Showing 183001 words to 186000 words out of 275313 words

Chapter 62 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

ta bi bayan Mami cike da farin cikin da bata nuna a fili ba. Har suka isa asibitin bbu wanda yace komai cikin motar, Dinar tayi parking a space din da aka tanadar don haka a asibitin snn ta bude motar ta sauka, Mami ma ta sauka, Heedayah ta dau basket din abincin ita ma ta sauka, Zayyad ne kadai dakin da Khaleel dake xaune yana shan grapes a roban grape din, Tun da Mami ta shigo yake kallonta, Kafin kuma ta karaso gun gadon ward din ya sauke idonsa, Zayyad ya gaisheta ta amsa da murmushi tace "Ya mai jiki?" Yace "Alhmdllh" Gaisheta Khaleel yyi not looking at her, ta amsa tace "How are you feeling now?" Yace "Alhamdulillah" Xaunawa Mami tayi tace "Toh Allah ya kara lafiya" Dinar tayi masa ya jiki ita ma ta xauna, Kallonsa kawai Heedayah dai take, ya d'an kalleta suka hada ido, ta buda ido tace "How are you feeling?" Ya gyada mata kai yace "Fine Alhamdulillah, in sha Allah" tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" Heedayah ta xauna kusa da Mami, Shi dai Khaleel ya ci gaba da shan grapes dinsa slowly, bayan wani lkci ya daga kai suka hada ido da Mami dake ta kallonsa, Mami tayi saurin cewa "Nace ga abinci nan abokin ka ya dibar maka koh?" Zayyad ya mike kafin Khaleel yace komai sanin bai son cin abincin ya tafi gun basket din abincin don debar masa, dai dai nan aka bude kofar ward din, Khaleel ya dakata da kai grape din hannunsa bakinsa yana kallon wa enda suka shigo, Manga ne da Bala, ko wannensu sanye da manyan kaya irin na mutanen kirki, ga bakin glasses da suka kwama, Khaleel ya mayar da grape din hannunsa ya ajiye, Mami dai sai kallonsu take, Manga na kallonta da katon muryarsa yace "Sannu Hajiya" Mami tace "Yauwa" Bala yace "Ya me jiki?" Mami tace "Mun gode Allah" Manga yace "Madalla" karasawa yyi gadon yana kallon Khaleel, Shi dai Zayyad bai yrda ya juyo ba yana xuba ma Khaleel abinci, Manga dake kallon Khaleel yace "ya jikin?" Khaleel yace "Na warke" Manga yace "To madallah" Zayyad ya juyo ya mika ma Khaleel abincin hannunsa, Bala yace "Sannu da jinya" Zayyad yace "Yauwa" Mami ta mike tace "To xa mu koma, may be kafin in tafi gobe da safe xan leko in sha Allah" Khaleel ya kalleta yace "Toh nagode kwarai" Jikin Heedayah yyi sanyi, she wants to talk to Khaleel amma har yanxu bata samu ta yi masa magana ba, Mami bata yi ma su Manga sallama ba ta fita ward din, Dinar ta mike tayi ma Khaleel Allah ya kara lfya, tayi ma Zayyad sai anjima snn ta fita, Manga ya bi su da kallon gefen ido, A hankali Heedayah ta mike tana kallon Khaleel dake ta kallonta, ta sauke idonta kasa sai kuma ta karasa gun sa tace "Xa mu tafi, Allah ya sauwake" yyi shiru bai ce komai ba, tace "Do you need anything?" Ya d'an kalleta snn yace "Nothing Heedayah" tace "Toh Allah ya sauwake" Yace "Are you travelling together with them tomorrow?" Heedayah tace "I don't know too" yace "Ohk, ki tafi suna jiran ki" Ta gyada masa kai ta nufi kofa su Manga suka bi ta da kallo, ko kadan bata san su waye ba sai a snn Khaleel ya ga amfanin rashin barin ta gansu da yyi daren ranan, tana kulle kofar Bala ya