Showing 123001 words to 126000 words out of 275313 words

Chapter 42 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

tace "Yanxu da gaske Rakiya sakin ki Amadu yayi?" Mami kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Ehh haka ne" Kaka ta kuma rushewa da kuka tace "Toh Allah ya bi maki hakkin ki, Allah ya saka maki, muna nan dake sai yayi hawaye da idonsa bbu ruwana da koma meye ya samesa, nima yau kwana tara rabon da in sa ido a kansa bbu xuwa gaisheni bbu kirana, gashi sun yi fada kaca kaca da yayan nasa Umaru, dama fa yana da bakin hali kawai boyewa yake yi, amma yanxu tunda anyi walkiya mun gangosa ai sai kowa yyi ta kansa, Deedayar ma a rabasa da ita kada wataran ya da6a mata wuka kawai" Mami dai bata ce komai ba, Kaka na kara bin parlon da kallo tace "Maa sha Allah, da gatanki kaca kaca ai ba ayi shegen namiji da xai walakanta ki ba wllh, daga kin taimakesa kin auresa kin rike masa makauniya tsakanin ki da Allah sai cin mutunci ya biyo baya, to wllh yyi ma kansa, Kar ki sa komai a ranki, kyakkyawar xuciyar ki baxai ta6a bari ki tagayyara ba, nima kai na da na haifesa baxan bi ta kansa ba balle ke, kuma ido xan saka masa kar yayi min rashin kunya" Mami tayi murmushi kawai, Mai aikinta ta fito kitchen ta duka har kasa ta gaida kaka, kaka tace "Yauwa sannu" Mami tace "Ki kawo kayan kari" Kaka tace "Dama ban ci komai ba wllh" A can daki Mami ta sa Mai aikin ta kai ma kaka breakfast. Bayan kaka ta gama breakfast din tana ta sakace sakacen hakori don an ci nama ba kadan ba, Junaid ya shigo dakin da sallama kansa a kasa, tabe baki kaka tayi ta rungume hannu ta kauda kai, yana murmushi ya xauna nan saman carpet din dakin yace "Sannu da xuwa kaka" Kaka tace "Aa ba ruwana da makaryaci gaskiya, kai da ka gilla min karya kana Abuja kuma me ya kawo ka kaduna?" Dariya yyi yace "Kaka bacci nake lkcn da kika kira ban san ma inda nace maki nake ba" Kaka tace "Toh Allah ya kyauta, ai gani nan dai na xo kuma da kyar idan baxan yi kwana biyu a nan ba don ya fi min alkhairi" Heedayah ce tafe tare da Farida ta dalilin kiransu da aka yi daga Admin an xo masu visiting.... watanninsu hudu kenan a makarantar, ko sati biyu basu yi da dawowa makaranta daga hutun First term ba, a watannin nan hudu Heedayah is one of the best student in Jss2, bbu wanda xai ce a makance ta san abubuwa da dama na boko a rayuwarta, xuwa yanxu kam girma ya d'an fara bayyana a jikinta, kyawunta kuwa sai gaba yake tamkar diyar larabawa, sosai Guardian mother dinta ta makaranta ke ji da ita jininsu ya hadu ba kadan ba, Farida tayi breaking silence din tace "But it can't be Mami or even Yaya, sbda Yaya ya kawo min textbooks dina last week ai baxai xo ba satin nan na sani, Mami kuma is in Abuja" Heedayah ta kalleta da manyan idanuwanta tace "Then who??" Farida tace "Toh ni ma ban sani ba" har dai suka isa admin block aka yi directing dinsu karkashin one of the trees na cikin makarantar, tun daga nisa Heedayah ke kallonsa haka ma Farida, wayarsa yake dannawa idonsa sanye da bakin glasses da ya haska sa sosai, baka ganin komai daga nisan sai dogon hancinsa, Farida sai kallonsa take, lkci daya ya daga kai yana kallonsu, murmushi ya sakar masu, Heedayah ta mayar masa cikin sanyayyan muryarta tace "Ya Sudais" Mikewa yayi still smiling at them.


