Showing 102001 words to 105000 words out of 275313 words

Chapter 35 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

sannan ta kai Hajiya Zuwaira da kawarta da kanwarta parlonta, mikewa Heedayah tayi da sauri ta bi bayanta, Mumy ta bi ta da wani kallo ta gefen ido, Mami ta ciro ma bak'in nata ruwa da lemo a fridge ta ajiye masu tace "Tunda ku na gida ne bari in sallami bakin parlor, abokan aikina ne da matan yayan Barrister, Ina xuwa yanxun Hajiya" Hajiya Zulaiha tace "Ba damuwa Rahinah, mu kam na gida ne" Mami ta fita Heedayah ta bi bayanta da sauri duk da kiranta da Hajiya Zuwaira ke yi, Mami ta kalleta tace "C'mon je ana kiran ki my frnd" a hankali ta juya ta koma cikin parlon ta nufi gun Hajiya Zuwaira, Mami tayi wucewarta... Mami na dawowa main parlor Hajiya Hauwa tace "Kinga ki shiga ki gaida Kaka tana iya cewa ai kin ganta kin shareta, kinsan halin abar tamu...." Dariya Mami tayi tace "Ae kuwa" Mumy tace "Ae haka ma kawai xata ce" Mami tace "Bari in je in dawo" daga haka ta nufi hanyar dakin kaka, dakin masu aiki ta fara shiga, tana kallon sabuwar mai aikin me suna Talatu tace "Don Allah ki debi abinci da su samosa da cake ki kai can parlona akwai baki guda uku" Talatu ta mike da sauri tace "Toh Hajiya" Mami ta juya ta fita ta wuce dakin kaka, kaka na share windanta da tsintsiya bayan ta cire duk labulayen dakin da ma xanin gado Mami ta shigo da sallama, Da fara'a tace "Sannu da isowa kaka, fatan mun same ku lafiya" Kaka ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Ita Deedayar bata da labarin ni na haifi Amadu da ya biya kudin gyaran idon nata ne da har yanxu bata shigo ta gaisheni ba? Kinga Amadu fa bai ta6a sanin yarinyar nan ba wllh, bbu dangin iya balle na baba, to kuma ya ina mahaifiyarsa baxata xo ta gaisheni ba sbda idonta ya budu, to ni da nasan haka ne xai faru da nace ma Amadu ba da yawuna ba idan aka gyara mata idon, ace tun dawowar ku ba ki xaunar da ita kin sanar mata wacece ni da abinda ya kamata tayi idan ta gan ni ba, kin ga rashin gaskiyar jama'ah ko? To ni dai ba ruwana, ai ba wani ya haifar min Amadun ba, kwanana uku ina nakudar sa wllh" Mami da ke ta kallon kaka tace "Toh kiyi hakuri, kuma Heedayah har yanxu ba wai ta gama sakin jikinta da mutane bane, Kar ki manta kaka tun da aka haifeta makauniya ce ita, Kinga da girmanta ta fara ganin duk wani halitta, to banda ynxu da ta fara sakewa ai da ko mutum ta gani ta dingi ihu kenan tana tsoro" Kaka ta daga hannu tace "Toh ni ina ruwana, ni dai ba ni ce na haifi wanda ya tsintota yyi silar gyaran idonta ba, Taimakonta Allah Taimakonta Amadu a duniyar nan, don haka ai ban cancanci raini wajenta ba, baki ga kallon rainin hankalin da naga tana min ba, ni a gaskiya da na sani da an barta a makancen ma kawai tayi ta ma mutane ladabi a hakan" Mami bata kuma ce mata komai ba ta juya ta fita don ranta ya gama baci, Sai bayan da ta fita kaka tace "Wa ya sani ma ko 'yar ta ce ta makala ma Amadu don kawai ya aureta, mutane dai bbu gaskiya" Mami na fitowa ta wuce parlonta, Tayi ma su Hajiya Zuwaira sannu