kalli Khaleel da jajayen idonsa bayan ya cire glasses din idonsa yace "Kafin in isar maka da abinda ya kawo mu, wacece warcan matar da ta fito, a ina ka santa? Kuma yaushe ka saki jiki da bare har haka ku ke mu'amala bamu da masaniya?" Khaleel yace "Bana tunanin you have any business to do with that Boss" Manga yyi wani nishi yana kallon Bala yace "Follow her, get few information" Bala ya fice da sauri, Manga yace "Anyway, ba wani abu ya kawo mu nan ba illa mu sanar maka our next operation na dauke Alhaji Ahmad is in 3 days time, wnn lkcn idan ka kuskura ka kawo mana cikas, Arne yyi alkawarin aikaka lahira, amma kar ka yi tunanin a take xaka mutu, idan ka mutu a take ka ci riba ma kenan, wllh wllh idan ka sake kawo mana wani cikas a wnn operation din sai dai ayi wani Brainiac din ba kai ba, idan kana da sama da mu a duniyar nan ka fito ka nuna" Khaleel yyi wani murmushi ya ci ga da shan grapes dinsa, Bala ya karasa dai dai kusa da Khaleel cikin husky voice yace "Be careful with us, don't mess with us....." Daga haka ya fice daga ward, Khaleel ya juya yana kallon Zayyad ya diro daga saman gadon fuskarsa a murtuke ya nufesa yace "Why did you let them know where we are?" Zayyad ya buda hannu yace "I only told Maska, yace Oga Arne na nemana nace ina tare da kai you are sick, is anything wrong with that...." Khaleel sai kallonsa yake yana huci, can ya nufi kan gado ya dau wayarsa ya fice daga ward.



I'm not okay, I just have to write this... Thanks for d call and text I couldn't reply or answer to.




Da Magrib Heedayah na dakin kanninta tare da Nannynsu da ke shiryasu tayi masu wanka, tun dawowarsu tare da Mami daxu daga asibiti Mami tace ta shiga gidan nasu gun Amminta, Ammi ce ta bude kofar dakin tana kallon Heedayah tace "Gwaggon ki ta iso Heedayah, come out and meet with her" Heedayah ta mike ta d'an buda ido tace "Yakumbo?" Ammi tayi mata murmushi tana nodding mata kai, Fitowa Heedayah tayi dakin da sauri don Yakumbo na daya daga mutanen da take son gani ido da ido, kafin ta karasa main parlor suka yi kicibis da Yakumbo, Yakumbo ta koma baya ta kare mata kallo daga sama har kasa sai kuma ta rushe da wani matsanancin kuka tace "Allah ya ga xuciyar mu, bama nufin kowa da sharri a duniya, bama nufin d'an kowa da sharri, yanxu Heedayah ce wnn nake gani Aisha? Heedayah ce wnn ta xama gandareriyar yan mata haka aure yau ko gobe?" Kuka take yi sosai ta koma parlor ta xauna tana cewa "Xuciyar mu daya laya, bama nufin kowa da sharri duniya da lahira.... Yau ba ga ranan hakuri ba amma da mata duk kin bi kin daga ma mutane hankali kin dami mutane, kowa na jin haushina ana ganin kamar hada baki muka yi da 'yan kinnafas din, toh ni dai duk a gaggauta neman gafarana don an xalunce ni da mummunan xato wanda har duniya ta tashi baxai gogu a raina ba, aka shiga tsakanina da d'an uwana da na rike tun yana karami duk sbda an sace Heedayah a gidana kamar ni na sace ta...." Heedayah dai sai kallonta take, can ta tafi ta rungumeta da murmushi fuskarta, Yakumbo dai sai kuka take, Ammi kuma ta xauna saman kujera tana karasa saka ma Ashnaah kayanta, knocking aka yi, Ammi ta kalli Heedayah dake ta kallon Yakumbo kamar