Showing 153001 words to 156000 words out of 275313 words
Chapter 52 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
mike ta wuce sama kamar xata yi kuka. Shuraim na fita junaid ya shigo, yyi ma Mami sannu da xama ta amsa tana kallon hannunsa ya wuce sama. Karfe sha daya da wani abu junaid ya bude kofar dakinsu Farida, Farida tayi bacci Heedayah kuma na kwance cikin blanket tana waya da Khaleel, jin an bude kofa ta katse wayar da sauri, tayi still barin da taji an kunna switch din dakin, bayan few seconds ta sauke blanket din a hankali, mikewa xaune tayi tana kallonsa tace "Yaya" ya ajiye mata ledan hannunsa yace "Ga abincin" murmushi tayi masa tace "Nagode" ya daga mata gira yace "Good night" daga haka ya juya xai fita ya kusa cin karo da Mami, da sauri Heedayah ta mayar da kanta cikin blanket din, Ya fara kame kame ya ma rasa abinda xai ce ma Mamin tasa, Mami ta kalli ledan da ya ajiye sannan ta karasa ta bude ledan, takeaway ne na fried rice with full chicken lap, ga chivita drink, sai kuma tsire a wani takarda daban, mayar da ledan tayi ta rufe sannan ta ce "Toh fita" juyawa yyi ya fita dakin ta fita ita ma ta kulle, a hankali yace "Mami kiyi hakuri, naga bata da lafiya ne kuma kar ta kwana da yunwa, right from time kinsan bata cin tuwo" Mami tace "Kuma gaskiya ne, kai me conscience, ni kuma mara shi..." Da sauri yace "Aa wllh Mami ba haka bane" dakinta ta shiga, ya d'an yi jim sannan ya bi bayanta xuwa dakin, tace "Aa yi tafiyarka ka kwanta...." Yace "Kiyi hakuri Mami" kujera ta nuna masa tace "Sit" ba musu ya xauna, ta xauna gefen gado tana facing dinsa tace "Tell me, what is ur intention na makale ma Heedayah da kake yi ina hanaka amma baka ji" ya sunkuyar da kansa yyi shiru, tace "Answer me, xan kwanta ina da aiki gobe" Yace "Nothing Mami, matsayinsu daya da Farida" Tace "Good I hope it shouldn't pass that Junaid..." Dago kai yyi yana kallonta tace "Yess, matsayinsu ya tsaya daya da Farida, tashi ka tafi good night" Yyi kasa da murya yace "But me yasa kika ce haka Mami?" Tace "Me yasa nace me?" Yace "Abinda kika ce" Tace "Ban gane tambayar ka ba" ya sauke idanuwansa kasa yace "But Mami...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yace "I would have wished us to be together till end" Mami tace "As???" Jin ya ki cewa komai ta hade rai tace "Kaga you stop beating about the bush and save my time, go straight now" yace "Mami kawai Ina sonta, kuma Ina jin xan iya aurenta" Kallonsa Mami take bbu ko kiftawa, can tayi wani murmushi tace "Ita Shaheedar fa?" Ya d'an hade rai yace "Dama kece ke sonta ba ni ba" Tace "Haka kace?" Yayi shiru, tace "Toh ba da ni xa ayi wnn haukan ba, Shaheedah da maganarta ke kasa kusan shekara uku sbd selfish interest dinka kace min ni ke so ba kai ba...." Yace "Don Allah Mami ki bar maganan nan wllh bana jin xan iya auren Shaheedah, idonta ya bude da yawa, kuma I can't marry someone living all alone abroad da sunan tana karatu" Mami tace "Fine then, idan kai ka haife kanka sai mu gani ai, ita Heedayar an gaya maka ikon mu ce??" Bai kuma ce mata komai ba, tace "I will advice you ka cire idonka a kanta don baxa ka ta6a samun ta ba, beside nawa take da har xaka ce kana sonta da aure, did you think xaka kara min shekara daya ne nn gaba, ba dai cikin shekaran nn Shaheedah xata gama ba, xaka sha mamaki" mikewa yyi yace "Sae da safe" tace "Allah ya tashemu lfya" daga haka ya fita dakin ya kulle mata kofa. Washegari da safe Farida ta gama hada few kayan da xata tafi da shi gidan yayarta a Abuja, Heedayah dai na xaune dakin duk ta xama abun tausayi, Farida ta koma kusa da ita tace "Ko xa kiyi ma Yaya magana yace Mami ta bar ki mu je tare" Heedayah ta share guntun hawayen idonta a hankali tace "Baxata bari ba, I know she is angry at him now bcos she caught him giving me food yesterday night" Farida tace "To yanxu wa xai yi mata magana ta ji? Nobody, cewa xata yi baki da lafiya" mikewa Farida tayi