Showing 189001 words to 192000 words out of 275313 words
Chapter 64 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
yyi murmushi yace "Gaskiya ne" Kaka tace "Atoh" kallon Mumy kaka tayi ta nuna ma Alhaji Ahmad tace "Kaga uwar gidan Amadu can, ita ta haifi Shureen din da nake fada maku, mu dai kawai a bar kaza cikin gashinta....." Alhaji Ahmad ya kalli Mumy yace "Mun sameku lafiya Hajiya?" Mumy na kirkiran murmushi cike da karfin hali tace "Alhmdllh wllh, sannun ku da xuwa...." Yace "Mun gode, Allah ya saka maku da alkhairi ya duba gabanku da bayanku....." Kaka tace "Na dai ce a bar kaza cikin gashinta amma wllh tllh mu muka san abinda muka gani, amma kawai dai a bar kaza cikin gashinta, to matar da.... Bari kawai dai a bar kaza cikin gashinta" Mumy dai sai xufa take, Shi dai Abban Heedayah kansa na kasa, Ammin Heedayah ta d'an kalli Mumy sai kuma ta dauke kanta, kaka tace "Tunda mu dai muna sonta kuma ba mu cuceta ba ai shkkn tone tone ba kyau, amma dai Heedayah ta sha wahala wllh" shiru duk aka yi a parlon, kaka tace "Bari dai kawai shirun ya fi, amma tunda nake ban ta6a ganin mugunta a fili da bakin hali irin wanda na gani ba, to wnn bai wani dameni ba don wllh kanta tayi ma, ni baxan tona mata asiri in fadi irin tsana da kyara da tsangwamar da ta dinga yi ma Heedayah ba ta nuna ita baxata riketa ba, ta xo har gida ta dinga xugani kar in amsheta ince ma Amadu xan masa baki idan bai mayar da ita inda ya tsintota ba, to wllh baxan tona mata asiri ba, Allah kuma ya rufa min asiri yanda na rufa mata amma kaga warcan...." Ta fada tana nuna Mami, tace "Surutu ba shi da amfani, amma wllh tllh ta dalilin Deedaya ta amince ta auri Amadu don ta riketa ganin bata da gata, kasan abokiyar aikinsa ce dukaninsu lauyoyi ne, mijinta ya mutu ya bar masu uban dukiya ina jin da kyar idan bata fi Amadun ma kudi ba, amma ta yrda ta auresa duk sbda Deedaya tunda an ki riketa a gidan, baxan dai fadi warce ta ki riketa ba, in gaya maka Rakiya ta sadaukar ta auresa ta rike Deedayah fiye da ynda bafillatanar uwarta xata riketa, ko ku kunga wani alamar cutarwa tare da Deedayah da ku ka ganta??" Abban Heedayah ya girgixa kai yace "Ko daya" Kaka tace "Atoh, don haka idan ma duk shekara ka dinga kai Rakiya makka wllh baka biyata ba, duk da ni dai bance a kai ni ba tunda sbda Allah na yi ba sbda a kai ni Makka ba, Amadu kuma ynda xaka biyasa kawai ka bar masa Deedayah na har abada ya ci gaba da rikon abarsa, da ace yana da d'a namiji me hankali ne ma sai ka basa auren Deedayar, to babu, Allah bai basa ba, sae dai da ace ita Rakiya na da d'a namijin amma banda Junaid sae a hadasu kawai don ita ma ta bauta mata, amma dae baxae ma yiwu ba, Heedayah ba gantalalliya bace...." Heedayah dake ta kallon kaka ta dau lemo daya ta mike tayi wucewarta dakin kakan tana turo baki. Xaunawa tayi gefen gado ta bude drink din hannunta tana sha, sae kuma ta mike da sauri tana duba dakin ko xata ga wayar kaka, ta gansa ta nannadesa da handkerchief ta ajiye a kusa da pillow, dauka tayi ta duba ko akwai kati, ganin akwai tayi dialing number snn ta kai kunne, ba a dau lkci ba ya fara ring aka daga, sallama tayi, aka amsa calmly daga daya bangaren, tace "Ka shigo Kadunan ne?" Yace "Yea tun da rana, I've been waiting for ur call tun daxu" tace "Bamu dade da isowa ba, ya jikin?" Yace "Na ji sauki sosai, Alhmdllh" tace "To kana shan maganin?" Yace "Ai kin ce in sha, so I just have to take it" Tace "Toh Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen, where are you now?" tace "Muna gidan Yayan Abbana yanxu...." Yace "Ohk, how about Mami" Tace "Ita ma ta xo nan din" yace "A nan xa ku kwana?" Heedayah tace "Aa xa xan bi Mami mu koma can gida" shiru ya d'an yi, sai kuma yace "Can I come later?" Ita ma tayi shiru kafin tace "Just pretend as if u came to greet Mami" Yyi murmushi a hankali yace "Ohk, but...