ta samu TV, nan kuma Kaka kawai take gani wajen a xaune, mikewa Heedayah tayi ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Khaleel bakin kofar, ta koma baya tana kallonsa da mamaki, can tace "Anyi discharging din ka ne?" Ya gyada mata kai yace "Ur Dad... is he in?" Tace "Ehh yana sama" Juyawa tayi tana kallon Ammi tace "Ammi it's ya Khaleel" Ammi tace "Ohk, let him in" shigowa parlon yyi, Ammi na kallonsa tace "Sannu da xuwa" ya gaisheta ta amsa tace "Daxu Abbansu Islam ke ce min anyi discharging din ka.... Ya karfin jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh naji sauki, na xo yi masa godiya ne" Ammi tace "Ohh bbu komai ai, he is coming downstairs now, have a sit...." Xaunawa Khaleel yyi yana gaida Yakumbo dake ta kallonsa tayi mitsi mitsi da ido, can ta share hawayen idonta tana kallon Ammi tace "Shi kuma wnn din waye?" Ammi tace "Shine Honorable ke gaya maki ai" Yakumbo ta tabe baki tace "Toh ni dai ce masa nayi wa ya sani ko shi yayi kinnafin din nata da ya gaji ya ga ba sarki sai Allah ga yasin ana ta jifarsa da shi ya maido ta" Ammi ta d'an hade rai tace "Haba Yakumbo, wani magana ne wnn, Heedayah dake hannun mahaifiyar makociyar mu a kaduna, shi dai ta dalilin sa aka kawota nan gidan, ba wai wani abu ba" Yakumbo tace "Atoh ni babu ruwana wllh, ke baki ga kirarsa bane kamar ta mutan da, ai irin su ne ke kinnafin din yanxu, a ajiye batun wani kyansa, wllh duk haka suke ba muna gani a TV ana nuna mana su ba kullum" Ammi bata kuma cewa komai ba sai dai ranta ya baci sosai, Shi dai Khaleel kansa na kasa, Heedayah sai kallon Yakumbo take kamar xata yi kuka, Yakumbo ta kyabe baki ta bude yar jakarta ta fiddo tissue da aka nannade ta warware ta ciro goronta ta fara ci tace "Na nannade kayana kada kura ya fada kai in cutu...." Ammi dai ko kallonta bata yi ba ta kalli Heedayah tace "Ku je da shi gidan Dinar ya gaida Mamin ki a can kafin Abbanku ya sakko" A sanyaye Heedayah ta mike tana kallonsa, ya mike yyi ma Ammi godiya, amma shi ma gaba daya jikinsa yyi sanyi, ya bi bayan Heedayah da har ta kai kofa, Yakumbo tace "Toh Allah ya maka albarka, ai da ba don kai din ba da har yanxu ana ta xargina ana kullatata a xuciya, 6atan wnn yarinya bbu irin bakin jinin da bai ja min ba a duniya, duk inda na kutsa nuna ni ake da d'an yatsa har ya kai ya kawo na dena fita, ko kasuwa na shiga anyi ta leko ni kenan a shaguna" Heedayah ta kulle kofar bayan Khaleel ya fito, tana kallonsa cikin sanyin murya da damuwa tace "Kayi hakuri plss, Ammi na ta gaya min haka take, she's strange because she is old" Yyi mata murmushi bai ce komai ba, tace "Baka yi kama da kidnapper ba, kuma baxa ka ta6a kama da su ba" Kallonta yake without blinking, xata wuce a hankali yace "Why did you think so" Ta juyo da sauri tace "Dama me yasa xaka yi kama da kidnapper? My Yakumbo is just saying that out of frustration, Allah ya raba ka da kama da su, they are the deadliest set of beings on earth...." Sauke idonsa yyi bai ce komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta har suka isa gate, ta kallesa tace "Seems you are not still happy about what Yakumbo said..." Da sauri yace "Noo, it's nothing, nasan haka tsofaffi