Showing 144001 words to 147000 words out of 275313 words
Chapter 49 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
ki, is that so??" Cikin breaking voice dinta tace "Ehh, kuma ban kara ganin Ammina da Abbana da Yakumbo ba har da Nanny, and nobody is willing to take me to them, I've missed them so much, nobody is saying anything about them to me, nobody is willing to take me to them, Ina son in ga Ammina...." Kallonta kawai yake yi, hawayen da ya makale idonta ya gangaro sai kuma ta fashe masa da kuka a hankali tana kallonsa, ya dauke kansa daga kallonta, cikin rawar murya tace "Ni ina son in ga Ammina, I want to meet with my mother..." Shi dai bai ce mata komai ba tayi kukanta me isarta tayi shiru, Ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya jinginar da kansa da kujeran motar cikin cool voice dinsa yace "Xa ki ga Ammin ki in sha Allah" Tana kallonsa cikin sanyin murya tace "When, and did you even know them?" Ya girgixa kai yace "Ban san su ba.... amma in sha Allah I will take you back to ur parent soon, I am promising you this.... But... you just have to trust me" Ta goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "How long will that take??" Yace "Not so long" tace "Tell me who are you pls" yace "Khaleel Muhd" Tayi shiru tana kallonsa, soft smile ya sakar mata murya can kasa yace "Trust me Heedayah" ta gyada masa kai kawai, yace "So anyi seizing wannan wayar da na baki ko?" Ta gyada masa kai nan ma, sai kuma da sauri tace "Toh me yace maka da ka kira wayar?" Ya d'an buda ido yace "Nothing much, I didn't even listen to him..." Yana magana yana kokarin ciro abu a aljihunsa, ya ciro wani karamin waya sosai kamar na wasan yara ya mika mata yace "If there is anything I will call you, or you call me, xa ki ga numberna Brainiac...." Ta marairaice tace "Aa ni dai kaga Ya Sudais ya kamani da waya bana son wani ya kara ganina da waya" Yace "Then if there is anything how will I communicate with you Heedayah" shiru tayi kamar me naxarin abinda yace, kamar xata yi kuka tace "Tsoro nake ji" yace "Wannan wayar ai bashi da girma, it's very portable ko a dankwalinki xa ki iya barinsa no one will know of it" Tana ta kallon wayar taki amsa gabanta na faduwa, ya kamo hannunta ya sa wayar a ciki ta xaro ido tana kallonsa, shima yana kallon kwayar idonta yace "You have to collect it" Bata ce komai ba ya sake hannunta, yace "Xa ki shiga ciki yanxu kar a nemeki ko?" Ta gyada masa kai cikin sanyin murya tace "But you promise that I will meet my parent, should I confide in you?" shiru yyi yana kallonta, yace "But you have to be patient, and naga you are so much comfortable with ur guardians here, I can see they love you wholeheartedly...." Ta fashe masa da sabon kuka tace "Basa ce min komai a kan iyayena" ya kwantar da murya yace "That's because they love you dearly, and sun daukeki kamar 'yar su" Goge idonta tayi bata ce masa komai ba sai dai hawayen ya ki tsaya mata, yace "Tunda basa maki maganan parent din ki kema kar kiyi masu, u will look so ungrateful..." Tace "Amma kai ai xaka samar min iyayena ko?" Yayi murmushi yace "I owe u that" murya can kasa tace "Thank you" Yace "No thanks" tace "Xan wuce gida" ya bude lock din motar yace "Ohk...." kafin ta bude motar, yyi kasa da murya yace "But did you have anything to do with that soldier?" Ta turo baki tace "Noo..." Daga haka ta bude motar, sai kuma ta juyo da sauri tana kallonsa tace "How did you know I was kidnapped?" Kallonta yake ko kiftawa babu, sai kuma ya sauke idonsa kasa yace "That will be story for another day..." Tayi narai narai da ido ta dawo cikin motar tace "Tell me plss" yace "Xan gaya maki amma sai mun sake haduwa, ki wuce ciki kar a nemeki, it's already getting dark" Bata kuma cewa komai ba ta sauka motar yyi mata murmushi, ta rufe motar ta karasa katin dake layin, ta baya ya fice daga layin snn yyi reverse ya hau saman titi, duk wnn abun tana tsaye gun me shago tana kallonsa ko kiftawa bbu. Hadadden