Showing 93001 words to 96000 words out of 275313 words

Chapter 32 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

su xo wucewa su gan ni su tafi da ni, don girman Allah ka gaya min asibitin in je jay...." Yace "Toh wai da kike ta kirana ni na kawo ki India ne baiwar Allah?" Tace "Amma silar ka na xo ai, Allah sbda kai na biyo Suraj duk da nasan Mahaukaci ne, to wa xan kira idan ba kai ba" Junaid ya ma rasa me xai ce mata, ita kuwa sai rera masa kuka take a kunne, can ya ja tsaki yace "Ina kike yanxu" Tana kuka ta gaya masa ya katse wayarsa, bbu ynda ya iya haka ya dau kudi ya fita hotel din ya kulle dakin, Tricycle ya samu xuwa Inda tace masa take, ai ko ya sameta gefen hanya ita kadai xaune kan jakan kayanta, yana sauka daga tricycle din ta mike xaune duk idonta yyi suntum sbda kuka, yana mata wani kallo yace "Ashe ke karamar yar duniya ce tunda har xa ki shigo India ki rasa wajen kwana duk yawon da kike da maxa kasashe daban daban" Ita dai bata tanka sa ba ta dau jakarta ta saka cikin Tricycle din da sauran kayanta sannan ta shiga ta xauna, yyi kwafa ya shiga adaidaitan suka koma hotel din da yake, Sai karfe kusan daya da wani abu suka shigo hotel din, tana ganin wani dakin xai biya mata tace "Aa jay kada ka wani kashe kudin ka, ni dai gwara kawai ka harhada ka biya min kudin jirgi in koma Nigeria" Bai tanka ta ba yyi wucewarsa sama ta bi sa da kaya tana tangal tangal don ko daya bai dau mata ba, yana bude dakin ya shiga ya bar mata a bude ta shigo sannan ta kulle tana bin dakin da kallo, saman gado ya nufa ya dau bargo da pillow ya jefa mata a kasa snn ya kashe wutan dakin yyi kwanciyarsa, ta ajiye kayanta ta dau pillon da bargon ta shimfida bargon sannan ta daura pillon a kai, a hankali tace "Nagode, amma xan d'an kunna dim light sbda xan yi wanka" Ko tanka ta bai yi ba ya juya mata baya yana danna wayarsa, bayan kusan minti goma ya ga ta kunna wuta mara haske sosai ta shiga bandaki, yana jin alamar tayi wanka ta fito, mamaki ne ya cikasa sosai ganin naked ta fito daga bandakin walking majestically, a hankali ya ajiye wayarsa ya rufe ido ya tsiri baccin da bai yi niyya ba a lkcn, ta gama buruntunta ta cika dakin da kamshin turare iri iri da ta fesa a jikinta, shi dai idonsa na rufe gam, xagayawa tayi kusa da shi tace "Don Allah ka d'an ban wayarka xan kira yayata, tun daxu take kirana sbda tashin hankali ban dauka ba gashi ynxu bani da isashen kati" yyi banxa da ita har sannan idonsa a rufe, ta kai hannunta me sanyi a hankali fuskarsa tace "Kayi bacci ne Jayy?" Lkci daya ya mike xaune ya sauke mata lafiyayyen mari yace "I swear to Allah ba karamin aikina bane in fitar dake hotel din nan yanxun nan, are you mad????" Mikewa tsaye tayi da rigar baccinta iya cinya bbu komai ciki ta dafe kuncinta tana kallonsa, yyi mata tsawa yace "Baxa ki tashi gabana ba sai nayi ball da ke" gyada kai tayi ta juya tana karkade karkade ta xaga Inda ta shimfida bargo ya bi ta da wani irin kallo, yyi wani kwafa ya koma ya kwanta ya rufe ido.... Daren ranan dai bai yi bacci ba sai juye juye yake shi kadai, sae dab da asuba bacci ya daukesa, hasken ray din rana da ya sauka fuskarsa ne ya farkar da shi, ya mike xaune da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa, gefensa ya ga Salima kan gadon tana bacci hankali kwance, bbu abinda baya gani a jikinta ta cikin shegen kayan baccin da ta saka, tashi yyi da sauri ya shige bandaki, tun da yake dai da girmansa bai ta6a missing sllhn asuba ba ko a jam'i ko ba a jam'i ba, da asuban xai yi raka'atainil fijr snn yyi sllhn sa amma wai yau shine har kusan 8 bai yi sllhn asuba ba, ransa a bace ya wanke baki yyi alwala ya fito ya shimfida darduma ya tada sllh, ya kusa minti sha biyar saman darduman bayan ya idar