Showing 219001 words to 222000 words out of 275313 words
Chapter 74 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
kada sosai, lkci daya ya nufeta, sosai xuciyarta ya shiga bugawa ta fara matsawa daga wajen tana kallonsa a tsorace, har lkcn Heedayah bata daina ihun da take tana kwalo ma Junaid kira ya xo ya taimake su ba, Haka ma Farida dake sama tana nata ihun, Khaleel na isa gaban Mami ya duka with both kneels a kasa yana kallonta a sanyaye yace "Ki gafarceni Ummi, it wasn't intentional I was blackmailed, i was forced and threatened to do what I did, ba yin kai na bane wllh, ko da ina yin hakan baxan maki ba Ummi..." Hawaye ne ya kawo idonsa ya kasa kallon Mami, Mami dai sai kallonsa take har sannan gabanta bai daina bugawa ba, tace "Kana ma yi kenan?" Ya daga kansa yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ina yi" Xaro ido Mami tayi tana kallonsa, hawaye ya shiga kai komo a idonta tana girgixa kai tace "Kana nufin kai Kidnapper din ne dai??" Ya gyada mata kai trying hard not to allow the tears in his eyes to flow, a sanyaye Mami tace "Why did u choose such life for your self Khaleel" Hawayen da yake ta avoiding ya shiga sakko masa, Mami na hawayen ita ma tace "Ka gaya min me yasa ka xabi wnn rayuwar Khaleel, me ya shigar da kai wannan mummunar harkan?" Cikin rawar murya yace "I was raised such way Mami, a haka na taso, a cikinsu na taso, a cikinsu na rayu..." Mami tace "Iyayenka fa?" Sauke kansa yyi kasa hawaye na sakko masa sosai yace "I was never opportune to know them, ban ta6a saninsu ba, ban san iyayena ba" Ya daura fuskarsa a kafarta tana jin saukan hawayensa yana shessheka da kyar yace "Su ne iyayena, bani da kowa a duniya sai su Ummi, da su na gan ni," Dukawa Mami tayi ta xauna bakin stairs ta dago kansa with shock tace "How is that Khaleel?" Kasa bata amsa yyi hawaye na sauka idonsa xuciyarsa na masa xafi sosai, tace "Kayi min magana Khaleel" cike da karfin hali yace "Ban san me xance ba Ummi" Kuka sosai Mami take tace "Tell me more about you Khaleel" Ya share hawayen idonsa yace "Zayyad knows better, suna cikin manyan mu a lkcn don Zayyad is 45 now" Mami tace "Baka ta6a tambayarsa ko yasan wani abu a kanka ba" Khaleel ya girgixa mata kai wasu sabbin hawayen na xubowa idonsa.... Xuwa yanxu gaba daya sojojin dake layin na entrance din parlon Mami ana kokarin cire kofar, Gaba daya junaid ya shiga tashin hankalin da ya wuce misali, har snn kuma suna jin ihun Heedayah da Farida a ciki kamar xa su tsaga gidan, sbda rudewa ya ma mance da kofar kitchen dake ta baya duk da bai ma san Heedayah na kitchen din ba, lkci daya Shuraim ya xaga xuwa bayan gidan jin kamar ta nan Heedayah ke ihu, yana isa kofar ya bubbuga da karfi, Heedayah ta juya a mugun tsorace ta kara kwala wani sabon ihun tana cewa ta shiga uku, gaba daya ta mance da akwai kofa a kitchen din ita ma, yace "It's me ki bude kofar" da sauri ta karasa gun kofar ta bude hannunta na rawa, tana ganin Shuraim ta rikosa cikin kuka tace "Ya Shureen wllh Kidnapper ne shi, Mami tace min shine yayi kidnapping dinta amma kar in gaya ma kowa, wllh yana parlon ya kulle kofa....." Saketa