parlor ne me dauke da maza hudu sai aikin shan giya suke suna caca caca duk sun cika parlon da hayaniyarsu, yana daga tsaye jikin wani pillar kusa da dinning area na parlon ya rungume hannunsa yana kallonsu yyi supporting kansa da kafarsa a jikin pillar din, 3 qtr ne jikinsa sai singlet, idonsa na kan abinda suke but hankalinsa baya kai, daya daga wa enda ke xaune cikin parlon na kyakyata dariya kamar ta6a66e yace "Kayy... xo ka barar mana da wnn mutumi ko bakinsa xai rufu don Allah" Sauke kafarsa yyi kasa ya karaso cikin parlon cikin tafiyarsa ta kasaita, ya ja wani tsadadden kujera me kama da na office ya xauna, daya daga cikinsu da suke kira Maska yace "Genius akwai damuwa ne, two days u are dull, ko miskilancin ne ya taso" Khaleel bai ce masa komai ba, Zayyad din cikinsu ya dau kwalin cigarette ya jefa masa yace "May be u need this" Dauka Khaleel yyi ya jefar saman center table din da suke caca caca yace "Yyi min kadan sae dai in kai xan kyatta ma ashana" duk suka kwashe da dariya, Khaleel ya shafa sajensa yace "Ina son maku wata tambaya" Maska ya d'an gwalo ido yace "Tohhhh Brainiac ne xai yi ma learners tambaya, are we safe at all, anyway muna jin ka" Khaleel ya daura kafarsa kan center table yace "1...2...3... To 4 years back..." Duk suka xuba masa ido da kunnuwa suna sauraronsa attentively, ya langwabar da kai yace "Anyi kidnapping wasu yara kananu duk mata guda hudu...." Sai kuma yyi shiru, Maska yace "Ehen muna jin ka, what about that" Khaleel ya sauke idonsa kasa yace "Shine nake son sanin ko xa ku iya tuna wa enda suka daukosu kuma da inda suka dauko su" Kamar hadin baki duk suka fashe da wani mahaukacin dariya nonstop, bin su ya dinga yi da kallo har bayan minti biyu suna dariyar, can ya mike ya fixgo Zayyad ya kai masa naushi a baki, kan kace me, Zayyad ya kai masa shi ma, nan kuma suka yi charging kansu, don da kyar aka samu aka rabasu aka rike Khaleel, Salim ya janye Zayyad suka bar parlon, Khaleel ya share xufar fuskarsa ya koma saman kujeran da yake ya xauna, Maska yace "Dama duk yau baka fita workout ba, you are just lying down all day, ko ba komai you will feel strong now" Sufyan da Saif da shigowarsa parlon kenan suka tsaya bakin kofa suka kalli d'an show din da aka gama suka karaso parlon da ledojin gasassun kaji, Saif yace "Are you really okay Khaleel?" Ko kallonsa Khaleel bai yi ba, Maska yace "Wai wasu yara da aka yi kidnapping 4 years ago yake tambayar inda aka dauko su kamar wani wasan kwaikwayo, yara nawa aka yi kidnapping 4 years ago" Sufyan yace "4 years ago kuma? kai ko ka so kanka da yawa Kay, lkcn muna yaku bayi fa" dariya sosai duk occupant din parlon ke yi, Khaleel ya shiga bin su da kallo, Saif ya xauna yana facing din Khaleel yace "Su waye suka yi kidnapping din yaran a cikinmu, snn idan shekaru hudu kake magana ai yawanci wasu cikinmu duk an kashe su, su Gwaska, Kamilu, Fago, Rabilu, Ahmed... Su ne masu kidnapping din a lkcn ko ka manta, ynxu Fago kadai da Kamilu ke raye, su xaka tambaya" Khaleel yace "Har da Maska aka dauko yaran idan shi ya manta ni ban manta ba" Maska yace "Ni Maskan?" Khaleel yace "Ehh, warce aka nemi daya aka rasa a wnn lkcn, har oga yace duk ynda xaka yi, kayi providing dinta kayi kawai" Maska ya koma ya xauna thinking deeply, can ya wani tafe hannu yace "Ohhhhh.... Ohkkkkk I remember, wnn makauniyar????" Khaleel ya kallesa smiling a hankali yace "Exactly" Maska ya xaro ido yace "Kai ai yarinyar nan har yau ban yarda ba aljana bace wllh wllh, she just disappeared, ko sama ko kasa bbu ita, Allah fa ya so ni lkcn nan da kwanana ya kare, so what about that now?" Khaleel yace "Inda aka dauko yaran nake son sani?" Maska yace "Oho, ni kawai mun hadu ne a bakin daji muka wuce da su, I don't know inda aka dauko su, amma fa ina jin Gwaska da Ahmed ne suka taho da su daga wani kauye" Sufyan yace "Kayy but may I ask you?" Khaleel yace "Go on" Yace "Meye ya tado da batun kusan shekara hudu?" Khaleel yace "Ba komai, Ina wani