Showing 87001 words to 90000 words out of 288345 words

Chapter 30 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

756

jiya take son ta koma gida dayake bata damu ba"
Hajiya batace komai ba,Da Badariya tazo gaisheta sai tace ta kira mata ni,Ina Dakinta tazo ta kirani ina jin tace Hajiyar su Raliya na mike na fita da Hijabi suna falo na duka na gaisheta cikin Fara'a ta amsa ni tana fadin"Haka ake yi Fa'iza abu ya faru haka bazaki kirani ki fadamin ba..?
Sai dai naji a bakin Raly.?
Kaina na kasa ban ce komai ba sai ta Cigaba da fadin"ba'a haka Fa'iza irin wannan sai ki kirani ki fadamin ko ba a Uwar kika Daukeni ba..?Goggon karofi ta karbe d'iyarta kenan.?
Goggo na gefe tayi dariya kafin tace"Ba ruwana Hajiya ke da Diyar ki"
Kaina na kasa na shiga bata Hakuri sai tace bakomai su Mama haushi duk ya cikasu kallona tayi tana fadin"Ya abun ya faru ne ina so na sani saboda naji in zan iya taimaka wa"
Kafin nayi mgana Anty Binta ta karb'e da bayanin yadda ake ciki Hajiyar su Raliya,ta gyada kai kafin tace"Akwai Kanina yana aiki da Hukumar EFCC din achan Abuja, bari na nemesa naji ko zai iya taimaka mana"
Nan da nan bakin Mama ya washe a gaban mu ta kirasa suka gaisa ta rattamai bayanin komai sai ya nemi sunansa da inda yake aiki Anty Binta ta fadamata sai ta turamai yace ta bashi nan da zuwa Dare zai bincika mata halin da ake ciki.
Bata wani jima ba, tayi ma su Mama sallama,akan yadda akace in sha Allahu gobe zata dawo ita da sauran yaranta Mama godiya kamar zata kwanta mata Hajiya ta kalleta kafin tace"Bakomai kada ki damu babba ne a wajen zai binciko komai..Zan iya yin komai saboda Fa'iza kamar diya take a wajena Ahalina Ahalinta?ne,zan iya bakin kokarina bazai gagara ba insha Allahu"
Basa kaunar su ji an ambaceni kuma basa kaunar alfarma ta barayina har waje na rakata ni da Badariya,Direba ya zo da ita ta shiga mota tana ce min sai zuwa gobe,Ta tambayeni su Amir nace suna cikin gida,na dawo cikin gida naji ana ta maimaita zencen nidai a raina ina fatan Allah ya kawo mafita.
Washegari da wajen yammah sai ga Hajiya ta dawo ita da Raliya da yayyin Raliyan suna zuwa ni suka nema daman suna zuwa gidana,Ita kuma Hajiya ta nemi su mama ta gayamusu halin da ake ciki,Hukumar ta na bincike ne,sannan akwai yuyuwar komai da ya fita da saka hannun Yaya Ishaq saboda haka in sun gama Bincikensu zasu yi mgana, sannan sun hana Belinsa saboda cases din na da girma Hankula sun kara tashi tace dai a Dage da addu'a komai zai daidaita.
Wasa wasa har an shud'e Sati Biyu shuru dai mgana d'aya sai sun gama Bincike,Gajiya nayi da zama na Tattara na koma gida na da yara Goggo ma ta koma Karofi mama an barta da Anty Hure ne mutum yamai suma sun koma kowa ya Saduda yasan Allah ke yi,Mama ta saka ana ta Sadaka da Saukan Qur'ani ni kuma agida banzauna ba ni da yara muna ta kai ma Allah kukan mu,Ban kara bi ta kan Zobo da kunin aya ba,Saboda Halin da nake ciki ko makaranta yaran basu koma ba Hafsa ce ta koma makarantar ta tana zuwa.
