Showing 228001 words to 231000 words out of 275313 words

Chapter 77 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

sanyin murya yace "Are they afraid of me??" Heedayah na kallonsa tace "No they are not, why will they be? Kawai suna tausayin ka ne sosai" Ya girgixa mata kai yace "No they are..." Da mayafin jikinta ta shiga goge masa idonsa tace "Aa, ba tsoron ka suke ba, duka suna tausayin ka ne, they are feeling your pain" Shiru yyi yana kallonta, ta sakar masa murmushin karfin hali, Ya sauke idonsa cikin raunin murya yace "Yanxu Mami ce mahaifiyata??" Wani murmushin ta kuma yi masa ta gyada masa kai tana kokarin boye nata hawayen tace "I am glad you are reuniting with ur family, even though basu sanka ba baka san su ba, they are all very happy to have you back in there mist" Kamo hannunta yyi yace "Meeting with you is something I will never forget till death Heedayah, ban taimake ki shekarun baya don in sake haduwa dake ba...." Murmushi kawai Heedayah ke yi tace "Destiny... Allah ya riga da ya rubuta ta dalilin ka xan hadu da iyayena kai ma kuma ta dalilina xaka yi reuniting da family dinka" Murmushin yyi shi ma yana gyada mata kai, har ranta taji dadin murmushin da yyi, lkci daya kuma ta ga murmushin yyi fading, a hankali tace "Are you okay?" Ya sauke idonsa yace "You know what?" Ta girgixa masa kai, yace "Ina tsoron kada family din ki su rabamu after knowing who i am" a sanyaye tace "No one is separating us in sha Allah" ya girgixa kai yace "Bbu wanda xai so 'yar sa tayi mu'amala da thug..." Da damuwa tace "You are not a thug, in sha Allah babu kai bbu mutanen nan daga yanxu..." Shiru yyi yana kallonta, tace "Yes, you have nothing to do with them, and justice shall prevail...." Bude kofar ward din aka yi duk suka juya Shuraim ya shigo da sallama... Kallo daya yyi masu ya dauke kai, ya karaso ciki ya ajiye ledan hannunsa, ya kalli Khaleel dake kallonsa yace "How are you feeling now" Khaleel yace "Alhmdllh na ji sauki" Shuraim yace "Allah ya kara lafiya" Khaleel ya amsa da "Ameen, thank you" Heedayah ta d'an kalli Shuraim tace "Ina yini ya Shureen" ba tare da ya kalleta ba yace "Lafiya" Kallon Khaleel yyi yace "Allah ya sauwake xan koma, later Dr xai yi discharging din ku" Khaleel yace "Toh nagode kwarai" Kofa Shuraim ya nufa Heedayah ta bi sa da kallo har ya fita, Kallon Khaleel dake kallonta tayi, ta d'an yi murmushi ta nufi ledan da Shuraim ya kawo taga gasasshen kaza ne sai tiriri yake, ta kalli Khaleel tace "In dibar maka?" Khaleel yace "Aa na ci abinci yanxu" plate ta dauka xa ta diba tace "Toh ni xan ci" Bai ce mata komai ba har ta gama diba ta juyo, still taga yana kallonta, a hankali yace "Ina son maki tambaya Heedayah" Tace "Ina ji" yace "Tell me, meye tsakanin ku da Shuraim din nan?" Heedayah tace "Nothing, kawai dai Abbansa guardian dina ne, and I was raised in there hope after parting with my parent" Khaleel yace "Amma kin san yana son ki?" Shiru Heedayah tayi tana kallonsa, can tace "So na kamar yaya kenan" Khaleel bai kuma ce mata komai ba, Junaid ya shigo ward din Mami na biye da shi. Karfe uku na yamma aka yi discharging Khaleel daga hospital, mota daya suka shiga tare da Junaid da Zayyad, Mami da Heedayah da wata sisters din Mami biyu da suka xo daga gombe suka shiga motar Mami... Junaid na xaune gefen gado a bedro dinsa yana kallon Khaleel da yaga kamar ko magana me yawa bai son yi, duk abinda junaid xai ce masa a takaice yake amsawa kuma baya kallonsa, ganin ya gama buttoning din shirt dinsa Junaid ya mike yana nuna masa turarurrukansa dake gaban mirror, ba musu Khaleel ya nufi gun turaren ya dau daya ya fesa snn ya juyo yana kallon junaid, junaid yayi masa murmushi yace "kayi kyau" Khaleel ya sauke manyan idonsa cikin sanyin murya yace "Thank you Bro" Mikewa Junaid yyi yace "Ana jiran ka...." Daga haka ya nufi kofa, Khaleel ya bi bayansa suka fita dakin, Heedayah ta bude kofar dakinsu kenan ganinsu ta tsaya, Khaleel bai yrda ya kalleta ba ya fara sauka stairs ta bi sa da