Showing 246001 words to 249000 words out of 275313 words
Chapter 83 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
tayi tace "Waow..." Ta kallesa cike da farin ciki tace "I really like it ya Shureen, irin wanda nake so ne wllh" ta isa kusa da shi ta xauna arm din kujera tana murmushi sosai tace "Thank you...." Ta gefen ido ya kalleta amma bai ce komai ba, ta turo baki tana kallonsa tace "Nace thank you" yace "I prefer a cup of tea to that thank you" dariya tayi tace "Ohkk" daga haka ta mike ta dau hanyar kitchen ya bi ta da ido.... Shayi ta hada masa ta xubo masa pepper soup din offals a bowl snn ta fito, har ta shigo parlon kallonta yake ta isa gabansa ta durkusa ta ajiye bowl din offals din da cup din shayin ta wara masa ido tace "Is the thank you enough?" Yana kallon pepper soup din yace "Sure you are wlcm" ta dau spoon ta deba ta xai baki ya cafkota, xaro ido tayi, yace "Mayar ciki" da sauri ta fiddo a tafin hannunta tace "Toh xan karo maka sakeni..." yace "Wnn za ki ajiye" ganin ba saketa xai yi ba ta mayar da naman cikin bowl din, a hankali ya saketa yana kallonta, da mamaki take kallonsa ita ma, ya sauke idonsa ya dau cup din shayin ya fara sha snn yace "So what have you decided?" Tace "About?" Yace "Our talk yesterday" Shiru tayi na d'an lokaci, sai kuma ta kallesa tace "I've decided discard my request, cause ba a forcing soyayya, I will console Farida in ce mata may be kai din ba alkhairi bane gareta Allah xai bata wanda ya fi ka" kallonta kawai yake ko kiftawa bbu, can yyi murmushi yace "That's because you are soo self centered, kanki kawai kika sani, you can never sacrifice ur love for her, nasan kuma da ita ce she will gladly do that for you" Heedayah tace "I am not being self centered, kaga kai ba sonta kake ba, ni ma kuma I will never agree to ur so called frnd, to ae hakan ba shi da amfani, ita ya kamata tayi hakuri tunda ba wai sonta kake ba" Shuraim dake ta kallonta yace "Haka nace maki bana sonta?" Tace "To tunda kana sonta snn ita ma tana sonka, ni me yasa xaka min dole, you are not being fair to me kenan?" Wani murmushi yyi yana ci gaba da shan shayin hannunsa, Khaleel ne ya fado mata ta xaro ido gabanta ya fadi, ta san yana can yana jiran kiranta, a hankali tace "Ya Shureen can I go now ina yin wani abu ne a sama" ya d'an kalleta kafin yace "Noo, wait in gama sai ki wuce" bata ce komai ba, bayan ya sha shayin ya ajiye yana kallonta yace "Take them back to the kitchen" tace "Pepper soup din fa?" Yace "I am full" tace "Ai baka ci ba" yace "Na sani" mikewa tayi ta dauka ta wuce da su kitchen gaba daya..... Tsaye ta gansa parlon yana kallonta yace "Mu je waje xan maki magana" Ta kalli agogo kamar xata yi kuka bata ce ma Khaleel xata dade haka ba, kofa ya nufa ta bi bayansa har suka fita parlon..... Abban Heedayah na xaune parlonsa tare da Ammi sai mom Islam, Abba ya kalli Ammi da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya kuma tayi shiru, yace "Say something Aisha" Ammi ta girgixa kai a hankali tace "But ur Excellency what's wrong with the Junaid da xa a biye mata don tace bata so? Idan ma bata sonsa ga Shuraim dama ni hankalina ya kwanta da shi" Abba