Showing 132001 words to 135000 words out of 275313 words
Chapter 45 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
6ata fuska ta kalli gate din gidan sae kuma ta karasa ta tsaya tana kallonsa yace "Me yasa kika sa mayafi Heedayah? Baya maki kyau" a hankali tace "Mami ce tace in sa Yaya" yyi shiru yana kallonta, can yace "Alright" ta daga masa hannu ta nufi cikin gidan. Yan uwa da abokan arxiki har sun fara cika gidan biki ana ta shiri, Mami ta shiga parlon da sallama girls dinta da suka yi anko na atamfa me tsada na biye da ita a baya, sosai kayan ya amshi Heedayah da ta sakale gyalen gefen shoulder dinta, tayi wani sanyayyan kyau duk da bata yi kwalliya ba sai eye pencil da ta saka idonta da chappet da ta goga lips dinta, Mumy ce xaune parlor da kawarta Hajiya Sadiya, sai Hajiya Amina mahaifiyar Sudais da step mother dinsa, sun dai kusa goma sha biyu a parlon duk dai ana tsara yanda abubuwa xa su kasance, masu tafiya kasuwa na shirin tafiya, Tunda Mami ta shigo Mumy da ta yi ture ka ga tsiya ga daham dinta a wuya ke kallonta, farin ciki ba na wasa ba Mumy tayi don ta wani hakikance kan kujera sai kace sarauniya, Lkci daya murnan Mumy ya koma ciki ido hudu da tayi da Heedayah dake bayan Mumy, Heedayah dai ta xama cikakkiyar budurwa don idan ka ganta ma baxa kace she is just 16 ba, Doguwa ce fara sosai kuma siririya, hancinta is worth noticing ko da kuwa daga nisa take, ga karamin bakinta me xagaye da jan labbe, gaba daya ta sauya daga lkcn da take 13 don idan ba saninta kayi sosai ba baxa kace ita ba ce, Mumy ta hadiye abu da kyar ta kalli Hajiya Sadiya dake kallon Heedayah ita ma ba ko kiftawa, Heedayah da Farida suka durkusa suka gaida Mutanen parlon, ita Mum din Sudais dama ko ganeta bata yi ba Hajiya Hauwa ce kadai ta ganeta don sai kallonta take tana murmushi, Mami tayi hanyar dakin kaka don ta gama gaisawa da occupant din parlon, mikewa Heedayah da Farida suka yi suka bi bayan Mamin tasu, Mumy tayi kasa da ido ta bi Heedayah da kallo har suka shiga dakin kaka, da mayafinta ta share d'an guntun xufan da taji ya keto mata.....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Rungume kaka Heedayah tayi ta kankameta cike da murnan ganinta, rabonta da kaka tun da suka yi hutun jss3 third term, sae da kaka ta kare mata kallo daga sama har kasa sannan ta turata tace "Aa ni ki rufa min asiri kar ki cuceni ki kada ni kasa ana bikin jikokina, ki bar ganin kin tsayince kamar falwaya, nima ina yan mata haka nake duk da dai yanxun ma ni ba guntuwa bace" Mami tayi dariya ta xauna tace "Sannu kaka...." kaka tace "Yanxu Rakiya fisabilillahi auren 'ya yan Umaru fa ake kika ki xuwa sai yau, ke da ya kamata ace tun ana sauran sati daya xaki tattaro kayanki ki dawo nan, xumunci fa ba abun wasa bane ba abun yadawa bane, idan ma ke baxa ki xo ba ai sai ki turo mana Heedayah tunda ta mu ce, ki bar ganin an sakar maki ita ki xata galaba kika ci a kanmu, ni ce nan nake ta tausan Amadu amma kiris ya rage ya kwace 'yar sa tunda ba ke kika tsinto masa ita ba, Kuma ba ke kika warkar mata da idonta ba" Ba yabo ba