kallo, Junaid ya juya ya kalleta ta dauke kanta da sauri, Tsaye Khaleel yyi bakin stairs yana kallon mutanen dake xaune parlon, Ganin junaid ya karasa cikin parlon ya bi bayansa walking slowly, nan saman carpet duk suka xauna, Mami sai kallon Khaleel take tana kokarin ganin hawaye bai sakko mata, Khaleel ya gaida mutanen dake parlon gaba daya cikin sanyin murya, ko wannensu dai kallonsa yake, Mami ta nuna masa wasu dattijai mata biyu a hankali tace "Ur aunties, kannin mahaifin ka kenan..." Khaleel ya kallesu amma ya kasa cewa komai, hawaye suke suma suna kallonsa, Mami ta nuna masa uncles dinsa, snn ta nuna masa sisters dinta biyu, ta nuna masa duk cousin dinsa dake parlon su ma, bbu wanda baya goge hawaye a parlon, Khaleel dai ya kasa cewa komai sai bin su yake da ido lkci daya shi ma hawayen ya kawo idonsa, Mami ta goge hawayen dake xubo mata ta nuna masa su Dinar tace "Ur sisters, sauran aunties dinka da uncle suna hanya" mikewa Farida tayi ta karasa kusa da shi ta rungumesa ta fashe da kukan dake cin ta cikin rawan murya tace "I am happy meeting with you big bro, Alhmdllh for reuniting with us..." Khaleel was just short of words, he can't believe all this are his families, bai ta6a tunanin yana da su a duniya ba balle su hadu watarana, sai yake ganin abun kamar a mafarki xai iya farkawa a ko da yaushe, Dinar da Amira ma kukan suke suna kallon Khaleel, Khaleel ya dafa Farida cikin sanyin murya yace "I am happy meeting with you too sis"

*Sorry for the late update, mu hadu gobe da noon in sha Allah*



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Mami na xaune compound din gidan ta tare da Abba da wata colleague dinsu, Abba yace "So now how do we go about it??" Barrister Khadijah tace "Kun san inda matsalar take ynxu?" Abba na kallonta yace "Aa sai kin fada" tace "An tafi station da shi Khaleel din tun farko, a can kuma yyi denying he isn't a Kidnapper so did Barrister Rahinah, so ynxu idan aka kai maganar station to get all the thugs arrested, first tambayar da xai fara biyowa shine... Khaleel isn't a Kidnapper how did he know that they are?" Shiru duk su Abba suka yi suka yi suna kallonta, Barrister Khadijah tace "The matter is so complicated..." Abba yyi murmushi yace "Noo, it's not Barrister, bbu complications.. Of course Khaleel wasn't a Kidnapper amma a cikinsu yake, a cikinsu kuma ya rayu ta dalilin rabasa da suka yi da iyayensa suka kai sa cikin nasu, don haka bai san kowa ba sai su, his being in their midst ba shine ke bada tabbacin yana harkan da suke ba... Baya tare da su a mugun abinda suke aikatawa, kuma sbda baya taren da su ma yasa xai tona masu asiri, ai a case din nan baxa mu nuna we have anything to do with Khaleel ba, baxa mu nuna akwai wani alaka tsakaninmu da shi ba, we will act as though he is a stranger...." Barrister Khadijah tayi murmushi tace "What if the Kidnappers have enough proof that will look as though he worked with them? That aside we need to think deep su ma dubarunsu yawa ne da shi, they can blackmail him just as they did few days ago....." Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "And ku bar cewa he wasn't a Kidnapper, he was, kuma kamar yanda Barrister ta fada baxa a rasa proofs din ba, may be images or videos of him a tare da su, tunda ai a da yana tare da su har ma yana contributing" Barrister Khadijah tace "Definitely kenan dole sai an tafi da evidence din baya tare da su police station before their arrest...." Abba yace "Exactly, and this evidence just have to come from Khaleel, a cikin evidence din kuma dole cikin 100% ya wanke kansa da kansa ko da 70% ne, sai ya bar mu da sauran struggles din wankesa...." Mami ta girgixa kai tace "Duk da haka Khaleel me laifi ne sosai a wajen hukuma, da ya tashi ya gansa cikin hoodlums abinda ya kamata yyi shine ya jawo hankalin hukuma tun farko, idan kuma baxai yi hakan ba sai ya bar cikinsu kawai...." Abba yace "But did you listen attentively to his story yesterday Rahinah?" Shiru Mami tayi tana kallonsa, Abba yace "on several occasions yayi yunkurin guduwa daga cikinsu, amma bayan kwana biyu sai kuma ya ga ya koma cikinsu, yana kuma jin kamar idan bbu su baxai iya rayuwa ba... Did you listen to that?" Mami ta kasa cewa komai, Barrister Khadijah na gyada kanta tace "Asiri gaskiya ne" Abba yace "Toh don haka mu baxa mu ga laifinsa ta nan ba unlike hukuma, yanxu abinda xai faru kawai evidence xai fito daga Khaleel, I will talk to him about it now, later in the evening kuma xa mu hadu" a sanyaye Mami tace "Toh Allah ya kai mu, Shuraim ya koma ne?" Abba yace "Jiya ya koma" Mami tace "Toh Allah ya tsare sa" Abba yace "Ameen, I sent you text daxu baki yi replying ba" Mami tace "Oh, I wanted calling you in maka bayani ne, baki sun yi yawa ne a gidan wllh" Abba yace "Ohk" Mami tace "I spoke to him about it this morning, sai yace min a daga xuwa wani lkci har a gama wnn case din" Abba yace "That's thoughtful of him, Allah ya kai mu, is he inside?" Mami tace "Ehh yana ciki" Abba yace "Alright then, xan koma great barristers sai mun hadu da yamman, but before then idan kun shiga ciki ku turo min Khaleel din" Mami tace "Toh shkkn I will" Bude gate aka yi duk suka juya, Mumy ce ta shigo tare da tawagarta har da Salima, ganinsu Abba ta karasa da fara'a inda suke zaune, Mami na kallonsu tace "Sannun ku da xuwa" Gaisawa suka yi, Su Sadiya da Baturiya suka gaida barrister ya amsa yana danna wayarsa, Mumy tayi kasa da murya tace "Ashe abinda ya faru kenan Hajiya Rahinah? Toh Allah ubangiji ya tsare iya haka, Allah ya rabamu da mugun ji ko mugun gani, muna taya ki murnan dawowan dan ki bayan shekaru masu yawa..." Mami tace "Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bada lada" Mami ta mike tare da barrister Khadijah suka yi ma Abba sallama suka wuce ciki tare da su Mumy da kawayenta. Mumy sai kallon Khaleel da ya shigo parlon ya gaishesu take, bai kara second daya a wajen ba ya fita daga parlon xuwa wajen Abba dake jiransa a waje, Mumy tayi tagumi tace "Allah sarki rayuwa, gashi mu bamu ta6a sanin kina da d'a namiji ba ma balle, da yake babu hakki sai gashi bayan an cire rai, toh Allah ya bar mu da 'ya yanmu dai har mutuwa" Mami dake parlon da su Hajiya Zuwaira da step mum din Sudais dai bata tanka ta ba, Mumy tace "Toh an samu an sa ranan Junaid din kuwa? Don barrister ba gaya min xai yi ba wllh" Mami tace "Tukunna dai" Mumy ta d'an saci kallon Sadiya basu dai ce komai ba. Khaleel ya xauna saman kujeran dake facing Abba ya gaishesa, Abba ya amsa da murmushi yace "Ya karfin jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh na ji sauki" Abba yace "Toh maa sha Allah, Allah ya kara lafiya" Cikin few minutes Abba ya gama magana da Khaleel ya gaya masa duk yanda xa a yi snn suka yi sallama ya wuce, Khaleel ya koma ciki yana kara naxarin abinda Abba yace masa. Da yamma misalin karfe biyar Khaleel ya nufi kofar fita parlor bayan ya sallami Mami, sai da ya kusa kofar Mami tace "Be careful.... and pray, Allah ya tsare ka" juyowa yyi yace "In sha Allah...." a hankali Dinar tace "Allah ya tsare" Bai juyo ba yace "Ameen" Heedayah dake xaune dinning ita da Farida suka bi sa da ido su ma, kasa daurewa Heedayah tayi ta mike ta bi bayansa, babu wanda yace mata komai har ta fita parlon, parking space ta ga ya nufa, tace "Ya Khaleel" ya juyo ganinta ya tsaya, ta karasa inda yake da damuwa tace "Where are you going to?" Murmushi ya mata yace "Xan fita ne, anjima xan dawo in sha Allah" tace "Xaka fita xuwa ina? Kana son su ganka ne kuma?" Yace "Aa ba inda xa su gan ni xan je ba" tace "Toh xan bi ka, should I go and tell Mami?" Yace "No" ta marairaice tace "Plss mana, I don't want anything to happen to you" yace "Nothing will happen to me Heedayah" shiru tayi tana kallonsa, yace "To rakani gun motar sai ki koma ciki and pray for me" a sanyaye tace "In sha Allah" Murmushin sa me kyau yyi mata, tace "Da motar yaya xaka fita?" Yana tafiya tana biye da shi yace "Ehh" Ta madubi Junaid dake warming din motar tasa ma yayansa yake kallonsu har suka