yace "Ke dole kike son ayi mata? snn still wanda tace take so ai d'an gidan ne shi ma naga" Ammi ta kallesa da sauri tace "Wa kenan??" Abba yace "Wan Junaid din, Khaleel..." Da mamaki Ammi ke kallonsa, can tace "Haba ur Excellency, ni gaskiya ban amince da wnn xancen ba, me yasa xa a biye mata kamar ita ta haife mu??" Abba yace "Abinda yyi Junaid shi yyi yayansa, haka ko ba haka ba?" Ammi tace "Aa wllh, his past..." Sai kuma tayi shiru, Abba kallonta kawai yake, Mom Islam tace "His past is nothing to write home about.... And kina duba reputation na gidan nan ko?" A hankali Ammi tace "Exactly Maimuna" Murmushi Mum Islam tayi sannan tace "Amma kar ki manta Aunty, Mahaifiyar wnn mutumi bata san wacece Heedayah ba, bata san 'yar wacece ita ba, bata san daga inda take ba amma ta yrda ta amince ta riketa bayan shi wanda ma ya tsinceta an ki rike masa ita cikin iyalinsa" Kasa cewa komai Ammi tayi, Mum Islam tace "It isn't Khaleel's fault he found himself in such life, kar ki manta yau da Heedayah ba hannu na gari ta fada ba Allah kadai yasan wani irin rayuwa xata yi, Allah kadai yasan abinda xata xama, albarkacin wnn bai kamata ki kyamaci d'an wannan baiwar Allah da ta inganta rayuwar 'yar ki ba ba tare da hakan ya bata wahala ko shakku a ranta ba...." Murmushi kawai Abban Heedayah ke yi bai ce komai ba, Ammi dai ta kasa cewa komai.....
*Wlh nayi busy fans ayi min uxuri, it's just for sometimes plss...*
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Karfe goma saura Heedayah ta farka daga baccin da ta koma da safe, kallon sabuwar wayan da Shuraim ya kawo mata dake ajiye gaban mirror tayi, ta mike xaune, sai kuma ta tashi ta tafi ta dauko ledan ta dawo ta xauna ta ciro wayar daga kwalinsa, ta dau sabon sim card da ya siyo tare da wayar tana jujjuyawa, can dai ta saka cikin wayar ta duba ko da kudi a layin taga dubu biyar, number Khaleel ta yi dialing ta kira, har ya katse bai daga ba, can ta kara kira ya dauka, tayi masa sallama, ya amsa yace "Whose line?" Tace "Nawa" Yace "Ohk okay, an kawo maki wayar ki daga Kaduna?" Tace "Aa sabuwar waya ce" Yace "That's good, ya mutanen gida?" Tace "They are fine, are you still leaving gombe today?" Yace "Ina hanya" Ta wara ido tace "Amma ban ji hayaniya ba" Yar dariya yyi, tayi shiru tana sauraronsa, his laugh was unique, bata ta6a jinsa yyi dariya ba, yace "Motar haya kike son ki ji na hau?" Tayi murmushi tace "Aa ni bance haka ba" Yace "Ohk, motar kawu na ne... And i am together with his driver" Heedayah tace "Toh Allah ya tsare, kun kusa?" Yace "Obviously" tace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Yace "But...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yace "Is it necessary sai mun tsaya kano?" Bata fuska tayi tace "Ni ba necessity dinka bace ai... It's not necessary" Ya wara idanuwansa yace "Sorry ba haka nake nufi ba, anyway in sha Allah xa mu tsaya kano" Jin ta ki cewa komai yace "Kin yi shiru" Kamar xata yi kuka tace "Wato xa ma ka iya wucewa baka tsaya ka gan ni ba" Yace "Noo, baxan iya ba" Tace "Toh Allah ya kawo ku lfya" yana murmushi yace "Ameen" Daga haka ta katse wayar, Har xata ajiye sai tayi dialing number Shuraim da