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yyi kasa da murya yace "Shkkn dai, I will come in sha Allah da daddare...." Bude kofar dakin ta ji anyi ta katse wayar da sauri ta xame daga kunnenta ta ajiye kan gadon ta jawo pillow ta rufe ba tare da ta kalli wanda ya shigo ba, satan kallon mirror din kaka tayi taga Shuraim bakin kofar, ya shigo ya rufe kofar dakin ya karaso ciki, ita dai ta ki juyowa, can kuma ta mike da xumar xata fita still wanting not to look at him, calmly yace "Don't move...." Tsayawa tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace "To me nayi" yana kallonta daga sama har kasa ya karasa har gabanta yace "Kina da grit din da xa ki tafi gidan saurayi kamarki ki kwana ki yini, and you are happy and comfortable bcos nobody is saying anything to you about that right? Everyone is just concentrated on ur reunion with ur parent, and ur stupid mind is letting you think you are right ko??" ita dai bata ce komai ba, Ya d'an daga murya yace "Now tell me, uban me kika je yi gidansa at the first place, and uban waye shi din, why did u follow him to his home, What were u busy doing for 24 hours in his home?" Ta fashe da kuka tace "Ni fa Ya Shureen ban sani ba, kuma ba gashi na dawo ba dai....." Ya dinga kallonta bbu ko kiftawa, ta marairaice tana kallonsa ita ma ganin ko kadan bbu wasa tattare da shi, yyi kasa da murya fuskarsa daure yace "Now tell me, meye tsakanin ki da shi, and a gidan uban wa kika san sa? Snn a ina kika kwana a gidan nasa" Turo baki tayi kafin tace komai ya Fixgota dab da shi ta 6ara baki xata yi ihu bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, and he gave her the first kiss of her life, a french kiss it was, everything happened in just a minute, lkci daya ya saketa ya fice daga dakin.... Ta kusa minti biyu tsaye bata ko motsi bayan fitarsa, a hankali ta kai hannu bakinta da ta ji yyi mata sanyi, sai kuma ta sulale kasa a hankali ta xauna gabanta na wani irin bugawa, ganin abun take kamar a mafarki, ta sake kai hannunta bakinta, lkci daya ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba ta mike da sauri ta fada kan gadon kaka ta rufe fuskarta da pillow tana kuka sosai.... Kiran sllhn Magrib ya sa kaka ta shigo dakinta baki har kunne, har sannan Heedayah na kwance saman gado tayi kukanta ta koshi tayi shiru, kaka ta washe baki tace "Sannu Deedayah, har kin tashi? Kina son wani abu ne?" Heedayah ta turo baki ta girgixa mata kai ta mike xaune tace "Suna parlon?" Kaka tace "Wani parlon, sai kace dai gantalallu, sun sallameni sun wuce amma ubanki yace xai dawo gobe da safe, bari in sa a kawo maki abinci idan abincin bai maki ba ma sai a samo maki abinda ranki ke so" Heedayah tace "Mami fa??" Kaka tace "Ai ta riga su tafiya, kinsan matar akwai kamun kai, in gaya maki gwamna ma yace bana da ita xa aje makka idan Allah ya yarda, ni dai nace masa A'a amma ya ki saurarata to bbu yanda na iya tare xa mu je da ita yace, anjima kuma xa a kawo min motata a adana min a garejin Amadu abinda na tambayi ubanki kenan farat daya ya bani" Kaka ta nuna mata dankwalelen Zinari na zobe tana washe baki tace "Matar gwamna kuma ta bani wnn, wai tana so na, yanxu gobe xan je in gaisheta da safe, sannan Babanki yace idan xa su koma Abuja in hada kayana tasss, to ni bana son in tsaya muna musu da shi ina matsayin babba shi yasa nayi shiru rai bbu dadi, Maryam kuma na can dakin uwar Sudais ta kasa wucewa gida ni da naga yanayinta ma na xata bori xata hau, wato ta girgixa ba kadan ba, Allah ubangiji ya rabata da hawan jini farat daya dai, ga shi bbu wanda ya bi ta kanta sai Rakiya da ni ake ta kulawa don ma ban tona mata asiri na fadi irin tsanar da ta maki ba, gwamna kuma yace xai ba Rakiya wani mukami na