Showing 108001 words to 111000 words out of 288345 words

Chapter 37 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

730

sana'a ce da zai bar ni ina gantali da sunan girki.
Badariya ke fad'amin a gaban Anty Binta yace bazai iya hanani abunda nake so ba,kamar yadda shima ban taba hanasa abunda yake so ba. daganan sai ya kashe bakin su,Nasan sun yi min abubuwa da Dadama ammh ban rike su a raina ba, Mama har gaban abada matsayin uwa take gareni ina yi mata alheri sai dai bata tab'a karba ba har Atamfofi na taba siyan musu dukkan su Har Hajiyar Dala Mama ta Dawo min dashi tace a Fad'amin ban yi arzikin da zan siya mata zani ta Daura ba.tun kafin Ubana Sidi yasan kudi ta sani bazan Rud'eta da abun duniya ba.
Bana damuwa da mganganunta,Anty Binta dai ta amshe tana fadin nima haka na rika tatsan kaninta abun nasu ma kamar sun haukace Koda yaushe Goggo ke nuna min Ribar Hakuri tabbas kuma nima naga Ribar wannan hakurin da nayi shiyasa nake nuna musu komai ba komai ba ne.
To ni ina naga lokacin biye musu ma..?
Ina da abun yi lokaci na sana'ata ne da ya'ya na,ko D'an nasu da suke takama da shi Fa'iza ta daina ara masa lokacinta yanzu ballatana su.

****

Kiran sunana da Amir yake yi ne ya Dawo dani Daga tunanin da na shiga Firgitgit na sauke Tagumina ina fadin"Uhm me kuke fad'i..?
Amir yace"Umma wannan dogon Tunanin fa..?
Gyara zama nayi ina fadin"Ina tunanin watarana zakayi aure ka kawomin suruka nima"
Sai ya bata rai su Anum suka saka Dariya ya daka musu tsawa Hafsah tace"A"a kyalesu su dara Mallam"
Sai ya yi fushi ya wurgar da Sandar Hannunsa ya wuce fuu ya shige Dakinsu,Na bisa da Dariya Saboda shi yasha fadi'n bazai yi aure ba sai yayi kudi ya kaini Saudiya.
Su Anum na bari suna rubutu kan karamin allon na koma kusa da Hafsah ina fadin"Hafsah inaga fa hostel zaki koma ki fara bincikawa tun yanzu"
Sai ta dakata da abunda take yi ta kalleni tana fadin"Meyasa..?
Mikewa nayi ina fadin"Ba yanzu zaki san dalili ba.Ki dafa ma yaran nan indomie ki? hada da kwai,kuci ni cikina ya cika"
Da Toh ta amsamin tabi ni da kallo tana mamakin meyasa nake wasu abubuwan kwana Biyu haka fa Sa'adatu tace na gayamata zan bar mata sana'ar zobo da Kunin aya nan da Lokaci kad'an,kuma naki cewa komai, bayan haka Ni kaina nasan Hafsat ta fara zargin wani abu ni kuma bazan bari ta fahimci komai ba ko Goggo bata san abunda na Kudura a cikin Raina ba, har gobe ina jin bakinciki da Yayata mariya bata kara takowa inda nake ba sai dai mu had'u a karofi ko in naje gidanta tunda yanzu na samu sake Fita free,to ina ma jiran sa kenan..?
Shi da sai ya yi wata uku bai zo ba,nima ko nake gaban kaina.
ammh indai gidana ne Ya mariya ta daina zuwa tun sanda mai shi ya yi mata iyaka da shi.
Cikin Sati d'aya na gama Had'a kayana waje daya,Ranar ma cewa nayi basai anyi zobon yammah ba, na safe daga daya kare a barsa haka,Da Daddaran nace ma Hafsat gobe zan tafi karofi tare da ita su Anum kuma Gidan Mama zan kai su,mamaki ya sa ta kasa mgana nima ban kara ce mata komai ba Domin ta shiga D'akina taga kayana a had'e waje daya kamar wacce zata tashi,ko zata yi Hijira.
Ni ko da na koma D'aki sai na shiga Tunane tunane na tuna sanda na saka Ahmad a makaranta har barazana Ishaq ya yi min in ina nuna mai iko kan ya'yansa sai ya rabani da su ya kai ma Mama su,niko a lokacin sai nace mai kada yayi gaggawa ya bari Lokacin da zasu koma karkashin kulawan maman?ai ya kusa,
sannan na fad'amai suma ya'ya na ne, sannan komai nayi musu ban fadi ba ni uwace garesu kuma in yana ganin don yace na kula dasu ai baya biyana, balle yace aikin kudi nake yi masa.daga Lokacin bai kara tada mganar ba.
Na kwana sallah da neman zabin Allah duk da zuciyata naso ta karye Saboda in na kallesu bansan yaya zasu ji in yau suka wayi gari bana tare dasu ba sai dai ko bana so lokaci yayi da zan hakura da rayuwa tare da Ishaq kabir karofi.
Allah mai aiko da kaddara a lokacin da yaso washegari da safe su Anum na shirin tafiya makaranta ni kuma ina dakina ina faman jan casbaha ina hawaye,Kirjina yana ta zafi Saboda yanayin da nake ciki naji Hayaniya afalo da Mganganu sama sama,da Sauri na fito da Hijabina sai naga Jamal hankalinsa tashe yara duk sun yi cirko cirko a falo.
Hankali tashe na karisa ina fadin"Lafiya Jamal me ya faru ne..?
Cikin wani irin yanayi yace"Wlh Yaya Ishaq ne EFCC suka kama shi Daga? Wajen aikin su na Abuja. tun jiya yana Hannunsu,Zainab ta kira Mama ta na kuka take fad'amata"
Sai naji na Rude yara ma suka fara tambayan me ya samu daada.
Cikin Tashin Hankali nace"Me yayi..?su waye EFCC..?
Cikin tashin hankali yace"Wata hukuma ce ta federal goverment da ke kula da sace sacen kudad'en gwammatin kasa,To abun dai kamar shiryawa akayi ance wasu miliyoyin kudi ne suka yi batan Dabo a ma'aikan su Yaya ishaq da aka tsannanta Bincike sai aka gano da saka Hannanunsa kudaden suka fita, shine hukumar tazo ta kamasa ance ko ganinsa basu bari an yi ba har yanzu.."
Sai na sulale na zauna kan kujera ina salati Amir ne yabi bayana da Salatin su Anum kuma kuka suka saka suna Kiran sunan Daada cikin kad'uwa nace"Hafsah cire mu su kayan makaranta mu..mu tafi gidan Mama"
Jamal Ahmad ya Dauka yana Lallashi ni kuma sai na koma D'akina na kalli kayana da suke had'e waje d'aya sannan na Maida su gefe a Fili na Furta"Ashe har yanzu Lokaci bai yi ba..?
Shin sai wani Lokaci ne ya Dace na Fara wata Sabuwar rayuwar..?

