Showing 30001 words to 33000 words out of 275313 words

Chapter 11 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

ki" rungume hannunta tayi ta jingina da motar ta ki cewa komai wai tayi fushi, bai kuma ce mata komai ba har suka isa gida, Mai gadi ya bude masa gate ya shiga yyi parking, fitowa yyi ya xaga ya bude side dinta yace "To na ji ke mace ce, sakko" ta turo baki xata sakko ya dagata ya fito da ita, tace "It is going to rain" kallon sky yyi yace "How did you know?" Tace "Ina jin kamshi" ya kalleta da kyau ya sake kallon sama, da hadari amma ba sosai ba, ya kama hannunta suka nufi cikin gidan, tare ya tafi dakin Mami da ita ya dau system din ya kamo hannunta suka fita, tana bin sa a hankali tace "I want to take tea" Yace "Me yasa baki gaya ma Mami a can gida ba" tace "Tace baxata sake bani tea ba" downstairs ya sakko da ita ya xaunar da ita saman kujera yace "Wait for me" ya ajiye system din hannunsa ya wuce kitchen ya kunna gas ya sa mata ruwan tea, Yana tsaye kitchen din yana jiran ruwan shayin ya tafasa aka fara iska sosai, muryar Heedayah ya ji with all her strength tace "Where are youuu" ya kashe gas din ya fito, tsaye ya ganta duk a tsorace, ya karasa inda take yace "I'm here" ta kamo hannunsa tace "Kar ka bar ni, ina jin tsoro" tana rike da shi ya tafi ya kulle duk windows din gidan har upstairs, lkci daya aka fara ruwa sosai, ya duka dai dai fuskarta jin kamar magana take yi yace "What?" Tace "I told you I smelt rain" d'an murmushi kawai yyi yana tunanin baiwa ne kilan nata, downstairs suka koma ya xaunar da ita saman kujera yace "Let me make the tea for you" da sauri tace "Noo, kar ka bar ni, ka tafi da ni plss" tare ya koma kitchen din da ita, tana makale jikinsa har ya hada mata shayin sannan suka dawo parlor, ya ajiye shayin saman center table yace "Ki jira ya huce" bata yarda ta xauna ba sai da ta tabbatar kusa da shi ne, ta jinginar da kanta shoulder dinsa tayi shiru, ya dau wayarsa ya haske fitila don tuni aka dauke wuta da ake iska, missed calls na Mami ya gani guda hudu, yayi dialing number ya kai kunne, yana fara ring ta dauka, a fusace tace "Junaid da ku ke tafiya baka ga hadari bane, me yasa baka dawo min da yarinyar ba??" Yace "Mami ni ban lura ba sai da muka iso nan gida" Mami tace "Where is she now?" Ya haska fuskar Heedayah ya ga idonta a lumshe, ya mayar da wayar kunnensa yace "She's sleeping" Mami tace "I don't care ko kana tuki cikin ruwa ko baka yi, just in the next 20 mins ina son ka dawo min da ita, I don't want to call you back after this" daga haka ta katse wayarta, kallon Heedayah ya sake yi xai kwantar da ita ya duba karfin ruwan da ake a waje ta bude ido da sauri ta rikesa cikin muryar kuka tace "Noo where are you going" yace "Ba Inda xanje kiyi baccin ki" kin sakesa tayi, ya koma ya xauna, ta kwanta jikinsa, Yana ta xaune parlon ita kuma tana ta bacci, har kusan karfe shidda, har sannan kuma ruwan ko raguwa bai yi ba sai ma karuwa, idan akwai abinda bai iya ba a rayuwa to driving ne cikin ruwa, sarai kuma Mami ta san hakan, duk motsin da xai yi Heedayah sai ta kara makale masa, bayan wani lkci ya haska fitilar wayarsa a fuskarta yaga fararen idonta a bude, duk tunaninsa bacci take, yace "Kin tashi?" A hankali tace "Idan nayi bacci xaka wuce ka bar ni ni kadai" Ya kwantar da ita jikinsa sosai yace "Noo baxan tafi in bar ki ba yi baccin ki" sai bayan Magrib ruwan ya tsagaita yana son yaje yyi sllh Heedayah ta ki sake sa duk da har sannan bata koma bacci ba, haka ya wuce dakinsa da ita yyi alwalan a can sannan yayi sllh suka fito tare, tace "Where is my tea?" Gaba daya ya manta da shayin dake kan center table, yace "let me make another one, wannan yyi sanyi" cikin few minutes ya hada mata wani shayin amma ba mai xafi ba, suka koma parlon ya xaunar da ita ya kai mata cup din baki, ta rike ta fara sha.... Tana gama shan shayin ya dau makullin motarsa yana rike da ita da