Heedayah isn't free

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Heedayah tace "Ina yini ya Sudais" ya cire glasses din idonsa yana kallon kwayar idonta yace "Lafiya lau ya karatu?" Tace "Alhmdllh" gaishesa Farida ma tayi, ya amsa mata da murmushi yace "How is study?" Tace "fine Alhmdllh" yace "That's great" Yana kallon Heedayah yace "Hope you are enjoying it in here yan matan Mami" Ta gyada masa kai tana murmushi tace "Sure" yace "That's nice" Heedayah tace "Ya Sudais Kaka fa" Yace "Tana gidan su Farida ai" Heedayah tace "Okay but when we went back for holiday bata nan, ban ganta ba" yace "Baki ce Mami ta kai ki wajenta ba" A hankali Heedayah tace "Ta ki" Sudais yace "Ohh may be she is busy" komawa yayi ya xauna inda yake yace "Ku ai makarantar ku ne ni bari in xauna" Dariya Heedayah tayi tace "Yes, beside we are not that lazy" ya xaro ido yana kallonta, Farida dai tayi murmushi, sun kusa awa daya tare da Sudais a wajen, yawanci duk xancen da suke na karatu ne, and he was so amazed at how intelligent Heedayah was ya kasa daina kallonta even for a second, Daga karshe dai ya mike yace "Ya kamata ku je ku ci gaba da karatu yanxu, but ku baku da d'an supermarket din nan na cikin makarantar?" Heedayah tace "Aa muna da, they sell everything" Yace "That's sweet" Dubu ashirin ya fiddo aljihunsa ya mika ma Farida yace "Ke ce babba ku siyi duk abinda ku ke bukata, I don't really know what u will like shi yasa ban siya komai ba while coming" Farida tace "Last week fa yayanmu ya xo kuma ya ba mu kudi, we have enough money" Yace "Yes I know, but kina nufin ni ba yayanku bane?" Murmushi tayi tace "Not at all ba haka nake nufi ba" Yace "Toh amsa" Ta amshi kudin tace "Toh mun gode Allah ya saka da alkhairi" Heedayah tayi murmushi tace "We appreciate ya Sudais" Yace "You are welcm all" Daga haka suka rabu da shi, Heedayah sai waigosa take don sai taji bata son su rabu, she is going to miss him much. Mami na kitchen da safe tare da mai aikinta suna hada breakfast kasancewar ranan asabar ne baxata fita aiki ba, Daga nan parlor kaka ke cewa "Ai ni da na biye ta Umaru baxai ma bar ni in xo nan ba, kinsan da yake ba sata kadai ne abun kunya ba, Ina ga kunyar xuwa wajen ki da nake yi suke, tunda sun san abinda suka tafka shi da d'an uwan, to kuma yau sati na kusan daya a nan duk safiya ina lura da jik'a jik'an aikin da me aikin nan taki take ba kan gado kamar yar maguzawa, kuma kawai don na mata magana ki ce don me? Ni sai in iya tattara yanawa yanawa in tafi duk inda Allah yayi wllh" Mami dai na jin ta a kitchen tayi murmushi bata ce komai ba, ko kadan bata son kyaran da Kaka ke yi ma mai aikin nata, abu kadan yarinyar tayi sai fitinar kaka, ta lura duk inda me aiki take jininsu bai haduwa da kaka, kaka ta kara daga murya tace "Toh idan na koma gida yanxu ba sai Umaru ya min dariya ba har da shewa, kin ga ko gwara in tafi duk inda Allah yayi, don tun farko ya hanani xuwa, kawai daga na fada gaskiya ki ce min ba haka bane wato dai a fakaice makaryaciya kika kirani, masu aikin jaraba suna neman hada ni da ke, to ni