Showing 180001 words to 183000 words out of 275313 words
Chapter 61 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
motar ta daga ma Heedayah hannu tayi hanyar gate dinsu Dinar, Alhaji Ahmad ya shiga da motar cikin gidan, yyi parking a parking space, bude motar Heedayah tayi ta sauka, shi ma ya sauka yana kallonta, ta sunkuyar da kanta, duk sai ta ji kewar Mami sosai, Alhaji Ahmad ya nuna mata bangaren Mahaifiyarta yace "Mu je" Gaba ta shiga ta nufi inda ya nuna mata yana biye da ita a baya, Bbu kowa a babban parlon, Heedayah ta nemi gefen kujera ta xauna amma da ganinta kasan a takure take, Abbanta na kallonta yace "Mu je wajen Ammin ki" mikewa tayi ta bi bayansa xuwa corridor din dakuna biyar, ya bude kofar bedroom din Ammi ya ga bata ciki, wani kofar ya bude ya ganta xaune saman darduma a dakin dake dauke da gadaje guda biyu na yara, komai na dakin na kids ne, Abban Heedayah ya juya ya kalli Heedayah da ta rakube gefe daya yace "Come in" shiga dakin tayi tana kallon girls din dake kwance kan each bed, wa enda kila su yi shekara uku, Ammi sai kallon Heedayah take, a hankali Heedayah ta duka kusa da ita tace "Ammi mun dawo" Ammi ta sakar mata murmushin karfin hali amma ta kasa cewa komai, fita Abba yyi daga dakin, a boye Ammi ta goge hawayen dake kokarin gangaro mata tace "Have you eaten?" Heedayah ta gyada mata kai, Uwar tayi shiru, can tace "To tashi mu je ki kwanta" Mikewa Heedayah tayi, Ammi ma ta tashi, ta karasa twins dinta ta rufe ko wannensu da blanket ta xauna gefen daya gadon ta tofa masu addu'a snn ta mike tana kallon Heedayah tace "Mu je" kofa Heedayah ta nufa Ammi na biye da ita, Ammi ta kulle kofar dakin bayan sun fita, ta tafi ta bude wani kofar tana kallon Heedayah, karasowa Heedayah tayi Ammi tace "Sai da safe" Heedayah ta shiga dakin Ammi ta kulle kofar, ta wuce nata dakin tana goge hawayen da ya ki tsaya mata. Har kusan karfe biyun dare Ammi ta kasa bacci banda sllh bbu abinda take tana kara gode ma Ubangijin ta, she just can't believe her daughter is back after 5 years, bata son tuna baya, bata son tuna shekaru biyar din nan da suka wuce da halin da ta shiga, she just want that memory to erase off her heart, ta share idonta daga karshe ta mike ta bude kofar dakinta a hankali ta fita, dakin Heedayah ta nufa ta bude kofar in a way it won't make any sound, haske wutan corridor dake a kunne yyi reflecting dakin, Heedayah dake kwance idonta biyu ta kasa bacci gaba daya ta ji bbu abinda ke damunta irin rashin lafiyar Khaleel tun da ta kwanta bayan tayi wanka take juye juye, mikewa xaune tayi da sauri jin an bude kofa, Ammi ta shigo dakin ganinta a xaune ta kunna wutan tace "Baki yi bacci ba?" Heedayah ta shiga mitsika idonta kamar me bacci tace "Na farka ne yanxu" Ammi ta isa kusa da gadon ta xauna tana kallonta, Heedayah ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Nayi missing din ki Ammi, I've missed you so much" Ammi ta jawota jikinta tana murmushi tace "I missed you more daughter" shiru duk suka yi, can cikin sanyin murya Ammi tace "Do you remember when you let Yakumbo's house that very day?" Heedayah ta d'an yi shiru sai kuma tace "Yes, wasu mutane ne suka tafi da mu a motarsu da su Ladi, ban san inda suka kai mu ba, we walked a long mile, suka kai mu wani waje, I can't see, I only can hear, so I don't how the place looks like, har muka yi bacci muka tashi a wajen, it seems suna kashe mutane coz then ina jin karan gun shot, sai wani ya daukeni a bicycle muka yi ta tafiya ya kai ni wani waje ya ajiyeni ni kadai ya tafi ya bar ni.... He just left me and go not considering that I am blind..." Hawaye ya cika idon Heedayah tana kallon Amminta dake saurarenta, Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Taimakon ki yyi ya fitar dake kilan kar a kashe ki a wajen" Heedayah tace "But he just abandoned me by the road side" Ammi tace "He is an angel for that, da sun kashe ki