Showing 207001 words to 210000 words out of 275313 words

Chapter 70 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

ta jingina jiki gabanta na wani irin faduwa flashback din shekaru shidda da suka wuce da muryarsa na sake dawo mata, sai yanxu ta tuna inda ta ta6a jin muryarsa, shi ne wanda ya kama hannunta ya saka mata bread bayan an sanar masa bata gani a lkcb, snn shi ya xo ya dauketa ya sa ta a bike ta tuna ihun da ta dinga yi and he told her he have gun wanda hakan ya tsoratata sosai a lkcn, yess muryarsa ce, ji tayi gaba daya jikinta ya dau rawa kafafuwanta sun kasa daukarta, ta fi minti biyar a haka can ta bude kofar kitchen din a hankali ta fito parlon, yana durkushe yanda ta bar sa, jin an bude kofar kitchen din ya juya ganinta yace "Heedayah...." Bata ko kallesa ba ta wuce sama da gudu xuciyarta na bugawa, ya bi ta da ido... Sai kuma ya dafe kansa da yyi masa nauyi lkci daya, a haka Mami ta shigo parlon ta samesa, ya dago da sauri, tace "Lafiya Khaleel??" yyi murmushin karfin hali yace "Aa ba komai, sannu da dawowa" Tace "Yauwa, ina Heedayar?" Yace "Ta wuce sama yanxu" Mami ta sake hannunsu su Ashnaah ta nuna masu sama duk suka wuce, ta xauna tana kallon Khaleel tace "Is everything okay?" Ya sauke idonsa kasa ya xauna nan kasa yace "In sha Allah" Tace "Baka sha lemon ba?" Ya kalli drink din da Heedayah ta ajiye masa yace "Xan sha" tace "Ko a kawo maka abinci?" Ya girgixa mata kai yace "Alhmdllh na ci abinci" Ita dai sai kallonsa take, bayan few seconds yace "Dama ina jiran ki dawo ne, xan wuce" tace "To xaka shigo anjima" ya gyada mata kai yace "In sha Allah" ta mike tace "Toh shkkn Khaleel, bari a kira Heedayar" da sauri yace "Aa mun yi sallama da ita" Mami ta juya tana kallonsa ya mike yace "Nagode Ummi, sai anjima" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta koma ta xauna a hankali, ko kadan bata gane feeling din da xuciyarta ke samu idan taga wnn bawan Allah, muryar Yakumbo taji tana cewa "Rahinah ashe kina da babban d'a dama bani da labari, wnn ma har ya fi Junaidun nutsuwa da kunya naga" Mami ta kalleta tace "Wa kenan?" Yakumbo tace "Au har ya tafi kenan, nan na samesa tare da Heedayah" Mami tayi shiru, can tace "Aa ba d'a na bane, ya xo gaisheni ne" Yakumbo tace "Toh ai d'an d'an uwanka ko yar uwarka naka ne, jini ai ba wasa bane, ga kamanninku nan tare da shi kuma kice ba d'an ki bane, kuma ko ba komai suna yanayi da Junaidu sosai, ke kanki ma idanunku iri daya ne da nashi, to ita kuma Aisha bata da niyyar dawowa ne ta debi sojoji suna gadinta tana xaga gari don neman suna, kai samun waje ma dai bai yi ba wllh, tun safe an shanya mu ba alamar wucewarmu fisabilillahi, ita kuma wancan tsohuwar me gilla karya har yanxu bata iso ba ta kuma ce min da sassafe xata xo, Amadi dai yace a taho da ita, Kar mu je bbu ita ya kullace mu tunda ta nace sai ta bi mu" Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta ya tsaya mata a xuciya daban. Farida ta rufe laptop dinta tana kallon kofar bathroom don kusan minti talatin kenan da shigan Heedayah har yanxu bata fito ba, har lekowa Mami tayi daxu tana tambayar Heedayar tace mata tana bayi, kuma ita bata ji alamar wanka take ba, mikewa tayi ta isa bakin kofar ta kwankwasa, jin bata amsa ba ta bude kofar bathroom din, durkushe ta ganta bandakin ta hade kanta da gwiwa, da mamaki Farida ta karasa ciki ta dago kanta tace "What's wrong Heedayah" hawaye ta gani sha6e sha6e fuskarta, Farida ta buda ido tace "Subhanallah, me ya faru? What happened?" Heedayah ta fashe da kuka a hankali, Farida ta dagota hankali tashe tace "Ki gaya min me ya faru Heedayah, me aka maki?" Heedayah ta rungumeta tana kuka sosai amma ta kasa cewa komai, Farida ta fito da ita daga bandakin ta xaunar da ita gefen gado tace "Don Allah ki gaya min menene? An maki wani abu ne" cikin rawar murya Heedayah tace "I don't want to say anything about it Farida..