lauyanci ina jin a gwamnati, ni dai kawai nayi shiru ne amma ga dai Amadu me yasa xai ce sai Rakiya idan ba kyasa ta yyi ba, balle ma da aurenta a kai take gantali, don Amadu ai bai saketa ba, yanxu gobe xan lallaba Shureen in basa duk abinda yake so ya kai ni gwamnet house...." Sai da gaban Heedayah ya fadi da kaka ta ambato Shuraim, Kaka kamar xata yi kuka ta nemi waje ta xauna a hankali tace "Allah sarki Sudess baya nan wnn abun alkhairin ke faruwa, bai kamata a mance da shi ba don shine silar xamanki a gidan nan" Heedayah dai tayi shiru, can tace "Kaka ni fa gidan Mami xan wuce" Kaka tace "To ai ta tafi idan ba dai Shureen ya ajiye ki ba, yana can parlon Baffansa bari in je in samesa" Heedayah da hankalinta ya tashi da sauri tace "Aa kaka kar ki ce masa...." Kaka tace "Aa ba ruwana ya xa ayi a bari ki kwana a nan ba da son ranki ba, ba sai Allah ya kama mu ba idan ranki ya bace, bari inje nasan idan Baffan nasa yyi masa magana xai kai ki har parlon Rakiyar idan xai iya" Bata jira cewar Heedayah ba ta fice, Kai tsaye ta shiga bangaren Baffa, shi da shuraim kadai ne xaune parlon, kaka ta kalli Baffa da yyi shiru ganinta, snn ta kalli Shuraim da kansa ke kasa, tace "Me ya faru kuma?" Baffa ya sauke ajiyar xuciya bai dai ce komai ba, Kaka ta nemi waje ta xauna tace "Nace me ke faruwa, shi gashi ya xauna gabanka kamar me neman gafara, laifi yyi ma uban nasa ne?" Baffa yace "Aa, ko daya, muna tattauna wani batun ne daban" Kaka tace "Toh ni ba wannan ba, Heedayah ce tace xata tafi gidan Rakiya kuma kaga bbu me kai ta, gantalallen dreban ka dare nayi yake kama gabansa, don haka nace Shureen ya je ya ajiyeta kada mu shiga hakkinta, kaga dai tana da hankali bata ce xata bi iyayenta ba sai uwar rikonta, kaga kuwa ai ba butulu bace ita" Baffa yace "Toh xai ajiyeta idan xai wuce" Kaka ta mike tayi ficewarta daga parlon ranta fess, ga sabuwar mota, ga zinari, ga tafiya makka, gobe kuma xata gwamnet house, Baffa na kallon Shuraim da ya ki dago kansa yace....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you.
Have u ever wondered how desserts are made?
Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from?
Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because
Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught:
*Profit analysis
*Ways to handle desserts
*Dessert marketing.
This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos.
Registration is on and the fee is just N3000 Naira.
Class starts on 27th august,2021.
And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕
WhatsApp 08135358038
Call 📞 08135358038
IG: najaatu Yakudima
Baffa na kallon Shuraim da ya ki dago kansa yace "It's time for Magrib and you will be going for duty, idan anyi sllh ka ajiye Heedayah gida kawai, we will talk tomorrow in sha Allah..." Shuraim ya mike yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya nufi kofa Baffa ya bi sa da kallo har ya fita. Ana idar da Magrib Shuraim ya shigo gidan, ya karasa kofar dakin kaka ya bude yana kallon ciki, Heedayah na xaune saman darduma ta idar da sllh, Kaka na rike da tsintsiya tana tattare tattaren dakin ta juyo tana kallonsa tace "Ka ci abinci kuwa Shureen?" Yace "Na koshi" Tace "To har xaka wuce?" Yace "Ehh" tace "Atoh gaskiya ka jira ta ci abinci gashi nan na je na amso mata, sllh tayi yanxu" Shuraim yace "Xan yi wucewata..." Kaka tace "Toh ka tafi, ko ni ba sai in kai ta ba" Heedayah dai kanta na kasa ta ki dagowa, ba don Khaleel da yace mata xai xo anjima ba dama da bbu inda xata je gwara ta kwana a gidan kawai, but he said he is coming after Magrib tasan kilan ma yana can yanxu, Kaka tace "Kinga ki rabu da shi yyi wucewarsa ki dau abincinki ki ci, ko ni da Umaru ba sai mu kai ki gidan ba, wa xai ja ma aji a nan, ni ko ke?" Heedayah tayi kasa da murya tace "Ni a koshe nake na ci abinci" Kaka ta mike tace "A saboda me? Me kika ci, kar fa ki biye ma Shureen, ki ci abincinki ki koshi, idan kuma shayi xa ki sha sai ki hada" Heedayah tace "Na ci abinci kafin mu taho" Kaka ta juya tana kallon Shuraim kafin ya ce komai yace "Ina waje" daga haka ya juya yyi ficewarsa, Kaka tace "To ko in juye maki abincin a cooler ki tafi da shi?