Showing 267001 words to 270000 words out of 275313 words

Chapter 90 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

matan dakin sun yi wanka wasun su sun shirya, Mom Islam ce ta shigo dakin tana kallon saman gadon tace "Au har yanxu bata tashin ba?" Farida tace "Eh ta ki tashi" Karasawa bakin gadon Mom Islam tayi ta yaye Duvet din tana kallon Heedayah, da sauri ta rufe fuskarta da pillow, Mom Islam ta xauna gefenta xata dago ta taki yarda, Mom Islam ta hade rai tace "Meye haka kike yi" Heedayah dai bata ce komai ba kuma ta ki bari a ga fuskarta, Mom Islam ta janye pillon ta dago ta tana kallonta, sosai idanuwanta suka tashi sbda kuka, Kallonta Mom Islam ta tsaya yi da mamaki, Heedayah ta sakar mata kuka ta fada jikinta tana shessheka a hankali, murya can kasa mom Islam tace "What's wrong dear?" Kasa cewa komai Heedayah tayi hawaye masu xafi na sauka idonta, Mom Islam ta mike ta dagata, har sannan rigar bacci ne iya gwiwa a jikinta, Mom Islam na kallon Farida tace "Ina Hijab dinta?" Farida ta dauko Hijab din ta mika ma Mom Islam, ta sa mata sannan ta kama hannunta suka fita daga dakin, Farida ta bi su da kallo don har ranta take tausayin Heedayah, tana lura jiya da daddaren ma bata yi wani baccin kirki ba. Mom Islam ta rufe kofarta bayan sun shiga dakinta ta xaunar da Heedayah gefen gado tana kallonta tace "Now tell me what ur problem is Heedayah?" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Nima ban sani ba" Mom Islam ta hade rai tace "Baki sani ba kamar yaya?" Heedayah ta bude hannu hawaye na sauka idonta cikin sanyin murya tace "I am just being afraid...." Mom Islam tace "Afraid of what in particular?" Kasa cewa komai Heedayah tayi hawaye na sauka idonta sosai, Mum Islam ta xauna gefen gadon ta jawota jikinta tace "Ki kwantar da hankalin ki daughter, you need not to be afraid of anything" Heedayah ta gyada mata kai amma ta kasa cewa komai ta rufe idonta, Mom Islam ta saketa ta mike ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka ta fito tana kallonta tace "Tashi ki shiga kiyi wanka" Ba musu Heedayah ta mike a hankali ta cire Dogon Hijab din jikinta, snn ta cire rigan baccin ta amshi towel din da stepmum dinta ta kawo mata ta daura sannan ta shiga bandakin. Tana fitowa wanka Mom Islam ta tilasta mata ta sha shayin da ta hado mata, da Irish kadan, snn ta bata hijab ta saka ta kama hannunta xuwa dakin da warce xata yi mata shiri har a gama bikin take, matar kadai ce a babban dakin tare da me make up, sai wedding planner guda daya, babban akwati ne a gefenta me dauke da kayan Heedayah kusan kala sha biyar na fitan biki, Mai make up ma ga boxes din kayan make up dinta a gefe, Mom Islam ta sake hannun Heedayah tace "Ki je a shirya ki" Ita dai Heedayah bata ce komai ba ta tsaya tana kallon matan dakin, Mom Islam ta juya ta fita ta kulle kofar. Sai kusan karfe goma aka gama shirya Heedayah cikin wani dankareren tsadadden lace da ya haska ta sosai, kana ganinta ka ga amarya, lallenta me kyau ya haska hannuwanta da kafafuwanta, very light make up aka yi mata, tayi wani sanyayyen kyau kamshi sai tashi yake a dakin, hotuna kawai ake mata amma fuskarta bbu walwala, fashion stylist din dake kallonta tana murmushi tace "It's been long da naga amaryar da bata murmushi, smile plss angel, you look