Shuraim yyi ya nufi kofar kitchen din ya bude ya fita xuwa cikin parlon, sai a snn sojojin duk suka xagayo suka shigo gidan ta cikin kitchen din su ma, Mami ta mike da sauri daga bakin stairs da take xaune ganin Shuraim ya nufo su just as the soldier he is, tana kallon Khaleel a hankali tace "Don't ever admit you a Kidnapper, deny that" bata jira Khaleel yace komai ba ta nufi Shuraim kafin ya iso su tace "Listen Shuraim, magana muke yi da shi....." Kin sauraranta Shuraim yyi, ya bi ta gefenta ya isa gun Khaleel ya fincikosa ya kai masa wani wawan naushi biyu yana huci, Mami ta rikesa tace "Ban isa in maka magana bane Shuraim.... Are you alright ina magana baxa ka saurareni ba??" Turasa Shuraim yyi yana kallon sojojin da ke parlon yace "Seize him...." Sojojin suka nufesa, shi kuma ya fice daga parlon ta kitchen Mami ta bi sa da kallo, Heedayah na rakube jikin kofar kitchen ta waje har lkcn tana hawaye, tana ganinsa ta rikosa cikin rawar murya tace "Kun fita da shi ya Shureen?? Wllh Kidnapper ne, yana bindiga na ta6a gani..." wani kallo ya jefa mata yace "Waye ya kawosa gidan tun farko?? Ta dalilin wa ya samu fuskar fara shigowa gidan?" Hawaye na sauka idonta a hankali tace "Ni ce" wani kallo ya dinga yi mata, can ya fixgota har tana jin saukan numfashinsa a fuskarta yace "Da yaushe Mami ta gaya maki shi Kidnapper ne?" Kasa cewa komai tayi, ya hade rai yace "Baxa ki bani amsa ba" Da kyar tace "To... to ka sakeni" saketa yyi ta koma baya taki hada ido da shi, yace "Answer my question now" Tace "Daxu ta gaya min" Juyawa yyi xai bar wajen ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace "Yaya Shureen is he still inside plss" Bai ce mata komai ba ta ci gaba da bin sa, ta kofar main parlor sojojin suka fito da Khaleel, Duk yanda Mami tayi da su su sakesa basu saurareta ba don it's an instruction they are following, Junaid dai na tsaye balcony shi ma sai kallon Khaleel yake, A mugun fusace Mami ta nufi Shuraim tace "Baka da hankali dama Shuraim?? ban isa in gaya maka ka ji ba ashe??" Ba tare da ya kalleta ba yace "Mami wnn mutumin Kidnapper ne, kin sani, na sani, warce ta dalilinta ya fara shigowa gidan nan ta sani, So why are you covering up for him? beside you and people around you.... he is also very harmful to the society today, kin fi ni sanin wannan Mami, you are a lawyer, dole he have to be arrested ayi masa hukunci dai dai da abinda yake aikatawa, yanxu station xa a kai sa dole, I am sorry Mami, for your good, for our good, for the good of the society, babu xancen tausayi a case din nan, da xa a dinga bin tausayi da baxa ayi shari'a ba a duniyar gaba daya, he is guilty... kin boye shi yyi kidnapping dinki for a reason I never want to know, me yasa haka Mami??" Kallonsa kawai Mami take ko kiftawa babu gabanta na faduwa, can tace "Who told you that he is a Kidnapper?" yana kallonta a takaice yace "Heedayah, she said you told her everything today, he kidnaped you and requested the ransom of 30 million, which he was given...." Kallonsa kawai Mami ke ta yi, yyi kasa da kansa yace "I am sorry Mami, you can't cover him up anymore" yana fadin haka ya juya ya nufi