Showing 279001 words to 282000 words out of 288345 words

Chapter 94 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

726

kawo Result bai bata mgani ba allura kadai ya yi mata Sai Drip da ya saka mata ta samu barci,haka na ta sata ina kallonta Lokaci daya na zabga tagumi.
Engr ranar yasan ba na cikin sukuni Tunda ka'idan kafin na kwanta nakan kirasa,mu yi bamkwana yaga ban kirasa ba kuma ya kirani ban dauka ba Allah nagani ban ma ji kiran ba wayar na inda na idar da sallar Isha'i.
Sai ya kira Sharifa itace ta fad'amai nayi bakuwa tazo ba lafiya.
Sai yace ta kawomin wayar ta wayarta ne muka yi mgana na fadamasa Badariya ce ga kuma Halin da tazomin cikin damuwa.
Sai ya shiga lallashina da irin tausasan kalamansa.
Hankalina tashe nace"Abunda ke damuna ina mijinta yake da ya barta ta yi doguwar tafiya ita Kad'ai?
Engr yace"Allah masani kuma ga shi ba lambar shi mijin ballatana akira aji ko lafiya"
Kai tsaye nace"Sai dai in wayarta.Gata nan a hannuna"
Engr ya yi shuru kafin yace"ko kuma ki bari ta farka sai ki fara jin ta bakinta kada mu yi gaggawa"
Da haka ya samu ya lallasheni da zamu yi sallama yace"Kada ki damu zata farka cikin lafiya. In kika saka damuwa ina kike so ni kuma na saka kaina Babyna..?
Sai ya bani dariya daman Burinsa kenan yaga Dariyata,Kuma daman yasan in yace Bby sai nayi dariya don in yace min haka sai nace"Wata Bby da ya'ya zarata har hudu..?
Bby kamar wata Anum.?
Shiyasa in ya tashi zolayansa haka yake kirana tun ina jin wani iri har nazo na saba.
Shawaransa na bi ban kira kowa ba,To in ma zan kira bani da zabi Tunda wayar tana cikin Password ne Dole sai in ta farka tukunnah.
Ba ta kuma tashi ba sai da asuba,Cikin ikon Allah ta tashi da kwarin jiki Daki daya muka kwana na bar mata Kan gado ni na kwana saman Cafet.
Ba tare da taimakona ba tayi wanka ta Dauro alwala ta fara rama salolinta ni kuma na fita zuwa kitchen tunda na saba bana barcin Safe,Wani lokacin tare da su kafaya muke abun kari wani Lokacin sai dai su fito su ga nayi musu komai.
Yau ma hakan ce ta kasance,Indomie na Dafa sai na dafa musu kwai ni kuma daman na fi son sayayye sai na soya na Dafa Ruwan tea mai kayan kamshi,Na kuma soya Buredi,ina da Sauran Soyayyan Nama sai nayi musu pepe. Ko kafin takwas na safe na gama komai na goge kitchen din daman na fi yin abincin rana da yawa tunda ina aika ma su Maa da shi su yi ta saka albarka shi kan shi Engr bai sani ba sai dai in su Maa din suka fad'amasa domin ya yi min mgana ba Dawaniya ba ce..?
Nace masa ba Dawainiya bace,daga karshe sai yace Allah ya ba da Lada.
Koda na koma Daki Badariya na kwance ammh ba barci take yi ba,gaisawa muka yi na tambayeta jiki cikin sakewar murya tace min taji sauki..
Gefen gadon na zauna ina fadin"Kin kira yusuf kin fadamai halin da kike ciki..?wai ma tsaya da sanin sa kika yo wannan Doguwar tafiyar..?kuma baki fad'amin jiya zaki kamo hanya ba"
Shuru tayi kafin ta yamutsa fuska tace"Bai sani ba"
Kai tsaye na kalleta da tambayan"Bai sani ba..?
Bangane ba..?
Sai ta koma ta lumshe ido kafin tace"Miye baki gane ba..?
Nace miki bai san na taho ba,bama shi ba ba wanda ya sani"
Ban yi mamaki ba ganin yanayin yadda ta zo sai na muskuta kafin nace"To sai ki kira yanzu ki fad'a masa"
Kai tsaye tace"A"a.."