enamor, one experience this moment just once in lifetime...." Heedayah ta sauke idonta a hankali ta kirkiri murmushin karfin hali gabanta na faduwa, bude kofar dakin aka yi bayan anyi knocking Farida ta shigo rike da waya a hannunta, wara ido tayi tana kallonta ta karaso da sauri ta rungumeta tightly, a hankali tace "You look like a princess Didi, kinyi kyau sosai..." Lkci daya hawaye ya kawo idon Heedayah ta kasa cewa komai, Fashion stylist din dake kallonta tace "Kar ki bata fuskanki 'yan mata, today is ur happy day, an wuce wnn era din kuka ranan biki, chill and be happy plss, sai kace ba auren soyayya ba....." Heedayah tayi iya kokarin ganin hawayen bai sauka idonta ba... Wata frnd din Ammi ce ta shigo dakin don ganin ko an gama shirya Heedayah, ta kama hannunta suka fita xuwa inda Yakumbo da 'yan uwanta suke sai kaka da tayi kane kane cikinsu, ko wacce tayi shiga na kece raini, Yakumbo sai bada labarin yanda Aisha ta haifi Heedayah take kaka na kallonta tana kyabe baki, Dukawa Heedayah tayi har kasa kanta a sunkuye cikin mayafin da aka yafa mata cikin sanyin muryarta ta gaishesu, Yakumbo da kaka ne kadai basu amsa ba sai kallonta suke kai kace ranan suka ta6a ganinta, nan ko Khaleel ne kawai ya fado masu barin Yakumbo da tayi tsuru tsuru, tsofaffin parlon sai sa ma Heedayah albarka suke, Hajiya Fa'iza ta dagota suka bar parlon, Yakumbo tayi tagumi tace "Allah ga mu gare ka" gun manyan bakin gidan Hajiya Fa'iza ta kai Heedayah duk ta gaishesu snn ta mayar da ita bangaren Mom Islam, Kwanciya Heedayah tayi dakin, Mom Islam ta karaso kusa da ita ta mika mata wayar hannunta bayan tayi dialing number tace "Amshi xa ayi maki magana" A hankali Heedayah ta mike xauna tana kallonta, Mom Islam tace "Mamin ki ce, ki amsa" Heedayah ta sauke idonta ta amshi wayar ta kai kunne, muryar Mami ta ji, ta gaisheta cikin sanyin murya, Mami tace "How are you daughter" Cike da karfin hali Heedayah tace "I'm fine Mami, ya gida" Mami tace "Kuka kike Heedayah?" Girgixa mata kai Heedayah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Aa ba kuka nake ba, Mami baxa ki xo ba?" Murmushi Mami tayi tace "In xo ina?" Heedayah tayi shiru ta kasa cewa komai, Mami tace "kar ki damu ki kwantar da hankalin ki in sha Allah xan xo" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Da gaske Mami?" Mami tace "Ehh" Shiru Heedayah tayi, Mami tace "Hope kina cin abinci dai?" Heedayah ta gyada kai tace "Ina ci" Mami tace "Toh maa sha Allah, Allah ya maki albarka my daughter" A hankali Heedayah tace "Ameen" Mami tace "Sai na kira anjima" Da sauri Heedayah tace "Ba kince xa ki xo ba?" Mami tace "Ohh haka, sai na xo" Daga haka Mami tayi mata sallama ta katse wayar tana murmushi, Mom Islam ta karba tana kallon Heedayah tace "Tashi mu je ki gaida su Abbanki, sun shigo yanxu" Heedayah bata ce komai ba, Mom Islam ta dau mayafinta snn ta kama hannunta suka bar dakin, tafiya ce sosai suka yi har xuwa inda su Abba suke, Abbanta ne da Abban Shuraim, Baffan Junaid da Abban Sudais, all with few frnds, Heedayah kanta na lullube ta nufi gun Abban Shuraim da ta hango ta durkusa amma ta kasa cewa komai, lkci daya hawaye ya shiga sauka idonta, murmushi yyi ya kai hannunsa kanta yace "Allah yyi maki albarka daughter" Cikin sanyin murya Heedayah ta gaishesa sannan ta