Showing 147001 words to 150000 words out of 288345 words

Chapter 50 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

740

Qur'ani saboda Anum ma ta shiga ajin Hadda Baban ma yana yi musu na boko duk dare in mun gama su yi shirin kwanciya,ko yana son mgana dani sai nayi saurin jan Anum mu shige Daki mu kwanta ba Halin kuma wani abu saboda idon yara,da kuma idon Hafsah tunda tare muke kwana da ita.
Yau muna zaune bayan mun gama cin abinci da ni da yaran duka muna kasa ne ina musu karatun Qur'ani Anum tana izifi goma ne Amir kuma ya wuce ashirin,su Ahmad kuma suna kasa kasa izifi biyu,shi yana kishigid'e saman kujera yana kallon mu har muka gama,Sai Amir ya mike yana fadin"Daada yau ba zaka koya mana karatun ba ne,?
Yana daga kwance murya a shake yace"Ban ji dadi Amir sai gobe..yau ka famshe ni ka koya ma kannen ka"
Sai Amir ya amsa mai yace su Anum su dauko littafan makarantan su,sai suka dauko ya fara duba musu,ina gefe har na fara gyangyad'i saboda gajiya Hafsah daman in yana falon bata cika zaman falon ba,sama sama naji Anum na kiran sunana"Umma..Umma!
Sai na yi Firgigit na farka ina hamma cikin,lokaci daya nayi mika ina fadin"Nagaji ne menene kuke kirana..?.Amir yace"Umma kema ki zo mu yi karatun tare"
Wata Hamma ta kara kwace min cikin kasala nace"Amir nagaji wlh ka bari gobe"Amir ya ware ido yana fadin"Umma yanzu kin daina karatu fa?kila ma kin manta na baya"
Nace"in ji wa..?ban manta ba kawai Hidima ce ta sha kaina ammh zan dawo makarantar nan ayi hakuri dai yau mallam Amir"
Su Anum suka yi dariya ina tayasu yana daga kwance yace"Amir kai ne malamin Umman taku..?
Kafin yayi mgana fadi ba'a tambayeka ba ta mike ta isa garesa ta fara basa labarin Anum akwai shigen Surutu kamar wata aku,tana bashi Labari yana kallona yana mirmishi Lokaci daya yace"Kice Umma ta fara jin Turanci"
Anum ta kyalkyace da dariya tana fadin"Sosai Daada"
Gani ya yi ina mika bayana duk ya sake kawai sai ya mike yana ce ma Anum"Je ki ku cigaba karatun ku"
Sai ta koma wajen zamanta shi kuma sai ya taso da ina shirin mikewa ne sai naji mganarsa a kasa kasa daidai kunnena yana fadin"Naga duk kin gaji muje dakina na tayaki da Tausa, duk zasu sake kiji dadin jikin ki"
Ai ina jin haka na koma na zauna ina Kifta mai ido sai ya kuramin ido sai na zame masa kurma nace"E he..me kace..?mirmishi yayi kafin yace"Kinji ai me nace zaki iya tashi ne ko sai na Dagaki..?ya fada Lokaci d'aya yana dagamin gira sai na juya ina kallon yaran bakina sake shima sai ya kallesu hankalinsu baya kanmu alamun in tashi yayi min sai naki tashi sai kawai naga ya mike yana gyarawa ai ban san lokacin da na mike a guje na shige daki ba,tsayawa kawai yayi yana kallona yaran suka Dakata da karatun suna kallon sa Anum tayi farat tace"Daada me ya faru da Umma take gudu..?
Yana shafa kansa ya juyo yana fadin"ta gaji ne kafafunta sun sake, sai tayi gudu saboda su sauka''
Tana daga ido Lokaci daya tace"Exercise kenan Daada"
Yana zama kan kujera yace" yauwa my Anum"
Amir dai bai ce komai ba ammh sai Hararan Anum yake yi ta cika Kaudi da fadi ba'a tambayeta ba sai da ya mata mgana sannan ta daina damun Dadan nasu da mgana wanda ya shiga Zurfin Tunanin in fa ya tsaya biye ma Fa'iza to bazai samu daman gyara kurakuransa na baya ba, har sai nagaba sun zo sun iskeshi a ransa ya shiryamata wani wayau da bata isa wannan karon ta tsallake ba.