Wajen wata da'ya da Tsare Yaya Ishaq aka bama yan'uwansa Daman ganinsa Su Yaya Isa dai suka koma Abuja mgana ta tabbata ba yadda Yaya Ishaq zai fidda kansa saka hannunsa da yardansa aka fidda kudad'en,zai biya taran kudaden gabad'aya da tsabar kudi ko Kaddara.
Lokacin da labarin yazo mana Sai murnan kowa ta koma ciki kudi ba kadan ba wajen Million 70,ina Yaya ishaq yaga wannan kudin ko Kaddara..?su Yaya isa sun dawo suna mganar ya lissafa abunda ya mallaka, gida biyu nan katsina d'aya sai na Abuja sai mota sai gidan mahafinsa,Sai tsabar kudi miliyan d'aya da rabi asusun bankinsa sai fili a nan katsina,Hukumar tace zata zo ta Duba duka kaddarorin zata kwace zai zama karkashinta.
Sai naji na rude ina ta maimaita innalillahi acikin raina Hankali tashe na kalli Yaya isa ina fadin"Aikin sa fa Yaya isa..?
Ya kalleni cikin Tausayawa kafin yace"Ba mganar aiki Fa'iza ya samu ma ya fito lafiya"
Su mama sai kuka Daman a gidan ne ake maida zencen,Agidan muka kwana Dagani har yara saboda ana saka ran dawowar Yaya ishaq acikin Satin.
Haka ko akayi hukumar tazo ta Duba Gidajen da Yace kada a saka gidan Mama,Mama ta saka kuka miye amfanin gidan in bashi a Had'a dashi,Sannan akwai tsabar kudi a wajenta na sana'arta miliyan uku Anty Binta ma ta saka miliyan Biyu,suka tura ta asusun bankin Ishaq,Saboda kudin su rage nauyi.
muna ji muna gani Hukumar ta kwace gidan da muke ciki da gidan Mama da filin da ya siya acikin gari chan ma Abuja ta karbi wanda zainab ke ciki da motar hawansa, sannan sun bamu Notice Wata daya mu tashi Saboda wajen ya zama mallakin Gwamnati
Lalle mun ga tashin Hankali mai suna tashin hankali,Wannan labarin sai dai mun Dauki Dangana tunda zasu sake sa,Bai amsa laifinsa ba ya riga ya rantse bai da hannu akan lamarin, zasu sake sa ammh ba su kyalesa ba in bukatar wani Binciken ya shigo zasu kara nemansa,Shima da taimakon manya acikin lamarin mijin Hajiyar dala da Kanin Hajiya dake hukumar tare da Mutanen Mahaifin Zainab Dr.Lawal bako.
Mama ta tsine ma duk wanda ya saka Danta cikin bala'i tayi mugayen addu'o'i akan sa,Ta ce tunda ya jefa Rayuwar d'anta cikin bala'i shima bazai ga rayuwa mai kyau ba.
Watan Yaya Ishaq biyu a Hannun Hukuma suka sakesa,Daga Abuja tare da Dr.Lawal da Zainab da yara, sai su Yaya Isa da su Jamal suka iso da shi katsina ko da suka iso karfe goman Dare ne an so ya kwana sai gobe yace Zai je yaga Mama yasan tana cikin Damuwa.
duk da Dare ne, gida cike yake da masu dakon dawowarsa.
Mama na jin Dirin motarsu ta Fice da gudu ita ta bude masa Mota ya fito Allahu akbar Duk wannan fafan da kyau da nasabar ta Yaya ishaq ta tafi cikin wata Biyu.
ya rame ya fita Hayyacinsa sai sumar kai da kasumba ta rufe masa fuska, yayi duku duku kamar ba d'an kwalisa Ishaq Kabir Karofi ba.