gaishe da su Abbanta, Abban Shuraim na kallonta yace "Tashi ki je, Allah yayi maki albarka" mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, ta tadda Mom Islam wani parlon tana jiranta, mom Islam ta kama hannunta suka koma bangarenta don can ne bbu mutane da yawa, Bedroom ta kai ta xauna gefen gado, Mom Islam tace "Kun yi magana da Khaleel din?" Girgixa kai Heedayah tayi, Mom Islam tace "Ina wayar ta ki?" Kwankwasa kofar dakin aka yi, mom Islam ta karasa ta bude, Farida ce tsaye ta mika ma Mom Islam wayar tace "Ana ta kiranta Aunty" Mom Islam tace "Ohk, kar kiyi nisa Farida you will stay with her here" Farida tace "Toh" daga haka ta koma parlon ta xauna, Mom Islam ta dawo ta mika ma Heedayah wayarta, amsa tayi tana dubawa, taga missed call biyu na Khaleel, sai text message, bata shiga message din ba tayi dialing number Khaleel first, yana fara ringing ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne, murya can kasa tayi masa sallama, shi ma murya can kasan ya amsa yace "Ya kike?" A hankali tace "Alhmdllh and you?" Bai amsa ba yace "Where did you drop the phone?" Tace "Yana wajensu Farida, Ina dakin Aunt dina, she just brought it now" yace "Ohk hope kin ci abinci?" Jin yanda yake maganan a hankali tace "Are you okay?" Yace "Hopefully...." Shiru tayi, kafin tace "What's wrong?" Yace "I'm fine dear, you don't worry... Ban ga kwalliyar ki na safe ba" tace "Ba a turo min hotunan ba tukun" yace "Ohk" tace "Me kake yi yanxu?" A hankali yace "Just lying down" Kallon agogo dake nuna karfe sha daya tayi tace "Lying down har karfe sha daya?" Yace "Yea ynxu xan tashi" tace "Ohk, have u eaten?" Yace "Sure" a hankali tace "Ko dai baka da lafiya ne?" Yace "Ciwon kai nake yi, but I will be fine in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen, will call you later, xan shirya ynxu ana jirana" tace "But ka sha magani?" Yace "Yes, na sha magunguna na" murya can kasa tace "Toh sai anjima, Allah ya sauwake" yace "Alright dear, Ameen ngd" daga haka ya katse wayar, ta tsura ma screen din ido kafin ta shiga inbox dinta na msgs, ta fi minti biyu tana kallon message din da aka yi mata almost an hour ago kafin ta sauke idonta ta ajiye wayar, kwankwasa kofar dakin farida tayi ta shigo, tana kallon Heedayah tace "Ki taso mu je ki canxa kaya in ji Aunty" Ba musu Heedayah ta mike ta dau wayarta suka fita tare da Farida xuwa dakin da aka yi mata kwalliya, wani lace din da ya fi na daxu ta saka aka kara gyara mata fuskarta, aka yi mata hotuna snn suka fito. Karfe sha biyu Heedayah ta sauko parlon baki tare da Farida da Zainab, Junaid ne parlon da Sudais sai frnds dinsu hudu ko wannensu ya sa gezna fari kal, ta karasa a sanyaye ta gaishesu gaba daya, Junaid dai kallonta kawai yake yana murmushi yace "Aunty Amarya kin sha kyau" Sunkuyar da kanta tayi ta kasa kallonsa, Sudais ma dake tsokanarta taki yarda ta kallesa, tana son tambayar Junaid ina Khaleel ganin baya parlon amma ta rasa ta yaya, Farida dake gefenta ta kalla ta matsa dab da ita tace "How about ya Khaleel" Farida ta xaro ido tayi dariya, Heedayah ta riko hannunta da sauri murya can kasa tace "Noo, I am just asking" Farida na murmushi tana kallon Junaid tace "Yaya what of Big bro?" Junaid yace "He is outside, bai shigo ba" Farida tace "Me yasa bai shigo ba" Junaid