ta dau powder dinta a gaban mirror ta saka a handbag dinta kar ta manta, a hankali Heedayah tace "Ko mu gaya ma Ya Shureen yyi mata magana??" Farida ta juyo tana kallonta, dariya tayi sosai tace "He is not Shureen Heedayah, He is Shuraim" Heedayah tace "To ni ina ruwana ba Shureen naji kaka nace masa ba, ni dai mu yi masa magana koh?" Farida tace "Amma dai ke xa ki yi masa maganan" Heedayah tace "Ehh xan yi masa" Farida tace "Ina xa mu samo number sa?" Heedayah tace "Mami na da shi ai kamar, let me check" daga haka ta mike ta fita, a hankali ta bude kofar dakin Mami bata ganta a ciki ba, ta karasa gun wayarta da sauri ta dauka ta shiga contacts, searching sunan tayi sai ga shi ya fito with 080333.... Lkci daya ta haddace gaba daya ta ajiye wayar ta fice daga dakin, tana kallon Farida tace "Where is ur phone, I have crammed the digit" Farida ta mika mata wayarta Heedayah ta sa number snn ta marairaice tace "Are you sure we should call him Farida?" Farida tayi dariya tace "Yess try it, ki sa a handsfree in ji me xai ce" Heedayah ta xauna gefen gado xuciyarta na bugawa tayi dialing number, har ya gama ring ba a dauka ba, Farida dake ta kallonta ita ma xuciyarta na bugawa kamar ita xata yi masa magana tace "Redial it..." Heedayah ta kuma sending number ta sa handsfree tana xare ido, nan ma har ya gama ring no response, Farida ta ta6e baki ta cigaba da abinda take, a hankali Heedayah tace "May be baya daukan bakon number ko" Farida tayi mata wani kallo tace "As per shugaban kasa or governor dat he is ko???" Dariya Heedayah tayi, Farida ta ja tsaki tace "Ki je kiyi wanka may be Mami will change her mind idan ta ga mun shirya tare" A sanyaye Heedayah ta mike tace "Toh train xaku shiga?" Farida tace "Noo, Mami tace driver ne xai kai mu idan yace xai iya idan kuma baxai iya ba ban san yanda xa ayi ba" Bathroom Heedayah ta shiga bata ce komai ba, bayan kusan minti talatin ta fito daure da towel, wayar Farida dake kan gado ne ya fara vibrate, Heedayah ta xaro ido tana bin dakin da kallo don Farida bata nan, can tafi gun wayar tana gyara daurin towel dinta ta leka wayar taga number Shuraim ne, daukar wayar tayi xuciyarta na bugawa ta xauna gefen gado ta daga ta sa handsfree, sallama yyi daga daya bangaren ta wani xaro ido ta kasa amsawa, har sai da ya kuma yin sallama, kamar xata yi kuka tace "Uhn Ina ji" shiru yyi, a takaice yace "Waye wannan?" Ta kara gwalo ido tace "Ni ce fa" yace "Ke wa?" Ta turo baki tace "Ni mana" yace "Baki da suna?" Tace "Heedayah" Shirun 3 seconds yyi snn yace "Why are you calling?" Ta marairaice murya tace "Ya Shureen dama... dama" sai kuma tayi shiru, yace "Dama me?" A hankali tace "Dama Mami ce tace baxan bi Farida Abuja ba mu je gidan Maman Fadil, shine sai Farida tace ko xaka mata magana, shine na kiraka nake gaya maka" Yace "Faridar ta aiko ki wajena" ta xaro ido tace "Aa wllh, ba ta ma dakin ni kadai ce, na fito wanka yanxun nan sai naga wayar yana vibrate" yace "To baxa ki je Abujan ba" ta buda baki da farko, sai kuma ta fashe masa da kuka tace "Ya Shureen plss, wllh I want to go, ban ta6a xuwa ko ina ba tunda aka haifeni, nima ina son inje wani waje don Allah" Yace "Baxa ki je ba, xan xo kuma in gaya ma Mami bbu inda xa ki je" Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta fashe da kuka ta ajiye wayar tana kallonsa tace "Wllh sai naje ina ruwanka da ni to" Farida ce ta shigo dakin tana washe baki tace "Guess what Didi, Mami tace mu je amma kwana uku kawai xa mu yi mu dawo sbda health status din ki" Heedayah tace "Toh bayan kin sa na kira wnn Shureen din yace baxan je ba din kuma xai xo ya gaya ma Mami kar a bar ni in je" Farida tace "Kai haba, da gaske??" Heedayah ta fashe da kuka tace "Wllh" Farida ta wani tabe baki tace "Toh ba sai ya hana ba mu gani, duk kece kika dage a kirasa xaki laka min kuma daga karshe, gwara ki tashi ki fara hada kayan kafin ma ya xo, Mami ta ma driver magana yace idan