*03/07/2023*
*Janafty*
[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KANA NAKA..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Ina gaida Matar Abba,Maryam jumare.*
*Madalla da ke Hauwa'u(Real smasher)Fa'iza ta ce na gaishe ki*
*Fa'iza na gaida mai sunan k'anwarta Hafsah Hafnan,(Sahibatu) tace sannu da Himma.*
*Fa'iza ta ce na isar da sakon gaisuwarta ga uwar Dakin Gudayo da Yabi,tace madallah da kawar kirki irin ki Surayya Dahiru gwaram.*

*Ishaq na gaida Ahalin Masoyansa gabad'aya,yace na Fada muku. ya ji duk zagin sa da kuke yi groups groups,Har da masu sauya masa suna wai Isiya,Yace kwa yi ku gama shi da Fa'iza mutu ka raba takalmin kaza.*

*JANAFTY NA GAIDA MASOYANTA
MASU AIKO MIN DA SAKO GA FA'IZA DUK NA ISAR DA SAKON KU,TAJI KUMA TACE TA D'AUKA IN SHA ALLAHU ZATA MIKE TA TAIMAKI KANTA*

? ? ? ? *
Ranar da akayi addu'ar bakwai da Daddare,aka taramu saboda washegari zamu watse. kowacce zata koma gidan mijinta,Cikin taron har da Megidan Tamadina da abokan zamanta. sai manyan ya'yan gidan maza,sai mu sai Goggo da Baba Ati kamar kaka take wajen Tamadina ita kad'ai ta rage acikin dangin mahaifinsu da na mahaifiya tunda daman auran zumunci ne tsakanin iyayan nasu..
Bayan bude taro da addu'a da yi ma Mamaciyar addu'a sai d'an nasiha garemu na hakuri da rayuwa,duk yadda tazo ma bawa sai kuma aka gangarowa mgana kan abunda ta bari na magada.mu kenan to da yake bata bar wani abu ba,sai yan kayanta da gado da Sauran tarkace nan take kuma mukace mun yafe a raba ma bakuta,suka shiga saka mana albarka Megidan su ya ce Tamadina tun iya zaman da yayi da ita, bata taba sab'a mai da gangan ba,saboda haka ya yafe mata duniya da Lahira,haka Sauran abokan zamanta suke ta fad'in alherinta suna fadi'n bata yi musu komai ba mace mai kirki da son zaman? lafiya,Daga karshe Yaya mariya ta muskuta tana kallo Goggo Lokaci d'aya tana fadin"Goggo ya mganar bashi.shin ko sun san ana binta a bashi Saboda a biya a sauke mata nauyi..?
Maman isuhu ta kad'a baki tun kafin Goggo tace wani abu tace'"Allah ya jikan Tamadina ba mace bace mai cin bashi ba,ga yara nan duk sai su tsallakemu su kawo mata ajiyan kudadensu,wlh yadda suka bata haka suke karb'an su ko chanzasu batayi.bata taba cin bashi ba,macece mai godiyar Allah da Wadatar zucci"
Gabad'ayan mu dad'in wannan yabon mukaji,har sai da hakan ya nuna a saman fuskar mu,an tashi taron cike godiya da fatan Allah ya jikan Tamadina bayan Goggo ta sanar da Mutan gidan gobe zamu koma gidajenmu suka nuna alhininsu.
Bayan mutan gidan sun fice suka bar mu, mu kadai Ni ina gefe nayi tagumi bana mgana Amir ne kadai bai yi barci ba yana jikin Hafsatu,Yaya mariya ce da Yaya Asiya ke ta zencen su da Goggo da Baba Ati acikin Hiran ne Yaya Asiya tace"Baba Ati wai har yanzu ba'a samu labarin inda Dan'uwan Tamadina yake ba..?
Baba Ati ta sauke Numfashi kafin tace"Ke dai bari Asiya wlh ba'a samu ba.Kwanaki har chan karayen naje da muka kai yar gidan mallam Akilu aure chan. aka tabbatar min sun tashi sun koma cikin garin kano hannun wani Dan'uwan ita Zuwairan"
Yaya mariya tace"kuma babu lambar waya Baba Ati..?
Ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya babu..Ai tun lokacin zamanta a korafi batayi dogon Huld'a da kowa ba Zaman nasu ma da mahaifiyar Tamadina kakar ku kenan ba dadi gaskiya har da shi Mallam din saboda bata so auran ba,mahaifinta ya had'a abun akwai wanda take so shiyasa sanda aka kawota batayi huld'a da kowa ba,ko Haihuwar Usman din Rabo ne kawai da ya rantse yasa aka ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????samar dashi.
Sai kuma mallam din yazo ya rasu.to bayan ta fita Takaba,Danginta suka zo tafiya da ita.sai ta nuna zata tafi dashi to rayuwar nan ba wanda ya damu da rikon D'an da ba nasa ba, saboda ganin Nauyi ne in ma ta barsa anan d'in shiyasa ba Gaddama akace zata iya tafiya da shi Har ga Allah na zata zata rika kawosa ko don yar'uwansa da suka Had'a uba sai kuma gashi Tunda ta saka kafa ta bar Karofi yau shekaru sama da Arba'in da Doriya bata Dawo ba.sannan shima Usman din bai nemi Dangim mahaifinsa ba har yau din nan kuwa"
Ba kuma wanda yasan inda suke ahalin yanzu"
Gabad'ayan mu muka sauke Numfashi Yaya Asiya tace"To Allah yasa yana raye"
Yaya mariya tace"In sha Allahu ma yana Raye kuma in dai da rai da rabo watarana zamu had'u da shi"
Muka amsa gabadayan mu da Allah yasa Goggo ta gyara zama tana fadin"Duk inda yake in dai jinin ku ne zai nemeku jini ai ba karya ba ne".