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa na koshi da gaske" Kaka tace "Toh shkkn, ni dai na fita hakkin ki, idan kun je ki gaida Rakiyar" Heedayah ta mike ta dau mayafinta da karamin jaka ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, duk gaba daya a sanyaye take, kaka tace "Ni ban ma fiye son kina bin Shureen din nan ba, shi ma ba sanin xuciyarsa muka yi ba har yau" Heedayah dai bata ce komai ba ta fita ta kullo mata kofarta, sama ta fara wucewa ta shiga dakinsu Zainab, ta samu Zainab xaune tana Azkar a saman darduma, Zainab tace "Har xa ku wuce?" Heedayah tace "Ehh xan wuce" ganin yanayinta Zainab tace "Are you fine?" Heedayah ta sakar mata murmushi a hankali tace "Sure" Kallonta kawai Zainab ke yi, Heedayah tace "Yaushe xa ki xo gidanmu, baki ta6a xuwa ba" Zainab tayi murmushi tace "idan Kaka xata je xan bi ta in sha Allah" Heedayah tace "Toh shkkn, bye, sai da safe" daga haka ta fita dakin ta wuce dakin Mum din Zainab tayi mata sallama ita ma sannan ta fita. Har Heedayah ta isa gate gabanta faduwa yake, ta tsaya bakin gate din tana leka waje, ido hudu suka yi da shi yana xaune mota amma bai rufe motar ba, ta dauke idonta da sauri ta koma gefen gate din ta la6e, ji tayi kamar ta juya kawai ta koma ciki, ta fi minti biyu a tsaye bata sake leka waje ba, Shuraim ya sauka motarsa ya tafi gun gate din, tana ganinsa ta fara kame kame ba tare da ta yadda sun hada ido ba, tana tatta6a jakarta tace "Ina gyara abu na ne" yace "Wuce mu je" Ba musu ta bi gefensa ta fita gate din ta wuce gun motar ya bi bayanta, ta bude front seat ta shiga, sai tsinne kai take kamar mara gaskiya, ya shiga maxaunin driver suka bar layin, har suka dau hanya Heedayah jujjuya zip din dake jikin jakarta kawai take, she is very uncomfortable with him, shi ma kuma bai kalli inda take ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin Shuraim yyi parking dai dai gate din gidan Mami, ta kai hannu xata bude motar taji a rufe, ta sauke idonta kasa bata dai ce komai ba, shi dai idonsa na gaban motar, gabanta sai faduwa yake gashi ta kasa kallonsa, da dane ce masa xata yi ya bude mata motar, sun fi minti biyar a haka, can taji ya bude lock din motar, da sauri ta bude motar ta sauka ta rufe ba tare da ta kallesa ba ta wuce ciki ya bi ta da kallo... Sai da ta shiga gida taji hawaye ya kawo idonta, ta tafi can parking space ta fashe da kuka, tayi mai isarta sannan ta goge bakinta da mayafinta tace "Allah ya isa" Kamar me counting step ta nufi main entrance ta bude kofar a hankali, ido hudu tayi da Khaleel dake xaune parlon tare da Mami, da mamaki Mami tace "Wa ya dawo da ke?" Heedayah ta karasa cikin parlon a hankali tace "Ya Shureen" Mami tace "Yana ina?" Heedayah tace "Kila ya wuce" Tana kallon Khaleel ta xauna kasa kusa da Mami tace "Ina yini" Kallonta yyi yace "Lafiya lau" Mami tace "Kin ci abinci?" Girgixa kai tayi, Mami tace "Toh ki tafi ki diba" tace "Mami Farida fa?" Mami tace "She is upstairs" Heedayah tace "Yaya fa?" Mami tace "Bai dawo ba" Mikewa tayi ta nufi kitchen, Khaleel ya bi ta da kallo, ta juyo suna hada ido ta sakar masa murmushi ta karasa cikin kitchen din, Mami na kallonsa tace "Ina jin ka Khaleel" Ya shafa kansa yana murmushi yace "A can aka haifeni na taso nayi karatu duk a can...." Mami tace "So ur parent are still there" Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya tace "Theye are late" Mami ta dinga kallonsa with pity