system din Mami suka fita gidan, ya kulle gidan sannan ya nufi motarsa, sosai garin yyi sanyi, ya bude front seat ya xaunar da ita bayan ya ajiye system din a baya, ya xaga ya shiga motar suka bar gidan, dai dai kofar gidan Abba yyi parking, nan gabansa ya fara faduwa don yasan Mami won't take it likely with him this night, ya dai fito ya xaga ya bude ma Heedayah side dinta, ta laluba ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "Ina jin sanyi" ya saukar da ita yace "We are home" dai dai bakin gate suka hadu da Shuraim xai fito, Junaid na kallonsa ya sake hannun Heedayah ya basa hannu, Shuraim ya amsa yana kallon Heedayah daga sama har kasa, suka gaisa da Junaid, Shuraim xai fita Junaid yace "Ehm naga it's late already, pls can you go in with her, ina d'an sauri ne" Shuraim ya sake kallon Heedayah sannan ya kalli Junaid yace "Alright" Junaid yace "Thanks" daga haka yyi patting kan Heedayah ya sa hannunta cikin na shuraim yace "Ki gaida Mami, xan kawo mata laptop din gobe" juyawa yyi ya fita gate din ya nufi motarsa, Heedayah ta 6ata fuska xata yi kuka jin Junaid ya wuce ya bar ta, Shuraim dake ta tsaye Heedayah na rike da hannunsa gam, ya saci kallon motar Junaid ganin har yyi reverse ya xame hannunsa daga nata yayi wucewarsa masallaci, Heedayah dai na ta tsaye ga sanyi da take ji sosai sai juye juyen idonta take gwanin tausayi, Mai gadi ne ya fito daga dakinsa alamar shi ma xai wuce masallaci don yin Isha ganinta yace "Me kike yi a nan yarinya, ki shiga ciki mana" Cikin rawar murya tace "Bana gani ai" yace "Bakya gani kuma?" Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya cika idonta, kama hannunta Mai gadin yyi ya fara tafiya xuwa entrance din shiga gidan yaga tana bin sa a hankali, lkci daya jikinsa yyi sanyi, yace "To wa ya ajiye ki bakin kofa?" Tace "Sake ni yyi ya wuce ya bar ni" dai dai kofa suka hadu da Abba, Abba na kallonsu yace "Wa ya dawo da ke Heedayah?" Tace "Ban san sunansa ba" Kama hannunta Abba yyi ya wuce part din Mami da ita, Mami ta mike ganinsu, Bai ce ma Mami komai ba ya sake hannunta ya juya ya fita, kana ganinsa kasan he is angry and don't want to talk. Mami ta kamo hannun Heedayah tace "Ina Junaid din?" Heedayah tace "Ya wuce" Mami bata ce komai ba ta wuce daki da ita. Sai kusan sha daya na daren Mami ta tafi bangaren Abba bayan Heedayah tayi bacci, xaunawa tayi kusa da kujeran da yake xaune tace "I'm truly sorry barrister, hakan baxai kara faruwa ba in sha Allah, nasan you are not happy" Yace "It's okay, but pls ki sa ido a kan wnn yarinya fisabilillah, don't expose her much to anybody, let her be home all through, kin san condition dinta, tana bukatan kulawa sosai Rahinah, ina jin yarinyar nan tamkar jinina bana fatan wani abu ya sameta....." Mami tace "In sha Allah" yace "Yaushe Farida xata dawo?" Tace "Ranan laraba" yace "Alright, na sa a nema ma Heedayah lesson teacher soon, Shuraim kuma xai dinga mata karatun qur'ani da asuba na gaya masa, so after prayer kar ki bari ta koma bacci...." Mami ta kallesa sai dai bata ce komai ba... Dai dai wnn lokacin kuma Mumy na dakinta ta shige can cikin bathroom tana ta waya kasa kasa, Mumy tace "Kai ni har na gaji da bayani har yanxu baka fahimta ba, ce maka nayi makauniya ce fa yarinyar, kuma dududu Rabi'ah ta ma ta girmeta ina ga, yar yarinya ce fa sosai, bata wuce sha biyu ba ma kila...." Dariya sosai wanda take wayan da yyi yace "Haba Hajiya, to meye kuma xaki daga hankali kan yar yarinya? Ni wllh na xata ma kishiyar ce kike...." A fusace Mumy tace "To kai ina ruwanka? ba dai kudin ka kawai ka sani ba, ni fa na riga da na gama magana da kusan mutane uku, kawai raba kafa nake ta yi ta ko ina shi sa na kira ka ba wai wani abu ba don kai ka fiye shiririta, ina ruwanka da kankantan yarinyar?? kaga.... idan har ka shirya kaga xaka iya sai ka kirani gobe da safe ni kwanciya xan je inyi..." Tana kai wa nan ta kashe wayar ta fice daga