Da safe bani da masaniyar abun da ya kulla yara sun tafi makaranta Hafsah ma kusan tare suka fita Badariya na Daki bata fito ba, ni kuma na gama kaye kayen daki kafin na fita Tsakar gida sai na koma Daki ina lissafin kudin da suka Rage a hannuna na bama Hafsa kudi kafin ta fita zata shiga kasuwa ta siyo min aya da zobo na wajena bai wuce yau ba zai kare, sai kayan maggin gida da man girki da nace ta Siyo min ko ba da yawa ba. siyan kullum duk baka gane masa kayi ta ganin kudi na narkewa ka rasa ina suke zuwa.
Na dukufa ina kirga kudin Hannuna har ga Allah ban ji motsinsa ba sai kawai naji mganarsa yana fadin"Hajiya Fa'iza mai zobo da kunin Aya ana ta lissafi ne..?
Sai a lokacin na dago na gansa ya Coge a kofar shigowa dakin yana kallona yana min mirmishi,Sai nima na maida masa martanin mirmishin nasa ina fadin"Ka manta baka cike mai Turaren wuta da kwallacha ba"
Sai kawai ya karisa shigowa Dakin yana Fadin"sana'a goma da ashirin wai Fa'iza yaushe kika zama yar kasuwa haka..?
Dariya nayi ban yi mgana ba na zata zai zauna ne sai naga ya coge yana miko min hannu Lokaci daya yana fadin"A bani in taya kirgawa mana."
Kai na girgiza ina fadin"ina kudin suke balle ka tayani kirgawa? riban wannan satin ne duka duka dubu hudu ne da yan chanji"
Sai ya gyada kai yana fadin"Ina laifi ai motsi yafi labewa Allah dai ya kara Rufamana asiri"
Na amsa da Ameen ina kallonsa sai ya yarfa Hannu yana fadin"Na gaji da zama ne waje da'ya shine zan dan fita na mike kafa"
Sai na jinjina masa kai ina fadin"Ya kamata to a dawo lafiya"
Har ya kama hanya zai fice ni kuma na mike sai kawai ya juyo yana fadin"Fa'iza na manta"
Sai na juyo ina kallonsa Lokaci daya ina sauraransa kai tsaye yace"Taimakawa zaki yi ki shiga ki gyaramin Shimfid'ata da daki na duk yayi kura kafin na dawo"
Yadda yayi mganar ba wasa ne yasa kaina Tsaye nace"Shikenan za'a gyara in sha Allahu"
Sai kawai ya fice yana fadin"Allah yayi miki albarka FA'I TA.."
A fili na amsa da Ameen? har ga Allah a raina ban kawo wani abu ba Sai da na gyara Dakina da dakin yara,na falo daman na kimtsa shi,sai na shiga Dakin nasa na fara gyara masa,Tiolet na fara shiga na wanke na fito ina gyaran Daki na kakkabe Shimfid'a na gyara har ina sauya masa zanin gado naga nasa yayi datti sai na kudiri a raina zan hada da wankin yara na wanke masa da sauran kayansa da suka yi datti.
Ina cikin gyaran gado,ya shigo ban ji ko shigowarsa ba har ya samu nasaran rufe kofar damam abunka ga wanda ke da raunin ji,sannan gabad'aya hankalina yana ga abunda nake yi na duka ina saka zanin gadon jikin katifar na gama na mike kenan sai ji nayi an rumgumeni ta baya kam! Lokaci d'aya ana saki karfaffan ajiyar zuciya ni kuma har ga Allah na tsorata ban Zaci ganinsa ba gabana ya yanke ya fadi ras sai da kaina ya sara min jiri na neman kada ni, jinin jikina cak ya tsaya ya daina gudu ga shi ta baya ya rikeni sai na fara kokarin kwatan kaina ina fadin"Wa...ye..?
Cikin rawan murya hannayensa duka Biyu yasa ya zagaye cikina da karfin da na kasa motsi kawai sai na Dage iya karfina zan yi ihu zaraf ya juyo dani ina fuskartarsa Saboda yadda yaji ina zufa ne,ga haki Lokaci da'ya Fuskata ya tallabo da Hannayensa duka Biyu Lokaci d'aya yana fadin"Fa'iza..Fa'iza ni ne fa"
Sai da naji muryansa naji Numfashina na daidaita,Abun ka ga mai hawan jini abu kadan ke haye mana sai na sauke ajiyar zuciya ina kallonsa cikin mamaki shima kallona yake yi na bude baki nayi masa mgana cikin mamakin ganinsa kawai Dif!