yanxu my daughter" Heedayah tayu shiru, sai kuma tabe baki tace "Ni ban san me ya faru ba, seems I was knocked down by a vehicle, and daga nan sai Abba ya kai ni gidansa, and I began staying with them.... he has a son Ya Shureen" Heedayah ta d'an hade rai tace "Ni bana sonsa, baya dariya, baya min wasa, his mother is so mean, bata sona, his sisters are mingy also, they don't like me even for a second" Ammi dai sai kallonta take ko kiftawa bbu, Murmushi Heedayah tayi a hankali tace "Abba ne kawai yake so na, he was always there for me, he paid for my eye surgery, and Mami.... she is also my mother, I love her, I love them" Shiru Heedayah tayi tana kallon Mahaifiyarta, Ammi ta shafa kanta a hankali tace "Sure dear, she is ur mother, always take her as one, and take me as ur aunt" Heedayah ta kalli uwarta tayi murmushi bata ce komai ba, a hankali tace "But you remain my mother" Rungumeta Ammi tayi tana murmushin ita ma, Heedayah tace "Ya Junaid, Ya Sudais, they were always there for me...." Wara ido tayi tace "Kaka....." Ammi ta janyeta jikinta tana kallonta. Har aka yi kiran sllhn asuba Ammi na tare da Heedayah hira sai wanda ta manta ne bata yi ma Amminta ba barin hiran kaka, wani Ammi tayi dariya, wani tayi murmushi, wani tayi shiru, wani kuma taji hawaye ya kawo mata, she is just imagining, ashe dama akwai wa enda xa su rike yaron da basu san daga inda ya fito ba da amana ynda mutanen nan suka rike mata 'yar ta, bata san da me xa su biya Abba ba, bata san da me xa su biya Mami ba, but ta fi jin Abba don da bai dau Heedayah ya tafi da ita ba da bata san wani labarin xa a dinga yi ynxu ba, they owe him greatly.... Bude kofar dakin da Abban Heedayah yyi wajen karfe biyar na asuba yasa Heedayah tayi shiru daga labarinta, murmushi yyi yana daga tsaye bakin kofa yana kallonsu, can kawai ya juya ya fita xuwa masallaci, Sai a snn Ammi ta tafi nata dakin don yin alwala, Heedayah ta shiga bathroom din dakin da take. Bayan Heedayah tayi sllh ta shiga bandaki tayi wanka, ta fito daure da towel, sai ga Ammi tare da Mum Islam sun shigo dakin, Gaisheta Heedayah tayi, da fara'a mum Islam ta amsa tace "Jiya kafin ku dawo nayi bacci wllh, kayan ki na gidan Dinar in amso maki ko? Naga har kin yi wanka" Heedayah ta gyada mata kai, Mum Islam tace "To bari in tafi in karbo maki yanxu" daga haka ta fita dakin, Ammi na kallon Heedayah tace "What are you taking for breakfast?" Heedayah ta xauna gefen gado tana kallon Amminta a hankali tace "Ammi baxa mu tafi can asibitin ba?" Ammi tace "Da asuba xa a je asibitin? ai xa ki bari gari ya waye ko?" Heedayah tayi shiru, sai kuma tace "Toh" Ammi ta tafi ta dauko mata body lotion kafin Mum Islam ta dawo. Karfe bakwai da rabi Farida da Dinar suka shigo parlon Ammi... Matan step brothers din Abban Heedayah da Kanwar Ammi da few family frnds ne xaune parlon, ko wannensu ya xo gidan nuna farin cikin bayyanar Heedayah bayan shekaru biyar, Ammi suka gaisa da Dinar da Farida da fara'a don ta ga kamanninsu da Mami tace "Tana ciki ku shiga" Mai aikin Ammi ce ta nuna masu dakin da Heedayah take da kanninta, Heedayah na xaune dakin tana ta kallon 'yan kanninta dake ta xuba mata shirme ko wannensu na son bata labari duk da ba wai sun santa bane amma jini ba karya bane, nan kam ita kallon girls din masu kama da ita tana karama take amma hankalinta ba a gun su yake ba, Ammi tace mata xa su je kai abinci asibiti amma bata ji ance ta xo su tafi ba tun daxu... Farida ce ta fara shigowa dakin, Heedayah ta mike da sauri ta rungumeta sosai tace "Farida..." Farida dai bata ce komai ba, haka Dinar da ta nemi waje ta xauna, Heedayah ta koma inda take a sanyaye ta xauna, tana kallon Dinar tace "Ina kwana Maman Fadil" Dinar tace "Lafiya lau" cikin sanyin murya Heedayah ta sunkuyar da kanta tace "Kiyi hakuri Maman Fadil, I don't know what came over me, I am sorry..." Tana fadin haka Farida ta fara kuka Heedayah