fallasa Mami tace "Toh sai yah xo.... ina jiransa" A hankali Heedayah ta xamo kasa tace "Ina kwana kaka?" Ko kallonta Kaka bata yi ba tace "Ina da labarin sun yi hutu yau kusan sati biyu amma kin ki barin ta xo ta gaisheni ta gaida wan Amadu sannan ta tafi gidan shi Amadun ta gaishesa idan ya kama har kwana biyu tayi, wannan dai ba yi bane, fitina a kwance take dai idan kika tada ta ke kika sani... Ko jiya sai da Amadu yace xai je ya dauketa nace ban ki ta tasa ba amma yyi hakuri muyi bikinmu mu cashe lafiya, bayan biki sai yaje can ku ci kanku bbu ruwan wani, wllh tllh haka aka yi ki tambayi wnn yaro Shureen ai tare suka shigo jiyan" Shuraim dai na tsaye dakin yana danna wayarsa, Mami taki cewa komai, Shuraim ya gaida Mami, ta amsa da murmushi tana tambayarsa ya aiki, Farida dake danna wayarta ita ma tace masa "Ina yini" yace "Lafiya lau" Murya can kasa Heedayah tace "Ina yini" ya ci gaba da danna wayarsa bai ce komai ba, kaka tace "To dai wnn shine dalilin ma da na kira ki nace na ji ku shiru, Amadu ne ya xo nan xai daga mana hankali wai xai je amso yarinya, ni dai na samu na lallabasa ya wuce, wnn yarinya dai ya fi kowa iko a kanta kema kin sani sai dai idan kina da karancin tsoron Allah, don haka ki raba kanki da fitina ki daina kokarin rabata kwata kwata da uban rikonta ba wani ya tsinto masa ita ba, jifa jifa sai ki turata da wnn yarinya Farida su je suyi kwana biyu gidansa haka ake yi ba ki yi bake bake a kan yarinya ba ke kadai, da bai tsintota tana galantoyi ba a ina xa ki santa Rakiya? to ga dai akwatina nan, daya matsiyacin mijin kwara biyar ya kawo gasu can a gantale ko budewa jama'ah bana yi, dayan kuma d'an albarka guda takwas da uban kaya a wani jakar ya kawo... Ku yi ta dubawa tunda na yadda da ke baxa ki cuce mu ba, kinsan akwai masu sace kaya idan sun xo gani, yanxu dai kasuwa wnn yaran xa su rakani, in je in siyo masu mafici, matankadi, gwa-gwa, maburgi, ludayan miya, 'yar kwalla karama me ado, turmi da kwarya, duk gantalallun iyayen basu siya masu ba basu san shi aka kai mana lkcn mu ba auren yyi albarka da izinin Allah, wai su 'yan xamani to ba dani xa ayi wnn lalacewar ba, xan tafi yanxu da kai na in siyo masu a bakin dogo, nace wnn mutumi Shureen ya kai ni a mota ya ki, da yake tunda ya samu sojan nan ya fara saka ilifon dinsu yake ganin kowa bbu gashi, ynxu kafin ku shigo sae kinga fitsaran da yyi min, to sojan karya ma da bai isa rike bindiga ba har ynxu, uban wa xai basa bindiga dama, ni dai har yau ban gansa da bindigan wasan yara ba balle na gasken amma har shine xai dinga raina ma mutane wayo" Ta gefen ido Shuraim ya ke kallonta, Mami dae sai murmushi take ta ki cewa komai, Heedayah ta taba jakarta da sauri jin kamar vibration, mikewa tayi ta shige bandaki, Shuraim ya bi ta da kallo har ta rufe kofa, Jin rufe kofar bayin kaka ta bi dakin da kallo don ganin waye ya shigar mata bandaki, da sauri tace "Rufa min asiri kar ki min amfani da bayi ki fito ki tafi ki shiga na masu biki...." Heedayah har da sa makulli snn ta fiddo wayar a jakarta, miss call tagani guda daya na