gate, Junaid ya sakko balcony ya taho gun Mami yace "Mami this is just the right thing to do, babu xancen tausayi a lamarin nan, he deserves this, idan ba rashin kunya ba gidan da kayi garkuwa da mutane ka sake dawowa, me ya dawo yi har da rufe kofar parlor? is he even alright...." Hawaye ne ke sauka idon Mami ta ki ce masa komai ta wuce ciki da sauri, Heedayah da Farida na rakube waje daya a parlon ko wannensu na xare ido, har sannan a tsorace suke gaba daya, ko kallonsu Mami bata yi ba ta wuce sama xuwa dakinta, ta dau wayarta ta shiga dialing number Barrister, Abba na parlonsa tare da Mumy da gaba daya ta daina fahimtar bayanin da yake mata na cewar gobe xa su tafi kai ma Junaid gaisuwan Heedayah a kano, ganin yanda tayi still Abba yace "Are you there?" Da sauri ta dawo tunanin da ta tafi ta mike tsaye tace "Junaid kuma?" Abba yace "Eh Junaid" Mumy tace "Gobe goben nan?" Abba yace "In sha Allah" xufa ne ya shiga karyo mata duk da Ac dake aiki a dakin, Ita fa ko jiya ita da Sadiya da Salima sai da suka sake komawa gun Mutumin nan na Salima suka kara masa kudi ya kuma tabbatar masu Shuraim sai ya auri Heedayah, kuma sai ynda tayi da Heedayah, xa kuma ta dinga mingling da manya manyan matan kasar suna fita kasashe tare, xa tayi suna sosai a kasar, Wani murmushi tayi ta girgixa kai sanin xuwa kai gaisuwar ba ma abinda xai yiwu bane, sae dai idan ba uban kudinta ta kai jiya ba, Abba ya jawo wayarsa dake ring, da yake tana gefensa ta saci kallon screen din wayar taga an sa Barr Rahinah, Abba ya daga kiran ya kai kunne tare da sallama, Mami tace "I need this favor from you pls Barrister..." Abba dake sauraronta jin yanayinta yace "Are you okay Rahinah?" Tace "Ka kira Shuraim yanxu don Allah ka dakatar da shi abinda yake shirin yi, do that now plss Barrister" da mamaki Abba yace "Me yake shirin yi" Mami ta sakar masa kuka tace "Do that before it's too late Barrister, ka dakatar da shi, ni ya ki saurarata...." Abba yyi confuse da xancen Mami sosai, bayan Mami ta katse wayar yayi dialing number Shuraim yana fara ring Shuraim ya daga, Abba yace "Where are you? And what is happening Shuraim?" Shuraim yace "Bana kusa Abba, is there any problem?" Abba yace "Ohk, ko me kake yi I am instructing you to hold on to it, and come back home now" Shuraim yace "No Abba, it's something important yanxu haka mun kusa station..." Abba yace "Station? Me ke faruwa?" Shuraim yace "Kidnapper din da yyi kidnapping Mami ne ya dawo gidan yau, anyi nasaran kamasa yanxu haka muna hanyar police station" Mikewa Abba yyi yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ina Rahinar da yaran suke yanxu?" Shuraim yace "They are safe home, but Mami na nuna a kyalesa but I didn't listen to her being that it will be the greatest mistake to make..." Abba ya kasa cewa komai, a ransa kuwa tunani yake is Rahinah even okay? can yace "You don't worry, Kar ka biyeta ku yi tafiyar ku gani nan xuwa nima yanxu" daga haka Abba ya katse wayar, ya dau makullin motarsa Mumy ta bi bayansa da sauri tana cewa "Me ke faruwa barrister?" Yace "Idan na dawo xan maki bayani, I have to leave now" Abba na shiga motarsa