Mamaki ya isheni na mike ina fadin"To ni bani lambarsa na kirasa na fad'amasa kina wajena kada hankalinsa ya tashi in yaji bakya gida"
Da sauri tace"Bazan baki ba Anty Fa'iza"
Ina kallonta nace"Saboda menene..?
Sai ta muskuta ta mike ta gyara zama kafin tace"Saboda bana so yasan inda nake. Na gaji Anty Fa'iza Ina so na rabu da auran Yusuf ko na huta da wannan bala'in da nike ciki"
Ta karishe fada cikin gunjin kuka sai naji Tausayinta ya fad'amin.
Na karisa gareta na zauna gefenta na rumgumota jikina ina Lallashinta Fadi take yi"Nagaji nagaji. Bala'in yau daban na gobe Dabam,ga na Matarsa ga na mahaifiyarsa ta tsaneni bata son ganina bata barina nayi girki ta karbe makullin Store sai taga dama zan ci abinci,matarsa kuma har gidan take zuwa tamin Tijara,ban ce komai ba shi ma kamar ta shanyesa baya iya Daukan mataki in nayi mgana sai yace nayi hakuri yana raga mata ne Saboda Hajiyar su, Wlh nagaji ne Anty Fa'iza gwara ya sakeni na koma gida yafiye min zaman auransa na rashin kwanciyar Hankali"
Tana gama fad'amin haka ta fashe da kuka ma ban tausayi ga wanda ya Saurara ni kaina ta rauna na min zuciya ina tuna a baya nima fa na Fuskanci iri wannan rayuwar da Badariya take fuskata.
Cikin Bubbuga bayanta nace"Subhanallah har yanzu matsalolin nan basu gyaru ba..?
Shi Yusuf din bai dauki wani mataki ba..?
Sannan yanzu me ya faru kika taho.?
Badariya na gunjin kuka tace"Yaushe zai iya daukan wani mataki yana taorin matarsa yana tsoron uwarsa,Kwanaki fa har yaji nayi na tafi lagos na kafe bazan koma ba sai ya sauyamin gida da Hajiyarsa saboda bala'in ya yi yawa da yunwa nake kwana da nayi mgana sai tace Danta ya gaji da ci da juya nazo ba na Haihuwa sai ci nayi kashi abinci fa sai dai na siya,shi bazai iya mgana ba sai dai ya bani kudi a hannuna na rika cin abinci gajiya nayi sai nayi tafiyata Tunda bata amince ya sauyamin gida ba,Dakyar ya lallasheni na dawo da alkwarin zai sauyamin gida na ni kadai ammh kuma mgana ta shiriran ce,Shekaran jiya matarsa tazo gidan tana ta zagina tana ce min Juya in sha Allahu dukiyar da na shigo ci bazan sameta ba har tana zagin Ubana dake Kabari ni kuma raina ya baci na Rama shine ta jani da Dambe har mukayi fad'a,Du keni in Daketa muka yi Lokacin Hajiyar bata nan daganan sai akace taje gidana gaishe da Hajiya bata nan najata da fad'a har nayi Sanadiyar barar mata da ciki daman ina bakin ciki. Yusuf baya nan ammh Hajiya ta kirasa a waya tace ko ya sakeni ko yaga bacin ranta.
Shi ya kirani yana kuka yake fad'amin ni kuma da naji haka nace gwara a rabun kowa ya huta tunda yaki saki na sai na zabi na tafi inda bazai ma sani ba ballatana ya nemi shiyasa na yanke shawaran zuwa wajen ki Anty Fa'iza na tabbata ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahinceni"
Kafin ta gama bani labari naji raina yayi wani duhu jikina duk ya yi sanyi Badariya mai kaunata ce ban so kaddaranta tazo a haka ba, ammh kuma bawa bai isa ya tsara ma kansa Rayuwa ba,muna namu ne Allah kuma na nashi nashin ne kuma na gaskiya.
Kuka take yi kamar ranta zai fita ina Lallashinta da ban hakuri kfin nace"To yanzu shi Yusuf din yana ina..?
Badariya tace"baya nan,Rabo na da shi tun jiya a fligth mode na saka wayata,mun rabu dai yace yayansu yace ya dawo sai a zauna kada ya sakeni sai indan ya dawo ni kuma daman na shirya tafiyata Shiyasa ban Tsaya ba"
Tun daga yanayin mganarta nasan da gaske ta gajin,sai ban matsa mata ba na kyaleta sai dai nayi ta bata baki da ban hakuri kafin na barta naje nayi wanka na shirya ko da na fita falo su kafaya sun tashi suka gaisheni na amsa sun shirya zasu shiga makaranta sai nace su dibi abun karyawa su karya kafin su fita ni kuma na Dibar mana ni da Badariya na kaima har Daki.