*Karshen littafi na D'aya*

*Nan na kawo karshen Littafi na D'aya na KANA NAKA,akwai sauran gwagwamarya,ga dai Ishaq a hannun EFCC,ko ya zata kaya..?*
*Ya matsayin aikin sa?Ina kudurin Fa'iza..?Zata tafi ne ko zata sauya ra'ayi..?ya makomar auran Zainab da Ishaq..?tunda da yuyuwar Abuja zata gagareshi shiga wannan karon?ya Mama zata yi..?Ishaq shine duka karfinta,Wani irin Daukaka ce take Bibiyan Fa'iza..?*
*Duka tarin amsoshin ku suna cikin Littafi na biyu da na uku,akan farashi mai sauki regular N500,sai kuma tsarin VIP1000,wannan karon bana son tsarin kati,a turo ta POS, akan wannan acct no din 0552179550 Jamila Umar gt bank,Zamu tafi Hutun sallah,sai bayan sallah in muna Raye zamu dora daga littafi na biyu,ammh in dan kun cika adadin ku na Mutane 250 da suka siya,ni nasan ina da masoya Fa'iza ma nada masoya ku yi Dafifi wajen rakata har border domin jin Abunda zai cigaba da gudana a rayuwarta da Ishaq,Janafty tace ta gode Allah ya hadamu a aljannah Ammen*