bandakin ta kwanta kan gadonta tana fata ta samu bacci ko xata ji saukin xafin da ranta ke mata, rabonta da baccin kirki tun ranan da ta dawo kaduna. Da asuba Shuraim na dawowa masallaci ya shiga parlon Abbansa don gaishesa don kusan tare suka dawo masallacin, Abba dake hada wasu files ya amsa ba tare da ya kallesa ba yace "Yau xa ku fara karatun da Heedayah koh?" Shiru Shuraim yyi da farko, yana mamakin why all of a sudden Abba xai fi karkata hankalinsa gaba daya kan makauniyar nan, Bai ma ce suyi har da su Rabi'ah ba wai Heedayah, jin shiru Abba ya juya ya kallesa, Shuraim yace "Sure in sha Allah" Abba yace "Good, a can parlon Aunt dinka xaku dinga yin karatun" shiru ya kuma yi na kusan second goma sannan yace "I prefer mu yi a inda nake yi ma su Rabi'ah" Abba yace "Ina kenan?" Yyi kasa da kai yace "Balcony" Abba yace "Noo, akwai sanyi waje, you look for another alternative" mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa ya fita, gaba daya ji yyi ya kara tsanar Heedayah har ransa, WTF, ba don he can't look into his father's eyes and tell him baxai yi ba da bbu abinda xai hanasa yin hakan, ya fi minti biyar tsaye a parlor kafin ya nufi part din Mami ya tsaya ya kwankwasa kofar fuskarsa daure.

For those forwarding this book to various groups bayan sun san na kudi ne, ni baxan ce komai ba, but su yi adalci, it's not fair hakan ba na kyauta bane littafin, na hada su da Allah su yi hakuri su daina hakan ba don ni ba.....

Masu neman complete Heedayah su ma sai su biya dari uku a basu sharp sharp don naga sun ma fi masu subscribing for daily update yawa, idan ba complete bane damasu baxa su biya ba sai dai su karanta a titi yana galantoyi, to ku biya a baku complete, I have change my mind, kawai da evidence din ku xa ku taho sai a baku complete din....🌚🌚🌚


Heedayah na kudi ne, ba kyauta ba, try and subscribe to read happily bbu burden a kanka....

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Mami ta bude kofar parlonta jin ana knocking, suka yi ido hudu da Shuraim, sauke idonsa yyi da sauri, murya can kasa yace "Ina kwana" A takaice tace "Lafiya.... Ya aka yi?" Yace "Karatu xa mu yi?" Mami tace "Da wa?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Ban san sunanta ba" Mami tace "Toh sai kayi kokarin sanin sunan nata coz gida daya ku ke ynxu" daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, Mami ta karasa sa ma Heedayah kayanta don har tayi wanka, ta dau hula ta sa mata a kanta sannan tace "You listen and pay attentive kin ji, Kuma kiyi kokari sosai, idan kin dawo xaki koya min nima" tace "Toh Mami" Mami ta kama hannunta suka fita xuwa parlor, har sannan yana tsaye, dai dai kusa da shi Mami ta tsayar da Heedayah, sannan ta juya ta koma ciki ta kulle kofarta, Heedayah ta kai hannu tana laluba wajen ta ji inda yake, hannunsa ta ta6a, bbu bata lkci kamar jira yake ya buge mata hannun yace "Are you stupid" Ta janye hannunta da sauri kamar xata yi kuka tace "Ni me na maka??" Ya kalli left sannan ya kalli right ya fixgo hannunta ya fara tafiya, bin sa take hawaye cike idonta tace "Ni ka sake ni bana so, baxan yi karatun ba kuma, baxan yi ba...." Ko saurarenta bai yi ba har ya isa wani area cikin parlon wanda ya kasance study area din Abba, sannan ya saketa yana mata wani kallo yace "Kika ce baxa ki yi karatun ba??" Cikin kuka tace "Ehh ni baxan yi ba, ka kai ni wajen Mami" ya ja kujera ya xauna yace "Sai ki kai kanki ai" durkushewa tayi a kasa ta fashe da kuka sosai tace "Ni sai na gaya ka da Abba wllh...." bude kofa aka yi Shuraim ya juya da sauri bai jira ya ga wanda ya bude kofar ba ya xamo kasa kusa da ita ya dake cike da karfin hali yace "Okay, sorry mu yi karatun ynxu" ta make kafada tace "Ban so" satan kallon cikin parlon yyi duk da bai ga wanda ya fito ba har sannan, ya wani hade rai yace "I said sorry" Kamar jira take tace "Ban so nace" sai kuma ta fashe da wani sabon kuka, kamshin