ya bar gidan ya dau hanyar station din da Shuraim ya sanar masa xa su je, a hanya ya kira Baffan Junaid ya sanar masa abinda ke faruwa da Dakta.... Khaleel na xaune an sa masa handcuffs both legs and hands a inda xa ayi interrogating dinsa cikin Police station din... Bin Shuraim kawai Khaleel ke yi da ido har Mami ta iso tare da Heedayah kamar yanda aka yi instructing Yan sanda biyu su tafi su taho da su station din, Dpo na kallon Mami bayan duk sun xauna ya nuna mata Khaleel yace "Kin san wancan Mutumin Hajiya?" Mami ta kalli Khaleel da ya sauke idonsa kasa tace "Na san sa" Dpo ya kalli Heedayah yace "Ke fa young lady?" Heedayah ta gyada kanta a hankali, Dpo na kallon Mami yace "Yana cikin Kidnappers din da suka dauke ki few days ago ko?" Mami ta girgixa kai tace "Aa baya cikinsu, bai kuma san komai kan xancen ba ma" Abba ya kalli Shuraim ya girgixa kai kawai, Shuraim dai sai kallon Mami yake da mamaki ko kiftawa bbu, Dpo ya kalli Heedayah yace "Ke kin tabbata dai wnn mutumin Kidnapper ne ko?" Heedayah ta daga kai tana kallon Khaleel da ya kafeta da idonsa, sauke idonta tayi da sauri ta kalli Shuraim dake kallonta shi ma, can ta girgixa kai tace "Ni dai ina xaton Kidnapper ne shi, ban san ko haka ne ko ba haka bane" Dpo yace "Xato? To me yasa har kika yi xaton haka?" Ta sauke kanta kasa tace "Because he is huge, and...." Murmushi Dpo din yyi ya nuna mata Shuraim yace "Isn't he Huge?" Ta kalli Shuraim sannan ta sunkuyar da kanta, Dpo yace "And what?" Tayi kasa da murya tace "And naga ya kwana biyu bai xo gidanmu ba kuma sai aka yi kidnapping Mamin mu, sai yau ya dawo" Juyawa Shuraim yyi ya fice daga wajen kamar xai tashi sama, Junaid ya bi bayansa, Abba dai ya ma rasa abun tofawa mamaki duk ya ishesa, Dpo na kallon Khaleel yace "Kai me xaka ce game da xargin da ake maka na xama Kidnapper?" Khaleel ya kalli Mami dake kallonsa, ya girgixa kai yace "Xargin da suka min ba laifi bane don na kwana biyu bana garin at the time da abun ya faru, Ina jin kuma a ranan da na bar garin lamarin ya faru" Dpo yace "Ina ka tafi?" Khaleel yace "Naje wani aiki ne a kudu" Dpo yace "Wani aiki kenan" Khaleel ya nuna masa ID card dinsa dake ajiye da counter dinsa a gefe daya abinda kadai aka gani a aljihunsa knn, Dpo ya dau ID card din yana dubawa, can ya gyada kai cikin gamsuwa yana kallon Khaleel.... daga karshe dai Khaleel have to be released bbu wani proof yana da laifi tunda daga Mami har Heedayah sun yi shunning laifin da ake xarginsa da. Bayan sun fita daga station din wanda tuni Junaid da Shuraim suka yi wucewarsu, Mami na kallon Abba da Baffansu Junaid a hankali tace "I am sorry...." Abba dai bai ce mata komai ba, ya nufi motarsa haka ma Baffan Junaid, Mami ta jira har Khaleel ya karaso amma ya kasa kallonta, tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Ku taho tare da Zayyad gobe, I want to know everything about you, amma bani kadai xan saurari labarin ka ba Khaleel, har Barrister da kuma duk wani wanda ke tare da ni, nayi alkawarin in har baka da wani laifi xa mu rufa maka asiri xa mu taimake ka Khaleel, and it's not too late to still search for ur parent...."