sannan ya mike ya buga gadon da karfi yace "Dauki kayan ki mu wuce airport...." Ta bude ido a hankali tana wani juye juye tace "Anya ma da jirgin xuwa Nigeria direct kuwa yau??? stopovers....." Yyi mata wani tsawa kafin ta karasa yace "Tashi ki dau kayanki ki fita ki samu wani wajen xama har a samu plane din Nigeria, not here anymore" ta marairaice tace "Toh amma ae ka jira inyi wanka in shirya tukun mana Jayyy" tana fadin hka ta mike tsaye dab da shi, ya dauke kai ya bar wajen, wayarsa ya nufa ya dauka ya ga miss calls din Mami har Uku, xaro ido yyi don kullum ana idar da sllh asuba yake shiga asibitin with breakfast, fita yyi dakin da wayarsa in a haste, sae da ya tsaya hanya ya siya masu breakfast snn ya wuce asibitin.... Mami na xaune kusa da Heedayah dake shan shayi a saman gado da kwai da bread, she looks very strong, an kuma sauya mata eye pads din idonta, tana jin an bude kofa ta dakatar da shan shayin tace "Mami Yaya ne?" Mami dai bata ce komai ba sae kallon Junaid take daga sama har kasa, coz duk a birkice yake, snn bai ta6a shigowa asibitin da jallabiya ba, kansa a kasa yace "Ina kwana Mami" Mami ta amsa ta dauke kai ta ci gaba da danna wayarta da take, yayi kasa da murya kamar munafuki yace "Mami na makara ne yau wllh...." Still bata kallesa ba tace "Ehh na ga alama" Yace "Ga breakfast...." Tace "Don't worry an kawo mana" Da mamaki ya dago kansa yace "Who??" Kafin tace komai aka bude kofar ward din ya juya don ganin wanda xai shigo....




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍




Sudais ne ya shigo ward din shi ma yana kallon Junaid kamar ynda Sudais ma ke kallonsa, Heedayah tace "Mami waye? Ya Sudais?" Mami tace "Eh" Sudais ya nufi Junaid yana murmushi ya basa hannu suka gaisa, Mami tace "Har ka dawo" Yace "Ehh na dawo Mami" kujera ta nuna masa ya xauna, Shi dai Junaid na tsaye har sannan ya ki yrda su hada ido da Maminsa, Heedayah tace "Yaya me ya sa baka xo tun daxu ba sai yanxu, Ya Sudais ne ya kawo mana breakfast fa" Ya d'an kalleta yace "Ban xo din ba" Ta buda hannu ta tabe baki tace "Ae kai da Mami" Sudais dake murmushi yace "Ko dai shi da ke?" Washe hakoranta tayi bata ce komai ba ta ci gaba da shan shayinta, can ta ajiye cup din tace "Ya Sudais me ya sa baku xo da kaka ba, Ina missing dinta" a hankali ta kara da cewa "I am also missing Abba" Sudais yace "Xa su xo in sha Allah" Junaid dake ta tsaye ya dake ya kalli Mami yace "Mami xan je in dawo" Bata ko kallesa ba tace "Ohk" a hankali Heedayah tace "Yaya Ina xaka kuma? You are just coming fa" Yyi banxa da ita ya fita dakin.... Rai bace ya koma hotel din ya bude kofar room din ya shiga ga mamakinsa Salima kara gyara ma kayanta wajen xama tayi, ga gadon ta gyara sa fess sae kamshi ko ina yake amma bata dakin, daukar kayan yyi ya fito fuska daure har haraban hotel din ya nufi gun masu gadi nan ya bar masu kayan bayan ya sanar masu me shi xata xo ta amsa, yana komawa ya ga handbag dinta a dakin, har ya dauka sae ya tsaya ya bude ciki, duk tarkacen kayan kwalliyanta ne ciki da prophylactic na mata har da maza and different types of pills ciki har da aborticide, ya girgixa kai cike da takaici ya rufe jakar ya fita dakin ya kai can gun masu gadi sannan ya koma dakinsa, wanka yyi ya shirya ya d'an kwanta, gaba daya jin sa yake wani iri, bayan kusan minti talatin ya mike a hankali ya dau wayarsa ya fita ya kulle dakin da makulli ya bar hotel din. Asibiti ya koma kafin ya shiga ya kira line din Salima, ba bata lkci ta daga tace "Jayyy" ya wani daure fuska kamar tana ganinsa, strictly yace "Ga kayanki can gun masu gadi na ajiye ki dauka, and don't ever try calling my line again idan ba haka ba xa ki sha mamaki, I repeat don't try calling my line again...." Salima ta marairaice