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai, cike da damuwa Farida tace "Don't you trust me Heedayah, talk to me plss" Heedayah ta runtse ido trying hard not to burst out again tace "Khaleel" Farida ta bude ido tace "What about him? Is he back??" Da kyar tace "Am thinking...." Sai kuma tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Farida tace "What are you thinking?" Rungume Farida tayi cikin kuka sosai tace "He is a kidnapper Farida, wllh kidnapper ne" Still Farida tayi jin abinda Heedayah tace, can ta dagota with so much shock tace "How did you know?? who told you that?" Heedayah tace "Shine ya fito da ni daga wajen kidnappers ya ajiye ni bakin titi years back" Heedayah bata kai Farida tsorata ba, Banda xare ido bbu abinda Farida ke yi kamar warce tayi ma sarki karya, cike da karfin hali tace "Who told you all this Heedayah?" Hawaye na sakko ma Heedayah tayi ma Farida bayanin komai, Farida da tayi mugun tsorata tace "Is he still in this house?" Heedayah ta buda mata hannu alamar bata sani ba hawaye me xafi na sakko mata, Farida xata mike Heedayah ta rikota tace "Promise me this will be a secret between us, don girman Allah kar ki gaya ma kowa not even Mami" hawaye ya kawo idon Farida ta koma ta xauna tace "Why secret Heedayah? Xa ki ci gaba da alaka da d'an kidnapper ne? What will be our faith?" Heedayah ta fashe da kuka tace "Not at all, baxan ci gaba ba, amma...." Farida tace "Amma me?" A hankali Heedayah tace "Yasa na fara sonsa, I don't know how that happened all of a sudden, ya cuceni ya sa min sonsa" Farida ta xaro ido tace "So xa ki ci gaba da sonsa kenan???" Da sauri Heedayah ta girgixa kanta tace "I hate everything about him now, he is disgusting, I now understand why I saw gun with him a gidansa ranan da daddare, I now understand why he is this rich with so many cars and houses, I now understand me yasa baya son daga kiransa a gabana, I now understand why yake yawan ce min I shouldn't leave him no matter the circumstances, but I have to leave him, kuma na bar sa har abada, na tsani komai nasa, nayi da na sanin sake haduwa da shi da kulasa da nayi, dama shi ya rabani da iyayena tun ban san kaina ba, ya kuma maida ni wajensu after many years sbda selfish interest dinsa" kuka take sosai tana girgixa kanta, Farida ta kamo hannunta amma ta rasa abinda xata ce mata, ita ma hawayen take sosai don tun ba yau ba tasan Heedayah ta fada son wnn mutumi, Mikewa Heedayah tayi ta tafi gun kayanta ta fara hadawa tace "I will be leaving with Ammi today...." Jikin Farida yyi sanyi sosai sai a snn ta gane sbda Khaleel Heedayah tace baxata koma Kano da Amminta ba after her graduation, sbda tana anticipating dawowarsa. Da ido kaka ta dinga bin Shuraim da ya gama saka kayansa a jaka tace "Yau naga jaraba ina ta magana mutumi ya mayar da ni mahakuciya, dubi fa yanda ka zabge kamar me wata cutar can warce bamu sani ba, tunda iyayenka gantalallu ne ai ni ba gantalalliya bace baxan bari ka cutu ba, idan ma wani abun ke damun ka sai ka gaya min in san nayi tun wuri, bbu wajen wani shegen aiki da xaka koma, to banda kai wa ke gareni a duniyar yanxu, dama ni da kai nafi sabawa a kan su Amadu ma, kawai shaidan ne ya shiga tsakaninmu, shekarunka nawa a wajena kafin algungumar uwarka ta amshe ka ta karfi da yaji" Shuraim ya juya yana kallonta