research ne kawai" Saif yace "Research akan matattu, wa ennan yara ai an rufe babinsu a duniya tun yaushe, tunda dai duk an yanke su a wancan lkcn" Khaleel yace "Gwaska ya mutu, Ahmed ma haka, amma Fago na nan ai" Maska yyi tsaki yace "Toh me xai maka?" Khaleel yace "Tare da shi aka daukosu, don haka baxai rasa sanin garin da aka dauko yaran ba" Tanko dake ta sauraron su a parlon tun farkon fara xancen bai ce komai ba yyi wani dariya irin na bossawa yace "Tunda shi Fagon ance maka bashi da wani memory me ma'ana da xai ajiye a kwakwalwarsa sai wannan abinda baxai amfaneka ba baxai amfane mu ba baxai amfane kowa ba, Kayy ka fito ka fada mana gaskiyar abinda ke faruwa da kai, meye na binciko maganar shekara 4?? ko dai ghost din yaran ne suka sa ka gaba suka ce sai ka je garinsu, share with us plss..." Mikewa Khaleel yyi yana kallonsa fiercely ya nufesa, dai dai nan aka bude kofar parlon, hakan yasa ya juya, wasu mutane ne su biyu suka shigo parlon cike da isa ana taku dai dai, tare da wani dake biye da su a baya hannunsa rike da bindiga, kowa na parlon ya mike ya gaida su, kana gani kasan manyansu ne, su suka kafa gagarumin kungiyar, Khaleel ya koma ya xauna, bakikirin cikin mutane biyun da suke kira da Oga Arne ya kalli Khaleel yace "Genius jiya Ina ka tafi da Magrib kasan akwai meeting, kowa ya hallara amma banda kai" Khaleel yace "Na shiga cikin gari ne" Oga Manga na bin duk kowa na parlon da kallo yace "Ina Zayyad da Salim" Maska yace "Suna sama" Oga Arne yace "Ayi kiransu" Saif ne ya tafi ya kirasu suka sakko gaba daya, Oga Manga yace "Ynxun nan dawowar mu kenan daga gidan d'an takarar jam'iyyar Ac wato Alhaji Sammani Abdulkadir Gaya.... Mun kuma gama magana da shi ya biya abinda muka bukata bbu ja in ja.... ynxu abinda ya rage kawai sai ynda xa ayi kidnapping din abokin hamayyarsa.... Nan da kwanaki kadan, to dai idan mun samu irin wnn aiki daga sama mu kan xauna mu nutsu mu tsara yanda komai xai tafi bbu wani mishkila, don kunga ba karamin aiki bane kidnapping din me takarar mukamin gwamna gaba daya, don haka Kayy xa mu so mu fara jin yanda kaga ya dace mu bi, yana xama a Abuja, Kano... Wani lkcn har Kaduna, snn mun samu rahotun yana lagos ynxu hka, sae dai baxa mu bi sa Lagos ba xae xo nan ya samemu" Khaleel dake ta sauraronsu yana shafa sajensa da ya kwanta ya dai yi shiru bai ce komai ba, Oga Manga yace "Ya ne Genius kayi shiru" Khaleel ya sauke kafarsa daga kan kujeran da ya daura yace "I will think about that overnight" Oga Arne ya karasa yyi patting dinsa yace "We trust you Brainiac, sai dai duk plan da thinking dinka kada ya wuce nan da sati uku, duk da dai there is till much time sosai, amma deadline din da aka bamu kenan daga sama, and we have not to disappoint them...." Bai ce masu komai ba duk suka bar parlon. Heedayah ce ta shigo dakinsu ta kulle kofar a hankali ta jingina jiki tana kallon Farida da dawowarta kenan daga gidan biki, kayanta take cirewa, Heedayah tace "Me yasa na maki magana baki amsa ni ba?" Farida ta ki kallonta tace "Ohh ban ji ba, Ina ta sauri in xo in cire kaya na gaji" Heedayah tace "Nop, kin ji" Farida ta juyo ta kalleta, sai kuma tace "Of course yes na ji" Heedayah tace "Then why did u ignore me?" Farida tace "Because that's what you want, u need privacy this days" Shiru Heedayah tayi tana kallonta, can tace "Ohk about that guy Khaleel? Bbu abinda ke tsakaninmu believe me, he just wants us to be frnds, nothing more, and I didn't tell you ya bani waya ya Sudais ya gani yyi seizing da muka je gidansu biki, I think that's all that u think I am hiding" Farida dai ta tabe baki bata ce komai ba tana ci gaba da cire kayanta, a hankali Heedayah tace "I am sorry if you think I am hiding things away from you Farida, but I am scared..." Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Farida ta kasa kallonta, can tace "I am just trying to be a protective sister, nowadays ba ko wani namiji ake kulawa ba, most especially someone like that man.... I won't say he didn't look responsible amma ae ba a goshi ake rubutawa ba, ni dai i want you to be extremely careful with him, ba mu san xuciyar sa ba, kuma kar ki manta inda muka gansa bakin hotel though we don't judge a book by just it cover, bamu san me ya kai sa can ba, amma samarin Kaduna sun wuce tunanin ki Didi" Heedayah bata iya tace komai ba, Farida ta juya tana kallonta tace "Be careful plss Heedayah" Heedayah ta gyada mata kai murya can kasa tace "In sha Allah sis, but ya kara bani wani karamin wayar" tana fadin haka ta tafi gaban mirror ta bude ta daga dictionary ta dauko wayar tana nuna ma Farida, Farida tace "But tell me did you like him" Heedayah ta d'an yi shiru sai kuma tace "He is kind... And gentle" Farida tayi murmushi tace "Toh me da me yake ce maki a waya" Heedayah ta d'an juya ido tace "Nothing, kawai labarin duniya, sae kuma labarin karatu.... He is always telling me to study hard, very hard... " Farida tace "Ohk that's good, if there is anything apart from that you let me know" Murmushi Heedayah tayi tace "Alright" daga haka ta juya ta fita parlon ta koma kasa don Mami take taya girkin dinner coz it's already six. Bayan Magrib Heedayah na xaune parlor da Farida suna cin rice and stew da veggies da Mami ta girka da pepper chicken sai tamarind drink me sanyi, Murya kasa kasa Farida ke ba Heedayah labarin abubuwan da suka faru gidan biki kar Mami ta jiyosu don ga fadan gulma da ta kawo take yi, snn kuma ga fadan abinci na gabanta tana surutu which is a bad table manner, irin abubuwan da kaka ta dinga ma jama'ah take fadi ma Heedayah, da ynda ta laka ma wata satan zinarinta kunne daya, daga karshe aka ga zinarin a bandaki ya fadi alamar dai da kaka ta shiga alwala ne ya fadi, Heedayah ta tabe baki tana girgixa kai tace "Will kaka ever change?" Farida tace "I don't think so gaskiya, har sai da aka kira Baffa ya dawo gidan, Abba ma ya xo wllh, matar sai kuka take gwanin ban tausayi ta harhada kayanta xata wuce, Kuma fa wai step sister dinsu Abba ce she is staying in kano, tana ma da manyan yara kaman mu..." Heedayah tace "Toh me Kakar ta ce da aka ga dankunne a toilet dinta?" Farida tace "Kuka ta xauna ta dinga rusawa wai wani ne dama ke son hadasu fada da matar shine ya kai dan kunnen bandakinta ya boye" danna bell din parlon aka yi, Zainab me aiki dake xaune kusa da kofar dakinta tana kallon Tv ta mike ta nufi kofar ta bude, gaishesa tayi ta basa hanya ya shigo parlon, Tun da Heedayah tayi ido hudu da green ta dauke kai da sauri ta ci gaba da cin abincinta, Ya karaso cikin parlon Farida ma bata sake kallonsa ba tace "Ina yini?" Yace "Ina Mami?" Farida tace "Tana sama, sis Zainab kiyi mata magana" mikewa Zainab tayi ta wuce sama, ya ajiye ledan hannunsa saman table sannan ya xauna kan kujera, da kyar Heedayah tace "Ina yini" Bai ce komai ba, Mami ce ta sakko tace "Shuraim" ya daga kai yace "Ina wuni" tace "Lafiya lau, ya aiki" yace "Alhmdllh, kaka ta bada a kawo maki" Mami tace "Toh nagode kuwa, Allah ubangiji ya basu xaman lafiya su kuma amaren" Yace "Ameen" Mami ta kalli Farida tace "Ki kawo masa abinci" ya mike yace "Aiki xan wuce ynxu, daga can gidan nake shine ta bani in taho maki da shi" Mami tace "Kai kullum kana da excuse one way or the other idan aka ce a xubo maka abinci Shuraim, Farida bring him the food idan kin kawo kar ya ci ya wuce" Daga haka Mami ta wuce sama, Farida ta mike ta wuce kitchen, murmushi ya d'an yi ya koma ya xauna, Heedayah dai sai juya abincin gabanta take ko da wasa ta ki yrda ta kalli direction dinsa.... Can ta mike ta dau plate din abincin ta wuce kitchen, a saman tray Farida ta daura abincin da spoon sae drink da glass cup, ta xuba veggies din a wani bowl duk a kan tray din, farida na kallon Heedayah rike da tray din abincin tace "Kinsan bana son Shuraim din nan kwata kwata Didi, amma Ina son uniform din jikinsa, wllh Ina bala'in son uniform din, suna masa shegen kyau sosai, may be because he is a kind of huge, kuma baya