tace "Ban gane kayana na gun masu gadi ba jay, me ya kai kayan gun masu gadi juma? Ai na dau spare key kafin in fito" shiru Junaid yyi da mugun mamaki jin abinda tace, can ya ciro makullin aljihunsa yana kallo, wani tsawa yyi mata yace "I swear to Allah kada ki yrda in dawo ya in sameki hotel room din nan, duk abinda na maki ke kika ja ma kanki kinji na rantse...." Ta fashe masa da kuka tace "Toh wai ina kake son in je yanxu Jay? Bayan na gaya maka wanda ya kawo ni ma yyi blocking dina kuma bani da kudin komawa Nigeria? Haba Jay sai kace baka ta6a sanina ba" cikin fushi yace "Good... nima ynxu xan yi blocking din naki but before then I am still warning you kada ki yrda in dawo in ganki dakina, wllh sai na maki abinda baki yi tunani ba" Bai jira cewarta ba ya katse wayar yayi blocking din nata sannan ya shiga cikin asibitin trying to calm himself, shi ma ciki bai wani ga fuskar Mami ba hakan ya sa ya fito haraban asibitin ya xauna.... Har aka yi azahar Junaid na xaune ne haraban asibitin ya ki shiga ward din, bayan azahar kuma Sudais ne ya fita ya siyo masu abinci ya kawo, Mami na xuba ma Heedayah, Heedayah tace "Mami ko dai Yaya ya wuce ne?" Mami bata ce mata komai ba, Sudais yace "Yana waje, ko xa ki je?" Ta make kafada tace "Aa ba ruwana da shi ai" Da daddare bayan isha Junaid ya shigo ward din da dinner da ya siyo masu, Mami da Heedayah ne kadai dakin Sudais baya nan, Yana ajiye masu kuma yace "Mami xan tafi in kwanta" Mami tace "Good, Ka jira Sudais he went to get something sai ku tafi tare" Da mamaki yace "I tot yyi lodging hotel ai" Mami tace "Yes he did, amma nace ku tafi tare naka hotel din" Junaid yace "Ohk" daga ya nemi waje ya xauna ya d'an kalli Heedayah bai ce komai ba ya fiddo wayarsa yana dannawa silently, sai wajen takwas da rabi Sudais ya shigo ward din ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Mami Abba ya kira ku?" Mami tace "Yes Ina sllh ya kira but I followed the call yanxu" yace "Ohk" ya dau apple daya ya kama hannun Heedayah ya saka ciki, kin sake hannunsa tayi a hankali tace "Thank you...." Mami tayi murmushi bata dai ce masu komai ba, kallonsu kawai junaid ke yi amma ba directly ba, Sudais na juyowa ya maida idonsa saman screen din wayar dake hannunsa da sauri, Mami tace "Sudais kai yake jira ku tafi hotel ynxu" Sudais yace "Ohhh but ai nayi lodge a wani hotel Mami" Mami tace "Noo, ku tafi tare, you two should stay together" Junaid dai idonsa na kan wayarsa amma Mami yake saurara, can ya mike ya maida wayar aljihu yace "Toh sai da safe Mami" Daga haka ya nufi kofa, Mami bata tanka sa ba tace "Sudais baxa ka debi fruit din ba, ai sun yi yawa" Yace "Noo na sha ai" tace "Ohk sai da safe" yace "Allah ya tashe mu lafiya" Heedayah tace "Yaya Sudais byee" yace "Bye dear...." Junaid na tsaye bakin kofa bai fita ba, can ya tabe baki ya fita yyi wucewarsa, Sudais ya bi bayansa duk da har ransa bai so bin junaid ba amma baya son yi ma Mami musu, sai bayan da suka fita Heedayah ta fashe da kuka a hankali tace "Mami kinga yaya bai kulani ba koh, he don't want to talk with me" Dariya ta ba Mami sai dai bata yi ba, Mami tace "Kyaleni da shi xan yi maganinsa" Tunda suka bar hospital din Junaid bai ce da Sudais komai ba, haka shi ma Sudais din, nan ko Junaid is just imagining ace su je hotel din ya tadda Salima a dakinsa, suna isa hotel din suka sauka tricycle din Sudais ya bada kudi, Junaid ya jira aka basa canji sannan suka shiga hotel din a tare, Junaid ya tsaya gun masu gadi yana tambayar ko mai kayan daxu ta xo ta dauka, suka amsa masa da eh, bin bayan Sudais yyi xuwa cikin hotel din, a hankali Junaid ya fara murda kofar dakin ko makullin bai sa ba ya ji kofar a bude, lkci daya xuciyarsa ya fara tafarfasa ya shiga