Abincin ma dakyar ta sauko taci,Tasha dai tea,sai Soyayyan Buredi shi kuma kadan taci sai amai haka ta shiga Tiolet tana kwarara shi ni dai ban ce mata komai ba ne ammh naga Ciki Sabo a tare da Badariya.
Su kafaya kafin su fita har Daki suka shigo suka Duba Badariya sannan suka min sallama suka tafi makaranta Dukkansu sun iya mota,suna da kuma Motocin su yau wannan ta tuka gobe wanchan ta tuka.
Suka barmu da Badariya tana bani labarin zaman hakurin datake yi a gidan Yusuf ba kwanciyar Hankali,ni kuma ina kara Tausanta da kalmar nan ta Hakuri ita na rike kuma naci Riban Hakurina.
Sai yammah Dr din yazo ya kawo sakamakon bayan ya yi mata bayanin tana da shigar ciki na wata Biyu da wasu kwanaki ta kiyaye aikin wahala sannan ta rika cin abinci ta samu Hutu Badariya ta kasa mganar har bayan Tafiyanta ni ce nace mata"To ina zaki kai wannan rabon Badariya..?
Baki san abunda Allah ya kaddara Tsakanin ku ba tace ke da Haihuwa sai dai kiga anayi tun ba'aje ko'ina ba sai Allah ya nuna mata bata isa ba. Kinga sunan juya da suke kiran ki sai ya kare daga yau"
Bata ce min komai ba sai dai tana ta sharan kwallah Saboda matsalan Badariya yasa sai dare muka yi waya da Engr da ya tambayeni ya ake ciki na Fad'amasa yadda ta fadamin da kuma cikin da aka gano a jikinta.
Engr ya fara fad'a yana fadin"Shima dai kamar wani sakarai haba .Ba'a haka sai ya sulhunta lamarin ita matarsa ai karkashinsa take in bata son a zauna lafiya ya yi mganinta mana ita kuma mahaifiyarsa matsayinta Dabam ya kamata in dai yana son matarsa ya san yadda zai iya gyara kowani bangare ammh a bar yarinya na Fuskantar wannan matsalan bai Taso ba Faa'izaa ki riketa a wajen ki Sati mai zuwa zan dawo da kaina zan kira mijinta mu yi mgana, in yana sonta ya gyara gidansa in kuma bazai iya ba to kowa ya kama hanyarsa"
Har mamakin Engr na rika yi haka yake da fad'a sai dai nasan shi baya Daukan re ni jarumi ne kuma jajirtattace ne,Da na fad'ama Badariya abunda yace sai taji dadi jin yace zai Shiga mganar zuwan Badariyq yasa su kafaya suka koma gida nima da Badariya ta kara jin sauki munje da ita ta gaida su Maa muka yini achan sai Dare Direba ya maidamu gida.
Badariya sai fadi take yi"Gaakiyan dangin mijin ki masu karamci ne Anty Faa'iza"
Sai dai nayi mirmishi Saboda abunda na sani ne aka sake fad'amin.
Kafin satin da Engr zai dawo Badariya ta murmure tunda ina takura mata taci abinci duk da tana amai ga laulayi da Zazzabi take kwana,wayarta tana Kashe shiyasa bamu ji labarin irin neman da Yusuf ya yi mata har Lagos ba,Da kuma irin yadda Hankula suka tashi tunda duk an nemi kowa bata wajen su ni kuma kila ana tunanin ina amarci kila Badariya baza ta zo wajena ba.
Sai ana gobe Engr zai dawo zainab ta kirani a bakinta nake jin hankulansu duk a tashe suke Badariya ta bar gidan mijinta ba'a san inda take ba.
Tana bani Labarin yadda Hankalin Mama da su Yaya ishaq ya tashi da shi kan shi Yusuf din sai naji kamar na gayamata gaskiya sai kuma na fasa akallah dai na jira dawowan Engr sai na tada Hankalina na nuna Damuwata da Alhini na.
