata ba cuta" Rabi'ah tace "To Heedayah fa?" Kaka ta kalleta da sauri tace "Aa ke kuma baki son gaskiya, waye kuma Heedayah? Me tayi xa a doketa, to ko ma tayi in dai shi ba wawa bane akan me xai doketa, ko kula ku kinga tana yi a gidan nan, to ai ita ba gantalalliya bace kamar ku" Khadijah ta mike tana hararan Kaka ta wuce part din Mumy, Rabi'ah ta ja tsaki ta mike ta bi bayan Khadijah, kaka tace "Oho dai an dai sha mazga" Farida ta ja tsaki tace "Haka xa mu yi ta xama kenan baxa mu ci abinci ba, ni dai baxan sha cornflakes ba" Heedayah dake shan cornflakes dinta ta ta6e baki tace "Ni ina ruwana, wnn da kike ganinsa din nan mugu ne, wllh duka xai maki in kika fita" Farida tace "To a ina ya san ni da xai dokeni? And ni fa Ina ce shine Sudais" Heedayah tace "Aa ba Yayana bane, wannan Ya Shuraim kamar naji suna ce masa, I never liked him even for once" Farida tace "To da ina yake tun da na xo ban gansa ba" Heedayah tace "Ban san Inda yake ba, but yana dawowa every Saturday" Farida ta ta6e baki tace "To kawai bai san ni ba sai ya dokeni" Heedayah tayi dariya tace "That's because he is wicked" mikewa Farida tayi tace "To kinga mu lallaba mu je in xubo mana" Heedayah tace "Ni baxan je ba" Farida tace "Plss mana I can't go alone, da sauri fa xan xuba mana mu dawo" Heedayah ta juya manyan idanuwanta tace "To ki jira in gama shan Cornflakes dina" Farida tayi tagumi tace "Tohh" Heedayah na gama shan Cornflakes din Farida ta ja ta suka fita main parlor, bbu kowa parlon sai Tv dake kunne, Farida na rike da hannunta suka shige kitchen da sauri ta kulle kofar, Sajida da Karime ne suka yi lunch a gidan, Farida ta bude warmer da abincin ke ciki ta debi shinkafa knn xata bude na miya aka bude kofar kitchen din, Shuraim ne ya shigo da wayar rechargeable a hannunsa, tana ganinsa ta fasa ihu ta saki murfin warmer din hannunta, Heedayah ta ja gefe a tsorace, cafkota yyi, ta rikesa tana basa hakuri a tsorace, Bai ko saurareta ba ya rike hannunta ya dinga lafta mata wayar hannunsa, Kaka ta shigo kitchen din a guje tana cewa "Wayyoo wllh uwarta lauya ce daure ka xata sa ayi shureen, idan ka doke wasu ka kwana lafiya to ita wllh a seff xaka kwana bbu me ceton ka, yau fa kwananta hudu da xuwa gidan, ta dawo daga tsadadden makarantar kwanan nan, duk da dai fitinanniya ce ai tayi min wanki yau kuma ta wanke min bandaki, ko da yake jika jika tayi amma ai tafi munanan kanninka..." Sai da Shuraim ya lafta mata son ransa sannan ya saketa, ta durkusa a wajen ta dinga ihu tana kiran Mami, ya kalli Heedayah da ta rakube gefe daya a tsorace hawaye cike idonta, ya nufeta fuska daure kaka ta dakata da surutan da take ta shige gabansa tace "Aa nan kuma ne xan sa 'yan anguwa su lallasa min kai, uban me xaka mata?? Ai wllh idan ka doki gantalallun nan ka kwana lafiya to kana ta6a Deedayah maka ka xanyi a kotu, me makauniyar tayi maka, duk da dai ita ma ba kyalle bace" kallon kaka kawai yake fuska daure, ta kama hannun Heedayah ta fice daga kitchen din tana cewa "Ni dai ba ruwana" Farida ta wani hararesa ta mike xata bi bayansu, xai cafkota ta fice a guje ta shige dakin kaka... Uku saura Mumy ta dawo gidan, su Rabi'ah suka tsara mata abinda ya faru da safe, tayi shiru tana sauraron su, can tace "Tafi maxa ki kira min Shuraim din" Khadijah ta kwanta saman gado tace "Tabbbb" Rabi'ah tace "Ni dai kar ma kiyi masa magana Mumy, wllh dukan mu kawai xai kara yi" Karime ce ta shigo