Showing 204001 words to 207000 words out of 275313 words

Chapter 69 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

sanar masa, kece dai baxa a sanar ma ba sbda ba a san xuciyar ki ba" Mumy dake ta xufa daga xaune sai kallon Kaka take xuciyarta na bugawa sosai, Cike da karfin hali tace "Ita Heedayar na son shi ne???" Kaka tace "Ko bata son shi idan ita ba butulu bace ai baxata ki d'an Rakiya ba, Junaidu kuma ai mutum ne ga kyau ga kudi ga ladabi, snn abunsa bai rufe masa ido ba, halinsa sak na uwarsa Rakiya, ashe ma wai sun ta6a haduwa da uban Deedayah da dadewa sai da ya amshi lambar Junaidun ya gani a wayarsa yyi saving, to yanxu dai Shureen ne kadai bamu san kansa ba a xancen aure, amma tunda xan aurar da Sudais in aurar da Junaidu ai shkkn sai yyi ta xama a tuxurunsa shi" Mumy dai bata ma san abinda kaka ke cewa ba banda xafi bbu abinda take ji, gashi ta kasa xaune waje daya, Kaka tace "Toh yanxu xuwa xan yi can gidan in ji me ya same Shureen din duk da bashi da mutunci koko?" Mumy dai ta kasa cewa komai, gaba daya ta shiga wani mugun tashin hankali, Junaid ya auri Heedayah? Inaa this is impossible, Bata san lkcn da ta girgixa kai ba da karfi tace "Baxai yiwu ba wllh" Kaka ta saki baki tace "Meye baxai yiwu ba Maryam?" A firgice Mumy ta kalleta tace "Au, A'a ba komai, ba komai" Kaka ta dinga kallonta can ta mike ta tabe baki tana karasa rufe jakarta tace "Toh Allah ya kyauta, auren Junaidun da Deedayar ne baxai yiwu ba tunda ke kika halitto su ko, to ai kuwa sai dai bakin ciki ya kashe ki Maryam, Rakiya dai kina ji kina gani sai ta xama surukuwan gwamna in sha Allah, sadaukarwarta da jajircewarta baxai tashi a banxa ba, sai in har ta cuci Deedayah wanda Allah shaida bata cuceta ba a shekaru shidda da suka yi tare.... Abinda ma ta hakura ita ma Rakiyar xata koma gidan mijinta tunda Gwamna ya sa baki a lamarin har gwamnan Kaduna nan sai da yyi mata nasiha kuma ta hakura tace xata koma" Mumy ta mike gaba daya tashin hankali ne bayyane fuskarta ta nufi kofa kaka ta bi ta da kallo snn ta tabe baki ta ci gaba da abinda take tace "Aniyar ki ya bi ki gantalalliya" Gidan Hajiya Sadiya Mumy ta tafi, tun daga parlor Sadiya na xaune da yaranta Mumy ta rushe mata da matsanancin kuka, Sadiya ta mike da sauri ta ja ta suka wuce ciki da mamaki tace "Subhanallahi, lafiya Maryam me ya faru?" Cikin kuka sosai tace "Sadiya kinji wai da Junaid xa a hada Heedayah aure...." Sadiya ta gwalo ido tace "Waye kuma Junaid?" Mumy ta kara rushewa da kuka tace "D'an wajen Rahinah, shi wai xa a ba Heedayah" Sadiya ta bude baki tace "Ke a ina kika ji haka?" Mumy tace "Daga wajen kaka nake take gaya min yanxu, snn wai Rahinah xata dawo gidan Barrister, ni wnn ma bai wani dameni ba, wllh har raina ina jin idan Shuraim bai auri Heedayah ba xan iya mutuwa, takaici xai iya kasheni, kawai na tashi a tutar bbu kenan, shkkn a haka xan kare bbu riban komai, ga kishiya kuma xata dawo, snn Salima ta sa na kai uban kudi gun mutumi wai Shuraim xai ji sonta da sha'awar aurenta har ya kasa daurewa sai ya furta, to yau gashi shekara daya kenan bai ta6a xancenta ko makamancin xancenta ba balle har yace xai aureta, ni yaya xanyi da raina Sadiya?? Sadiya ta rasa abun cewa, can dai tace "Toh ke a ina kika ga kaka ta fasa maki wnn labarin, kakan da kowa ya santa da xuki tamalle...." Mumy tace "Wllh wnn ba xuki tamalle bane, cewa tayi ba a ma son kowa ya ji, kuma ita kanta Rahinar ma bata da labari sai kwanan nan xa a sanar mata tunda Heedayah ta gama secondary, tun jiya an rasa gane kan Shuraim ban san me ke damunsa ba, uban ma yyi yayi ya fada masa damuwarsa amma ya ki, tun asuban fari nake xaune parlor nake jiran fitowarsa ya tafi masallaci, wllh bai fito ba naje na kwankwasa kuma bai bude ba, shine na xo fada ma Baffansa halin da ake ciki tunda uban yyi watsi damu bai sake bi ta kansa ba, ban samu Baffa ba shine ya shiga gun kaka, a nan take gaya min wnn bakin labarin" Sadiya da tayi shiru tana sauraronta tace "Jiya tun yaushe kika lura Shuraim din na cikin damuwa?" Mumy tace "Tun bayan dawowar mu daga graduation da ya shiga daki bai sake fitowa ba" a hankali Sadiya tace "Dadina da ke rudewa baya sa ki fahimci komai wllh