*Janafty*




*KNKB2001*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Duka na tattara yaran muka bi Jamal zuwa gidan Mama hankali tashe,Har da Hafsah muka iske gidan cike da mutane,Kawayen mama da su Anty Binta,Anty mahma da sauran makotan abokan arzuka.
Yadda naga Mama na kuka sai da ta karyamin zuciya ni kaina na shiga tashin hankali mai tsanani. na kasa dora wannan sabuwar kaddarar data bullo mana lokaci d'aya a kan mizani. abu d'aya na sani ina da yakana da yakinin na yarda da Allah sannan na aminta garesa kowani tsanani yake,kuma dukkan sauki daga garesa ne.
Sai?ban bi ayarin yan kuka ba. Na koma gefe ina hailala da yi ma Allah kirari da istigifari,domin nema ma Yaya ishaq mafita da salama acikin sabon halin da ya wayi gari acikinsa.
Ganin ba wanda ya tuna da kiran mutanen karofi sai na Dauki wayata na fita daga falon Mama nayi nisa da Hayaniyar mutane,na kira Goggo na shaida mata abunda ke faruwa Allah Sarki dan'uwa rabin jiki sai Goggo ta Rud'e hankalinta ya tashi ta dinga Daukan Salati tana Direwa,mun rabu tace gatanan zuwa bari ta shaida ma su Yaya Isa halin da ake ciki.
Ni da kaina na kira Yaya Asiya na gayamata Halin da ake ciki. itama tana ta salati tana Direwa,kowa in yaji abunda ya faru sai ya tambayi garin yaya..?mu kuma bamu da masaniyar yadda abun ya faru,abu d'aya muka sani ana Tuhumarsa da Batar wasu makudaden kudad'en gwamnati, lamarin akwai d'aga Hankali aciki.
Zuwa yammah gidan Mama ya cika da jama'a yan jaje da masu zuwa kallon abunda ke faruwa suna komawa gefe suna dariya. Da yammah hatta Dangin Mama na yamai sun iso mazan su da matansu har da Hure,itama sai uban kuka take yi ba kiran sunan Allah ballatana Salati.
Goggo ta iso tare da Yaya Isa da Yaya Salisu,basu jima da zuwa ba sai ga Hajiyar Dala ita da megidanta ashe yana gari duka an taru a falon Mama ana faman maida zencen,ni dai ina gefe sanye da Hijabi bazan ce ban yi kuka ba sai dai ban yi kuka na fitar Hayyaci da su mama suka dinga yi ba. ni nafi muka duka lamurana ga ubangijina, yara ma haka suke kuka tun ballatana ganin manya nayi Amir kad'ai ne bai yi kuka ba,sai Hawaye domin shi yazo wajena yana fadin"Umma da gaske yan sanda sun kama Daada.?shikenan bazai Dawo ba..?
Sai na jawosa jikina na share masa hawaye Lokaci d'aya ina fadin"Basu kamasa ba sun dai rikesa suna masa tambayoyi,ka yi ma Daada addu'a da ikon Allah zai jibanci lamarinsa, Sannan ya warware al'umaransa ya Dawo gida lafiya"
Sai ya dagamin kai Daganan bai kara kuka ba. na riga na cusamai yakinin Da sanin Allah komai ya faru sannan garesa ne dukkan wata mafita take.
Mijin Hajiyar Dala babba ne a matakin gidan Soja yasan manyan mutane sosai sai bige bigen waya yake domin nemam makaman zencen,Ammh shuru kake ji har Dare sallah kawai ya fitar da mazan matan mu kuma muka gabatar da tamu acikin gida,
A d'akin Badariya nake yada Saukata in nazo tana kwance sai kuka take yi, su Anty Mahma na bata baki da na idar da sallah ina azkar Lokaci d'aya bakina na motsi ban jirka daga inda nake ba sai da na Daga Hannunwana na rokar ma Yaya Ishaq sauki da salama acikin kaddaransa,na Roki Allah ya kubutar da shi cikin Aminci.
Tare muka shafa addu'an da su Anty mahma ta kalleni tana fadin"Sannu Fa'iza kin fi mu karfin gwiwa,muma bari mu tashi mu yi sallar mu roki Allah sauki kan al'amarin yafi wannan koken koken da muke ta yi"