sannan tace "Heedayah taso mu je" Mikewa Heedayah tayi ta bi bayanta suka fita, Mami ta wuce da ita dakin kaka suna isa kofar ta juyo tana kallonta tace "Idan mun shiga ki xauna a kasa ki gaisheta, ita ce kaka" Heedayah ta gyada mata kai sannan Mami ta bude kofar suka shiga dakin, a bakin kofa Heedayah ta xauna tace "Ina wuni" Kaka dake share bangon dakinta ta juyo ta kalleta ta ajiye tsintsiyar tace "Toh ki gode ma Allah ki gode ma d'a na Amadu, kuma ni nan nice kaka ni na haifi Amadun da yyi silar gyaran idonki, ko iyayenki na da rai yau basu da iko a kanki kamar yanda Amadu ke da iko a kanki amma ya xa ayi in shigo kina xaune rike da goran panta da kenk ki kasa ce min komai kin ji kowa na min sannu da xuwa kaka" Heedayah dai sai kallon kaka take, duk Inda ta bi da hannu sai ta kalla kai kace TV ta samu, Kaka ta kalli Mami dake jira ta fitar da Heedayah daga dakin tace "Kin gani ko Rakiya, hararata fa take" Mami tace "Wani harara kuma kaka, ance maki yarinyar har yanxu bata gama sabawa da komai ba, yaushe ma ta fara ganin ki idan ba yanxu ba, sai fa a hankali xata saki jiki da kowa ta dawo kamar ko wani mutum, ynxu haka da xa ki kawo mata mage ko tsuntsu bata san su ba bata ta6a ganinsu ba, sae dai sunansa, to kinga kuwa dole ayi ma mutum uxuri, ranan da idonta ya bude tsoron kowa ta dinga yi, kuna hada ido xata fasa ihu, sbda duk rayuwarta a duhu yake banda ynxu da Allah ya yaye mata" Kaka tace "Haka abun yake?" Mami ta daga Heedayah dake ta xaune tana kallon kaka tace "Sai hakuri kaka, ni xan tafi in ji da mutane" Daga haka ta fita da Heedayah dake waigo kaka... Fitowa kaka tayi tana kallon mutan parlon ganin Mumy tace "Xo Maryam" Mumy ta mike ganin kaka ta nufi nata bangaren ta bi bayanta har suka shige parlon Mumy, Kaka ta xauna saman kujera ta fashe da kuka tace "Rakiya ce ta shigo ta min wankin babban bargo bbu abinda ta mance bata gaya min ba, a takaice dai a baibai kirana tayi da fitinanniya, ni dai ina tsaye bance mata uffan ba ta ja hannun makauniyar da Amadu ya kashe kudi ya warkar suka fita" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Mumy tace "Ikon Allah, to ke me kika yi xata maki haka daga dawowarki" kaka tace "Wllh Maryam daga nace mata Deedayah lafiya bata shigo ta gaisheni ba naga kamar ma hararata take da na shigo ko bata gane ni bane ta min irin wnn kallon, Kar ki d'a d'a kar ki raga, Rakiya ta hau ni da bala'i wai ni bana yi ma mutane uxuri, ai Deedayah a duhu take ynxu Allah ya fito da ita Amadu ya fito da ita haske, Kuma ai dole ta ji tsorona tunda ita ma ta ji tsoronta da suke asibiti, to idan Rakiya na da hankali da tunani sai ta hada kanta da ni? Ni fa na haifi Wanda yayi silar warkewar Deedayan" Mumy ta hade rai tace "Gaskiya wnn raini ta maki, bata kyauta ba, gani take ta fi kowa Iko da yarinyar a gidan nan daxu fa daga Barrister ya kawota parlona na fita kitchen hada mata shayi matar nan ta shigo ta dauke ta" kaka tace "To kuwa ta ci kanta, Kuma sai na sa an karbe Deedayan hannunta in ga ta tsiya, idan ma Amadu baxai bani ita ba ke ya baki