Maryam, daga dawowa graduation shkkn sai shiga damuwa, to wllh son Heedayah ce ya jefasa damuwar nan bbu tantama, ba ya ganta jiya ba har sun yi hoto, kinga dai bakiyi asaran kudin ki ba kenan kamar yanda kika ce" Lkci daya Mumy ta dakatar da kukan da take tana kallon Sadiya da idanuwanta kamar xa su yi magana, Sadiya tayi wani dariya tace "Alhmdllh, yanxu komawa gida xa kiyi cikin dubara kiyi masa xancen Heedayar sai ki ga reaction dinsa, lallabasa xa kiyi sosai" Mumy ta goge hawayenta da sauri tace "Toh bari in je, in sha Allahu son nata ne ma yasa shi damuwar" Ko minti daya bata kara a gidan ba ta fice ta koma gida, a waje tayi parking ta shige compound, Rabi'ah na xaune parlor tace "Shuraim ya fito?" Rabi'ah ta girgixa mata kai tace "Amma Abba na dakin nasa, ya sa na kai masa breakfast" Da sauri ta wuce dakin, Abba na tsaye kansa, shi kuma yana xaune gefen gado with cup of tea a hannunsa, kana ganin idonsa kasan bai yi bacci ba daren jiya, Abba ya kalli Mumy bai dai ce komai ba, da damuwa Mumy tace "Barrister ya gaya maka meye matsalar?" Abba yace "Ba sai ya gaya min ba, koma menene Allah ya yaye masa" Mumy ta hade rai, Abba na kallon Shuraim yace "Idan kayi breakfast din ka sameni dakina" daga haka ya fita dakin, Mumy ta bi sa da harara ta tafi ta kulle dakin ta sa makulli ta dawo ta ja stool ta xauna tana kallonsa da damuwa tace "Ka gaya min gaskiya Shuraim, jiya lafiyan Allah muka fita gidan nan da kai xuwa wajen graduation din Heedayah muna dawowa kuma shine har yanxu aka rasa abinda ya dame ka, tell me the truth son did you in anyway have feeling for Heedayah?" Shuraim ya daga kai yana kallonta, ta kwantar da murya tace "Kar ka ji komai ka gaya min I am ur mother, nasan tunanin ka idan kace kana son Heedayah kilan ka samu matsala ta wajena, to ba haka bane, in dai nice I won't stop you from loving Heedayah, you can go ahead and ask for her hand in marriage from her parent" Kallonta kawai Shuraim yake, dai dai nan aka buga kofar dakin, Mumy ta kalli kofar tace "Waye wnn" shiru ba ace komai ba, ta mike ta isa kofar ta bude, kaka ce tsaye tace "Xaki ce waye bayan kinje kin daddago ni Shureen ba a san me ke damunsa ba" Bata jira cewar Mumy ba ta shiga dakin tana kallon Shuraim tace "Auxubillahi, me ya same shi haka? Ko jifansa aka yi gun aikin" Mumy ta wani harareta, sai a snn ta fara da ta sanin xuwa wajenta ma ta sanar mata, to amma ai xuwanta yyi amfani tunda ta samu information da yawa, Kaka kamar xata yi kuka tace "Me ya sameka haka Shureen, me aka yi maka" Shi dai bai ce mata komai ba, ya ajiye cup din shayin ya mike ya wuce bathroom, kaka ta bi sa da kallo tace "Toh kinga tsiyar ana masa magana ya shige bandaki ko? Dubi fa yanda ya wani xabge kamar wanda yyi jinya, duk da a rame ya dawo mana daga legas din amma ai bai kai haka ba, asiri aka masa a can ne bamu sani ba, shi kuma Amadu tunda idan wani abu ya samesa ba shi yyi asara ba shi yasa ya ki bin ta kansa, to wllh idan abu ya samu Shureen sai ya samu kowa, duk cikin jikokina waye me sona banda shi..." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni sai in fasa xuwa Gwamnet house din, baxan tafi in bar jikana a haka ba ban san me ke damunsa ba, damuwa dake kisa lkci daya yanxu, idan abu ya samesa ai na shiga uku" Cire mayafinta tayi ta linke ta ajiye ta xauna gefen gadon ta ciro wayarta ta mika ma Mumy tace "Kira min Umaru, ni na ma fasa xuwa Gwamnet house din su yi tafiyarsu" Mumy ta ji sanyi sosai a ranta sanin in har Shuraim xai bude baki yace Heedayah yake so kenan ai sai inda karfin kaka ya kare, amma tsoronta yanxu bata ma san ko son Heedayar bane ke damunsa kawai ita dai lalube take cikin duhu tana fatan shi din ne, idan kuwa ba shi bane shkkn ta shiga uku. Heedayah sun fito tare da Mami da twin sisters dinta xa su shopping mall, Mami xata yi ma Ashnaah da Ashfa shopping kasancewar a ranan karfe sha daya xa su yi set off for kano, Yakumbo da Farida kadai suka bari a ciki don Ammi ta tafi gidan wata frnd dinta kafin su wuce, Mami na gyara ma twins din takalmansu aka bude gate din gidan, Heedayah ta daga kai don ganin wanda xai shigo, tsaye yyi bakin gate din yana kallonta kamar yanda ita ma ta take kallonsa.....