mun shirya mu fito" tashi Heedayah tayi tana share idonta ta dauko kayanta kala uku, Farida tayi kasa da murya tace "Make it Five, we are going to deceive Mami, sai ana gobe xa mu koma schl xata ganmu a gidan nan" Heedayah ta wara ido ta karo wasu kayan, Farida ta taya ta shirya kayan a jaka, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta daura dankwalin. Heedayah na gama shiryawa bayan ta fesa turare Farida tace "Ki tafi kice ma Mami thanks for allowing you, ni kuma xan kai mana kayanmu mota" Heedayah ta fita dakin ta shiga na Mami da sallama, Mami na xaune dakin tare da Junaid dake tsaye bakin mirror dinta ya rungume hannunsa, Heedayah ta kallesa tace "Ina kwana Yaya" yace "Lafiya lau" Heedayah ta karasa gun Mami tana murmushi tace "Mami thanks for letting me" Mami tace "Kwana uku kawai xa ku yi" Heedayah tace "Ehh Farida tace min haka" Mami tace "Kin sha drugs din ki? Kuma ki tafi da su kar ki manta" Heedayah tace "Toh" Mami tace "Ki kai cup din nan kitchen" Heedayah ta dau cup din da Mami ta sha tea ta fita, Mami tace "Kaga da ba don aiki ba da sai ka ajiye su, wani lkcn driver din nan na gudu sosai" Junaid dai bai ce komai ba, Heedayah na saukowa stairs aka bude kofar parlon, ido hudu suka yi da Shuraim, ta dauke kai da sauri ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon ta wani hade rai, wucewarta tayi kitchen ta tafi sink da cup din tana murguda baki, kamshin turarensa ta jiyo ta juya da sauri, ya karasa shigowa kitchen din yace "You have the guts ki wuce baki gaisheni ba koh" Ta marairaice tace "Allah sarki ya Shureen ba mun gaisa a waya ba, ai mun gaisa kuma Mami tace inyi sauri shi sa nayi sauri, amma idan na fito ai xan gaisheka dama, kayi hakuri don Allah" kallonta kawai yake yi, can ya juya ya fita, ta wani turo baki hade da murguda masa sannan ta bi bayansa, xaune ta samesa kan kujera, tayi kasa da kai tace "Ina kwana" yyi banxa da ita, wucesa tayi sai da ta isa stairs ta waigosa, hada ido suka yi, ta da'n xaro ido tace "Na gaisheka kuma baka amsa ba, Ina kwana" hade rai yyi yana kallonta tayi wucewarta sama da sauri, kin xuwa ta ce ma Mami yana parlor tayi, Ta shige dakinsu ta fara hawaye tace "Kinga har ya xo yace mata kar a je da ni ko" Farida ta xaro ido tace "Da gaske" Heedayah ta xauna gefen gado tana matsar kwalla tace "I hate him, ni na tsanesa" Zainab me aiki ce ta tafi ta gaya ma Mami tayi bako, Mami tace "Waye?" Zainab tace "Wannan sojan nan" Mami tace "Oh Shuraim, gani nan fitowa to" Zainab ta juya ta wuce, Mami na kallon junaid tace "I still don't like the way u and Shuraim are interacting.... Kamar wasu strangers" Junaid bai ce mata komai ba, tace "Toh ni ka wani xo ka tsaya min a daki kamar Soja idan nayi maka magana kayi shiru kamar kurma, do you have any problem?" Nan ma dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita dakin ta bi sa da ido, tabe baki tayi ta mike ta dau handbag dinta da wayarta ta sauka downstairs, tafiyar su Farida take son gani kafin ta wuce aiki dama, bayan sun gaisa da Shuraim tace "Daga gida kake ko gun aiki?" Yace "Daga asibiti nake" tace "Toh yau bari in kawo breakfast din da kaina kila kaci" Farida ce ta sakko da jakar Heedayah, Mami tace "Kuna ta 6ata min lkci" Farida tace "Mun gama" Daga haka tace "Ina kwana" tayi wucewarta, Shuraim yace "Lafiya" Mami tace "Wai Abuja xa su tafi gun third daughter na, suyi 3 days kafin resumption" yace "Ohk ita kadai?" Mami tace "Noo with Heedayah, ai duk da bata jin dadi ba damuwa taje ko?" Shuraim yace "Ki bar su su tafi, ai naga ta ji sauki" Mami tace "Aa da sauki sosai, Ina ga stress din bikin ne kasan bata saba da wahala haka ba, banda haka ana xaune lafiya me xai janyo tayi pass out haka nan" Shuraim bai ce komai ba, Mami tace "Driver nace ya ajiyesu, Junaid xai fita aiki yanxu da shi na so ya kai su" Shuraim ya kalli agogo da ke nuna tara da few minutes, ya d'an yi shiru kafin yace "Ohk should I drop