Kamar an kawo wutar lantarki an Dauke haka naji Jikina ya amsa ya koma kuma ya saki Lokaci da'ya, sakamakon bakin Yaya ishaq da na tsinta dumu dumu acikin nawa bakin yanayin da ban san yadda zan kwantata muku ba.ni dai da Hankalina Yaya Ishaq bai taba sumbatata baki da baki ba,ban ki in muna cikin auratayya yana bukatar natsuwa yana yi shima ba cikin soyayya ba ko natsuwa ba. cikin Tilastawa da neman biyan bukatar sa.
Shiyasa sai na rude na gigice na fita daga Hayyacina ban kara Dimaucewa ba sai da naji Hannayensa na kara kaina ajikina da zafi zafi duk inda Hannunsa yakai a jikina sai ya taba,tsayuwa ce ta nemi gagaranmu sai kawai ya bini muka zube bisa Katifar da na gama gyara masa ya kasance ina kasansa shi kuma yana sama na,bazan iya fassara yanayin ba abu d'aya na sani yayi nasara motsa sha'awata da nayi shekaru da Binneta yayi nasaran yayyafa mata ruwa data Farfad'o batare da sanina ba,Doguwar rigar yadi ne ya jikina daga sama ya zage zif din yayi kasa da ita,ba san da wani lokaci hakan ya faru ba na dai san naji hannayensa suna kai da kawo saman kirjina sannan hancinsa na shinshino duka fatar jikina tare da Game numfashinsa da karamin Nishin dake fita da kofofin Hancina.
Na fita daga duniyar da muke ciko ko nace ya taimaka wajen fitar dani daga Hayycina har yayi nasaran raba ni da Rigar jikina hannayensa dumu dumu acikin maraata,Fatar jikinsa tana gogar fatar jikina numfashi na ya sarke sai wani Uhmm...!
Kawai nake saki,wani irin tafiya ya dinga yi dani tafiyar da tunda nake bantaba sanin ana iya kai macen wannan bangaran ba,Ban kawo ma kaina abunda yake shirin faruwa dani ba sai da naji bakon al'amarin da bayan shudewar mintina Arba'in yana kokarin kwace natsuwata kamar almara naji wani bakon al'amari na kokarin Ratsani Ratsawar da na manta ya yanayinta,kansa na tsakanin wuyana cikin Shakar Nunfashi naji yana karanto addu'ar da sai in zaka kadaice da matarka kake karantata kamar irin an buga kaina Gaf!yayi gaba sai yayi baya sai naji ni Tsamo Tsamo na dawo duniyar da ya tafi ni ina Dago idanuwana da suka yi min nauyi na kallesa a saman kaina daga ni har shi mun rasa suturun jikinmu,shi kokarinsa ya kai ga inda yayi alkawarin jinginewa na har abada ai kamar an sako min wani karfi bansan Lokacin da nayi wani yunkuri d'aya ba sai ga shi na barar da shi a gefena har keyarsa na bugun bango????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
n Dakin na tabbata ba karfina ba ne Ya riga yayi laushin da bazai iya moran ma kansa wani abu ba.
Kafin ya dawo hayyacinsa nayi gefe ina Raruman kayan na,daga inda na turesa ya Dafe keyarsa dishi dishi yake ganina Tsabar Halin da yake ciki cikin muryan da ta shige ba'a ko jinta ya kira sunana"Faaaa...izaaaa"
Naji dai jan sunan nawa ammh ban tsaya bin ta kansa ba,na rarumi zanin Gadon da na cire zan wanke na nade jikina da shi ba inda jikina baya rawa,kuka kawai naji ya Sarkeni kawai sai na fashe da kuka har da Shessheka.
Da rarrafe da jan jiki ya kariso gabana sai ji nayi ya rikoni nayi saurin kwace kaina cikin ihu nace"kada ka sake ka tab'ani..'
Kada ka sake..".