yace "Ba abinda ke damuna, bana jin dadi ne kawai, Amma yanxu Alhmdllh, xan koma bakin aikina" ta mike tace "Allah ya tsine ma aikin, idan ma xaka bini in kaika asibiti ka bini wllh, tunda shi Umaru bai daga kirana ba shi yasani, shi kuma Amadu xai ga barbadin bala'i yanxun nan kuwa" daga haka ta fice daga dakin, xaunawa Shuraim yyi gefen gado jin kansa na juya masa ya dafe kan xuciyarsa na bugawa, kaka na shiga parlon Abba ta samesa ya gama shiryawa xai wuce aiki, cike da bala'i tace "Amadu ba gwara abu ya sameka ba da ya samar min Shureen, uban me ka ta6a tsinana min tunda na haifeka dama, wato bakin ciki da rayuwar da Shureen ke yi a duniya kake yi ban sani ba, ban da bakin ciki ya xa ayi d'an ka bashi da lafiya amma ko a jikinka ka wani shirya xaka fita inda ku ke giggilla karyar ku..." Abba dai kallonta yake kafin yace "Baaba Shuraim ba yaro bane, idan yana ga barin damuwarsa a xuciyarsa ne mafi alkhairi garesa ba sai a kyalesa ba" Kaka tace "To anki kyalesan, kuma aniyarka ya bika wllh, in sha Allah bbu abinda xai samar min shi...." Abba ya d'an yi murmushi bai dai ce komai ba, sarai yasan meye damuwar son din nasa, ta juya ta fice daga parlon ta koma dakin Shuraim, Mumy dai na ta xaune main parlor tana ta addu'ar Allah ya sa son Heedayah ne ya sa shi damuwar nan, kuma Allah ya sa ya sanar ma kaka komai ya xo cikin sauki kenan. Zayyad ne durkushe an daure hannunsa da igiya ta baya, oganninsu ne tsaye kansa ko wanne na nuna sa da bindiga, Zayyad ya kalli sauran colleague dinsa dake tsaye gaba daya a katon parlon, Oga Manga ya karasa gaban Zayyad da katon muryarsa yace "Brainiac ya sauka kasar nan jiya, yana ina??? We are asking you this for the last time Zayyad" Zayyad ya juya da jajayen idonsa yana ma Salim wani irin kallo, Oga Arne ya kai masa kyakkyawan naushi a fuska cikin tsawa yace "Baxa ka bamu amsa ba??" Zayyad yace "Ni bamu hadu da shi ba har yanxu Oga, na gaya maku kun ki yarda" Oga Bala na nuna masa wayarsa yace "Amma kun yi waya ko...." Zayyad ya kalli wayarsa da Ogan nasa ke nuna masa yace "Ehh" Oga Manga yace "Ina yace maka yake?" Zayyad yace "Naje gidansa kamar yanda ku ma ku ka je, ban samesa ba gidan a kulle yake" Salim yace "Amma a waya daxu yace maka xai je gidan budurwar tasa" Zayyad ya sake jefa masa wani kallo, Oga Arne ya hauresa yace "True or false??" Zayyad yace "Ai ban san gidan ba nima" Oga Arne yyi wani dariya ya koma kan mighty chair dinsa ya xauna ya daura kafa daya kan daya yace "Ku tafi da shi ku tabbatar ya fadi inda gidan yake, snn a tafi a dauko mana mahaifiyar ita yarinyar yau din nan" Wani kara Zayyad yyi ya buga tsalle ya dawo da hannunsa dake daure ta baya gaba, ya haure Oga Arne dake kan kujera da kafarsa snn yyi hanyar bedroom da gudu ya bude wani daki ya shiga ya sa makulli yana huci, da sauri ya tafi gaban mirror ya fiddo karamar wayarsa ya shiga dialing number din Khaleel, yana jin suna kokarin balle kofar gaba dayansu, har wayar ya katse Khaleel bai dauka ba, gaba daya Zayyad ya hada xufa, ya sake kira praying hard Allah ya sa Khaleel ya dauka sai gashi ya dauka, da sauri Zayyad yace "Brainiac ka dauke Barrister din nan a gidanta with every other person, su Oga Arne xa su je gidan yanxun nan, I am giving them the address nowwww....." yana fadin haka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar ta bayan mirror ya durkusa a dakin ya sunkuyar da kansa kasa, suna 6alla kofar Zayyad ya dago da sauri nan ya zayyano masu full address din gidan Mami ya kara da cewa "Xan iya kai ku gidan ynxu ma...."




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....