them" Mami tace "Haba Noo, Kai da ka kwana asibiti kana aiki, bari a lallaba kawai driver din ya kai su" Shuraim yace "Xan kai su..." Da damuwa Mami tace "To aikin fa anjima, kaga xaka ba kanka wahala sosai" Yace "Aa ba wahala" Shiru Mami tayi tana kallonsa. Ko da Farida ta koma sama waya ta tadda Heedayah ke yi, Heedayah tayi shiru ganinta, daga daya bangaren Khaleel yace "Wa xai kai ku Abujan?" Heedayah tace "Uhm" shiru yyi kafin yace "Ohk, but you can leave where you are and talk to me" Farida ta dau handbags dinsu ta fita, Heedayah ta bi ta da kallon gefen ido, a hankali tace "Driver xai kai mu" yace "Yanxu xa ku fito?" Heedayah tace "Ehh mun ma kai kayanmu cikin mota" Yace "But can't you convince them that ku bari ko nan da xuwa 12 ku taso?" Da mamaki tace "Saboda me?" Ya mike daga xaunen da yake a katon parlonsu yace "Convince them plss Heedayah, hanyar nan bbu kyau ynxu" Tayi shiru sai kuma tace "How did you know that?" Yace "Stop questioning me, just kar ku fito yanxu" Ta hade rai tace "Bayan mun riga mun gama shiryawa kuma mun kai kaya mota, idan naje nace ma Mami hanya bbu kyau ai tambayata xata yi me ya faru da hanyar kuma wa ya gaya min, wa xan ce ya gaya min??" Shiru yyi yana sauraronta, ta turo baki tace "Ni dai ana jirana a parlor byeee" yace "Wait Heedayah...." Tsayawa yyi tana sauraronsa, yace "Don't you no that kidnappers suna hanyar Abuja" da mamaki tace "To ai ba kullum suke fitowa ba...." Yace "Noo yau xa su fito" ta xaro ido tace "Ta ya kayi ka sani?" Yace "Na sani, bana son wani abu ya sameki kuma" tace "To me ya sa xa su fito yau din?" Yace "Akwai wani da suke targeting, yau xai bi hanyar.... So if they should meet people on road suna harbi ta ko ina ne" Heedayah ta bude baki lkci daya jikinta ya hau rawa tace "Su harbe mu??" Yace "Aa bance xa su harbe ku ba, but prevention is better than cure right?" Tace "Toh kai ya aka yi kasan they are targeting someone when you are not a kidnapper?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Plan dinsu yyi leak ne" Bude kofar dakin aka yi Farida tace "Idan xa ki ajiye wayar nan ki ajiye ki fito mu wuce, ko wani karya yake tsara maki tun daxu haka" tsaki Farida tayi ta fita, Heedayah tace "Ni dai bye ana jirana" Daga haka ta katse wayar, sai dai banda faduwa bbu abinda gabanta yake tana naxarin maganan da yyi mata, then how did he know about kidnappers, ta bi dakin da kallo taga Farida ta sauka downstairs da handbag dinta balle ta saka wayar a ciki, wani karamin purse ta fito da ta saka wayar ciki snn ta dau mayafinta ta yafa, ta boye purse din a cikin mayafin ta fita dakin, corridor ta tadda Junaid a tsaye, ta sakar masa murmushi tace "Yaya xan yi missing dinka" a hankali yace "Are you sure" ta gyada masa kai, bude mata hannu yyi, ta bi corridor din da kallo kafin ta karasa ta basa light hug lkci daya kuma ta janye jikinta amma ta kasa kallonsa ta juya da sauri tace "Byee" har ta fara tafiya yace "Heedayah" tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa bayanta ya kamo hannunta ya sa mata kudi yace "In case you will want to buy chocolates" juyowa tayi tana murmushi tace "I appreciate, thank you so much" yace "You are welcome" daga haka ta sauka downstairs, Farida ta gani bakin kofa tsaye sai cika take, Mami kuma tayi forcing Shuraim yau dai yana shan just tea a gidanta, Heedayah na ganinsa ta daure fuska tace "Mami mun gama fa" Mami tace "Ku jira sa a compound" Heedayah ta karasa gun Farida suka fita compound din tare, Farida tace "Ke ki ji wai Shuraim ne xai kai mu Abujan" Still Heedayah tayi tana kallon Farida ko kiftawa babu, Can ta juya ta kalli motar Shuraim, sai kuma ta 6ata fuska ta fara matsar kwalla tace "What about the driver?" Farida tace "Oho Mami har tace ya wuce kawai" Heedayah tace "How are we going to cope travelling with him?" Farida ta sauke ajiyar xuciya bata ce komai ba, Heedayah tace "Did he even know the way to Abuja?" Nan ma dai