bbu ruwana kafin ki koreni gwara ko xuwa nan da sati biyu ne in tattara komai nawa in yi wucewata, ko tsinke baxan bari ba wllh" Danna bell aka yi, Mami dake ta murmushi tace "Zainab tafi ki duba waye a kofa" Tace "Toh Hajiya" daga haka ta fita, kaka ta bi ta da wani shegen kallo tayi mitsi mitsi da ido tace "Algunguma me raba xumunci kawai" Zainab na bude kofa ta gaida wanda ta gani tsaye da ladabi, ya amsa yana kallonta, with respect tace "Wa xa a ce?" Yace "Barrister" tace "Toh" sannan ta juya ta koma, kaka ta sake bin ta da harara har ta shiga kitchen din, sannan tayi kwafa tana kara gyara xama, da ladabi Zainab tace ma Mami "Hajiya wai Barrister ne" Mami dake juya farfesun kayan ciki dake saman gas ta kalleta tace "Barrister? Daga ina wai?" Zainab tace "Aa bai sanar min ba" Mami tace "Koma ki tambayesa daga ina" Zainab ta juya ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace "Hajiya cewa yayi Barrister Ahmad Aliyu" Mami dake kwashe farfesun a warmer don har yayi, bayan few seconds tace "Kiyi hakuri ki koma ki tambayesa akwai matsala ne? Wa yake nema" Juyawa tayi ta sake fita, Kaka dai na ta xaman parlor kamshin farfesu duk ya cikata don da farko cewa tayi xata tafi, har jakarta tace xata tafi ta dakko a sama, amma tunda taji irin kamshin dake tashi ta share batun jakar tayi mukus sai kame kamen fada da take ta yi, Kaka tace "Toh waye ya danna mana kararrawa naga bai shigo ba har yanxu" Zainab xata koma kitchen tace "Bako ne kaka" Kaka tace "Wani jarabbben bako da sassafen nan ko karyawa ba mu yi ba yunwa ta dame mu, girkin ma da iya cikin mu kawai aka yi, wani bako kuma" Zainab na shiga kitchen din tace "Hajiya cewa yayi xuwa yayi ya gaida Kaka" Mami tace "Ohk toh xan wuce sama ynxu sai ki kashe gas din ruwan xafin nan ki tafi kice ya shigo tana parlor" Zainab tace "Toh" daga haka Mami ta fito parlor, Kaka tace "Nan dai da sati uku xuwa hudu xan koma gidan Umaru tunda shaidaniya ta fara shiga tsakaninmu, ba ruwana da fada da ke" Mami na murmushi tace "Aa kaka bbu wanda xai shiga tsakaninmu baki dai fahimce ni bane, bari in sakkowa ynxu in kawo maki kayan karin" Daga haka Mami ta wuce sama, Kaka tayi kasa da murya tace "Ni yau naga jaraba duk sai yunwa ya gama cutar jama'ah ya lahanta 'yan hanjinmu sannan a bamu kayan karin, ni dai na gaji wllh...." Zainab ta bude kofar parlon tana kallon Barrister tace "Bismillah" Da sallama ya shigo parlon, Kaka ta saki baki tana kallonsa da mamaki, har ya karasa cikin parlon kallonsa take baki bude, ya xauna yyi kasa da murya yace "Ina kwana Baaba" Kaka ta rufe bakin tace "Ikon Allah, to batan hanya kayi Amadu koko xuwa kayi ka kawo mana tashin hankali a nan muna xaman xaman mu?" Ya girgixa kai yace "Aa na dai xo ne in gaishe ki" Kaka tace "Ni a wa?? Iyye? Nace ni a wa xaka xo gaisheni, dama ka hada abu da nine bani da labari?