Showing 192001 words to 195000 words out of 288345 words

Chapter 65 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

738

d'aya ina kokarin bama kaina karfin gwiwa.
Acikin zuciyata kuma ina maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel domin samun karfin gwiwa,Nan take Direba ya juya muka koma.
Ban kara yadda na zauna haka ba saboda kada zuciyata ta kara raunana muna tafe ina salati da Hailala acikin raina,sai dai kuma kukana ya kasa tsayawa ina na zucci sannan hawaye sun kasa daina ambaliya a saman fuskata muna tafe ina yi ina saka hannu ina sharewa sannan ina faman jan Hanci da majina.
Wlh bansan mun iso Karofi ba sai da naji yana tambayana inda zamu je sannan na daga ido na ga inda muke,sannan nayi masa kwatance,Ina jin wayata acikin jaka tana zuzu alamun ana kira ammh bana cikin yanayin da zan iya duba wayar ma.
Bamu jima ba sai gamu a kofar gidan Goggo,muna isowa na bude mota na fito karamar pos din dake hannuna na Laluba dubu hudu ne yan Dubu Dubu Sabbi na cire na bama Direba ya karba yana godiya Yaran da basa rabo da kofar gidan Goggo,su suka yayyameni ana fara sauke kayan suka rika jida suna shiga cikin gidan Goggo da shi,Nima bayansu nabi cikin wani yanayi har ga Allah ko gani bana yi jiri ke dibana ga ciwon kai mai Tsanani,ina ji muryan Direban na fadin"Allah ya kawo miki mafita"
Ko amsa shi ban yi ba. na shige gidan goggo,a tsakar gida na isketa tana tambayan yara kayan waye ?ina Sawo kaina Tsakar gidan nace"Nawa ne Goggo"
Muryata a shake,na bata amsa baki sake Goggo ke kallona cikin mamakin ganina bata rufe baki ba. taga ana shigowa da freezer,suna kiciniyar inda za'a sauke Goggo ta nuna musu dakin da ta ke sauke karikitaanta suka shiga da su,sallaman ma Goggo ce ta sallame su ni ko ban iya tsayawa a ko'ina ba sai akan Daya daga cikin kujerun falon Goggo na zauna Dabas ina Numfarfashi kamar wacce tayi gudun Tsere,Goggo ta shigo ta tsaya a saman kaina,Hijabin jikina na cire kan kujeran ma sai naji? sama sama nake jin kaina. kasa na koma na zauna,ina Kokarin tare kukan dake neman tasomin.
Cikin mamaki da al'ajabi Goggo tace"Fa'iza daga ina?kun fasa tafiyar ne..?yanzu nan su Nasara suka fita suna shirin tafiya tace kin kira kince su Dakata ga kinan zuwa lafiya.?ina yaran ina shi Megidan naki..?
A jere Goggo ta rika jefomin Tambayoyin,ammh na kasa amsamata ko d'aya daga ciki sai na koma na Dafe kaina ina kokarin daidaita yanayina,Goggo bata hakura ba ta cigaba da kallona tana Nazari na sai ta Fahimci na fita daga hayyacina Idanuwana sun kumbura alamun nasha kuka sai ta Firgita cikin jimami da Fargaba tace"Fa'iza ki yi min mgana mana naganki da uban kaya sannan ke kadai kika zo ina su Amir..?ina shi Ishaq din..?
Ambaton su Amir yasa na fashe da wani marayan kuka zargin Goggo sai ya tabbata ta ji jikinta yayi sanyi sai ta koma ta Durkushe a gefe na tana fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Fa'iza ba dai Ishaq din ne ya sake ki ba?
Ban bata amsa ba na cigaba da Dirzan kukana Goggo na tayani da Sallalami fadi take"Haka Allah ya kaddara. Fa'iza ki yi hakuri"
Ta kasa zama ma mikewa tayi tana fita tana Dawowa cikin wani yanayin da na kasa Fassarawa,sai da nayi kukana ya isheni sannan na lallashi kaina Lokacin Goggo ta kawo min Ruwa da abinci tana fadin"Wannan wata irin kaddara ne..?bai rabu dake? tun kuna samun matsala ba sai yanzu da kowa ke ganin abubuwa sun daidaita?
Sai da na sha ruwa naji na samu natsuwa sannan na Dago jajayen Idanuwana na sauke a kan Goggo ganin yadda ta rud'e ne hankalinta a tashe yasa na bude baki nace"Ba sakina ya yi ba Goggo.."
