Showing 264001 words to 267000 words out of 275313 words
Chapter 89 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
d'an yi yace "And whats making you afraid because u are getting married?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Nima dai nan sani ba" Yyi kasa da murya yace "In dai kina sona you need not to be afraid, I am not a beast, or am I?" Ta sauke idonta kamar yana ganinta bata ce komai ba, yace "Talk to me" A hankali tace "Baxa ka dinga bani tsoro ba?" Sauraronta yake da mamaki, can yace "Wani irin tsoro?" Tace "Nima ban sani ba" Ya d'an yi murmushi yace "Baxan baki tsoro ba wife" Sun dade sosai suna magana da Khaleel har kusan la'asar, a dai dai lkcn kuma frnds din Mami da sisters dinta da su Hajiya Zuwaira da step mum din Sudais suka iso daga Kaduna da Boxes set shidda cike da kaya.....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
A hankali Heedayah ke saukowa stairs xuwa sitting room dinsu, Hijab ne har kasa jikinta ta karaso cikin parlon da ya cika da sanyin Ac, kamshin turaren da ya gauraye ko wani angle din parlon ne ya sa ya daga kai suka hada ido da ita, ya sauke idonsa, ta xauna saman kujera tana kallonsa cikin sanyin muryarta tace "Good evening" ya d'an kalleta yace "Evening, how are you??" tace "Alhmdllh" Ya cire face cap din camouflage dake kansa yace "Ya preparation?" Tace "Alhmdllh" Ya gyada kai bai ce komai ba, tace "Ya karin hakuri?" Yace "Mun gode Allah" Shiru ne ya biyo baya, ta mike xata tafi kitchen yace "Noo don't bring anything, I am okay... Sit let's talk" Ba musu ta dawo ta xauna tana kallonsa, Banda glowing da kamshi bbu abinda take, haskenta ya karu sosai ta dawo kamar balarabiya, Yana kallonta yace "Just came to wish you a happy married life in advance, after that sai ki fadi ko da wani abu da kike bukata? baxan samu daurin auren ki ba coz I will be leaving for Lagos today in sha Allah, daga can kuma xan wuce UK for few weeks...." Da damuwa tace "Me xaka je yi UK ya Shureen?" Yace "Course" A hankali tace "Allah ya kai ka lafiya" yace "Ameen, tell me what u want Heedayah" Ta sauke idonta kasa tace "Bana bukatar komai kawai addu'ar ka" Yace "Alright in sha Allah" Bata kuma cewa komai ba ya kalli agogo dake nuna karfe biyar da some minutes yace "I will be leaving now, my flight is 8:00pm" A hankali tace "But ina son inyi maka tambaya ya Shureen" Yana kallonta yace "I'm all ears" Cikin sanyin murya tace "You are actually nice, why don't u feel free with everyone a daina misperceiving din ka?" Murmushi yyi yace "What are u insinuating?" Tace "Nasan ka fahimce ni" Yace "It's nature Heedayah, let me give you this short story...." Shiru tayi tana sauraronsa, yace "Few years back lkcn ina aiki a hospital din Baffana, akwai wata nurse Auxiliary nurse by name Hameedah a hospital din, she is was 19 then, just as pretty as you, I had feelings for her because of her personality most especially her being religious and calm, but because of my so called nature I couldn't approach her, I don't know why I act that way also... I made so many attempt but failed approaching her, kowa a asibitin yasan abinda ya kai ni kawai nake yi in bar wajen, har ita magana bai ta6a hadamu ba sai na aiki shima briefly, ana sauran 2 weeks ta bar clinic din I couldn't hold it any longer, nan na yi iya kokarin fara mata magana coz I was dying in silent with her love, kamar dai yanda kika ga na fara maki magana months back..." Heedayah ta daga kai tana kallonsa, Murmushi ya sakar mata ya ci gaba da abinda yake cewa "A nan kuma nake tambayar Hameedah when will she get married tace min yau sati daya kenan da aka sa mata rana abinda ya sa kenan xata bar asibitin, from what I noticed bata son wanda xa a aura mata coz she was in tears, and that was how I loose Hameedah har ta tafi kuma bata ta6a sanin I have feelings for her ba, a lkcn you were just 14 a gidanmu...." Shiru Shuraim yyi yana kallonta, Heedayah tace "You said