Khaleel, tana ta tsaye ko xa a kara kira amma shiru, ta jira ta jira har Mami ta kwalo mata kira ta fito dakin, kaka na tsaye da Farida ana jiranta xa a je kasuwa, Shuraim dai sae kallonta yake, kaka tace "Toh uwar me kike min a bandaki kika dade haka" Heedayah ta turo baki tace "Ni ba abinda nake yi" Kaka tace "Toh ni ba ruwana ki sa mayafi mu tafi kasuwan, ke muke jira" Heedayah na son bin kaka amma tana tunanin xa a kara kiranta a waya, ta marairaice kafin tace komai kaka ta ja hannun Farida tace "Mu yi ta kanmu ba xuwa xata yi ba gantalalliyar" Daga haka suka fita xuwa kasuwa, Shuraim yyi ma Mami sallama ya fita, Mami ta fara sauke akwatin don duba kayayyakin ciki. Farida kam tayi da ta sanin bin kaka kasuwa don tun daga kan Mai adaidaita aka fara don bata basa cikakken kudinsa ba, kafin magana tayi tsawo Farida ta bude jakarta ta fiddo dari biyu ta mika masa ya ja machine dinsa ya wuce, kaka ta shiga kasuwar tana xaginsa, Farida tace "Kaka tun daga gida fa ya dauko mu xa ki basa naira dari..." a mugun fusace kaka tace "Uwarki Rakiya ke nemo min kudina ko a bishiya nace maki nake tsinkowa, kawai yarinya baki da amfani na xo da ke kasuwa saura kiris a min duka kina kallo, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin haka ba, Ashe ke shashasha ce, da Jamila ce yau sai ko ita ko barawon, Aa barawo mana, banda barawo wani d'an adaidaita ne xai amshi dari uku hankali kwance bbu tsoron Allah kamar mun hau jirgi, ko xuwa makka daga nan nawa yake aka ce maki? Toh ba ruwana daga yau kika sake cewa xa ki bi ni kasuwa sai na miki barbadin bala'i" Farida kamar tayi kuka sbda tsaye mutane suka yi ana kallonsu, kaka taga wani me mafici ta duka ta dauka tana cewa "Kai nawa nawa wnn, jikokina ne xa ayi ma aure jibi, da yake barbadadu ne iyayen ko batun maficin basa yi...." Hayaniyar da ta ji gefenta ya sa ta mike da sauri tana kallon abinda ke faruwa, wata dattijuwa ta gani tsaye tayi mitsi mitsi da ido tana dungurin wani me siyar da kaya irinsu tafarnuwa, kanunfari, citta da dai sauransu, sai cewa take "Ni xaka gilla ma karya kace baka harareni ba??" Jama'ah suka fara taruwa ana bata hakuri, cike da bala'i take cewa "Ni sai ya gaya min wa ya tsaya masa a Najeriya da xai harareni.... daga nace ya bani tafarnuwar ashirin ya bani kwaya biyu nace ban so, kawai sae mutumi ya harareni?sannan ya kara da gilla karyar cewar bai harareni ba, ya san wacece ni kuwa?" Mutumin dake ta kasa kayansa yace "Na sani mana, tunda gashi kin kawo ashirin xa ki siyi tafarnuwar da ko na hamsin babu a kasuwa" kaka ce ta kai masa naushi a baya tace "Amma kai dai anyi lalatattce, yanxu ka dubi wnn tsohuwar da ta haifi kakan ka ka rufe gwalmadaddun idon ka ka dinga xaxxaga mata fitsara??" Sai kallo ya koma kan kaka, Farida ta kasa motsi inda take, can kawai ta juya ta koma titi don neman adaidaitan da xai mayar da ita gida, Kaka da wnn yar dattijuwa suka hadu suka yi ma me kaya tatas, daga karshe shi kansa dariya abun ya basa don ko kallonsu bai kara yi ba sai kasa kayansa yake a 'yar rumfarsa, kaka ta juya kan masu bada hakuri