suke" A tare suka shiga gate din Dinar, ya tsaya bakin kofar parlon ta shiga sanar ma Mami xuwansa, a hankali ya xauna saman kujeran da ya gani a wajen, lkci daya hawaye ya kawo idonsa abinda tun da ya san kansa bai ta6a yi ba, sai dai ya ga ana kuka amma shi bai ta6a ko digon hawaye ba don ya taso xuciyarsa a kekyashe ne, Bai ta6a jin ya tsani rayuwarsa irin na wnn lkcn ba, he just hate everything about him immediately, a da ya kan ji hakan amma baya wani tasiri a xuciyarsa don in few minutes yake dawowa normal, yau kuma sai yaji hawaye na xuba idonsa sosai, fitowa Heedayah tayi tace "Ya Khaleel an ce ka shigo" Jin bai dago kansa ba ta isa gabansa tace "Ya Khaleel" durkushewa tayi gabansa ganin hawayen idonsa, lkci daya ta rikice ta kamo hannunsa tace "Are you okay? Me ne ya faru, ko kirjin naka ne ya fara, tell me plsss" ya girgixa mata kai trying hard to control the tears ya kamo hannunta amma ya kasa cewa komai ya xamo kasa, kuka take sosai tace "Plss ka gaya min what's wrong ya Khaleel, me ya same ka" cike da karfin hali cikin rawar murya yace "I... I want.... you to be a father... mother... and sibling... to me" Shiru tayi hawaye na sauka idonta tana kallonsa, ganin ya sauke kansa kasa hawaye na ci gaba da sakko masa ta rungumesa ita ma hawayen na xuba idonta tace "Did you lost them??" Gyada mata kai ya dinga yi amma ya ki cewa komai, tace "Talk to me plss, did u lost them" cikin sarkewar murya yace "I never had them" ta fashe masa da kuka sosai tace "I promise I will be, I promise you that..." Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta sake sa da sauri har lkcn tana kuka ta mike, Mami ce tsaye bakin kofar ta fito da mamaki tace "What happened???" Heedayah dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take, Mami ta daga kan Khaleel da ya sunkuyar da kansa ya ki dagowa, ganin idonsa tace "Subhanallah what happened, are you Okay" ya girgixa mata kai cike da karfin hali ya mike cikin sanyin murya yace "I... I came to thank you Ma, I appreciate ur care toward me...." Hawayen dake sauka idonsa yasa Mami ta ji lkci daya nata idon ya cicciko tace "But you don't need to dear, you don't need to..... Come in" kama hannunsa tayi xuwa parlon Dinar, Heedayah ta bi bayansu tana goge hawayen dake xubo mata, Xaunawa Khaleel yyi saman kujera lkci daya yaji ya samu nutsuwa, xuciyarsa ya daina masa xafin da yake masa with just Mami's word, daki Heedayah ta wuce ta ki tsayawa a parlon don gaba daya xuciyarta tayi rauni abinda yace mata, Mami ta sa mai aikin Dinar ta kawo abinci da ruwa ta ajiye masa, shiru yyi kawai yana kallon abincin, tun da ya san kansa sai dai ya shiga eatry ya ci abinci bai san dadin abincin da aka girka a gida ba, muryar Mami ya ji tace "Ka ci abincin" Ya kalleta snn ya xamo kasa a hankali ya xauna ya bude plate din abincin, shinkafa ne da miya with many meat sai coslow a wani d'an bowl a rufe, ya dau spoon ya fara cin abincin a hankali, Mami dai sai kallonsa take don exactly yanda Junaid ke xaman cin abinci ya xauna, Dinar na sakkowa xata dauko ma Fadil fresh yo a kitchen ta tabe baki tayi wucewarta kitchen din, kawai ita dai ta ji ranta bata yarda da Khaleel ba, ga