kamar yanda ka fara min magana months back, do you have any intentions that made u start talking to me ne dama?" Kallonta kawai Shuraim yake ko kiftawa bbu, ta sunkuyar da kanta sbda haka, jin bai ce komai ba, a hankali ta dago tace "Ohk I am sorry for the question" Ya girgixa mata kai yace "You need not to be, yes Heedayah, I had intention... feeling free with you by all means..." Tace "What's ur intention?" Ya jinginar da kansa a hankali jikin kujeran murya can kasa yace "I just repeated my first mistake, I've made two same mistakes" Heedayah na kallonsa ta girgixa kai tace "Ban fahimta ba" Shiru yyi yana kallonta, tace "Ka fahimtar da ni" Yyi murmushin karfin hali kafin yyi magana aka kwankwasa kofar shigowa parlon, a tare suka kalli kofar, Farida ce ta shigo parlon da sallama, gaida Shuraim tayi bayan tayi masa kallo daya ya amsa with smile, ta kalli Heedayah tace "Aunty na ta nemanki Heedayah" Heedayah tace "Toh gani nan xuwa" Juyawa Farida tayi ta bar parlon, Shuraim ya dau face cap dinsa ya saka snn ya mike yace "I've kept you here for so long, ki shiga ciki...." Mikewa tayi tana kallonsa, Bai yarda ya kalleta ba yace "As I have said earlier, I wish you a happy married life in advance Lil sis, Allah ya baku xaman lafiya da xuri'a dayyaba" Bata ce masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta juya ta bar parlon tana tafiya a hankali ta koma bangaren Stepmum dinta ta hanyar da baxata hadu da mutane ba don gidan cike yake da mutane. Daki ta tadda Mom Islam tsaye alamar ita take jira, Mom Islam ta hade rai ganinta, cike da fada tace "Wai kina da hankali ma kuwa Heedayah, what's wrong with you, Gobe daurin auren ki xaki tafi ki xauna da wani for the past 30mins yanxu, da ban aika ki taho ba dama baki da niyyar tahowa kenan?? Me ke damun ki haka kamar mara ilimi?" Sunkuyar da kai Heedayah tayi bata ce komai ba, Mom Islam tace "Toh daga ynxu har xuwa gobe da xa a kai ki dakin ki baxa ki sake fita gun wani ba, shi Shuraim din kuma sai ya sa maki ido kamar bai san abinda ya kamata ba, me da me ma yake ce maki har na minti talatin din?" A hankali Heedayah tace "Aa kawai nasiha yake min Aunty, that's all" Mom Islam tace "Toh Allah ya sa kin dauka, ga farfesu can an kawo maki ki dauka ki cinye tass kafin in dawo, ga wani ruwan wankan na yamma can na hada maki" Daga haka mom Islam ta fita daga dakin ta kulle kofar. Heedayah ta cire Hijab dinta ta linke ta ajiye a hankali ta nufi gun da bowl din ke ajiye ta xauna saman carpet me laushi ta bude tana kallon naman kazar dake ta kamshi da tiriri, da kyar ta iya cin yanka biyu a ciki ta rufe tana ta6e baki, wayarta dake gaban mirror din Stepmum dinta ne taji ya fara ring ta mike ta isa gaban mirror din tana kallon sunan gaban screen din, sosai jikinta yyi sanyi don tun daxu yake ta kiranta, ta dauka ta koma gefen gadon ta xauna ta daga ta kai kunne, amsa sallamansa tayi cikin sanyin murya tace "Good evening" Yace "Evening dear, ina kika shiga?" Tace "Kitso aka min, I just came in ynxu naga kiran, kayi hakuri" Yyi kasa da murya yace "But bana son kitso fa dear" Ta buda ido sosai tace "Uhn da gaske?" Yace "Yeah..." D'an murmushi tayi tace "To in kwance kenan?" Yace "Aa wahala xa ki sha, ki bari gobe sai in kwance maki da daddare" Tace "Uhn, Aa Farida da su Rabi'ah xa su taya ni kwancewa anjima" yace "No leave it, I will loose it my self all alone" a hankali tace "Toh shkkn" yace "Hope kin ci abinci dai yau?" Tace "Ehh na ci daxu" yace "Alright, Farida tace min kina tunani da yawa, tunanin me kike?" Wara ido tayi tace "That's not true" yyi murmushi a hankali yace "Now tell me, how do you want our married life to be Heedayah, duk yanda kike so haka xa ayi" Shiru tayi jin abinda yace, cikin cool voice dinsa yace "Kin yi shiru dear" Ta sauke idonta kamar yana ganinta murya can kasa tace "I just want you to be caring and understanding..." sai kuma tayi shiru, yace "You list them, abinda kike