parlon, Mumy tana kallon su Khadijah tace "Ku fita" duk suka mike suka fita, Karime ta xauna kasa tana ta6a baki tace "Hajiya ji nayi daxu a waya tana gaya ma wani wai an kusa fita da Heedayan waje ayi mata aikin idon..." Mumy ta gwalo ido tace "Haba??" Karime tace "Wllh kuwa haka na ji...." Mumy ta gyara xama tace "Wa kika ji tace xai fita da ita?" Karime tace "Wannan ne ban sani ba Hajiya" Mumy tace "Har dai yanxu baki san Inda kaka ke boye maganin nata ba ko?" Karime tace "Ai yanxu kaka ta ma daina sa ni gyaran dakinta, Sajida ce ke yi" Mumy tace "Toh watan barin gidan Sajida ya tsaya" Karime tace "Wllh daxu da safe kafin Hajiyar ma ta fita aiki ga dai ni a xaune amma Sajida ta sa taje dakinta ta dauko mata makullin mota, ni ta ma daina bari in shiga dakinta ynxu...." Mumy tace "Akwai wani aikin da xan baki yanxu, kuma in sha Allahu idan kika yi kokari kika cika aikin, dubu biyar xan baki kyauta..." Karime ta washe hakora tace "Hajiya ai ko baxa ki ban komai ba...." Bude kofar parlon da aka yi yasa duk suka yi tsit, Shuraim ne ya shigo da sallama, fuska daure Mumy tace "Wannan ai walakanci ne, ayi shinkafa dafaduka jiya, yau kuma ayi shinkafa da miya, tunda Sajidar tace maki baxata yi ba ke ba sai kiyi ba..." Juyawa Shuraim yyi xai fita Mumy tace "Ina kuma xa ka?" Yace "Naga kuna magana ne ai" Mumy tace "Kawai masu aikin jaraba suyi ta sa mutum magana, suna ba mutum wahala" Bai ce komai ba shi dai ya fita, Karime ta kalli Mumy, Mumy tayi kasa da murya tace "Yaushe ya xo?" Karime tace "Tun safe" Mumy tace "Tashi ki tafi xan neme ki anjima" Mikewa tayi ta fita... Kaka nata aikin linke linke a dakinta, Farida na dakin tana taya ta, Kaka tace "Toh dama idan ba ke ba waye xai taya ni, ita wancan makauniyar ba wai amfani gareta ba" Heedayah dake kwance tayi rub da ciki tana jin kaka bata dai juyo ba, Farida tace "Kaka wai shi ma a nan gidan yake xama?" Kaka tace "Wa?" Farida tace "Wannan da ya doke mu mana" juyawa Heedayah tayi daga kwancen da take tana kallon direction din da take jin muryarsu, kaka tace "A'a yana can Zaria yana karo karatu, ko massers naji suna kiran karatun, kinsan bbu yanda ba ayi da shi ya fita waje kamar yanda Sudess yaje can yake yi ba amma ya ki, uwarsa kuwa kamar tayi hauka don ta kwallafa ran fitansa, kin santa da fafa, so tayi ta bi duk kawayenta tace d'an ta na kasar waje yana karatu, to da yake shi ma Amadun kila ba wani son kashe kudi yake ba ya goya masa baya kar ya fita, duk sati kya gansa salalo salalo wai ya xo gida hutu, duk ya bi ya takure jama'ah...." Bude kofar dakin aka yi sai ga Shuraim, Farida ta juya da sauri ta ci gaba da linkin da take, kaka tace "D'an Halak, yanxun nan take tambayata uban me ke dawo da kai gida, shine nake bata labari" da sauri Farida tace "Ni fa ba shi nake tambayar ki ba...." Tana fadin haka ta nufi kofa ta fita ya bi ta da kallon gefen ido, ya kalli Heedayah dake kwance, kaka tace "Ka ji wai ita kuma yau bata son tayi karatun, kuma duk inda malamin yake nasan yanxu yana hanya, dubu ashirin da biyar haka Amadu ke biyansa duk wata, to banda Allah wa xai biya mu, bbu fa abinda muka hada da ita....." Heedayah ta mike xaune tana sauraron kaka kamar xata yi kuka, kaka tace "Kasan idan ba mutum ke biya ma kansa ba sai yyi ta iskanci iri iri, sai ka ga uban tsaraban da Sudess ya yo mata daga kasar turawa, ni tsoro ma kamani yyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login