shi da innocent face, very innocent, but ita dai bata yrda da shi ba. Abba ya dau makullin motarsa xai fita parlonsa Mumy dake ta kallonsa a tsaye tace "Yau naga ikon Allah, Ina kuma xaka daga dawowa barrister ko hutawa baka yi ba, ga abinci can nace maka na gama ka dau makullin mota xaka fita" Yace "Nace idan na dawo xan ci Maryam, xan je can gidan Dr ne Yanxu" Mumy ta kyabe baki tace "Toh aiki kaje yi Abujan ko har yanxu kan batun 6atan Heedayar ne, ni fa wllh da na ji shiru bbu wani labari kuma babu wanda ya sake cewa komai na xata an ganta ne" Abba ya juyo yana kallonta yace "Eh an ganta, a gidan mahaifanta a nan garin Abujan" Mumy ta saki wayar hannunta ba tare da ta shirya yin hakan ba tace "Ban gane gidan iyayenta ba?" Yace "Yes biological parent dinta, idan kina jin Honorable Ahmad Yusuf Ishaq, shine Mahaifinta" Mumy ta masa wani kallo tace "Ban gane ba, wacce Heedayar wai kake fadi barrister, Heedayah da ba lallai a sake ganinta ba kake nufi ko warce?" Abba yace "Toh ki tambayi d'an ki xai fi yi maki bayani in details a kan abubuwan da suka faru, tare aka yi komai da shi a Abuja, as for now sai na dawo...." Bai jira cewarta ba ya fita, ta cire dankwalin kanta jin wani xufa dake keto mata tun daga saman kanta har kasa duk da Ac dake kunne parlon, da dankwalin ta dinga fiffita ma kanta iska can ta dau wayarta da screen din ya tarwatse ta shiga kiran Shuraim, yana fara ring ya daga tace "Duk inda kake kuma duk me kake yi ka barsa ka dawo gida yanxun nan ina jiran ka" Jin yanayinta yace "Lafiya Mumy??" Kuka ta sakar masa tace "Ni dai nace ka dawo yanxun nan Aliyu" Daga haka ta katse wayar ta sake jefarwa kasa tana xagaye parlon, gaba daya xuciyarta ta ki yrda ko na second daya da xancen Abba sai kace wani film, wai wani Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq shi ne uban Heedayah, ta ina?? Bayan ko kama da shi ma bata yi ba, yarinyar da aka ce an tsinto a daji, to amma kuma ai barrister baya mata karya wasu hawayen da bata san dalilinsu bane suka shiga sakko mata tace "Aikin banxa, uban wa xa ayi ma wnn karyar, Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq ne ubanta shine da ta 6ata ba a ji a duniya ba...." Tsaki ya ja ta nemi waje ya xauna tana kara tabbatar ma kanta raina mata hankali kawai Abba yake, ya ma san wanda ya ambato mata a matsayin uban Heedayah kuwa, abinda ance mata Heedayah ta shiga duniya kenan ba dawowa, mikewa tayi ta sake daukar wayarta tana neman layin Sadiya.



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Abba ne xaune parlon Kaka, ita kuma tana xaune daga kan darduman da tayi sllh hannunta rike da carbi, tun fara bayanin Abba kaka ke kallonsa kamar a lkcn ta fara ganinsa, har sai da ya kai aya kaka ta ki cewa komai sai xare ido take, Bude kofar parlon aka yi hade da sallama Baffa ya shigo, ya xauna saman kujera yana kallon Kaka ya gaisheta, jin tayi shiru bata amsa ba yace "Lafiya Baaba??" Kaka ta kunce ha6ar xaninta ta fara matsar kwalla tana shessheka tace "To dai tunda mu ke kallon banxa bai ta6a hadani da Heedayah ba Allah ya so ni, Umaru kaga shi yasa aka ce mutum ya ji tsoron Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login