ta haddace, yana fara ring ya katse, sai ga shi ya kirata, dauka tayi amma bata ce komai ba, yace "How was ur night?" Tace "Fine, good morning" Yace "Morning" Tace "Ya Shureen me yasa baka ce min so kake in bar maka laptop dina gaba daya ba..." Shiru ta ji yayi, can yyi murmushi yace "Saboda nace maki bani da nawa?" Tace "Toh ai ban sani ba" Yace "Toh xan kawo maki anjima" Ta wara ido tace "Aa wasa nake, you can use it har lkcn da ka gaji da shi" Yace "Okay kin kira ne just to hear from me kika fake da laptop?" Ta turo baki tace "Sbda laptop na kira ka" Yace "I see, ya kawarki?" Tace "She's fine, why do u ask?" Shiru yyi bai ce komai ba, ita ma tayi shiru, can tace "Ya Shureen me kake son gaya min da na raka ka jiya kuma ka fasa?" Yace "Naga ke yarinya ce shi sa na fasa" Dariya tayi sosai tace "Yarinya?" Bai bata amsa ba, tace "Meye ka sani wanda ni ban sani ba har yanxu??" Shiru yyi, can yace "Allah ko?" Tace "Eh mana, ni din ce yarinya?" Murmushi yyi yace "Ohk, xan nuna maki abinda ni nasani wanda ke baki sani ba" Ta ta6e baki tace "Babu wannan abun, nice ma nasan abinda kai baka sani ba" yyi shiru.... Can yace "Da yake ke har gidan da ba naku ba kin ta6a kwana ko?" Shiru tayi ita ma kafin tace "Ban gane ba" Yace "Ohk leave it" Ta hade rai yace "Wani gidan ne na kwana da ba namu ba?" Yace "Ni xa ki tambaya?" Tace "Toh ai dai naga ba gidan wani daban na kwana ba gidan saurayina ne" Yace "Haka ne, dole ki san abinda ni ban sani ba kam, i will hang up now ina wajen aiki" daga haka ya katse wayar, ta kalli screen din snn ta ajiye wayar tana hararansa, mikewa tayi ta fita dakin ta tafi bangaren Ammi, ganin tana da baki ta wuce bangaren Mum Islam, Mum Islam na kallonta tace "Sai yanxu kika tashi?" Ta xaro ido tace "Aunty sai karfe takwas da rabi fa na kara wani baccin bayan nayi wanka, mun fa gaisa da Abba tun sassafe" Mom Islam tace "To xauna dama ina nemanki" Heedayah ta xauna gefen makeken gadonta tana kallonta, Mom Islam ta xauna gefenta tace "Ki gaya min gaskiya Heedayah..." Sosai gaban Heedayah ya fadi ta dinga kallonta, Mom Islam tace "Heedayah tell me, ke a xuciyar ki wa kike so, but kar ki manta xaman aure fa ba abinda xa ayi na shekara daya ko na shekara biyu bane, xama ne na dindindin, xama ne na har abada, ba a fatan rabuwa sai in mutuwa" Heedayah ta sauke kanta kasa, Mom Islam tace "Ina jin ki, wa kika ji xuciyar ki ya kwanta da" a hankali tace "Aunty ni Khaleel nake so" Mom Islam tace "Kin tabbatar?" Ta gyada mata kai, Mom Islam tace "Me yasa baki son kaninsa?" Heedayah tace "Aa ni bance bana sonsa ba, kawai baxan iya aurensa bane, Ya junaid is among the people that did good to me, yana da kirki sosai, kuma ya nuna min kulawa yanda xai yi ma Farida, amma ni i can't marry him" Mom Islam tace "Shi kuma Khaleel me yasa kike sonsa?" Heedayah ta d'an yi shiru, Mom Islam tace "Ina jin ki" A hankali Heedayah tace "Ina sonsa sbda shi ne mutum na farko da ya fara taimakona a rayuwa, Ina sonsa sbda yana da hali me kyau if not of the situation he found himself, kuma na ga yana da rikon addini duk da haka, kuma ina tausayinsa sosai, I don't want anything to happen to him ta dalilina, Aunty