yace "He prefer staying out" Heedayah dai bata ce komai ba, Sudais na kallon Farida yace "Good afternoon kawar amarya" Xaro ido Farida tayi ta kallesa da sauri tace "Ohh yi hakuri, Ina yini, kun xo lafiya??" yyi murmushi yace "Alhmdllh, ya taro?" Farida na murmushi ita ma tace "Alhmdllh" gaida sauran frnds din nasu Farida tayi sannan ta ja Heedayah suka bar parlon da Zainab, sai da suka hau stairs Heedayah tayi kasa da murya tace "Farida Ina son in ga Ya Khaleel" Farida tace "Ohk, let me ask a ina yake" daga haka ta koma ta tambayi Junaid, Junaid yace "A compound muka bar sa, call him on phone" Farida tace "Ohk" juyawa tayi ta koma sama, a bangaren Mom Islam ta tadda su Heedayah tace "Ya junaid yace yana waje, ko xa ki je ki samesa?" Heedayah tace "Xan iya xuwa?" Farida tace "Toh amma idan aka gan ki fa? I think it's not proper" a hankali Heedayah tace "Baxan bi inda akwai mutane ba" Farida tace "Toh shkkn, amma kar ki dade" mikewa Heedayah tayi ta yafa babban mayafinta ta fita dakin, ta inda bbu wanda xai lura da ita ta bi har ta fito daga gidan tana ta dube duben inda xata ga Khaleel....





Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Karkashin wani bishiya Heedayah ta hangosa xaune kan kujera a wani bangare na compound din, tun xuwanta wajen ya ganta shi ma, ya sakar mata murmushi bayan sun hada ido, sauke idonta tayi ta nufesa walking slowly, mikewa yyi yana kallonta har ta iso inda yake, ya buda mata hannunsa, kasa karasawa tayi da farko, can ta bi wajen da kallo sannan ta karasa kusa da shi gabanta na faduwa ya rungumeta jikinsa, lumshe idonta tayi kamshinsa ya cikata, ya daura bakinsa a kanta murya can kasa yace "You look beautiful wife" Bata iya tace masa komai ba, suna tsaye har bayan minti daya sannan ta dago kanta tana kallonsa tace "How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdllh am fine, where you worried?" Gyada masa kai tayi tace "But ur body is warm" yyi murmushi yace "Not like in the morning, I don't take my drugs the way I am suppose to, but naje asibiti I'm feeling much better now" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sauwake" yace "Ameen, amma kin yi lunch ko?" Ta turo baki tace "Kai abinci dai ko da yaushe" Yace "Eh mana, ke baki ganki ba kamar a huraki ki fadi" Murmushi tayi tace "Tohm na ci" a hankali ta xame jikinta daga nasa, yana kallonta daga sama har kasa yace "Kinyi kyau sosai, you look like a princess" Murmushi tayi tace "Kai ma ai kayi kyau" Yace "Noo ban kai ki ba" kallon kyakkyawan fuskarsa tayi, ya kashe mata ido ta sunkuyar da kanta da sauri tana murmushi tace "Ina son in koma ciki ynxu kar a neme ni" yana kallonta yace "Alright dear, in an hour time mu ma xa mu tafi mosque in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Ya kamo hannunta yace "I pray this will be the best for I and you, I pray it's for lifetime...." a hankali ta xame hannunta tace "Ameen" daga haka ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo, a wani d'an corridor da ta bi ta fito ta tadda Farida na tsaye tana ta jiranta, Farida ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina ta tsoron kada Aunty ta xo tace kina ina, I don't know if it's proper da kika fita" Heedayah tace "But ai ban dade ba ko?" Farida na kallonta daga sama har kasa tace "Aa