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
*Mai tantama akan sabulai na gyaran jiki cewa basa Aiki toh ya cire _mg's_ domin kankat ne insha Allah, amare da uwargidaye harda ma yanmata ba cika baki ba ku gwada wnn sabulu ku bada labari, wa yanda basa san using cream sabulun mg's herbal whitening black soap ya wadace muku, jikinku zaiyi kyau yyi kamshi da glowing, and don't forget ba na bleaching bane organic products ne* 🤗
*Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai, akwai me saka haske bana bleaching ba, zai fiddo miki da ainihin color dinki yagoge dukkan dattin jiki, akwai wanda zai yi maintaining skin dinki yasaki fresh*
*Soap price 3k, Location.. kaduna, buh muna turawa ko Ina Amma delivery is not free*
Maiso kindly message... 08062991549
Call... 08064532391
_Note: Bai riga da ya shiga kasuwa ba tukun.._
*Mg's bakery*
You can still order ur birthday cake, cupcake,slice cake,meat pie,shawarma,samosa nd spring rolls for ur event @mg's bakery
Kindly call or chat
07046881166
07067210195
08062991549
Masu bukatar abayas,takalma da jakunkuna,ashobe,laces d atamfofi, materials nd the rest
07046881166
👏🤝
Mumy ce xaune dakinta tana ma Shuraim wani kallon tace "Kai me yasa baka da mutunci ne Aliyu?" Da mamaki yace "But Mum how do u expect me to know what happened bayan nace maki ni bana wajen, ni ban san me ya faru ba, ki tambayi Abba" Wani kallo ta dinga yi masa, Bayan few minutes jin ta ki cewa komai yace "Kiran kenan Mumy?" Ta jefa masa wani kallo ta nuna masa kujera tace "Xauna mu yi magana" Ba musu ya tafi ya xauna saman kujeran, tana kallonsa tayi kasa da murya tace "Aliyu ka gaya min tsakanin ka da Allah, ni dai nice na haifeka ba wani ba...." Shi dai Shuraim kallonta kawai yake, tace "Tell me, do you have any feeling for Heedayah?" Kallonta ya dinga yi da surprise, can yace "Wacece haka?" Tace "Auuu Heedayar ce baka sani ba?" Yace "Heedayah??" Ta hade girar sama da ta kasa, can yace "Ohh, Wai Heedayah guda dai da na sani? Feeling na me kenan?" Ganin sai hararansa take ya d'an yi murmushi yace "Idan ina da feeling for her xaki yrda wani tarayya ya hadani da ita ne?" Tace "Why not? Ba ubanka bane yyi wahala da ita da rainonta? Ina ce a gidan nan ta taso? kuma ae nasan irin rainon da aka yi mata ba wanda xai cutar da kai ko ni bane ko da wata alaka ta shiga tsakaninku" Shuraim yace "I don't have the feeling you are thinking Mum, ba gobe naji Abba yace xa a kai kudinta ba, Allah ya sanya alkhairi" Kasa ce masa komai tayi, but she look shocked, ya mike yace "Allah ya tashe mu lfya" Daga haka ya nufi kofa as if babu abinda ya damesa a lkcn, sai bayan da ya fita dakin nata ya kulle kofa ya ji kamar an axa masa abu me nauyi saman kirjinsa, xaunawa yyi a hankali saman kujeran parlonta na few minutes, kafin ya mike da kyar ya fice daga parlon gaba daya ya koma dakinsa. Washegari da safe Shuraim na kwance jin wayarsa dake vibrating a gefensa ya bude ido a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, Number Mami ya gani, ya kalli wayar for few seconds snn ya daga ya kai kunne, Mami tace "How are you doing?" Ya cire duvet din jikinsa ya mike xaune yace "Good morning" Tace "Morning ya gida?" Yace "Alhmdllh" tace "Idan ba damuwa ina expecting din ka nan da anjima Shuraim" ya d'an yi shiru har sai da tace "Are you there?" Yace "Alright, Amma yau xan koma Lagos ne" Tace "Ka xo din dai kafin ka tafi" Yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, ya ji kamar kar ya tafi gidan ya koma yyi kwanciyarsa still claiming he is fine duk