ki rike, abinda ma xai faru kenan wllh wllh, a ina take da iko da yarinya bayan ita ma makalewa tayi aka aurota dalilin yarinyar, da ba don yarinyar ba mu muka san wata Rakiya" Mumy tace "Ae shine, ni wllh a bani ita dama lkcn can shaidan ne ya shiga xuciyata ya hanani amsar ta amma wllh tllh ynxu xuciyata daya xan amsheta in riketa kmr yanda xan rike d'an cikina, abinda yarinyar har ta fara sabawa da ni da suka dawo har ta kusa awa biyu a parlona" Kaka tace "Toh kin ga dai, bari Amadun ya dawo shi ma gantalalle, xan ji ko maganan Rakiya xai dauka ko tawa" Mumy tace "Atoh dai" mikewa kaka tayi ta fita parlon, Mumy tayi wani murmushi ta xauna tana kara naxarin maganganun Kaka. Kafin Magrib duk bakin gidan suka watse har ma da makota da suka shigo duk da basu wani san Mami ba sai Mumy, suka yi mata sannu da xuwa suna ma Heedayah barka suka fita, Mami da kanta ta taimaka ma Talatu gyaran gidan don kai kace wani karamin walima aka yi a gidan, Mumy kuwa ta shige bangarenta da yaranta ta kulle kofa don ma kar su dauke ko da cup, Duk inda Mami tayi Heedayah na makale da ita, Mami har ta gaji da ce mata taje ta xauna ta kyaleta, Mami na kitchen suna gyaran kitchen din aka yi Magrib, sai da Mami ta tabbatar ko ina ya dawo fess ta fito parlor tare da Heedayah ta bar talatu ta karasa wanke wanken, Kaka ce ta fito dakinta, Mami tace "Sannu kaka, abincin ya ishe ku ai koh?" Can ciki kaka ta amsa tace "Ya Isa..." Daga haka ta nufi bangaren Mumy tana rike da wayarta tana cewa "Ina Maryam ta kira min Junaidu shiru ni ban gansa ba, ko a indiyar suka baro sa" Mami dai bata ce mata komai ba har ta shiga bangaren Mumy, Mami ta wuce nata bangaren da Heedayah. Bayan isha Abba na parlonsa tare da Shuraim sai su Rabi'ah da Khadijah, Mami ta shigo ciki da sallama holding Heedayah's hand, Gun Abba Heedayah ta nufa ta xauna tace "Abba sannu da dawowa" Yyi murmushi yace "Yauwa daughter, hope kinyi bacci da yawa daxu" ta gyada masa kai, Abba ya maida dubansa kan su Khadijah on a serious note yace "As I was saying, today should be the last day da yayanku xai maku fada ko ya doke ku ku je ku gaya ma Mamarku" Rabi'ah tace "Abba ba mu muka gaya mata ba fa, she just came in" Abba yace "Whatever.... Na gaya maku ni dai...." Abba ya kalli Shuraim yace "And you Shuraim duk ranan da suka kara fashin makaranta you do what ever you wish to them, don't think twice before punishing them" ya girgixa kai kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Abba it will be good idan Mumy tayi hakan, ni babu ruwana da lamarinsu a gidan nan, beside she said I should take my hands off their issues" Abba yace "And I am instructing you to keep on disciplining them, ko ban isa?" Bai kuma cewa komai ba, Mami na kallonsu tace "Ku kuma sai kace wasu yara xuwa islamiyyar ne ku ke fashi, amma ai ban ga kuna fashin boko ba" Basu ce mata komai ba, tace "That's bad, you two should stop that" Abba yace "Nan da one week Heedayah will join them also, kafin sati dayan an nuna mata abubuwan da ya kamata ta sani facially since ta san karatu