ai kinsan condition dinsa" a sanyaye ta kare maganar, Kallonta kawai Mom Islam take kafin tace "Anya ba tausayin Khaleel kike ba Heedayah?" Heedayah ta kalleta tace "Ehh ina tausayinsa kuma Ina sonsa" Mom Islam ta girgixa kai tace "Aa tausayin ya fi yawa nake kaga" Heedayah tace "Aa, bayan tausayinsa nasan ina sonsa, tun daga sanda muka fara waya da shi, Aunty kinsan fa har gidansa na ta6a kwana, his ways of life is perfect, yana rikon addini sosai, kuma in sha Allah nasan ya daina abinda yake har abada...." Mom Islam tace "Eh nasani" a hankali Heedayah tace "Wllh ina sonsa Aunty" Mom Islam tace "Toh shkkn Allah ya tabbatar da alkhairi dear" Heedayah ta sauke idonta kasa tace "Ameen, Yana hanya ma Aunty" mom Islam tace "Xai xo nan?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Ya ma ce min ya kusa" Mum Islam tace "Shine baki sanar ma kowa ba?" Heedayah ta kalleta tace "Yanxu muka yi waya da shi ya gaya min, naje xan gaya ma Ammi naga tayi baki, shine na xo nan" Mom Islam tace "Toh Allah ya kawo sa lfya" Heedayah tace "Toh Aunty me xa a dafa masa?" Mom Islam tace "Abinci ba matsala bane ai masu aiki suna can ma suna yin na rana, kawai xuwa xa muyi ayi masa sabon snacks coz wanda ke da akwai aren't fresh" Heedayah tace "Toh Aunty" Mikewa Mom Islam tayi tace "Ki tafi nawa kitchen din Ina sakkowa yanxu" Heedayah tace "Aunty kitchen nawa ne gidan nan?" mom Islam tace "Kitchen hudu ne" Heedayah tace "Ohk" daga haka ta fita. Sai da suka kusa gama snacks din da suke yi Mom Islam tace "Nasan bakin Amminki sun tafi yanxu ki je ki sanar mata" Heedayah ta wanke hannunta ta fita kitchen din, bangaren Amminta ta tafi, Kawar Ammi daya ce a parlon, Ammi na kallonta tace "Ya aka yi?" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta mike ta wuce bedroom dinta ta bi bayanta, Ammi na kallonta tace "You want something?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa Ammi ya Khaleel ne xai xo?" Shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Daga ina?" Heedayah tace "Daga wajen relatives dinsa a Gombe" Ammi tace "Toh ni bani xaki fadi ma ba ai, sai ki sanar ma Babanki" Daga haka Ammi ta fita daga dakin, Heedayah ta fi minti biyar tsaye kafin ta juya ta fita, kitchen ta koma gun stepmom dinta, Step mum din na kallonta tace "kin sanar mata?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Amma tace ba ita xan gaya ma ba Abba xan gaya ma" Mom Islam tace "Bari mu koma daki sai in kira private number dinsa yana gunsa idan ya daga sai ki sanar masa" Heedayah tace "Toh" har suka gama jikinta a sanyaye yake suka fita kitchen din tare xuwa bangaren Mom Islam. Mom Islam ta kira Abban Heedayah ta mika mata wayar bayan ya daga, nan Heedayah ta sanar masa Khaleel na hanya, Abba yace "Yau?" Heedayah tace "Ehh" Abba yace "To maa sha Allah, Allah ya kawo sa lafiya" Heedayah tace "Ameen" Amsan wayar Mom Islam tayi tace "Toh xaka sanar da xuwansa ne kar ya samu matsala wajen shigowa tunda bashi da wani appointment?" Abban Heedayah yace "In sha Allah" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar ta ajiye, a sanyaye Heedayah tace "Aunty me yasa kamar Ammi bata son ya xo?" Mom Islam tace "Aa