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you.
Have u ever wondered how desserts are made?
Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from?
Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because
Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught:
*Profit analysis
*Ways to handle desserts
*Dessert marketing.
This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos.
Registration is on and the fee is just N3000 Naira.
Class starts on 27th august,2021.
And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕

Contact 08135358038 for ur Dessert class





Mami ta mike tana rike da hannun twins din xata sauka kasa ita ma suka yi ido hudu da shi, tsaye tayi tana kallonsa, lkci daya Heedayah ta ji hawaye ya kawo idonta, yana murmushi ya karaso wajen walking slowly, yyi kasa da kai with respect ya gaida Mami, Mami ta sauke wani ajiyar xuciya tace "All this while bbu kira Khaleel? Sannan tafiya babu sallama" Ya kasa kallonta yace "Kiyi hakuri ban tafi da sim din da nake da numbers bane" Mami tace "To ka dawo lafiya?" Yace "Alhmdllh Ummi, ya gida" tace "Lafiya lau, ka shiga ciki, xan je Supermarket in dawo yanxu" yace "Toh in ajiye ku?" Tayi masa murmushi tace "Aa xan yi driving, motar ma na waje, kar ka damu ka shiga ciki" Yace "Toh Allah ya tsare" Mami ta kalli Heedayah da ta sauke kanta kasa tace "I will be back soon Heedayah, you stay back" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Mami ta kama hannun girls din ta wuce, Heedayah bata yarda ta kallesa ba ta juya ta koma ciki, ya bi bayanta yana kallonta. Babu kowa parlon ya xauna saman kujera still looking directly at her, ita dai ta ki yarda su hada ido, yyi kasa da murya yace "Heedayah" ta kauda kanta ta wani daure fuska, mikewa yyi ya dawo kujeran dake kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Ain't you happy seeing me?" Hawaye ya kawo idonta ta rufe fuskarta da kujeran, yyi shiru yana kallonta, can yace "To kiyi hakuri, idan baki son ganina I will go now" Ta dago tana kallonsa cikin rawar murya tace "You just left, no calls, no text...." Ya kwantar da murya ce "But I told you before leaving Heedayah, kuma ni ban tafi da wayata ba..." ta goge hawayen idonta da ya ki tsayawa, cikin sanyin murya yace "But I missed you with every second, I think of you everyday...." Ta d'an kallesa, sai a snn taga irin ramar da yyi, ya sakar mata cute smile dinsa yace "I missed you Heedayah" Bata iya tace komai ba, shima yyi shiru, bayan few seconds yace "Kuma ai jiya ku ka yi graduation dinku, i kept to my promise..." Tace "How did you know jiya ne graduation dinmu?" Yyi murmushi yace "I knew because I care Heedayah, nayi kewar ki fiye da yanda kike xato, I had no choice but to stay far away..." Yakumbo ce ta shigo parlon tana kallon Heedayah tace "Aa fasa tafiya tayi da ke Rahinar?" Heedayah tace "Uhm sun tafi" Yakumbo na kallon Khaleel a hankali tace "Auu, dama Rahinah na da wani d'an bayan Junaidu, ahh ba shakka" Heedayah ta kalli Khaleel dake kallon Yakumbo shi ma, cikin ladabi ya gaisheta ta amsa tace "Toh ya aka yi baka xo shagalullukan jiya ba, sannan ni bata ce min tana da babban d'a haka ba...." Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Nayi tafiya ne yau na dawo..." Yakumbo tace "Ba shakka, to ya sunan naka" ya sauke idonsa kasa yace "Khaleel" Yakumbo tace "Ba shakka, ita dai Rahinah Allah ya bata kyawawan yara maa sha Allah" lkci daya Yakumbo tayi tsit tana kallonsa da kyau tace "Aa wnn ai kamar na ta6a ganin ka ma..." Shi dai Khaleel bai ce komai ba don bai mance abinda tayi masa a gidansu Heedayah a Abuja ba, Yakumbo tace "Wllh sai fuskar yyi min kamar na ta6a ganinsa, toh shi Junaidu ba kullum yake dawowa gida bane, naga kullum ba a ganinsa a gida" Heedayah dai bata tanka ta ba ta mike ta tafi kitchen ta dauko masa ruwa da drink ta daura glass cup a tray din ta dawo parlon ta ajiye kusa da shi tana kallonsa, Yakumbo dai tayi wucewarta sama amma fa tana son tuna inda ta ta6a ganin Khaleel, Khaleel na kallon Heedayah murya can kasa yace "Ina kama da su Ummi ne?" Ta kallesa ta d'an yi murmushi tace "Aa, just the dimples" Shiru yyi yana kallonta, ta dau drink din ta mika masa, suka yi direct contact na ido, sosai gabanta ya fadi, shi ya fara sauke idonsa ya karbi drink din cikin sanyin murya yace "No matter the circumstances do not leave me plss Heedayah, idan kowa ma ya gujeni ke kar ki gujeni, I don't know what will become of me..." Cikin breaking voice ya fadi haka, lkci daya taji jikinta yyi sanyi tace "Me yasa kake yawan fada min haka, kana tunanin akwai abinda xai raba mu ne?" Ya gyada mata kai a hankali yace "Sure Heedayah, amma kar ki bari hakan ya raba mu..." Sakkowa kasa yyi kasa a hankali kneeling down right in front of her, ta ja baya ta xauna tana kallonsa da mamaki, cikin sanyin yace "I have never fell in love sai da na sake haduwa dake 1 year and some months back Heedayah, ban san meye soyayya ba, ban san ya yake ba, I was raised with a strong harsh heart, sai dai ban bari hakan yayi fatali da tausayina ba, Ina da tausayi sosai duk da dakakkiyar xuciyata..." Shiru yyi yana kallonta da lumsassun idonsa, ita kuma taki dago kanta tana ta naxarin abinda ya fada, can ta dago tana kallonsa tace "Sai da ka sake haduwa da ni? Dama mun ta6a haduwa ne?" Ya sauke idonsa kasa yace "Ehh mun hadu a lkcn da bakya gani, a lkcn da baki da sauran gata... Naji tausayin ki sosai, wanda tausayin yasa nayi maki abinda na maki" Kallonsa take ko kiftawa babu, can tace "Ban gane ba, meye ka min?" Yayi kasa da murya ce "Ni ne na dauke ki a den din Kidnapper na fito da ke a kan Motorcycle na ajiye ki gefen hanya Heedayah, and your words to me then were 'Are you leaving me?' Ban kuma ce maki komai ba nayi wucewata na barki, kin tuna??" A tsorace Heedayah ke kallonsa da manyan idanuwanta, can ta fara ja baya tace "Kai Kidnapper ne?" Ya girgixa mata kai da sauri as confused as he is yace "Noo Heedayah, kawai na kubutar da ke ne daga wajensu sbda tausayin ki da naji" Kallonsa take ko kiftawa bbu xuciyarta na bugawa, cikin sanyin murya yace "Ni ba su bane Heedayah, na dai taimakeki ne sbda kashe ki xa su yi" Ta hadiye abu da kyar tace "To ya aka yi kasan ina wajen, I was thinking daji ne, me ya kai ka wajen har ka san da ni??" Ya girgixa kai da sauri, da farko ya rasa abun cewa, sai kuma yyi saurin cewa "Na xo wucewa ne da Bike dina shine na dauke ki...." Bata kuma cewa komai ba ta sauke idonta kasa, lkci daya jikinsa yyi sanyi sosai don ya san bai gamsar da ita ba, bata gamsu da bayaninsa ba, gaba daya kuma ya rasa me xai ce mata, can a hankali yace "Heedayah" ta dago da sauri ta kallesa yace "Tunanin me kike?" Ta girgixa masa kai ta mike tace "Aa ba komai, xan karasa wanke wanken da nake yi a kitchen" bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen din da sauri, ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa, Heedayah na shiga kitchen ta kulle kofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login