turaren Abbansa da ya ji yasa yasan Abba ne a parlon, ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta a hankali yace "But nace kiyi hakuri, I'm sorry" ta turo baki tace "To me yasa xaka buge min hannu sbda bana ganin ka, kuma shine kake ja na don in fadi in ji ciwo" Ya kara satan kallon parlon cikin dakiya yace "To rama" ta kai hannu ta laluba kafarsa sannan ta maka mashi duka a nan, kallonta kawai yake da mamaki xuciyarsa na tafarfasa, still controlling himself yace "Shkkn?" Ta gyada masa kai a hankali tana goge idonta, ya koma saman kujera yace "To fara karatun" tayi kasa da murya ta fara karatun a hankali, har Heedayah ta tsaya a aya na 15 bai ji inda xa ayi mata gyara ba, her recitation was perfect and cool for her age, sai dai wayarsa kawai yake dannawa, Ya saci kallonta ganin tayi shiru sai dai bai ce komai ba still pressing his phone, ta turo baki tace "To ai a nan mu'allimata ta tsaya min" yace "Toh sai ki tsaya a nan din" yana fadin haka ya mike ya tafi kitchen, Sabuwar me aikin da Mumy ta dauka ne a kitchen din tana ta gyare gyare da goge goge, yace "Wancan yarinyar xaki dauka ki kai ta wancan part din..." Gaishesa tayi da ladabi tace "Wace yarinya yallabai?" Fita yyi kitchen din yace "Ki taho ki ganta" sai da ya tabbatar ta ga Heedayah sannan yayi wucewarsa sama, har part din Mami mai aikin ta kai ta, duk da sai faduwa gabanta yake don ba karamin warning Mumy tayi mata ba kan cewa ko bangaren Mami kar ta kuskura ta bi balle ta shiga, Mami ta bude kofa ta amsa gaisuwan mai aikin sannan ta kama hannun Heedayah suka koma ciki ta kulle kofar, Mami na kallon Heedayah tace "Ina me koya maki karatun?" Heedayah tace "Mami bai koya min komai ba" Mami tace "Me yasa?" Heedayah ta 6ata fuska tace "Mami mugu ne, I don't like him to teach me anymore...." Mami dai bata ce komai ba ta wuce can bedroom da ita, Heedayah tace "Mami he is wicked, ni nafi son wannan din nan ya koya min" Mami tace "Wa?" Shiru Heedayah tayi sai kuma tace "Yace min sunansa Fatima shi ma, kilan baya son gaya min sunansa" Mami na kallonta tace "A ina yake?" Heedayah tace "Wanda ya xo jiya ya tafi da ni" Mami tace "Sunansa Junaid, but you call him Yaya" tace "To, na fi son Yaya ya dinga koya min" Mami bata kuma cewa komai ba ta xaunar da ita saman gado tace "Kwanta kiyi baccin ki xan je in hada maki breakfast" daga haka ta fita dakin, Heedayah ta kwanta. Mami na tsaye kitchen su Rabi'ah suka shigo ajiye plates da cups da suka yi breakfast duk suka fice bbu wanda yace mata komai, ta gama dafa Indomie da kwai da shayi da take yi ma Heedayah ta fito kitchen din, a parlor ta tadda Abba alamar he is going out kuma ita yake jira ta fito kitchen, yana kallonta yace "Ina Heedayah, bata gaisheni ba yau" Mami tace "Let me bring her" daga haka ta wuce bangarenta, Duk wannan abun Mumy na ta kai komo parlon kai kace wani abu take yi, Abba dai bai ce mata komai ba don har ranan bata gaishesa bata masa magana a gidan, Yana ta tsaye parlon Shuraim ya fito shi ma xai fita, Abba yace "Yaushe rabon ka je gaida kaka Aliyu?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Abba bana dawowa da wuri ne ynxu" Abba yace "Ohk yau ka je ko da kuwa tsakar dare ka dawo, and you go with Heedayah ita ma ta gaisheta, she is complaining ba a kai ta ba jiya da naje...." Shuraim ya kalli Abba, amma bai ce komai ba, Abba yace "Su Khadijah ma nace idan sun dawo islamiyya su wuce can, so idan ka je sai ku dawo tare gaba daya" Mami ce ta karaso rike da Heedayah, Abba na kallonta ya dafa kanta yace "How are you dear?" Tace "Good morning Abba" yace "Morning Daughter, kun yi karatun yau koh?" Ai ko rufe baki Abba bai yi ba Shuraim ya nufi kofa, Heedayah tace "A'a bai min ba" Abba ya kalli Shuraim da har ya isa kofa cikin tsawa yace "Aliyu" Mumy ta karaso cikin parlon da sauri tace "Ba gane Aliyu ba?? Shi Aliyun malami ne ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login