ta mike ta koma kusa da ita ta rungumeta tace "I'm very sorry Farida, I don't know what really happened" ita dai Dinar har snn bata iya ta ce komai ba, da yake tasan Ashnaah da Ashfaa don Mum Islam kan shigo gidanta da su, sai ta jawosu tana masu wasa, a haka mum Islam ma ta shigo dakin ta samesu. Karfe goma saura Heedayah ta fita daga dakin, xuwa lkcn gidansu ya cika da 'yan uwa da abokan arxiki, ita duk wnn ba shine damuwarta ba, tana ta tsaye corridor sai ga Amminta, ganin yanda ta tsaya kamar tana cikin damuwa Ammi na kallonta tace "Do you need anything?" Heedayah ta sauke kanta kasa a hankali tace "Ammi an kai abincin da kika ce asibiti?" Ammi tace "Toh barin abincin xa ayi ta yi har yanxu ba a kai ba, Abbanki na Kaduna da na nan with ur Mami suna can asibitin, anjima nima xan je, and Shuraim is around now, ki tafi kitchen ki hada masa breakfast ki kai masa, yana parlon Abban ki" Da sauri Heedayah ta kalleta, lkci daya ta 6ata fuska tace "Ni dai Ammi baxan iya ba, kila ma dukana xai yi, ni dai gwara in kira Farida ta kai masa wllh" Ammi ta hade rai tace "Ke nace ki kai masa..." Hawaye ta fara yi tace "Ni fa har yanxu ban ma je asibitin ba faaaa"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Bude kofar parlon Heedayah tayi suka yi ido hudu da shi yana xaune parlon yana danna wayarsa, ta kara daure fuska ta tafi ta xauna saman kujera murya can ciki tace "Ina kwana" Jin bai amsa ba ta daga kai ta d'an kallesa, ajiye wayar hannunsa yyi still not looking at her yace "Congratulations for reuniting with ur parent" Tace "Thank you" bayan few seconds jin bai ce komai ba tace "A kawo maka breakfast in ji Ammi?" Ya mike yace "Not hungry" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo har ya fita, ta kyabe baki ta mike ta fice parlon ita ma, tana jin yana sallama da Amminta ta makale ta ki karasawa, Ammi tace "Breakfast din fa?" Yace "No na yi breakfast nagode" Ammi tace "Ohk hospital din xaka tafi yanxu?" Yace "Aa, Kaduna xan wuce" Ammi tace "Yau din?" Yace "In sha Allah" Ammi tace "Toh Allah ya tsare, sai mun xo" Yace "In sha Allah" Bayan Azahar Heedayah da Farida suka tafi asibiti tare da Amminta, she is just happy tun fitowarsu ko ba komai xata ga condition din Khaleel, Junaid ne kadai xaune ward din, Khaleel kuma na kwance yana bacci, Ammi suka gaisa da Junaid tana tambayarsa me jiki, yace "Alhmdllh da sauki" Ammi tace "Toh Allah ya basa lafiya, Allah ya tashi kafadunsa" Junaid yace "Ameen ya rabbi" Heedayah ta ajiye abincin dake basket din hannunta da suka taho da shi tana kallon Junaid a hankali tace "Ina yini ya Junaid" ya sakar mata murmushin da iyakarsa lips yace "Lafiya" Gaishesa Farida tayi ya amsa ta nemi kujera ta xauna, bayan few minutes Ammi tace "Toh idan ya tashi ka gaida mana shi, xa mu koma, Allah ya basa lafiya" da sauri Heedayah ta kalli Ammi amma dai bata ce komai ba, Farida ta mike ganin Ammi ta yi kofa tana amsa sallaman da Junaid ke yi mata, Heedayah kamar xata yi kuka ta mike a hankali, xata fita Junaid dake lura da ita ya kalli kofa ganinsu Farida sun fita ya riko hannunta ba yabo ba fallasa yana kallonta yace "Bayan tafiya gidansa da kika yi kika kwana, do u still have any undone business with him???" Heedayah ta buda ido tace "But he is sick and I have to pity him..." saketa yyi yace "Toh xauna kiyi jinyarsa" Ko kallonsa bata sake yi ba ta bi bayan Amminta da sauri ta fita. Suna komawa gida Ammi ta shiga gidan Dinar tare a Heedayah da farida, Mami na parlor xaune Dinar tayi tagumi tana kallonta tace "But you need not to be this worried Mami, ke komai sai ya baki tausayi, ba sanin wannan mutumin kika yi ba me yasa xaki damu kanki haka a kansa, beside yana samun lafiya ai ko, ni fa har yanxu I am not happy at the way ya kai Heedayah gidansa har ta kwana, no responsible person will do that, and dubi fa har waya ya bata a boye, what's the meaning of that, gidan iyayenta na asali