Heedayah dai taki yarda ta dago kanta, Mami tace "Wai baxa ki bani amsa ba?" Ta dago a hankali tace "Mami nace ba komai, kaina ne ke min ciwo" Mami ta hade rai tace "Ciwon kan yasa kika yi kuka har idonki ya kumbura?" Heedayah ta marairaice tace "Yayi min sauki ynxu Mami, ask Farida" Farida dai na xaune can karshen gado tana danna wayarta bata ce masu komai ba, Mami tace "Toh yayi kyau, keep on lying, and why did you change your mind about going to kano with them?" Heedayah tayi kasa da murya tace "Mami sati daya xan yi in dawo in sha Allah, kawai dai ina son in je" Mami dai bata kuma ce mata komai ba ta fita dakin, Heedayah ta goge guntun hawayen idonta, Farida ta mike ta dawo kusa da ita tace "Heedayah me yasa baki son gaya ma Mami, why are you hiding this serious issue from her" Heedayah ta kalleta bata ce komai ba, Farida tace "It's better ki gaya mata, kinga she likes the guy, gwara ta sani tun wuri wllh, damuwata daya yanxu ya san gidanmu, I don't think we are safe anymore" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Heedayah na ci gaba da share idonta tace "Tun da ya san na sani ynxu baxai sake xuwa nan ba, and just watch and see" Farida tayi mata wani kallo tace "Wa yace maki?? Mutumin dake son ki, snn sbda son da yake maki har ya tona ma kansa asiri ya gaya maki shi wanene, ae wlh baxai ta6a daina bibbiyar ki ba, tafiyar ki kano shine kadae mafita gare ki" Heedayah tace "Wait Farida, is he even crazy to come back bayan ya riga yasan na san komai a kan sa ynxu??" Farida tace "Ke baki san so ba ko?? Wllh ko xaki tona masa asiri in dai yana son ki da gaske baxai daina bibiyar ki ba" Heedayah ta hade rai tace "Then he will be playing with fire, I will have to expose him to everyone" Farida tace "Exactly Heedayah, yanxu ki tashi mu je ki sanar ma Mami first..." Heedayah tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Farida ta mike ta kamo hannunta, xame hannunta tayi cikin sanyi tace "Baxan iya ba Farida, kawai let just leave him, I don't want anything to happen to him ta dalilina, ni nasan baxai ma sake dawowa ba" Farida tayi shiru tana kallonta. Mami ce tsaye dakin da Yakumbo ke ciki tana xuge handbag dinta tace "Toh ni yanxu wa xai kai ni can gidan lauyan??" Mami tace "Driver xai ajiye ku yanxu" Yakumbo tace "Ya san gidan ne?" Mami tace "Aa tare da Heedayah xa ku je" Yakumbo tace "Toh ni dai Allah ya rufa mana asiri kada tafiyar nan ya sha ruwa yau, ita Aisha na can tana xaga Kaduna da sojoji bata da niyyar dawowa, komai dai sai an bata ma mutum rai, amma ba laifin kowa bane laifin Amadi ne" Mami dai bata ce komai ba ta fita su Ashfah da suka makale mata na biye da ita, bbu abinda suka mance na Heedayah yaran kawai dai ta fi su haske, dakinsu farida Mami ta shiga, Mami na kallon Heedayah tace "Idan kin ga dama kin gama kukan iskancin naki sai ki shirya ki raka Yakumbo gidan Abban ki...." Da sauri Heedayah ta juyo tana kallonta tace "Gidan Abba kuma, Ba yanxu xa mu tafi ba Mami?" Mami tace "Wannan kuma ban sani ba" Heedayah tayi shiru, Mami ta juya ta fita dakin, Bata fuska Heedayah tayi ta rungume hannu, Farida dai na tsaye jikin window tana kallonta, bayan minti kusan goma Yakumbo ta leko dakin tace "Toh ni dai idan baxa ki je ba ai sai yar uwarki ta xo ta rakani, bbu ruwana da wahala..." Heedayah ta kalli Farida tace "Farida ki rakata ni kaina ciwo yake min wllh" Yakumbo ta rike ha6a tace "Ga dukkan alama Rahinah ta sangarta ki, kuma wnn wlh ba halin xaman gidan miji bane, kaji min fitsararriyar yarinya kawai" Heedayah bata ce mata komai ba, Yakumbo na kallon Farida tace "Kinga shirya ki rakani kin ji yar nan" Farida tace "Toh" Yakumbo ta fice daga dakin ta koma gun Mami, Mami tace "Baxa ki ci abincin ba kafin ki tafi?" Yakumbo tace "Kyaleni da abincin nan ke dai, amma a gaskiya wnn Heedayar taki bata da hali ko kadan, ga rashin kunya fal cikinta, wai yarinyar ta dubi tsabagen idona tace ita baxata ba sai dai Farida ta kai ni, irin tarbiyar da kika mata kenan??" Mami tace "Kiyi hakuri bata jin dadi ne, amma dole ma xata bi ki" Yakumbo tace "Aa ba ruwana, ta sha xamanta ni Faridar ma ta fi min sau dubu" Mami ta fita dakin ta koma dakinsu Farida, fuska daure tana kallon Heedayah tace "Tashi ki shirya ki fito ku wuce" Heedayah ta mike bata ce komai ba ta tafi press dinsu ta bude ta fiddo hijab dinta har kasa, Farida ta bi bayan Mami bayan ta fita, parlor ta sameta tace "Mami can I go with them?" Mami tace "Kince kina da lectures by 2, but if you want to go, you can" Farida tace "Toh Mami" daga haka ta fita, Nikab Heedayah ta saka ta fito parlor tare da Farida, Yakumbo tace "Allah ya kiyaye, uban wa xa ki bi a haka?" Mami dake parlon ita ma a xaune tace "Da shi take fita Yakumbo" Yakumbo tace "Toh ai ba da shi na ganta jiya a gun taron ba, Kai ni fa idan ma xata ce ba nice yar ubanta ba bbu abinda ya sha min kai" da turanci Mami tace ma Heedayah ta tafi ta cire Nikab

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login