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Toh bbu ruwana kada ma raina ya baci ka tashi kayi ta kanka" Yyi kasa da kai yace "Aa kiyi hakuri nayi tafiya ne, aiki yyi min yawa...." Kaka tace "Ayyoo, Allah sarki.... Yawan aikin ne ya sa ka saki Rakiya kenan ashe?" Abba ya kalleta yace "Aa ni ban saketa ba" Kaka tace "Ohh don baka da kunya karya xaka yi a gabana? laifi kan laifi, me wnn baiwar Allah tayi maka da xaka yi mata wannan d'an banxan cin mutuncin, da girmanta da k'imarta da dukiyarta ka walakanta ta haka Amadu??" Sai kuma ta fashe da kuka Abba yace "Ni fa wllh ban saketa ba Baaba" Kaka ta dakatar da kukan da take tace "Ko dai wiwin kai ma ka fara sha, ka saki mace kace baka saketa ba sbda lalacewa ta same ka?" Yace "Wllh nace ban saketa ba dama tana da niyyar tafiya ne kawai" Sake baki Kaka tayi tana kallonsa, can ta kwalo ma Zainab kira ta fito daga kitchen da sauri, kaka tace "Tafi sama ki kira min Rakiya" Zainab na dawowa tace "Tana xuwa kaka" Kaka tace "Toh gwara dai ta xo" Har bayan minti goma Mami bata sakko ba, kaka ta sake mayar da Zainab, Zainab ta dawo tace tana bandaki, kaka ta mike tace "Toh ai ba komai bane idan ni na tafi na kirata da kai na, bbu wanda xai maidani karamar mutum daga ita har Amadun" Mami bata iya yi ma kaka musu ba bayan ya shigo dakinta, ta mike ta bi bayanta suka fita, kaka ta juyo tana kallonta tayi kasa da murya tace "Anya Rakiya ba a siyar da wiwi gun aikin ku kuwa?" Mami tace "Me ya faru?" Kaka tace "Da kyar idan ba wani ya fara tusa masa ra'ayin abun ba, naga kamar ba a saiti kansa yake ba, gashi yaki yadda mu hada ido, kuma alamar maganarsa bbu la'asar ko kadan, gatsau gatsau yake min" Mami tace "No ba gun aikin mu daya ba ai" Kaka tace "Ikon Allah...." Har sannan Abba na xaune parlor, Mami dai bata karasa ciki ba, kaka ta xauna tace "Toh maimaita abinda kace kan Rakiya Amadu" Abba yace "Nace ban saketa ba" Kaka ta kalli Mami tace "Ke kinji dai ko?" Mami tace "Ehh haka ne" Bude baki kaka tayi tana kallonta, can tace "Ban gane ba" Mami tace "Bana auren ne kawai, kuma ya saurari sammaci nan ba da dadewa ba, tunda ya ki bani takardata ta lumana" Kaka tace "Oh oh Allah na shiga uku, kina da hankali kuwa Rakiya ko kema kin fara shaye shayen ne, dama bai sake ki ba kika tattara kika yi tafiyar ki sbda rashin tsoron Allah?" Mami tace "Bana auren ne kaka shi yasa na tafi, na kuma masa magana ya bani takardata ya ki bani, don haka kinga kuwa dole in kai batun gaba" Kaka tace "A ina kika gansa kika yi masa maganan?" Mami tace "Na tura masa message severally..." Abba dake ta kallon Mami yace "Okay xan baki takardar ki kamar yanda kika bukata but sai mun ajiye yarjejeniyar bbu ke bbu Heedayah, ki cire hannun ki kan lamarinta...." Mami ta dakatar da shi tace "Sorry to say, wannan ne kuma baka isa ba barrister, baxan yarda da duk wani abu da xai cutar da ita ba don xamanta gidanka bbu abinda xai haifar sai cutar da yarinyar" Abba yace "Okay then, kema ki saurari sammaci" Mami tace "I will welcome that gladly" mikewa yayi yana kallon kaka da ta kasa cewa komai ta saki baki tana kallonsu yace "Na gaishe ki Baaba" daga haka ya nufi kofa. Salati kaka ta saki tace "Naga abinda ya isheni ni Patuu, me xan gani haka, ke Rakiya ashe dama auren ki ba mutuwa yyi ba kika tattaro kika dawo nan, meye a