Sai da naji ajiyar ran Goggo na samun Salama. cikin mganarta tace"Har na samu salama Fa'iza to me ya faru.?na ganki da uban kaya ko kun fasa tafiya Lagos din ne"
Kai tsaye nace"Aa ni ce dai na fasa binsu chan ne,ammh su inaga suna Hanya ma Goggo"
Cikin mamaki Goggo tace"To saboda mene Fa'iza..?
Kaina na kasa ina kokarin Danne abunda ya tasomin nace"Na GAMA AURAN ne Goggo."
Cikin Razana Goggo tace"Wata irin mgana ce wannan Fa'iza.?Daman ana gama ibadar Ubangiji ne ko a gaji da ita..?
Ina tsiyayan hawaye na dago ina fadin"Wlh Goggo na gama aure tsakanina da Ishaq. Bama shi ba na gama auren ko wani Namiji a duniyan nan,ba komai acikin aure sai kaskanci da zalunci da Tozarci Goggo"
Na karishe fad'a cikin Kuka mai Tsanani,sai Goggo ta saka salati Tana fadin"Haba Fa'iza wannan wata irin mgana ne..?aure fa Ibada ne mai yinsa bai taba Tabewa ba. Me akayi miki Fa'iza?meyasa tun a baya baki yi wannan Borin ba sai yanzu da naga komai ya daidaita har ita Saudatun kuna zaune lafiya da ita.?shi kan shi Ishaq din ya sauko Fa'iza sannan Meyasa kika yanke hukunci batare da kin tuna da ya'yanki ba.?wazai rike miki su Fa'iza?
Cikin Kuka da karfi nace"Zainab da Mama zasu rike su Goggo. bazasu mutu ba..chan ne dolen su tunda gidan Ubansu ne,ni kuma ba gidanmu ba ne nan ne Dole na Goggo"
Goggo ta tsorata da yanayina da bata taba gani ba cikin wata irin murya tace"Fa'iza bautar auran kika gaji da shi?Saki kika nema?
Kin san yadda al'arshin Allah ke girgiza saboda Sakin aure..?
Nima cikin kuka na bata amsa da cewa"To Goggo ibadan aure ai ba Bauta mutum ba ne..?sannan ba laifi ba ne in nace na gaji da auran ina da Dalili na Goggo"
Sai Goggo ta fara fad'a tana fadin"Dalilin menene..?wani Dalilin ne zai sa ki bar auran ki da ya'yanki Fa'iza abunda baki yi ba a baya ba sai yanzu..?anya kin yi tunani kuwa..?
Mikewa nayi ina ganin jiri na Dafe kujera ina fadin"Bazan fadi Dalilin ba Goggo ,ammh shi ya sani in ya fada muku zan kara muku bayani in kuma bai fada muku ba shikenan domin alkwari ne nayi masa baza'a ji wannan mganar a bakina ba"
Hijabina na kwasa da Karamar jakana na wuce dakin Goggo ina jinta tana fadin"Fa'iza zo ki bi mijinki..Bazan zama goggon banza ba"
Da karfi nace"Wlh tallahi ba inda zani Goggo. In kuma kika matsamin na fita Daga gidan nan to ba lalle ki kara ganina ba"
Jin abunda nace ne yasa Goggo ta saka Salati tana fadin"Ai shikenan tunda kin raina ni kina da uba,Bari Isa ko Salisu su shigo zan sa su kirasa,shi in yazo zaki fadamai Dalili sannan in yace ki koma gidan mijinki shi bazaki yi mai gaddama ba"
Ina jin haka na shige Dakin Goggo na Rufo kofar na fada kan gadonta na saki kuka,tun ina yi a Hankali har na fara yi da karfi,da dukkan zuciyata ya'yana nake tunawa ina tuna tun Tsawon Rayuwata in ba makaranta sukaje ba bamu taba awa daya bama tare da juna ba,sai yau da nake jin Nisa zasu yi dani na har abada,ina kwance ina tuna zama da nasu da yanayin yadda rayuwata da yarana ta kasance wlh sune duniyata ni ce tasu duniyar ina Tausayinsu na yadda Rayuwarsu zata kasance a bakon waje batare da ni ba,basu saba da kowa ba sai ni,nima ban saba da kowa ba,sai ya'yana bansan nima ta yadda Rayuwata zata fara tafiya daidai ba batare da su ba.