baki dade ba, turarensa ya sa maki?" Heedayah tace "Why do you ask?" Farida tace "Kamshin turaren naji kike yi" Heedayah tace "Aa ni bai sa min ba" Farida ta wara ido tace "Ko dai ko dai...." Heedayah ta turo baki ta bi ta gefenta ta bar wajen, Dariya Farida tayi tace "Mu je ki canxa kaya, Aunty tace you should keep changing after an hour" Heedayah bata ce mata komai ba ta ci gaba da tafiya Farida ta bi bayanta. Ana saukowa sallan juma'ah aka daura auren Aliyu Uthman da Fatima Ahmad a kan sadaki naira dubu dari biyu, daurin auren da ya samu halartar dumbin jama'ah daga garurruka daban daban har ma daga kasashen waje, kan kace me government house ya cika makil da bakin d'a suka xo taya murna da farin cikin wannan daurin aure.... Heedayah na xaune saman darduma tun bayan da ta idar da sllh, banda faduwa bbu abinda gabanta yake, ita kadai ce xaune dakin don Farida da su Zainab sun fita, ta kalli agogo dake nuna biyu saura, dai dai nan message ya shigo wayarta da ke ajiye gefen gado ta sa hannu a hankali ta dauko wayar tana dubawa, message din Khaleel ne ya shigo wayar, sosai ta ji gabanta ya fadi bata kai ga bude message din ba aka bude kofa dakin, Farida suka shigo tare da Zainab da su Rabi'ah, da gudu Farida ta tafi ta rungumeta sosai tace "I am wishing you a happy married life Didi, Welcome to our family once again as an in-law...." Kasa ce mata komai Heedayah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta ta janye jikinta daga na Farida ta fashe da kuka sosai, Wata kawar Yakumbo ce ta shigo dakin ta saki wani guda da karfi tana kallon Heedayah, mikewa Heedayah tayi ta shiga bandaki ta kulle ta durkusa kasa ta rushe da wani kuka kamar warce aka sanar ma mutuwa. Sai da Mom Islam tayi da gaske da ita ta bude bandakin da ta sa ma makulli bayan kusan minti talatin, tausayinta ya sa Mom Islam ta kasa yi mata fadan da tayi niyya, Banda kallonta bbu abinda take, don har idonta ya tashi, Mom Islam ta jawota jikinta cikin kwantar da murya tace "Haba Heedayah, Why are you behaving this way?" Kasa ce mata komai Heedayah tayi hawaye masu xafi na sauka idonta, Mom Islam ta kama hannunta suka fita daga dakin xuwa nata bangaren ta xaunar da ita tana kallonta tace "Ain't you happy?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "I am" Mom Islam tace "To ki daina kukan nan, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya da kwanciyar hankali ma har abada, kowa ma haka yaji yanda kike ji yanxu" Gyada mata kai kawai Heedayah tayi tana goge idonta, Mom Islam ta mika mata wayarta tace "Ana ta kiran ki" amsan wayar Heedayah tayi a hankali, Mom Islam ta mike ta fita dakin, Miss calls din Khaleel ta gani, ta fara shiga inbox dinta ganin msg hudu, na Sudais, Junaid, da Shuraim ne all wishing her a happy and peaceful married life, sai na Khaleel da ta bude a karshe tana duba content din nasa, lumshe ido tayi a xuciyarta ta amsa addu'o'insa da Ameen, daga haka ta ajiye wayar ta kwanta kan gadon stepmom dinta. Bayan la'asar Heedayah ta fito main parlorn su cikin wani ubansun gown da ya haskata sosai, da kyar Mom Islam ta lallabata ta fito din bayan an gama shiryata don yin hotuna, wajensu Abbanta aka fara kai ta suka yi hotuna, daga nan sister din Mom Islam ta dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login