so da wanda baki so a gidan aurenmu duk ki gaya min yanxu" a hankali tace "Ina son kayi hakuri da flaws dina ko wani iri ne, I want you to be considerate toward me, idan nayi maka laifi ka dinga considering dina...." Hawaye ne ya kawo idonta tayi shiru, yace "Ina jin ki...." Ta share idonta tace "Ka tayani son abinda nake so, ka ki abinda nake ki ko meye shi" yace "Like?" Tace "Da akwai abubuwa da yawa da bana so ai...." Yyi murmushi yace "To naji.... Baki tambayeni kids nawa nake so ba" ta turo baki, kamar ya ga abinda tayi, yyi murmushi yace "Ohk just two are okay" Xaro ido tayi tace "Two kuma?" Yace "Yes, if they are to be boys in sha Allah... Ahmad and Usman" Shiru tayi, yace "Isn't it?" Tace "Uhm to har da Aliyu, ni ina son sunan" yace "Really?" Tace "Ehh" murmushi yyi yace "Toh shkkn, sai ki haifi uku duk da biyu kawai nake so dai" murmushin ita ma tayi bata ce komai ba, murya can kasa yace "I love you Heedayah" Ta sauke idonta kasa cikin sanyin murya tace "I love you more" Shiru yayi yana jin kalman nata har ransa, a hankali tace "Kilan me yi min turare na jirana yanxu...." Yace "Turaren me" tace "Nothing" yyi murmushi yace "Ohk xan kira ki after Isha" Tace "Okay bye" katse wayar tayi ta mike ta sa Hijab dinta tana kallon bowl din naman da stepmum dinta ta bata, da xata samu inda xata xubar, xubarwa kawai xata yi don baxata iya ci ba, fita tayi dakin ta tafi inda me yi mata gyaran jiki take, bak'i ne daga garurruka daban daban cike a ko wani bangare na gidan jikin Heedayah yyi sanyi sanin they are all here to witness her wedding fatiha tomorrow Friday idan Allah ya amince. Heedayah na wani bangare daban na gidan wajajen karfe tara da su Farida da Rabi'ah, sun kusa su sha biyar a babban dakin, ita dai su Rabi'ah da Farida kadai ta sani sai sisters din Sudais, sauran duk 'ya yan abokan Abbanta ne da Amminta, Heedayah na kallon Farida dake kwance tace "Farida pls can you call ya Shureen with ur phone, he said he is leaving for Lagos, kiji ko ya isa lafiya" Farida tace "Oh Lagos ya wuce, baxai samu daurin aure ba kenan gobe?" Heedayah tace "Ehh, ki kirasa kiji ko ya tafi" Farida tace "Ke ki kirasa mana" Heedayah tace "Toh ai bai kamata ni in kirasa ba" Dariya sosai Farida tayi tace "To ai kya bari a daura auren ko?? Yanxu bbu igiyar kowa a kanki balle kice bai kamata ba" Heedayah tace "Ko?" Farida tace "Yes, daga gobe ne idan Allah ya yrda" Heedayah ta jawo wayarta a hankali ta shiga duba lambar Shuraim, dialing tayi ya fara ring, yana fara ring ta mike ta shiga wani dakin daban, katsewa yyi ya kirata, ta daga ta kai kunne hade da sallama tace "Ya hanya?" Yace "Alhmdllh, we just landed" Tace "Ohk, Allah ya huce gajiya..." Yace "Ameen nagode" Tace "Sai da safe" Yace "Ohk but I forgot ban maki nasiha ba, duk da nasan an maki tun kafin goben, let me just add this...." Shiru Heedayah tayi tana sauraronsa, a hankali yace "Duk runtsi duk tsanani kada ki bari frnds su ja ra'ayinki a rayuwa, snn ki saka a ranki bbu me taimako sai Allah, I am not talking of today, tomorrow, next year or even 5 years to come, I am talking of for ever...." Heedayah dai tayi shiru, cikin sanyin murya Shuraim yace "For 33 years da nasan mahaifiyata bata yarda da kowa ba sai Allah, mahaifiyata macece me yawon ibada, Azkar din safe da yamma da karatun Qur'ani basu ta6a wuceta a rana, snn ita din me yawan sadaka ce, ko kaka tana yabonta ta wnn fannin, mu'amalar ta da mutane was very good, bata da abokin fada a iya sanina, but all of a sudden kawaye suka ja ra'ayinta a kan abinda bai kai ya kawo ba...." Kasa cigaba Shuraim yyi, lkci daya xuciyarsa yyi rauni, bayan few seconds yyi gathering courage yace "It's so sad bayan duk wannan abubuwan da na lissafo na halayenta ta rasu tana sabon ubangiji, ta rasu tana shirka all because of just a little girl wacce xata yi jika da, kinga dai Allah bbu ruwansa, sai kaga mutum na sabo farkonsa amma daga karshe kuma ya shiryesa, wani