Tuna hakan yasa nake ta rafzan kuka,kukan da ya rikitani yasa naji zazzabi na rufeni,daman na shigo da jiri da ciwon kaina sai kuma abun ya yi min yawa,ina jin hayaniyar su Goggo a falo da mganganun mata da maza ban iya motsi ba,har ta kai ga suna ta buga kofar dakin Goggo Lokaci daya da kiran sunana ba amsa ba.
Naji muryan Yaya Mariya,naji na Hafsah da ta Yaya Isa ammh na kasa budewa saboda bazan karbi kalmar hakuri ba wannan karon sannan bazan yi mgana ba kuma bazan iya gaddama da su ba. gwara nayi nesa da Tambayoyinsu a wannan Lokacin,ni abu daya nake son ji ko gani ya',yana ina so naji Halin da suke ciki,ina cikin Dakin nan har Dare sai da aka kira mangariba na iya jan kafana na shiga Toilet nayi alwala na fito na rama Salollin dake kaina duka a zaune nayi su,wayata na ciro daga cikin pos dina,da naji ana kira Anty Fadila ce ina gani har ta gama ringing ban dauka ba kawai na ijiye wayar a gabana ana cigaba da Kira.
Ba wanda bai kirani ba acikin su har da Yaya Abdul'Ahad,Abba ne ya kirani a karshe sai naji kuka ya kara kwace min Cikin kukan nake fadin"Kayi hakuri Abba..Kayi hakuri"
Domin bansan me zan ce mai ba in na Daga wayarsa ina da Tabbacin Tuni Labari ya kai musu shiyasa suke ta kirana ni kuma bani da amsar Tambobyinsu a lokacinm
Kaina na Hada da gwiwa na cigaba da Kuka,gabadaya duniyar tamun zafin da bata tabamin ba. Lokaci daya rayuwata ta baya na sake dawowamin kamar yanzu abun ke faruwa, an yi an gama. na gama Daukan Tozarcin da na Dauka baya ina Bukatar Rayuwar yanci nima.
A chan Falo kowa Goggo ta kasa zama gabadaya Hankalinta a tashe yake,Har da su Yaya Isa ita kanta Yaya mariya ta kasa komawa gidanta Tunda Hafsah tazo ta gayamata Fa'iza tazo ammh ta rufe kanta adaki tana ta kuka.
Goggo ita ta saka Yaya isa ya kira mata Abba tamai bayani yace yana warri baya gari ammh zai kirani a waya yaji meke faruwa?
Ammh kafin nan bari ya kira Ishaq din yaji to yace yayi ta kiransa bai same shi ba,Zuwa yammah kuma Anty Fadila ta kira Abba tace Mijin Fa'iza da yaranta sun sauka a lagos ban da ita shi yake mata bayanin da Goggo tayi masa shine fa suke ta kiran wayoyina ban Dauka ba.
Jin har dare ban Bude kofa ba Abba yace gobe zai biyo jirgi zuwa Kano Daganan zai dauko tashar Mota zuwa Karofi domin yaji abunda ke faruwa.
Ba bugun kofar da basu yi ba tare da magiyan na bude kofa ammh ban bude ba,Zazzabi ne mai zafi ya rufeni da bazan iya tashi ba,ga yunwa ga rashin kwnciyar Hankali ga kuma karin kuka,su suka taimaka wajen kwantar dani cikin Halin ciwo,da har asuba ina ji ana kiran salla na kasa tashi ina kokarin mikewa wani jiri da ya Debeni Allah ne ya taimakeni na koma na zube bisa gado da a Kasa ne da Tuni zence ya sha bambam.
Ina kwance ina kuka ina tuna da su Amir yau mun kwana a mabambamta waje,abunda bai taba Faruwa ba sai zuwa na kano bikin Halisa sai kuma yau,Duniyar ma a sama sama nake jinta,tun ina iya jin abunda ke faruwa kad'an kadan daga Falon Goggo har duniyar ta Daukemin gabadaya.
Na gama Sadakarwa mutuwa zan yi, ni kadai acikin daki ba wanda ya sani.

****

Abba tun goma ya baro warri ta jirgi ya sauka a kano Direban gidan su Ammi yazo ya Daukesa bai zarto da shi ko'ina ba sai karofi ba kuma wai don ya gama abunda ya kaisa ba ne matsalan data kunno kai ne yasa ya yanke komai ya taho.