tace "Ku kuma meye xaku dame kunnanmu da bada hakuri, da ku wasu ne da suka san darajan iyaye ai matse d'an banxa xa ku yi ku daure ku nakada masa shegen duka...." Dattijuwar tace "Toh su ma din duk ba barayin bane, wa ya sani ma ko akwai barayin satan yara a cikinsu, ni abinda ya fi min ciwo shine hararata da yyi, ga fa yan dubu dubu a jakata kar yyi xaton gantalalliya ce ni, kanina na can Abuja wani babban mukami yake nema yanxu haka amma baxan fada ba don ban san xuciyar kowa ba a nan, to ina xan biye yan yunwa a titi inyi tashin hankali da su, tafarnuwar fa sadaka dama nake son inyi da shi ba wani abu ba" Kaka tace "Bar masa tsiyarsa, da xa ki bi ni mu tafi gidan d'ana Umaru buhun tafarnuwa gareni wllh, sai in debar maki rabin buhun" Tsohuwar tace "Ai kanina ya hanani shige shige, banda haka da na biki wllh" kaka tace "Ba wani shige shige, shi gantalallen kanin naki da ace ya ajiye maki buhun tafarnuwar me xai kawo ki kasuwa mutumi ya harareki??" Kaka ta bude jaka ta fiddo wayarta tace "Ni dai bani lambar ki, nima ina da 'ya ya a Habujan nan, ana gama biki dama xan je can" Tsohuwar tace "Ni dai ban yafe hararata da yyi ba wllh" Kaka ta kara kai ma me kayan dundu a baya tace "Ai ba don su Amadu xa su min fada ba da mun ja sa mun tafi caji ofis yanxu, amma ce min xa su yi meye hadina da ke" Tsohuwar ta fiddo wayarta a jaka tace "Ni ban san kan waya ba ke ki sa min naki lambar" kaka tace "Aa bana gane kan waya da rana, da dai mu nemi wani ya fiddo lambobin" Da sauri kaka ta juya tace "Auuu, ae da yarinya na taho ina take?" Nan kaka ta shiga duba Farida a kasuwa bbu alamar ta, wani mutumi suka samu kaka tace "Na ganka fes fes kamar d'an boko, don Allah ga wayata ka ciro min lambata ka ba ma wnn tsohuwar ita ma ka cire nata ka bani, Ashe bata yi makaranta ba bata san kan wayar ba" Kaka ta linke d'an takardar da Mutumin ya rubuta lamba ta saka a jaka, ita ma tsohuwar ta saka nata a jaka, kaka tace "Ni dai da kin ji ta nawa mu tafi gida kawai daga nan sai na debar maki tafarnuwar" Tsohuwar tace "Toh ai ba a son ina shige shige, toh amma dai mu je kawai" Mai maficin dake ta jiran kaka ganin xa su wuce yace "Mama kin fasa siyan maficin ne" kaka tace "Kai rabu da ni na fasa, iyayensu su xo su siya masu ai ba ni na haifesu ba, ubansu kawai na haifa" Daga haka suka bar wajen. Kaka na shiga compound tace "Toh ni Hajiya kaka ake ce min, xuwa makkata yayi hamsin...." Tsohuwar tace "Toh ni wannan shekaran ma kanina ya biya min Umra, kafin a fara axumi xan tafi, duk shekara sai naje makka sau biyar" Kaka ta tabe baki bata ce komai ba, can kuma tace "Toh mu lkcn da muka yi yayin xuwa makka kuna ina, kawai dai mun yi hankali me yanxu" Mutanen dake parlon har da Mumy suka gaida kaka da Sabuwar bakuwarta, bbu yabo bbu fallasa kaka ta amsa tayi hanyar dakinta, dattijuwar na kallon mutan parlon tace "Haihuwa aka yi a gidan ne" Kawar Hajiya Amina tace "Aa biki dai ake" tace "Ayyoo, naga parlon kamar ana cin kasuwa" Daga haka ta bi bayan kaka xuwa dakinta, Bala'i kaka ta dinga yi don me Mami xata wuce bata tsaya ba, tsohuwar