Bayan mun gama wayar na fad'ama Badariya sai ta tabe baki tace"Mama da yan'uwana kawai na damu ammh ba domin Yusuf ba"
Ban biye mata ba,ganin yadda tayi fushi illah na rika ce mata"Ke dai fad'i gaskiya kin yi kewarsa sosai ma ko baki yi don komai ba kya yi saboda abunda ke cikin ki"
Gajiya tayi ta kyaleni tunda taga na Rike mganar na ki saki,Washegari da Shirye Shiryen Dawowar Engr muka tashi,Badariya ta kama mun muka yi masa abincin kala kala na saukansa jirgin yammah ya biyo sai bayan mangariba ya iso gidan.
Lokacin n cakare cikin Riga da sikat na Atamfa mai ruwan ganye cikin kayan akwatin daya dinkamin ne Tunda anan Abujan Maa ta bada aka dimkamin bayan na fad'a mata Measurement dina.
Kayan sun karbeni Saboda Daidai jikina ne Badariya tamin Saukakkiyar kwalliya hade da Daurin maryam babbangida sai nayi kyau dani kamar a Sureni a gudu..
Ai ko Engr cak ya sureni haka ya Dagani Sama bai ji nauyi na ba,ya rika zagayen falo dani ni kunya duk kunya ya kamani ganin Badariya na wajen ashe tun Rumgumar Farko ta komaa ciki ta bamu waje.
Dakyar na iya lallabasa ya yi wanka ammh sai da ya yi kara'in nasa dai ta bakinsa dai ba yayan ya yi ba kanin ne duk ya batamin kwalliya yasa sai da na gyara Daurin? d'ankwalin Tunda har kan sai da ya sha Jagwagwala.
Sai bayan ya yi wanka ya yi sallar mangariba da aka kira Isha'i sai ya jamu jam'i ni da shi bayan mun Idar ne muka fita falo na gabatar mai da abinci sai yace na kira Badariya su gaisa na leka na sameta itama ta Idar da sallar Dariya naga tana yi min sanin Dariyan da ma'ananta yasa ban tanka mata ba ammh ina ce mata Engr na mgana afalo ta mike tana Fadin"An gama yar shillan dake..?
Sai na juya baya ban kara yarda mun hada ido ba na fice ina mirmishi.
In na zauna ina kod'a Engr sai aka ga kamar ina zugasa ne ammh mganar gaskiya Engr shi ya kaini duniyar ma'auratan da bansan ma akwaita ba.
Shi ya jiyar dani irin Dadin da mata suke ji a tare da mazajen su.
Shi ya kara fahimtar dani aure da zamantakewa ashe ni a baya wahala kawai nayi,ban taba Dauka haka Aure ke cike da Ni'ima ba sai da na Samu Engr.
Duk da kowani aure yana da nashi kalubalen,zo mu zauna a kace zo mu sab'a,ammh ni ta bangare na cika da Hamdala na kuma kara da Alhamdulillah.
Tunanin da ya cika raina kenan ina zaune gefensa yana cin abinci sama sama yake mgana saboda bai cika son mgana in yana cin abinci ba.
sallamar Badariya da shigowarta falon yasa ya Dakata ya dago yana amsawa
Nesa dani ta zauna tana gaisheshi ya amsa cikin fara'a kafin yace"Matata zubo muku abincin mana tunda na lura yau wareni akayi tunda naga an zubamin nawa ni kad'ai"
Mirmushi nayi kafin nace"Ni bana jin yunwa ne shiyasa sai dai in Badariya"
Da sauri tace"Anty Fa'iza ki gayamasa mun ci da muka gama girkawa tun a bakin Tukunya"
Hararanta nayi shi kuma sai ya kada kai yana fadin"Fa'izaa na yafe miki ba ma sai kin nemi gafarata ba"
Dagani har Badariya muka yi Dariya matsamim? ya yi sai da muka saka abincin muka ci kad'an tunda gaskiyanta ne tun a kitchen muka koshi sai dai an dauki Lokaci cikin ya Zazzage.
Saboda gajiyan dake jikinsa yasa yace sai da safe zasu tattauna da Badariya da wuri muka shige ciki,saboda yana ta fad'amin ya yi kewata in zai koma kafata kafarsa bazai iya ba.
Ai ko naga kewa haka ya rika min rawan jiki da Sambatu ni kaina na karbesa dakyau tunda nima nayi kewarsa sosai Rayuwa juyi juyi sai ga shi ni Fa'iza ke son al'amarin a baya Wlh tallahi al'amarin bai taba dad'ani da kasa ba.