Yau da safe Ishaq ya kirasa bayan sun gaisa yadda yaji muryansa yasan shima a rikice yake tun kafin ya yi mai mganar Fa'iza ya tsinke da Fadin"Abba Fa'iza zata barni. Ta ki yarda ta biyoni Lagos Abba. Kayi ma girman Allah kada ka bari Fa'iza ta bar gidana"
Daga jin yadda yake mgana ba cikin natsuwa ba ne Abba nata ya saurareshi yayi mgana ya kasa sai ma ya cigaba da fad'in"Abba jiya har mun shirya Fa'iza tace bazata bimu ba.Yara suna ta kuka Abba,Na kasa lallashin su,Mama da su Anty Binta ma sun kasa lallashinsu Abba wlh tallahi ba domin ajiyan sun kirani suna Bukatar ganina affice karfe bakwai na Safen yau bacda karofi zamu bi Fa'iza Abba,bazan iya tafiya Lagos batare da Fa'iza ba,Abba su Amir sun ki yarda su kwana wajena sai Anty Fadila ne ta koma da su gidanta suka kwana har kuma da Safen nan mun yi mgana tace Amir da Anum sun bar kuka ammh Ahmad kwana yayi yana kuka yana kiran sunan Umma. Abba ya Fa'iza take so nayi..?zata kasheni ni ne kwana na bai kare ba.? ka ganni nan ina Office ne ammh wlh Abba bani da Natsuwa kamar zararre nake ji na,ni dai ka taimakamin in na gama abunda nake yi zan sake biyo jirgi Abba ni dai Fa'iza tayi hakuri ta janye kudurinta"
A yadda yake mgana ba tsayawa yasa Tausayinsa ya kama Abba shi kanshi yayi mamakin abunda akace daga bangaran Fa'iza yarinyar da yake mata so na Dabam duk cikin su Mariya,tana da sanyin Hali ga Hankali da natsuwa sai dai shi sha'anin aure baka katsalandan in ka shiga ka zakewa sai kaji kunya in sulhu ne to zai nemi a zauna a samu Fahimtar juna ko don zuru'ar dake tsakani.
Dakyar ya Lallashi Ishaq da cewa ga shi yana Hanyar Karofin,kuma ya hanasa tahowa, da alkwarin da kansa zai kawo masa Fa'iza har Lagos da haka suka yi sallama yana cigaba da masa a magiya shuru yayi ya na tunanin a mganganunsa kamar shi ne bai da gaakiya domin yana ta nanata a bama Fa'iza Hakuri ta duba ya'yansu kada tace zata barshi.
Sannan kuma yana auna mganganun Ammi a jiya da Daddare da suka yi mgana shi dai bai kirasu ya fad'a musu komai ba,sai dai yana tunanin a wajen su Nana Fadila taji abunda ke faruwa,shi yace kada ta sanar da su Inno tukunah yaje ya gani ko zai iya Daidaita lamarin Kalaman Ammi alokacin sun saka ya fara nazari.
Ce mai tayi"Baban Nanah tsakani ga Allah kada ku zake kan sai Fa'iza ta koma Allah kad'ai yasan bakincikin da yarinyar ta Hadiya.
Nifa tun ganina na farko da ita na Fahimci tana da Damuwa,kuma duk sauran sun fita kama mai kyau da sakin jiki cikin mutane Nana Fatima ta fadamin tana da abokiyar zama tana chan Abujan"
Abba ya fadamata diyar abokin karatunsa ne Dr.Lawal bako abokiyar zaman Ita Fa'izan.
Ammi ta cigaba da fadin"Ku saurareta ta fad'a muku dalilinta kuyi ma kowani bangare adalci kada kuce zaku Tursasata"
Shi dai bai yi wani mgana ba,saboda bai je ya gani ba ammh mganganun Ishaq yasa ya fara auna maganganun Ammi sannan yana jin Tausayin yaran shima ai sun yi mgana da Fadilan shi ya ce ta dauke yaran zuwa gidanta har komai ya Daidaita. har ya isa Karofi yana fatan komai ya Daidaita
Sai dai me? koda yaje su Goggo na Cikin Tashin hankalin tun jiya ban bude kofa ba sannan ana ta Bugamin naki Budewa suna Tunanin ba Lafiya.
Cikin Tashin Hankali Abba yace"Tun jiyan data shiga bata fito ba..?