kuma xaka ga yyi ta abubuwan alkhairi amma rashin rabo xai sa ya 6ata ayyukansa a karshe, abinda ya faru da Mahaifiyata kenan, I am so sad about this, ina kuma yi mata fatan samun rahama wajen Allah, Ina fatan Allah ya dubi ayyukanta na baya ya gafarta mata..." Hawaye ya shiga sauka idon Heedayah, lkci daya jikinta yyi sanyi, cikin rawar murya tace "And all this happen because of me, da ban shigo rayuwarku ba ur mum will hold on to her strong faith, I caused everything..." Ta fashe da kuka sosai, Shuraim dake sauraronta ya lumshe ido a hankali yace "U caused nothing Heedayah, haka kaddarar ta yake, Allah ubangiji ya gafarta mata ya sa mu cika da Imani, Ina neman alfarman duk lkcn da kika yi sllh ki dinga sa ta a addu'ar ki, Allah ya yafe mata....." Heedayah ta gyada masa kai hawaye na ci gaba da sauka idonta cikin sanyin murya tace "In sha Allah" Yace "My point in here is that, duk tsanani duk runtsi kada ki bari kawaye su canxa ki, kada ki raunata imanin ki sbda su, you just keep it at the back of ur mind that komai yyi tsanani a rayuwa maganinsa Allah, ynxu da Mum ta hakura ta rike ki sbda maraicin ki duk da bata so, sai ki ga sbda haka sai Allah ya dubeta cikin lkci kalilan iyayenki xa su bayyana may be in just few months time, amma sbda nunawa da tayi xata ja da Allah shi yasa duk abubuwan nan suka faru, ba a kuma ga iyayenki ba sai bayan shekara biyar, snn ta dalilin ki aka yi mata kishiya" Heedayah ta kasa ce masa komai, yace "Abu na biyu kuma in life Heedayah, ki xama me taimako da rikon amana, ki xama me pure heart, I won't go deep into this, kawai xan baki misali daya xuwa biyu.... Taimakon Mami da rikon amana da tayi maki yasa tun a nan duniya ta ga reward dinta, coz d'an ta da aka dauke shekaru masu yawa har ta fidda rai da shi sai gashi har gida, kuma ta dalilin ke da ta rike din ta gano yaron nata, did you get me?? One never knows where his or her reward lies, don haka ki xamo me tausayi da taimako... Lastly ki xama me biyayya ga mijinki, That's all I have to say to you, Allah ya baku xaman lafiya...." Ta goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "There is something you wanted telling me daxu kafin Farida ta shigo, ka gaya min yanxu don Allah" Shiru ta ji yyi, bayan wani lkci yace "It's too late, telling you or not telling you will add nothing" Ta girgixa kai tace "Aa ka gaya min don Allah ya Shureen" Jin yyi shiru tace "Ka ji?" Kallon wayarta tayi da sauri jin alamar shigowan kira taga Khaleel ke kiranta, da sauri tace "Ya Shureen ana kirana, sae da safe" A hankali yace "Alright good night" daga haka ta katse kiran da sauri ta daga kiran Khaleel, sallama tayi masa ya amsa, tace "Ina yini?" Yace "Da wa kike waya?" Sosai gabanta ya fadi tace "Aa Mami na kira" yace "Wacce Mamin?" Rasa abinda xata ce masa tayi, da sauri tace "Auntyna ce" Yace "Ohk I see" Shiru tayi, yace "Har xa ki kwanta kenan?" Tace "Uhn" Yace "Ohk sai da safe" Jikinta yyi sanyi, a hankali tace "Amma kai kace xaka kirani mu yi magana after Isha" Yace "You've exhausted all the strength to talk to me, talking to someone, gobe da safe sai mu yi maganan, sai da safe" Kuka ta sakar masa, ya mike xaune daga kwancen da yake da sauri yace "Hasbunallah.... Look now kiyi hakuri ki daina kukan nan, sai ki gaya min gaskiyan da wanda kike waya idan kina son mu shirya" Cikin rawan murya tace "Ya Shureen ne, kuma wllh nasiha kawai yake min inyi maka biyayya" Shiru yyi kafin ya d'an yi murmushi yace "To Allah ya sa kin dauka" A hankali ta dinga goge idonta, murya can kasa yace "Haka xa a daura auren gobe a kawo min ke kiyi ta kuka ki hanani bacci ko?" Turo baki tayi bata ce komai ba, yyi murmushi yace "Baxan bari kiyi kuka mara dalili ba gobe"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Washegari har karfe tara Heedayah na kwance ta lullube har kanta da duvet, babu yanda Farida bata yi da ita ta tashi tayi wanka su yi breakfast ba amma ta ki, duk 'yan