Da Asubaa yana kwance ni na tsokane sa muka buga kafi siga dad'i,Da safe ma kafin mu tashi yace zai kara na bata fuska ina Fadin"Baka gajiya ne..?
Duk sai ka tsotseni ko..?
Yana dariya ya kamoni yana Fadin"Bamu gajiya zaki ce. kema ai ba gajiyan kike yi ba in fa kika ji ni nayi kamar zan sauka sai ki yi saurin rikeni kina Uhm uhm"
Ya karishe fad'a yana kwaikwayon yadda nake yi ga kunya ga Dariya Engr halinsa sai shi bakina ya Mutu murus na kasa mgana ya sumbaceni kafin ya Dagoni yana Fadin"Bafa tsotseki zan yi ba. Yarinya ina da Fertilerzer mai kyau kinga yadda kika koma..?Tife din gaske kenan ke da zaki bani dama nayi ta damawa ina cigaba da kara'i na"
Ai ko na basa dama kamar yadda ya bukata.
sai ya koma bayan mun natsa fad'i yake yi"Kamar ma ban yi ba. Wlh komai ya sauya ya kara sugar"
Kansa na dungure ina Fadin"Kuma sai akace komai kaji sai ka fad'a..?
Bakinsa ya kama yana fadin"To in kama bakina kenan..?
Harda wani ladabin Dole Mirmishi nayi kawai ban yi mgana shi kuma sai ya kamani ya Rumgumeni yana Fadin"Allah ya yi miki albarka. Allah yasa ki haifo kannen su Ahmad dozin Biyu haka"
Mukamikinsa na Tokare ya yi gefe yana wash,Sosa wajen ya fara yana Fadin"Yaushe kika zama Muguwa Faa'izaa..?
Ya ja sunan kamar wani abu,Hararansa nayi sai ya gane laifinsa da Sauri yace"To na rage Dozin Daya"
Tiolet na shige na barsa ina ji yana Fadin"To naji rabin Dozin ga su Amir goma kenan ina laifi Father of 10"
Sai dai na bige da mirmishi ina wanka Soyayya da kaunar Engr sun taru sun cikamin kirji sun hanani sukuni yadda yake kaunar ya'yana wlh ko Ishaq albarka shiyasa nake yi masa kara in muna mganar su sai dai nace ya'yan ka.
Yaran nan suna da lambarsa barin ma Anum uwar karambani sai dai yace min sun kira shi da wayar Mama Amir ma suna mgana da shi,Zumunci dai ne kila bazai Dore ba tsakanin Engr Da Ishaq kowa na ganin zumunci da wani matsala ne shi Engr haka nan baya so ya shigo masa shima Ishaq din har gobe yana kaunar Fa'iza shiyasa baya son Doguwar mu'alama da wanda ya hanasa mallakar Fa'iza a karo na biyu. sai dai yaran bai isa ya raba su da mahaifiyasu ba yasan Fa'iza ta shanye abubuwa dadama Saboda yaran nan suna mata kauna ta sosai kuma shima Engr yasan yana kaunar su Darajan yana Son Fa'iza yana jin kishin yadda yaran ke kiran Engr Baba sai dai ba shi da yadda zai yi yasan ni ko ya fad'a ko kada ya fada Engr mutum ne nagartattacen kuma Kishinsa duk akan Fa'iza ta auri wanda ya fisa ne yana ganin ta cigaba fiye da in da ta dawo ma auransa.
Da safe bayan mun gama karyawa Engr ya zauna da Badariya suka Tattauna ta fad'amai komai kuma ya gamsu a wajenta ya karbi lambar Yusuf ya kirasa suka gaisa ya fad'amasa sunansa Engr Abdulbasit Mijin Fa'iza yar'uwan Matarsa Badariya daman don ya shaida masa ne matarsa na wajen su da sauran bayanai yusuf ya rude Engr yace zai bashi address yazo nan Abuja yana son ganinsa.
Abun mamaki da Sassafe sai ga shi jiyan ma bai samu jirgi ba ne da Shigar dare zai yi irin yadda Hankalinsa ya tashi yana son Badariya kuma bazai iya Rabuwa da ita ba.
?Engr bai bari yaga Badariya ba sai da suka tattauna na tsawon awa Biyu sannan ya kira wayata yace na Turo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login