Nayi yake ban ce komai ba,kamar bazan yi mgana ba ammh kukan Badariya ya Dameni sai na karisa kusa da ita na zauna na Dagota zaune ina Share mata Hawaye ta kalleni nima na kalleni, kafin ta kara saka kuka tana fadin"Anty Fa'iza Yaya ishaq bamu san wani Hali yake ciki ba..Mama nata kuka"
Sai ta fada jikina ni kuma sai na riketa ina Lallashinta har sai da ta samu natsuwa sannan na kalleta ina Fadin"Kuka ba mafita ba ce Badariya.in mun yarda Allah ke da Kaddara sannan shike da sa'a da Aminci to mu mika masa duka Kukan mu, sai ya Dudemu ya share mana Hawaye.Tashi ki yi sallah ki rokar ma yayanki sassauci da warwarewar al'amarinsa,sai kiga da ikonsa komai ya Daidaita"
Da ga alamu mganganuna sun shigeta nan take ko ta mike ta shige Tiolet Halisa na gefe tayi tagumi sai itama ta mike tana fadin"Madallah da wannan Tunatarwa taki Anty Fa'iza.Da su mama ma za'a samu mai Tunasar da su da sun bar wannan kukan sun koma ga Allah"
Anty Mahma tace"Mai dakatar da kukan Mama abu d'aya ne sai in Ishaq din tagani a gabanta kila sai kukanta ya tsaya"
Ni dai ina jin su ban ce komai ba,Dakin na bar musu na fita falo neman su Ahmad,Saboda Halin da gidan ya yini ko abinci ba wanda ya nema ni kuma naga in mu manya ne yaran fa..?sai na shiga kitchen na Dafa musu jallop din taliya na zubo musu ina bin yaran daya bayan D'aya ina ba su suci abinci,ashe Anty Binta na takaice dani,D'an wajen Anty mahma ke kusa da ita na nufesa da karamin Filet din na zubamai ina fadin''Anwar taho kaci abinci..".
Ba zato kawai naji an yi sama da Filet din ya koma ya kife a kasa sai hankalin kowa ya koma kanmu Anty Binta na gani tsaye a kaina Tana faman Huci Idanuwanta sun kala sun yi jajir ta nuna ni da yatsa tana fadin"Acikin wannan halin da muke ciki ke har ta abinci kike..?ina lura dake tun dazu abunda ya faru bai Dameki ba, kamar ma murna kike da Faruwar haka me ake da auran mace irin ki Fa'iza macen kaddara macen da bata san mijinta ba"
Sai na kame a tsaye na kasa mgana sai dai na Sadda kaina kasa Mama ta Dakata da kukanta tana kallona, sai kuma aka rasa me mganar mazan duk suna waje ana ta buge bugen waya domin samun mafita.
Anwar ne yabi taliyar kasa yana ci,Alamun yana jin yunwa wata kawar Mama tace"yara fa najin yunwa, tayi Dubara da ta dafa musu in mu mun hakura saboda tashin hankali,su yara ne basu san komai ba"
Goggo tace"To shi yaro ma me ya sani.?shi dai yaci ya koshi"
Ganin ba'a bata gaskiya ba sai ta fara Borin kunya tana fadin"ku fa ganta wlh ko Damuwa ma batayi ba.kamar cewa ma take gwara da akayi hakan"
Goggo ce ta shigar min cikin bacin rai tace"Assha.Haba Binta ta ya ya mijin ta uban ya'yanta na cikin wannan Halin kice bata damu ba..?ai ba kowacce damuwace ke nuna kanta ba, in mu muna nuna Damuwar da kuka ita sai ta fimu hankali ta nuna Damuwarta wajen Ubangijin komai da komai, kinga kenan tafi mu Dubara mai kyau"
Sai aka fara fadin haka ne kuwa a wajen,ba'a bata gaskiya ba. ganin bata samu nasaran tozartani ba sai ta kalleni a wulakance ta juya ta tafi ni kuma sai na Dauki Anwar na tafi da shi domin na zuba mai wani abincin na basa yaci kada a Dauki alhakin karamin yaro da yunwa.
Har dare ba wata mgana mai Dadi,Domin har alokacin mahaifin zainab yace basu bari an ga Yaya Ishaq ba, duk mazan nan suka kwana da Safe kuma suka hadu suka Dauki Hanyar Abuja har da mijin Hajiyar Dala da shi a Hotel ya kwana da Safe da shi da Tawagansa suka Dauki Hanyar Abuja.