dake tsaye gefenta tace "Aa bata da mutunci ne kawai" Kaka tace "Wllh kuwa, tana nan fa kamar xabiya sai mugun abu a xuciya, idan xata tafi ba sai ta bar min yarinya ba, dama me muka hada da ita, ai yarinyar ce tamu, to ynxu xan kira Amadu in sanar masa rashin kunyar da ta min" Mumy dai na tsaye kusa da kaka jin fadan da take sai bata hakuri take kai kace ta kirki ce, wannan tsohuwa dai ta tabe baki tace "Toh ni ina tafarnuwata in wuce" Kaka na share xufar goshinta sbda fitina tace "Ai da satin da ya wuce muka hadu har buhu sai kin samu, to yanxu ni ina naga tafarnuwar da xan baki duk na rabar ma jama'ah" tsohuwar ta gyara yafin gyalenta ta fita dakin kan kace me tayi hanyar titi tana cewa "Ashe tsohuwar banxa na biyo" Da daddare Heedayah na kwance daki da jakarta a kusa da ita, Farida ta shigo dakin, ita dai tana ta mamakin me yasa Heedayah ke yawo da jaka tun dawowarsu daga gidan su Sudais, amma bata ce mata komai ba, Farida na kokarin cire kayanta tace "Mami tana kiran ki" Heedayah ta juyo tana kallonta, can tace "I tot tayi bacci" Farida tace "Bata yi ba" Daga haka ta shiga bandaki, Heedayah ta cire wayar jakan da sauri ta bude school bag dinta ta saka wayar a ciki sannan ta sa Hijab dinta kan kayan baccin jikinta ta fita xuwa dakin Mami, Mami na kallonta bayanta duka kusa da ita tace "Idan kin gama period dinki ki sanar min" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Mami tace "Kin ji abinda nace?" Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Ae ya tsaya" Mami tace "Tun yaushe?" Heedayah tace "Yau ban yi ba" Mami tayi shiru tana kallonta, can tace "Two days kenan kika yi flow?" Ta gyada ma Mami kai, Mami tace "Toh, sai ki sa ido xuwa gobe jibi idan still u didn't see anything sai ki gaya min" Heedayah tace "Toh" Mami tace "You can go" Mikewa tayi tace "Sai da safe Mami" Mami tace "Allah ya kai mu lfya" Daga haka ta fita dakin. Kwance ta tadda Farida da ta rufe ido kamar me bacci, Heedayah ta kashe wutan dakin ta kwanta, bayan kusan minti talatin ta tashi ta nufi schl bag dinta tana waigan Farida ta bude ta jakar ta duba, bata ga miss call ba ta rufe sannan ta tafi ta kwanta, wajen karfe dayan dare Farida ta juya tana kallonta taga bacci take, tashi tayi ta dau wayarta ta haska schl bag din tana kallo sai kuma ta karasa ta bude tana duba ciki, still tayi tana kallon wayar, a hankali ta sa hannu ta ciro sa daga cikin jakar tana jujjuyawa, can ya kunna sai ga hoton Khaleel gaban screen din, Farida ta juya ta kalli Heedayah sannan ta tabe baki ta mayar mata da wayar ta rufe jakar ta koma ta kwanta. Washegari da safe, bayan sun idar da sllh a dakin Heedayah tace "Yau xa mu je siyo takalmi da kika ce ko?" Shiru Farida tayi, Heedayah tace "Are you sleeping?" Farida tace "No" Heedayah tace "Baki ji me nace ba?" Farida tace "I will use the one I am having, ke xa ki iya xuwa ki siya" Heedayah bata kuma ce mata komai ba ta mike ta fita dakin don ita ce da wanke wanke da gyaran kitchen yau, in dai suna nan toh Mami ta hana Zainab yin komai, Junaid ne kwance saman 3seater yana bacci, ta