iso, sai a snn Heedayah ta gansa, ta wara ido tace "Lahh ashe kana nan Yaya" yace "Ina nan" Fitowa Junaid yyi daga cikin motar yana kallon Khaleel, Khaleel ya shiga motar, Junaid yace "Allah ya tsare" Khaleel ya amsa da "Ameen, Thank you" sai da Khaleel ya fito daga parking space Mai gadi ya bude masa gate snn Heedayah ta daga masa hannu a hankali, ya gyada mata kai, bayan ya fita compound din suka koma cikin gida tare da Junaid tana kallonsa suna dai dai entrance din shiga parlon tace "Yaya wai me kke shafawa a lips din ka?" Yace "Abinda kike shafawa a naki" dariya tayi yyi murmushi ya bude kofar ya shiga ta bi bayansa. Har Khaleel ya isa gidan oganninsu yana communicating da Zayyad ta text message, yyi parking a waje yyi deleting duk messages din snn ya nufi gate ya fiddo da spare key dinsa na gidan ya bude ya shiga ciki, direct entrance din shiga babban parlon ya nufa ya bude kofar parlon, duk suna xaxxaune parlon, wasun su na karta, ga giya ko wannensu na sha a glass cup, wasu kuma na smoking cigarette kida na tashi a speaker, Zayyad dake xaune saman kujera shi ma hannunsa rike da cigarette ya dinga kallon Khaleel kamar yanda duk sauran mutanen parlon ke kallonsa, Oga Bala ya kyakyace da wani mahaukacin dariya yace "I told you all a xuba masa ido xai dawo, to gashi ya dawo..." Wani dariya Oga Arne ya fashe da shi ma yana kallon Khaleel da kyau yace "Da ina ka tafi? Ka xata har karshen rayuwarka xaka iya rabuwa da mu ne? Ko dama kana da wasu a duniyar nan bayan mu? Ni in particular...." Xaunawa Khaleel yyi saman kujera yana kallonsu gaba daya, Oga Manga yace "Ka saduda ka gama boye boyen kanka ka dawo kenan? Lallaba ka da ake ya fara wuce gona da iri, xa mu dau mummunan mataki a kan ka wllh" Oga Bala ya nufi Khaleel ya dago kansa yana kallonsa da jajayen idonsa cikin katon muryarsa yace "Ka dawo daga raina mana hankalin da kke?" Calmly Khaleel yace "Ehh" Oga Arne yace "Good... akwai operation a Abuja, dawowar ka kawai muke anticipating kuma gashi ka dawo, so we are setting off today...." Khaleel ya girgixa kai yace "U are mistaken then...." Lkci daya ya mike yana kallonsu gaba daya fuskarsa a tamke yace "Na xo ne in sanar maku cewar daga yau na bar wnn mummunan harka da ku ka dulmiyar da ni a ciki tun ina d'an yaro, na bar wnn harka da ku ka cusa min a xuciya ba da son raina ba, snn Arne, Manga da Bala I want you all to put this at the back of ur mind that... in sha Allah karshen ku ya xo... Sannan kananun kwarin da ke tare da ku su biyo baya...." Tashi Oga Arne yyi yana masa wani kallo cikin tsawa yace "How dare you Khaleel? Mu kake ma magana haka? Mu kake kira ma karshe??" Khaleel yace "Eh kai, Manga da Bala...." Manga ya mike a fusace ya nufesa ya shakosa da karfi yace "A duniyar nan kana da sama da mu ne kake ikirarin xaka ga karshen mu? Har kai kana da gata a duniyar nan banda wajen mu, uban me kake takama da shi, dama tsintacciyar mage bata mage, an kawo ka cikinmu kana da shekara uku baka da gata baka da kowa haka muka ja ka jiki muka fifitaka fiye da kowa, muka jajirce wajen ganin an bar ka kai daya tak kayi boko a cikinmu, Wani hakuri ne ba mu yi da kai ba a shekaru talatin din da suka wuce, fita operation da kai sai ka bata ma kowa rai sau tari kayi spoil din mana show don ma kana yi kana shakka, bindigar da aka mallaka maka ba shi da amfanin da aka baka yyi maka sai na harbin Iska, sau nawa kake freeing abducted or kidnapped victims dinmu ka ja mana uban asara, sau nawa sbda kai asirinmu ke kusa tonuwa sai dai ka fitar da mu da kwakwalwarka, amma duk da haka muna ta tausan oganninmu sbda ba kowa Allah ke ba wa ba intelligence din ka ba, da ba don Arne ba da Oga Salahu ya dde da harbe ka har lahira shekaru goma da suka wuce, bayan ka ba wata yar minister da muka yi kidnapping damar guduwa wanda hakan ya kusa tona mana asiri muka shiga gararin rayuwa, ta dalilin ka sai da marigayi Oga salahu ya harbe Arne a kafa wanda har yau Arne yana samun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login