tana so mana, tunda kince ya kusa ki tafi ki shirya sabbin kayanki na can wajenta da tailor ya kawo last week, ki kawo akwatin gaba daya in xabar maki wanda xa ki saka" Heedayah tayi shiru, can tace "Nawa ni kadai Aunty?" Mom Islam tace "Aa ke da Farida da kannin Shuraim biyu, amma bai kawo nasu ba tukun" Heedayah tace "Toh a ina aka samu measurement dinmu?" Mom islam tace "Mami ce ta turo naku, kannin Shuraim kuma Uwarsu" Heedayah tace "Ohk" mikewa tayi ta fita xuwa gun Amminta, nuna mata trolleyn kayan kawai Ammi tayi, Babban trolley ne sosai, ta ja sa har xuwa bangaren Stepmom dinta, Mom Islam ta kwantar da akwatin ta bude, kaya ne duk a goge kala ashirin da biyar masu tsada sosai ko wanne kuma da mayafinsa, duk laces ne da atamfa, mom Islam na duba kayan a nutse tace "Ba su kenan ba ma, kilan basu gama ba tailors din" Wani ubansun lace me tsada ta fiddo ta ajiye mata, Heedayah ta dinga kallon lace din, Mom islam ta dauko wani akwatin cikin press dinta ta kwantar ta bude duk takalma ne da jaka kusan kala goma, Mom Islam tace "Naki ne, tun da aka kawo ban kai gun Ammin ki ba" Takalmi da jaka da xai tafi da lace din ta fiddo ta ajiye gefen gadonta inda ta ajiye kayan, Heedayah na murmushi tace "Nagode" Mom Islam tace "Ki shiga bandaki ki sake wanka ki fito" Heedayah ta cire doguwar rigar jikinta, ta shiga bandakin, ba a dau lkci sosai ba ta fito daure da towel din step mum dinta, a nan dakin tayi sllhn azahar sannan ta shirya, kallonta kawai Step mum dinta ke yi tana murmushi don sosai kayan su amsheta, Heedayah ta sunkuyar da kanta, Mom Islam tace "Kinyi kyau sosai my daughter" Murmushi Heedayah tayi tace "Nagode Aunty" Mikewa Mum Islam tayi ta dauko kit din kayan make up dinta, nan tayi mata very light make up, Heedayah ta dawo kamar ba ita ba, tayi kyau sosai kamar wata amarya, Mum Islam ta kara fesa mata turarurrukanta iri iri sannan ta dauko mata wani dankunnen zinari da zobe ta bata ta saka, mom Islam tace "Two month ago wata kawata ta kawo na daukar maki" Heedayah na murmushi tace "Nagode Aunty" Mom islam tace "Toh kuma ina kika bar wayar kar yyi ta kira" Heedayah ta xaro ido tace "Lahh yana dakina" daga haka ta fita da sauri ta tafi dakinta dauko wayar, miss call dinsa daya ta gani, ta shiga kiransa, bayan ya daga tace "Sorry bana kusa wllh, kun iso ne" Yace "Ehh mun ma shigo" Tace "Okay no problem ko?" Yace "Sure, tare da wani soja" Tace "Toh sai kun karaso" tafiya tayi da wayar ta koma gun Mom Islam, nan ta sanar mata sun shigo, mom Islam tace "To mu je in hada maki abinda xaki kai masa kar kiyi shirme" Tare suka fita xuwa kitchen dinta, dama ta sa yan aiki su debo duk abinda suka dafa a different cooler su kawo mata kitchen dinta su ajiye, mom Islam taga warmer din a jere, ta shiga budesu one by one, shinkafa da miya with cow meat, sai tuwo da miyar assorted egusi, da garnished cous cous da ya ji hanta, pepper soup na kaza sai xuba kamshi yake, last bowl din ta bude taga coslow ne ciki, Mum Islam ta kalli Heedayah dake tsaye gefenta tace "What's his favourite?" Heedayah ta bude hannu tace "Nima ban sani ba" Mom Islam tace "Toh a kai masa shinkafa da miya da coslow da pepper soup