Goggo na sharan kwallah tace"Tun jiyan nan Alhaji. Ni na fara jin tsoron ko lafiya yanzu da ka ganmu Tsaye mariya nace ta kiramin Isa ya kira mai balle kofa yazo balle kofar nan muga Halin da take ciki,daman tun jiya da tazo take ta faman koke koke"
Abba ya fito da waya yana fadin"Bazai yu yu? mai rai acikin Daki tun jiya ba'asan halin da ta ke ciki ba, akwai ciwo akwai yunwa dole a san yadda za'ayi a balle kofar nan bari na Kira Isan da kaina"
Ya daga waya yana kokarin daidaita yanayinsa,Yaya mariya da Hafsah sun yi tsuru tsuru Yaya Asiya sai kiran mariya take yi domin tunda suka fada mata itama Hankalinta ke matukar tashe.
Abba ya samu Yaya isa ya fad'amai Halin da ake ciki yace ga shi nan zuwa da mai balle kofar suna zaune Jugum Jugum sai ga su sun shigo.
Hankalin tashe gabada'ya a kabi bayansu mai balle kofa na aikinsa su Abba na tsaye cikin Zullumi.
Kofar tayi gaddama Saboda Sakata na sakata ta ciki Sai da aka warwareta sannan akayi iya budeta,chan bakin gado suka ganni ina Numfashi sama sama daga kirjina baya sauka a cikina iyakarsa nan yana sama da kasa Goggo da su Yaya Mariya suka yi kaina suna kiran sunana ina ko jin su bana yi lokacin ina kokuwa da numfashina ne ga jikina ya Dauki zafi kamar wuta.
Goggo ta tattaba jikina tana Fadin"Jikinta zafi."
Abba a rud'e yana daga kofaar Dakin yace"Muje asibiti..Isa daukota muje Asibiti"
Yana fada yayi waje a binsa Yaya isa ya Fada dakin cak ya Daukeni su Goggo suka biyo bayansa har waje suna fitowa sai ga su Anty Nasara Goggo ba takalmi ba Hijabi sai da Yaya mariya ta bata na jikinta tare da ita da Yaya Isa sai Abba suka Daukeni zuwa asibiti a halin Rayuwa da mutuwa.
Wani asibitin kudi dake cikin garin Dutsenmah suka kaini nan da nan suka karbeni suka shigar dani Likitoci suka Rufo kaina Saboda Numfashina Dake neman kwacewa sai da suka sakamin Oxygen,sannan suka min allurai da Drip,numfashina ya fara Daidaita Likitan dake on Duty haka ya rika yin fad'a yana fadin ina da Hawan jini meyasa ake tadamin Hankali..?ga jinina nan ya haye sama ina neman mutuwa Abba ya shaki mamaki yana kallon Goggo Lokaci daya yana Fadin"Fa'izar ke da hawan jini..?
Goggo ta dagamai kai tana fadin"Tana da shi shekarun wajen hudu muma bamu sani ba,domin bata gayama kowa ba ta mgangun da aka bata a asibiti yara suka gani suka gane"
Mamaki ya kara kama Abba duk da Hawan jini ya zama ruwan Dare a wannan rayuwar,ammh Fa'iza tayi kankanta a shekarunta ko shi da ya Haura Hamsin wlh ba shi da wannan mugun ciwon.
Gefe ya koma kawai yana kara nazarin wasu abubuwan,sai dai yayi mgana da likitan yace a kula dani komai zai iya kashewa saboda na samu lafiya,suna asibitin nan har Yammah sai sallah ke fitar da su Abba ko ruwa bai isa sha ba sai dai yana amsa wayoyin dake shigomai ciki har da na Ishaq Abba na Daukan wayansa yace"Kayi hakuri Ishaq mu bi komai a sannu. Yanzu haka nazo na iske Fa'iza ba yadda take gata ma a asibiti likitoci na kokarin ceto numfashinta"
Shima cikin karaya yace"Wlh nima Abba in naje asibiti na kwanta nima zasu kwantar dani. Nima bani da lafiya bani kuma da natsuwa"
Abba ya rintse ido kafin ya bude cikin Dattakonsa yace"To kai ma ka natsu kasan satin ka na farko kenan da Fara aiki plz ka tsaya kayi abunda ya kamata. Fa'iza na bukatar addu'anka, in ta ji sauki sai a zauna ayi sulhu a Fahimci juna insha Allahu komai zai Daidaita"
Da haka jikinsa yayi sanyi yana fadin"Allah ya bata lafiya Abba meke damunta..?
Kai Tsaye Abba yace"Hawan jininta ne Likita sukace ya tashi,Damuwa ne yasa jinin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login