takardan da kika ce kin gani parlon na ki to?" Mami tace "Aa ba wani abu bane, amma baxan dauka ba Kaka, ya bani takardata kawai bana auren dama sbda in ceci rayuwar wnn baiwar Allah na amince muka yi xaman aure da shi, amma tunda cin mutunci ya fara shigowa to baxan iya ba kuma baxan dauka ba, ni ba yarinya bace da xan tsaya ina kishi ko wani tashin hankali a kan namiji kuma, sannan duk abinda xai yi yayi amma Wlh tllh baxan basa Heedayah ba, tsaf matarsa xata iya kasheta ya rufe case din bbu wanda ya sani, kinga kuwa bai cancanci riketa ba" Kaka tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni dai, toh ni duk ba wannan ba yanda ya shigo yana mana magana gatsa gatsa ne ya dameni yanxu, bbu fa wani rusuna da yyi da wnn lamarin, sannan tunda ya san bai sake ki ba kuma ya xo ya tarar baki gidan ai ya kamata ya bi ki duk inda kika tafi ya ji dalilin tafiyar ki, Anya Amadu kansa daya kuwa?? Sannan ya shigo gaisheni bbu bada hakurin rashin gaisheni da bai yi ba na kusan shekara daya bbu alamar nadama a tare da shi kwata kwata" Mami dai bata ce mata komai ba ta tafi kitchen kawo mata breakfast. Sai da kaka ta cinye kayan cikin tass sannan tace "Ni dai Rakiya kiyi hakuri ki rufa ma Amadu asiri ki rufa min asiri, ki rufa ma Deedayah asiri kada ki kawo masa sammacin nan, Allah xai daidaita ku in sha Allahu tunda ke dai ba ki nufin kowa da sharri...." Mami tayi murmushi tace "Kiyi hakuri kaka, amma Wllh wllh kinji har na rantse na gama auren barrister, sannan ya gama rikon Heedayah, sai dai idan ba Barrister Rahinah bace ni" Kaka tayi mata wani kallo tace "Ka ji tsiya da wasali, to ai shi ma Amadun ba kyalle bane, sai dai ku yi ta gogawa daga karshe ya nanaki da kasa a banxa kawai, ta ina xa ki rabasa da Deedayah da yyi ta wahala da tun tana makauniya, a ta dalilinsa fa kika santa, Anya kina tsoron Allah kuwa Rakiya" Mami tayi wani dariya tace "Sai dai ni in nana shi da kasa kaka don na fi sa gaskiya, kuma In sha Allahu Heedayah baxata sake xama gidansa ba, ta gama xama tare da shi kenan har abada, har Allah ya bayyana iyayenta idan suna da rai...."




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Kaka ta daga hannu tace "Toh ni dai ba ruwana, wnn ai kunyata kan ku xa ku yi a idon duniya kawai, meye kuma fada a kotu a kan yar yarinya da ba ku hada komai da ita ba?? Idan haka ne a raba gardama a mayar da ita dai dai gun da aka daukota a ajiye, ko kuma a bani hotonta in baxama duniya neman Yan uwanta idan ma iyayenta mutuwa suka yi ai baxa a rasa yan uwanta ba, son xuciya ya hana Amadu yin haka, bamu san nufinsa a kanta ba gaskiya" Mami dai bata ce da kaka komai ba tana danna wayarta. Tun da Heedayah ta tashi yau take murna xa su tafi gida sbda hutun second term da suka yi, duk suka gama hada kayan da xa su mayar gida tare da Farida, bayan azahar aka xo daukarsu, tsaye su ka gansa jikin motarsa ya rungume hannu, ganinsu ya bude masu booth, suka xuba kayansu ciki, Farida na kallonsa tace "Ina yini Yaya" yace "Lafiya lau" Heedayah ma ta gaishesa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login