gani ne kawai bata ta6a yi ba" Mami tace "Allah ya kai mu" Bude kofar parlon aka yi, kaka ta shigo, Ko gaisuwan da ake mata bata amsa ba tace "Amadu baka san na dawo bane baka shigo ba? Tun fa yamma nake gidan nan" Abba yace "Aa dama Ina kokarin shigowa ne, Ina son in gama da su" tace "To ai dai nice dolen ka ba su ba koh?" Wani kallo Shuraim ya watsa mata, Abba dai bai ce komai ba, ta nemi waje ta xauna, Mami tace "Sannu kaka" kaka tace "Ehe" Abba yace "Ina yini Baaba" tace "Lafiya lau, Ina son magana da kai ne Amadu" Abba ya kalli su Rabi'ah yace "To na gama da ku" mikewa Mami tayi Heedayah na ganin haka ita ma ta tashi daga kusa da Abba, Kaka tace "Aa Ina kuma xa ki Rakiya koma ki xauna" Rabi'ah da Khadijah xa su fita kaka tace "Kai ku kira min Maryam idan kun fita" Abba dai sai kallon kaka yake, can yace "Lafiya dai ko kaka?" Tace "Eh lafiya lau" Bai kuma cewa komai ba sai ga Mumy ta shigo da sallama, ta nemi waje ta xauna tayi ma kaka sannu sannan tace "Ga ni kaka" Kaka tace "Toh Amadu shawara na xo baka idan kana son xaman lafiya a gidan ka...." Abba yace "Shawarar me fa?" Kaka tace "To wai me yasa baxa ayi ma Maryam kara ba a bar mata Deedayah wajenta tunda dai ta nutsu tayi hankali, ita Rakiya ba xama take ba aiki safe, rana, yamma, Ina jin har dare ma wani lkcn, to ni kuma a ynda nake ganin wnn Deedayar fitsararriya ce naga alama, don daxu bata san ina lura da ita ba ta harareni, kaga kuwa idan nace ta xauna wajena idan Rakiya ta fita kasuwancinta ai xagi na yarinyar xata dinga yi wataran in shiga uku, jikokina basu ta6a xagina ba ita ta xageni...." Da mamaki Abba ke kallonta, Mami dai bata ce komai ba kuma bata kalli direction dinsu ba, kaka ta ci gaba tace "Tunda dai ita Maryam xaman kashe xani take a gida bbu aikin fari balle na baki ba gwara a bar yarinyar gun ta ba sbda tarbiya, ni dai tun ba aje ko ina ba naga ta rainani balle ace ta xauna gu na" Mumy tace "To ai bbu komai ko ma gun wa ta xauna kaka, in ma gu na in ma gun Rahinar..." Kaka tace "Oh oh ai Rakiya aiki take fita kullum, ke dai me xaman banxa ya kamata a baki ki sa ido kan lamarin ta don naga yarinyar na bukatar sa ido, sakakkiya ce, ta xata a duhu take har ynxu" Shuraim dake sauraron kaka yace "Xai fi idan aka kai ta boarding a can xa a koya mata ladabi, xa kuma ta gane cewar ba a duhu take ba yanxu" Da sauri Mumy ta juya ta kallesa, Abba yace "Ehh in sha Allah boarding xata fara kamar yanda Shuraim yace" Kaka tace "Meye kuma boding?" Shuraim na kallonta yace "Makarantar kwana" Kaka tace "Amma kai axxalumi ne Shureen, me Deedayar ta tsare maka a gidan da kake son a kai ta makarantar kwana, Kai da aka ta6a kai ka kana yaro ka xauna?? Ba gudowa ka yi ba, to meye kuma xaka ce a kai marainiya??" Mumy tace "Toh makarantar kwanan da ake kwashe yara ma, wnn ae gurguwar shawara ce" Shuraim yace "Ae ba na gwamnati xa a kai ta ba" Kaka tace "Ni dai ba ruwana da muguntar ka na fulani, me xa mu ce ma Allah idan aka kwamushe 'yar mutane" Abba yace "Makarantar da Farida take ynxu xa a sa ta in sha Allah, boarding ce me kyau"