Na fad'a cikin ihu lokaci d'aya da kuka sai ya kasa kara tabanin ya koma gefe yana kallona,da kafarsa ya ja gajerun wandonsa ya saka kaina na maida kasa ina kuka,kamar ana dawomin da komai haka abubuwan da suka wuce suka rika dawomin na Dade bana fama da Kuncin zuciya tunda Allah ya samamin mafita ammh yau sai naji kamar komai anan yake faruwa kirjina yayi nauyi bakinciki ya cikani da na kasa sarrafa kaina agabana ya Durkusa kamar jaririn dake neman nono wajen uwarsa,yana shirin kara tabani nayi gefe da sauri ina kara rike zanin gadon dake hannuna gudun kada ya rabu da jikina,Sai ya Daga hannu cikin kasala da sanyin jiki,idanuwansa sun sauya Launi Jijiyoyin kansa sun mike gabad'aya cikin alamun Sararawa yace"Na bari naji bazan taba ki ba,ammh kiyi ma girman Allah ki bar kukan nan ki tsaya muyi mgana Fa'iza"
Sai a lokacin na dawo hayyacina na Fahinmci gadar zare ya hadamin Allah na sona da Rahma da na Rufta acikin shirinsa da na shiga uku.
Bani kuma da sauran mgana burina da na dad'e dashi acikin raina zai mutu batare da na cika sa ba.
Rokona ya cigaba da yi ganin naki daina kuka ganin yana magiya kamar zai yi kuka yasa na saurara da kuka na, sai dai ban daina jan Numfashi ina Jan majina ba,zaman dirshan yayi a gabana cikin wata irin muryan da bazaka taba cewa Ishaq kabir karofi gaye dan kwalisa ne ya mallaketa ba murya ce da zata iya kasaara jikin ko wacce d'iya mace mai lafiya in dai ta jisa da muryan ya fara mgana cikin karyayan sautin da ni kadai zan jisa yace"Haba Fa'iza haba fa'iza meyasa..?kin san halin da kika sani Tsawon wannan lokacin..?ki dubeni kiga yadda na koma a gabanki don Allah ki kara bani dama na gyara kuskurena na yarda na amince ni mai laifi ne ammh kada ki horani ta wannan bangaran na amince ki min duk abunda kika ga dama,ammh ba ta wannan bangaran ba ki bari na samu natsuwa daga gareki koma menene sai ya biyo baya.."
Sai da ya Dire mganarsa na Dago jajayen idanuwana na wurgasa masa wani harara da mamakin jin kalamansa na karshe,cikin karya wuya yace"Don Allah Fa'iza.."
Har da kokarin sake rikoni na ko kara matsawa baya shima yana kara matsaoni da karfi nace"Ka na matsowa wlh zan yi maka ihun kwarto wlh"
Cak ko ya tsaya yana kallona cikin mamaki yace"Kwarto fa,kwarto fa Fa'iza..?
Kai tsaye ina kuka nace"Eh Kwarto nace. kuma ka kara matsowa kusa da ni kasha mamakina"
Sai ya koma gefe na ya zauna yayi Tagumi kamar wani maraya Lokaci daya yana fadin"Ina cikin wani Hali don Allah Fa'iza ki bar ni na samu natsuwa daga wajen ki don Darajan don Allah Fa'iza ki ji tausayina"
Banza nayi da shi ina ta sharan hawaye ya kara kwaso magiya har ya gama ban ce masa komai ba, sai ya matso kusa dani na zaro mai ido sai ya koma da baya hannunsa a sama yana fadin"Wlh bazan taba ki ba..ammh in kika min haka kin min adalci kenan Fa'iza.?zina kike so naje nayi ko kuma kina so na fad'a wata Halakan ne..?
Idanuwana suna fitar da kwalla na Dago ina kallonsa cikin Muryata nace"Adalci ka ke mganar ban yi maka ba..?kai kasan menene adalci kuwa..?kuma? da kake mganar ka da ka fad'a zina ko halaka, au sai yanzu kasan Ana iya fad'awa wannan halakar.?ammh baka taba Tunanin matar daka jingine Shekaru Biyar baka taba waiwayanta da sunan bata hakkinta na aure ba.Ita baka taba Tunanin wata Halaka zata fad'a ba..?ko ita ba Mutum bace..?ko ita bazata iya fadawa zinar ba ne..?
Na fada cikin wani yanayi Lokaci kamar alokacin yake fadamin ya zabi Zainab sama dani sannan ya jingine aurena fiye da shekaru biyar ammh Saboda Namiji bai da kunya har zai iya nema na da wani abu..?
Wani irin kallo nake bin sa da shi kallon tarin takaicinsa da bakincikin da yayi shekaru yana kunsamin Hawaye suna kwarnya a saman fuskata.