kuma da ake ganin kamar shine silar xuwanta everything just happened coincidentally ba wai ya san sune iyayen nata bane, I see no reason da kowa xai wani dinga ganin kamar shine silar reunion dinta da parent dinta, it's not so plss, da ta ci gaba da xama a nan kafin hutunsu ya kare dole Mum Islam xata shigo ta ganta daga nan komai xai bayyana...." Mami dai sai kallonta take, Dinar ta ci gaba tace "But the way u people are treating d guy kamar ba shi da laifin dauke yar mutane ya kai ta gidansa ta kwana daga shi sai ita is alarming, who does that, nobody is even talking about this fa, duk mijin da ya fito xai aureta in har fa ya ji wnn labarin da karamin matsala xai ja ba, yarinya budurwa ta tafi gidan saurayi ta kwana ta yini duk a daga ma mutane hankali, but nobody is talking about it, ni fa shi sa Shuraim din nan ya burgeni wllh, ya san abinda yake" Mami tace "Enough Dinar, I trust Heedayah, kila dai kun yi mata wani abun ne da bata ji dadi ba ta bar maku gidanku amma ba abinda xai kai ta gidan namiji da son ranta, wanda Allah ya riga da ya kaddara dole sai ta bar gidan ma xata hadu da mahaifanta, ta silar wnn bawan Allahn kuma...." Sallamar da aka yi bakin kofa ya sa Mami tayi shiru, Farida ta bude kofar ta shigo parlon Heedayah na biye da ita sannan Ammi, a sanyaye Heedayah ta karasa gun Mami ta duka kusa da ita tace "Ina yini Mami" Mami ta sakar mata murmushi tace "Lafiya lau, kun dawo asibitin?" Heedayah tace "Mun dawo" Maman Fadil ta mike tana ma Ammi sannu da xuwa, Ammi ta amsa da murmushi ta xauna snn suka gaisa da Mami, Mami tace "Nima yanxu nake shirin xan tafi asibitin, da yau din ma xa mu wuce Abuja da Barrister amma nace bari in kara kwana daya in ga jikin bawan Allahn" Ammi tace "Allah sarki, da muka je ma bacci yake ynxu, and he is the one holding us back too don xa mu tafi Kadunan mu ba, ya ce mu jira ya ji sauki tukun mu je" Mami tace "Toh Allah ya bashi lafiya" Ammi ta amsa da "Ameen" drinks Dinar ta kawo ma Ammi da bata ta6a shigowa gidanta ba sai ranan, Ammi tace "Ae da kin barsa Maman Fadil, Ina Fadil din?" Dinar tace "Yana bacci a sama" Ammi tace "Allah sarki" Kitchen Dinar ta tafi ta ci gaba da girkin da take Farida ta mike ta bi bayanta, Heedayah dai na xaune kusa da Mami, Mami tace "Ki je ku yi girkin" Ba musu ta mike ta bi su kitchen din, Ammi ta mike ta dawo kusa da Mami ta xauna ta fara magana cikin sanyin tace "Hajiya muna alfahari da ke da Barrister, kun yi abinda ba ko wani d'an Adam Allah ke ba ikon yi ba, kun rike Heedayah xuciya daya ba tare da sanin daga inda ta fito ba, Allah ya saka maku da alkhairi, ya biya ku da aljanna, domin mu kam bamu da abinda xa mu biya ku" Mami tayi murmushin karfin hali tace "Allah ya taimaki nawa haka nima...." Ammi tace "Ameen" Suna parlon har kusan la'asar kafin Ammi ta mike tace "Xata koma gida tayi sllh" Mami tace "Nima sllhn xan yi nasan Dinar sun gama girkin sai mu je asibitin" Ammi tace "Toh Allah ya dawo da ku lafiya" Mami tace "Ameen, amma don Allah kar a sake kawo wani abincin, wanda aka kawo ma Allah ya amfana, Ga Dinar tayi girki ma yanxu" Murmushi kawai Ammi tayi, ta kara mata sallama ta fita parlon. Mami na idar da sllh Dinar ta fito da abincin da ta gama a basket, Mami tace "Kin yi ma Usman din magana?" Dinar tace "Ehh bari in dauko Hijab" Heedayah ta sakko daga upstairs bayan ta idar da sllh Mami tace "Ga abinci can a kitchen ki kira Farida ku deba kuyi lunch" Heedayah ta xauna a hankali tace "Mun ci abinci" Mami tace "Ohk" Shiru Heedayah tayi, can tace "Asibitin xa ki tafi Mami?" Mami tace "Ehh" A hankali Heedayah tace "In bi ki Mami?" Mami tace "Ba daga can ku ke ba yanxu?" Heedayah bata ce komai ba, Dinar dai ta saka hijab dinta ta dau basket din abincin ta fita waje bayan ta dau makullin motarta, har Mami ta nufi kofa ta juyo tana kallon Heedayah da ta bi su da kallo tace "To taso mu je" Heedayah ta mike ta dau mayafinta