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Kaka tace "Aa to ni tsorona kada a sace ta ne Amadu mu shiga uku" Abba yace "Aa lafiya lau, bbu wata matsala in sha Allah" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa kansa a kasa, Mumy ta bi sa da wani irin kallo xuciyarta na tafarfasa, Mami na lura da kallon da uwartasa ke masa har ya fita parlon, Abba ya dau wayarsa dake ring ya mike yace "Bari in amsa kira in dawo Baaba" mikewa kaka tayi tace "Aa to ni kuma me xan tsaya in maka, dama shawara ce kawai na kawo, amma tunda bafillatanin d'an ka yace a kai ta makarantar kwana kuma ka amince ai shi kenan, amma a gaskiya idan wani abu ya sami yarinyar nan baxan yafe maka ba baxan yafe ma Shuraim ba, don da kai ka haifeta baxa ka yi mata sha'awar xuwa makaranta kwana ba, me yasa baka kai 'ya yan cikin ka ba sai ita?? Shi dai rikon amana dama da wahala take sai wanda Allah ya ba..." bata jira cewarsa ba ta fice daga parlon, Mikewa Mami tayi ta nufi kofa Abba ya bi ta da ido har ta fita, Mumy ma ta mike ta fice daga parlon bacin ranta ya kasa boyuwa gaba daya, dakin Shuraim ta wuce direct ta samesa ya shimfida darduma ya dauko qur'ani ya xauna, cikin daga murya tace "Aliyu a kan uban me yasa kace a kai yarinyar makarantar boarding?" Shuraim dake kallonta yace "Aa, naga kamar ba wani son xamanta gidan ake ba...." Tayi masa wani tsawa tace "Uban waye yace maka baya son xamanta gidan?? Kai da wa ku ka yi haka?" Yace "No naji kaka ta ce ta fara rainata, so it's better we shouldn't let that go far..." A fusace Mumy tace "Toh kai Ina ruwanka da xancen da ka tsoma baki? Dangi uwa ko ta uba? Meye hadin ka da ita da har xaka bada shawara kan lamarin ta iyye? Meye damuwar ka da ita nace?" Yana bude qur'anin gabansa a hankali yace "Nima din ban fiye son ganinta a gidan bane shi yasa na kawo nawa shawarar for my own good" Mumy ta jefa masa wani shegen kallo tace "Sau da nawa da nawa kake xaman gidan idan ba gulma da munafurci ba Aliyu?? Sati da lahadin da kake dawowa yi a gidan ne xaka wani ce kai ma ba ganinta kke son yi ba? Uban ma me ta tsare maka tukun? To ynda ka kawo shawarar a kai ta makarantar kwana sai ka koma kace a sa ta a day, in har kana son wanyewa lafiya...." Da mamaki yake kallon Mumy yace "Toh Mumy ke kuwa meye na ki idan an kai ta makarantar kwana? Naga kema ba wani son xamanta kike a gidan ba fa, so it's better she should stay away from this house completely, hankalin kowa xai fi kwanciya, ni na xata ma xaki fi kowa murna da shawarar da na bada, I see no reason da xa ki daga hankalin ki don ance xa a kai ta boarding, sai dai idan da akwai wani abun daban..." Mumy da ta bude baki tana kallonsa tayi shiru ta kasa cewa komai da farko, can ta dake tace "Akwai wani abun kamar me, ban fahimta ba?" yace "No nima ban sani ba, kawai dai nayi tunanin haka ne" Ta hadiye abu da kyar tace "To bari in fito maka a mutum yanxun tunda ba tsoron ka nake ba Aliyu, ban ga dalilin da xa a kai yar tsintuwa tsadadden

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login