Kansa ya dafe cikin wani yanayi lokaci d'aya yana fadin"Na sani..nasan ni me laifi ne Fa'iza kiyi hakuri ki yafemin nasan nayi miki tarin laifukan da bazasu yafu lokaci d'aya ba, ammh ki duba ki gani wlh nayi nadama nayi nadama ki bani dama na gyara kuskurena"
Cikin kuka nace"Ina nadaman da kayi..?yaushe ka fahimci Fa'iza mutum ce kuma macece kamar zainab..?
Sai ya kasa mgana ya fara mgana cikin kame kame yana fadin"Tun tuni Fa'iza,Wlh tuni na gane kuskurena.
nayi nadama kema kin sani"
Kai tsaye nace"Babu abunda na sani.Abu d'aya na sani cewa baka sona baka taba kaunata ba.ka zauna dani ne saboda Baba..ka ce bani da amfani kace ni ba matar kwarai bace, ni ba matar rufin asiri? ba ce kace ni? Fa'iza ban dace dakai ba,Alfarma kake yi min,ka manta ka sha fad'amin baka Daukeni a bakin komai ba..?ka manta da kanka ka kirani ka nemi alfarman na barka ka yi rayuwar aure da Zainab ni kuma ka jingine aurena ba.?ko ba kai ba ne ka zabi wata macen sama dani ba?meyasa sai yanzu kake tsammanin komai zai zo maka da sauki..?.
Na karishe fad'a ina tsiyayan hawaye,wani Turiri da hayaki na fitowa daga kasan raina,Hannuwana ya riko jikinsa na rawa yace"Na sani ki bar tuna baya wlh a wanchan Lokacin bansa me ya shiga kaina ba ne,Ammh wlh na dawo hayyacina na gane kuskurena na fahimci sakacina da laifina na fahimci sakacin da nayi Wlh na tuba na tuba..nabi Allah na biki Fa'iza na dade da sanin kin fiyemin kowacce mace amfani a Rayuwata kuma na dade da sanin nayi kuskuran furta kalaman jingianan auran mu fa'iza,ki bani Dama mu sake gyara rayuwar auran mu a karo na biyu don Allah Fa'iza.."
Yafad'a lokaci d'aya yana jimke hannuwana cikin nasa sai kawai nayi Dariya lokaci d'aya da kuka kamar Mahaukaciya kafin nace"Fa'iza ce fa,kurma diyar Bebiya,Baka mummuna,Mara ilimin boko,mara gata mara kyau da nasaba,macen da bata chanchanci namiji kamar Ishaq kabir karofi ya so ta ba.Ni ce fa Fa'iza yar gargajiya nan,ina nan ban sauya ba.Ni ce dai wacce ka ke ciyar dani Saboda ina zaman kula da ya'yan ka, Fa'izan ne da ka ke tafiya wajen wata macen kafi wata biyu baka kirata a waya kaji yaya lafiyanta ba, Fa'izan da da bata san komai ba, sai ibadar aure da kula da ya'yanta da aka bar mata amanar su Fa'izan da ka rabata da kowa nata ciki har da mahaifiyarta marainiya da bata dukan wani gata, bata da uba bata da wani babban yayan da zai Tsaya ma rayuwarta ita ce dai wannan Fa'izan da Mama da Anty Binta suka maida abar wulakantawan su da cin mutumcin su, wannan fa Fa'izan da baka san ganinta Fa'izan nan ce da kake jin kunyar nuna ta amatsayin matarka, ita ce wacce kake jin kunyar duniya taga ya'yan da kuka Haifa tare ita wannan Fa'izan bata d"
Ban karisa ba ya rufemin baki da Hannunsa ina kuka,hawaye jage jage,da majina shima idanuwansa Jajir kamar zai yi kuka yace"Fa'iza ki bar tuna baya..Na rantse da zatin Allah na gane kuskure na,Wlh kin fiyemin kowacce mace a wajena yanzu.Ki yi min aikin gafara ki yafemin laifuka na nayi miki alkawarin zamowa mijin da baki taba jin Labarin kamarsa ba'
Don Allah Fa'iza ki yi hakuri"
Kauda kai nayi kada kalamansa su sakani rauni cikin shakewar murya nace"Saboda yanzu ka rasa komai yasa nake da amfani a wajen ka..?
Da Sauri yace"Wlh Talllahi ba haka ba ne. Allah ne ya dubeni da idon Rahma..Ya ganar da ni da wuri ba sai na mutu kasa ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login