Muka jinjina mata kai alamun gamsuwa ni ko araina sai na samu kaina da addu'an Allah yasa yana raye domin shi kad'ai ne shakikin Tamadina anan duniya mu kuma kawun mu Namiji kwara d'aya tak da yau zamu bugi kirji muce muna da shi acikin raina ina addu'an in dai yana raye Allah ya bayyana sa da gaggawa.
Washegari da shirin tafiya muka tashi. kowa kagani da Kuzarinsa ban da ni,kwata kwata kamar an zaremin lakkan jikina,Goggo sai fad'a take min wai na kwazzabi kaina bana cin abinci Yaya mariya na wajen tace"Kuma zama da yunwa bazai taba Sauya komai ba..Tamadina ta rasu sai dai mu yi fatan Allah yasa tana kyakyawan karshe"
Sai hawaye ya kecemin suka shiga tsere bisa kumatuna, bayan mutuwar da ta dake ni,yayi sanadiyar tasomin da ciwona da daman kamar jira yake na shiga hali makamancin sa,Mun had'a duka kayanmu na yara Hafsatu ta wanke musu ta had'a musu ta musu wanka,ta shiryasu haka ma su Yaya mariya sai kuma sabon kuka ya tashi muka zauna mu hud'u muka ci kukan mu muka koshi,muka share Hawayen mu. Goggo tagaji da bamu baki ta Hakura ta koma gefe ta zuba mana ido bayan ta kira Yaya Isa tace yazo ya Dauketa ita da Hafsatu da mariya da Baba Ati, Yaya Asiya kano zata wuce nima kuma gidana zan koma.
Da azahar sai ga Hajiyar Dala,mun dauka ma bazata zo ba ne ahalin taji Rasuwar. tunda Goggo da kanta ta kira wayar ta,ta fad'a mata,Tazo tayi mana gaisuwa ta bama Yaya Asiya dubu goma Sadaka batayi awa d'aya ba,Ta ce zata tafi, nan take zencen zata karisa katsina Tare da Direba take jin Haka yasa Goggo ta kalleni tana fadin"Fa'iza tunda kun gama shiri,sai ki bi goggon taki tunda katsinar zata shiga"
Da Sauri tace"Aa ba gidan Saudatu zani fa gidan Wani abokin Major ne. mahaifiyarsa ta rasu zan biya nayi musu gaisuwa suma na wuce"
Ina jin haka nima murya a sanyaye nace"Ki bari kawai Goggo zan tafi da kaina"
Sai goggo ta jinjina kai kafin tace"Shikenan"
Daga haka tayi mana Sallama tatafi Goggo ce ta rakata har Dakunan matan gidan tayi musu gaisuwa, kafin Tafiyarta sai da ta dawo sannan Yaya Asiya ta bata kudin da Hajiyar Dala ta bata Goggo ta karb'a tana fadin"Kudin ku ne ai Asiya ba ni aka bawa ba"
Yaya Asiya tace"Goggo mu bama bukata ayi sadaka Allah ya kai Haske kabarin mahaifiyarmu"
Goggo ta amsa da Ameen itama fita tayi da kudin Dakin Maman isuhu ta shiga ta bata kudin Dakyar ta karba, Goggo tace kun yi wahala damu wajen kwana takwas ku karba ku kara Allah ya Rufa asiri .sannan ta karb'a tana sharan kwallah da kara fadin Allah ya jikan Tamadina.
Yaya Isa ya kira yace gashi nan zuwa,Shinkafa suka dafa mutam gidan suka zubo mana yaran aka zuba mawa suna ci ni dai bakina yayi nauyin? bana jin Dad'in komai kaina wani Dum dum kawai yake yi duniyar ma ba daidai nake jinta ba.
Kwatsam sai gasu Sa'adatu da Habiba sun zo min gaisuwa nayi mamakin zuwan su sai da aka gama gaisawa sannan na kalle su ina fadin"A ina kukaji rasuwar sannan waya kwatanta muku gidan nan..?
Sa'adatu tace"Ai tun da naga an kwana biyu baki dawo ba nace ba Lafiya Megidan ma nata jimamin abun.? yace haka kurum bazaki je ki zauna ba ko don makaranta yara da muka ga an yi kwana biyu sai yace bari yaje gidan kakaninsu su Amir yaji ko Lafiya. to chan yaji abunda ya faru wajen kanwar Baban su Amir ce domin ina ganinta tana zuwa itace ta fad'amai mahaifiyarki ta rasu sai ya Nemi ta kwantatamai gidan nan sai ta mai kwantance mun d'an sha wuya kafin mu gane,sai dai kinsan gidan mutuwa baya boyuwa balle da naga ba'a gane ba sai na rika kwantance da cewa Bebiya bata mgana sai ko gashi an kawo mu"
Na jinjina kaina,kwallah na Taruwa acikin idona makota na ne da ban had'a komai da su ba,Ammh sun nemi inda nake sun zo min gaisuwa Su mama kuwa tun ranar uku basu dawo ba,bana saka ma Yaya Ishaq a lissafi bai Dauke ni da Daraja ba,ballataana ya Dauki dangina da iyayena abun Daraja Har afili na nuna musu jin Dadi'na na nuna su ga sauran yan'uwana da Goggo suka dinga saka albarka har da gurasa Habiba tazo da shi ita kuma Sa'adatu sai ta Dafo Dambun Shinkafa da yaji Zogale Goggo ta karba ta kai ma Mutun gidan suna fad'in Allah ya bada Lada
A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai? naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana"
Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba"
Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani.
Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama"
Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata.
Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma"
Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi.
Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login