dakin, Sudais ma ya shiga ciki, xaune suka samu Salima da takeaway din abinci tana ci a dakin, Sudais ya tsaya bakin kofa yana kallonta with so much surprise, Mikewa tsaye tayi ita kanta tayi shock din ganin Sudais, Junaid ya nufeta a mugun fusace ya sauke mata wawan tagwayen Mari cikin tsawa yace "Me na ce maki? What did I tell you???" Dafe kuncinta tayi tana kallonsa with shock, can ya fashe da kuka tace "Toh wai ina kake son in tafi bayan nace maka bani da kudi Jay, Banda sbda kai me xai kawo ni kasar nan??" Gun kayanta ya nufa ya dauke jakunkunanta biyu ya bude kofa ya watsar waje ya dawo ya nufota, tana ganin haka ta shige bandaki da gudu ta sa makulli, Sudais na yatsine fuska da mamaki yace "Me ye hadin ka da yarinyar nan? Me ya kawota nan? Dama da ita aka taho" Rai bace junaid yace "Saurayinta fa ta biyo ya koreta shine ta makale min nan, I don't even know her...." Katse sa Sudais yyi yace "Sorry but I can't stay under same roof with this lady, dama na kama hotel I can't just say no to Mami, it's better in koma can, but be careful with this lady she can be cunning" Junaid ya dau jakarsa shi ma yace "Mu tafi hotel din naka, I am not staying here either, dama kudin kwana 15 na biya for this hotel kuma nan da jibi xai yi expire so I prefer leaving too" Sudais yace "Better...." Daga haka suka fita dakin xuwa hotel din Sudais. Salima na jin alamar sun fita ta bude kofar ta leko ganin ba kowa ta fito dakin, ba karamin tsorata tayi ba ganin Sudais, ita a rayuwa ma akwai wanda ta tsana kamar shi kuwa, ko gaisuwa baya hada ta da shi dama, cije yatsa tayi ta xauna gefen gado a hankali tace "Anya ma Junaid din nan na da lafiya kuwa, upon everything yesterday he isn't still moved" Da sauri ta mike ganin bbu jakar kayansa ta tafi window tana lekawa taga Inda suka nufa, tricycle taga suka shiga, ta koma ta xauna ta marairaice tace "Dama Sudais ma na kasar nan ban sani ba??" Can ta gyada kai tayi wani murmushi tace "idan ka san wata baka san wata ba Junaid" Tun da Mami ta tashi yau da asuba take ta fargaba ita kadae don ranan xa a cire ma Heedayah eye pads din idonta, kuma ranan ake sa ran xata fara gani, daren ranan Mami sae da tayi sllh ta roki ubangiji yasa an dace, ya sa karshen wahalan kenan.... Karfe shidda da rabi likitocin suka fita da ita xuwa theatre, Mami dai na xaune bakin theatre din sae addu'a kawai take, ga faduwar gaban da yyi mata yawa, da taji motsi sae ta kalli kofa da sauri amma bbu wanda xata ga ya fito har karfe bakwai da rabi, kukan da ta ji Heedayah ke yi daga ciki ya fi daga mata hankali, tun daga nisa take kallonsa har ya karaso tare da wani likita baindiye walking slowly, likitan ya gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa don da shi aka yi ma Heedayah aiki 3 days back, shi ma dai yyi kasa da kai ya gaisheta, ta amsa tace "Ya hanya" Yace "Alhmdllh, ya kokari" tace "Mun gode Allah" baindiyen yayi tapping dinsa a baya da harshen turanci yace sae sun hadu anjima, daga haka ya juya ya wuce, dai dai fitowar wani likita yana kallon Mami yace "You can go in Madam, a Dr will explain everything to you inside" mikewa Mami tayi amma ta kasa tambayarsa ba ayi nasara bane aka ce ta shigo, kuma ta kasa shiga ciki, likitan yayi wucewarsa, kansa a kasa ya nufi kofar shiga theatre din walking slowly, Mami ta bi sa da kallo har ya shiga ciki, Heedayah na xaune saman gadon ta takure waje daya ta rufe fuskarta da pillon saman gadon tana kuka a hankali, likitoci biyu na tsaye suna jiran shigowar Mami, Daya daga likitan da turanci yace "Her brother?" Ya gyada masa kai sannan ya karasa gadon yana kallonta, likitan yyi murmushi yace "Yes it was successful, but it's a new world to her....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login