Nan kuma Yaya isa da su Jamal da Kawun Mama dake yamai da suka iso jiya,suka tafi tun a hanya ake ta kiransu sukace basu isa ba,bayan kuma sun isa sai suka daina Daukan wayoyin mutane hankula suka kara tashi Sai Dare sannan Hajiyar Dala tayi waya da megidanta yace shi ya wuce kano ma ammh yana ta kokarinsa abu ne da ya had'a da Gwammati, sunce zasu Tuhumesa ne kuma har Lokacin basu bari an gansa ba.
Wannan labarin ya kara Tada Hankula cikin kwana Biyu ba'ayi barci cikin salama ba,Yaya Asiya tazo jaje ita da ya'yan Goggo na Karofi har da Yaya mariya nima makotana duk sun zo,yimin jaje abun duniya baya boyuwa Tuni mgana ta bazu a gari,Mutane na maau saran Zobo da kunin aya a wajena suna ta kirana bani da sukuni ga masu son Turaren kamshi har da masu biki na abinci, bani da sukuni hakuri nayi ta bama Mutane ina gaya musu halin da nake ciki na Mijina na Hannun masu Binciken Gwamnati a abuja.
Goggo tunda tazo bata koma ba tana tare da Mama tana bata baki Hajiyar Dala data kwana biyu sai ta koma cikin kwana Biyar mama ta fita Hayyacinta su Anty Binta sun gaji da kukan sun hakura, Tuni wadanda sukaje Abuja sun dawo labarin bai Sauya ba, sai dai sun tabbatar da cewa Mahaifin zainab na iya bakin kokarinsa haka ma Mijin Hajiyar Dala ana ta shiga da fita.
Ganin sai zama haka kawai muke yi,Sai nayi tunanin gwara na tattara yara mu koma gida mu cigaba da gayama Allah,tunda ko mun zauna anan gidan abunda Allah ya tsara shi zai faru kuma bamu isa mu sauya masa kaddara ba, sai dai in muna addu'a sai kaddarar tazo masa saukakkiya.
Kwanan mu shida da Safe na samu Mama a dakinta ita da yan'uwanta na yamai bayan na duka na gaisheta ta amsa muryanta a shake kaina na kasa nace mata zan kwashe yara zamu koma gida, sai kawai tayi shuru batayi mgana ba,Hure na gefe sai ta tabe baki kafin tace"Ai ba sai kin gayamata ba ki yi gaban kanki kawai.Ai Anty ita ke da rashi saboda ita ke da D'a"
Baki da asara ko da an rasa Ishaq"
Sai mganganu ya fara tashi a tsakaninsu Mama ce ta katse da fadin"ku kyaleta ta tafi.."
Muryanta a shake ni kuma ganin haka sai na sanyaya murya ina fadin"Mama naga zaman bai da amfani ne ga d'awainiya gwara mu koma gida sannan ga makarantarsu duk ya tsaya zamu cigaba da gayama Allah a duk inda muke da ikonsa komai zai warware"
Wani kallo Mama tayi min kafin tayi tari ana mata sannu sai ta kara kallo kafin tace"Na dad'e da sanin baki da asara a komai Fa'iza, ki yi tafiyarki Domin zamanki bai da amfani ammh ki bar masa ya'yansa anan su d'in Dolensa ne saboda Mahaifin su ne, in suka rasa sa bazasu taba samun madadinsa ba"
Daga haka sai ta koma ta juyar da kanta tana share hawaye, jin abunda ta fada yasa na tashi na fita ni ba haka ne nufi ba ganin ta min gurguwan fahimta sai na fasa gudurina.
Goggo na sama na gayama yadda muka yi da Mama sai ta Dafa kafadata kafin tace"Da kin nemi shawara ta da baki yi mata mgana ba,me neman kuka ne fa aka jefe shi da kashin awaki.Ki rabu da ita ki zauna din har muga abunda Allah zai yi"
Tun da Goggo ta fad'amin haka sai na bar mganar Tafiyar ashe na gudu ban tsira ba mgana ta ding yawo tsakanin Dangin Mama da kawayenta Anty Binta Kirkiri a gabana tace Daman ban damu ba so nake nakoma gida na cigaba da sana'ata tunda shine a gabana,naji haushin wannan mganarta kuma ban kyaleta ba sai da na kalleta ido cikin ido sannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login