Showing 225001 words to 228000 words out of 288345 words

Chapter 76 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

704

Haddamu mun shafe izifi Hamsin da Takwas,sauran mu izifi biyu,Mu uku ne muka fara saukewa ni kadai ce Wacce ta Haura talatin sai wata yar shekara ashirin da takwas,sai namiji iyakarsa da Biyar,sauran suna bayan mu hadda nake yi ta sosai daman ina Saurin Dauke abu a kaina ko malaman suna matukar jinjina ma kokarina,ko Goggo tayi tamin Fad'a kwata kwata bana samun hutu saboda karatun hadda ga aiki,kada hawan jinina ya tashi nace mata ai ba cikin damuwa nake ba ba abunda zai faru da izinin Allah.
Ina dake ma karatun nan ne domin amfanin kaina da kuma al'ummata da ya'yana duk da basa tare dani,sannan na nuna ma duniya nakasa ba kasawa bace,kuma Samun fiffike daya na ilimi ba tawaya bane,ba kuma ina ja da karatun boko ba ne a'a ina so mutane su sani bazai zama tawaya ko Wariya don bakayi boko ba,sannan bazaka zaman abun wulakantawa ba domin baka iya Turanci ba.
Zan nuna ma Mutane cewa shima Haddan Qur'ani ilimi ne kuma mai girma. rashin karatun Boko ba tawaya ba ne ammh rashin ilimin addini shine babban Tawaya da koma baya. domin shine Ilimin Da Annabi yazo mana da shi,shiyasa na Dage kuma ni kaina nasan ina kokari matuka ko don kada na bama yan'uwana da Abba kunya.
A lokacin ne Yaya Abdul'Ahad ya daga zuwa kasar Calfonia karo karatu bai tafi da Raliya ba.Tunda tana da ciki Tsoho sai bayan ta Haihu daga baya sai ta bishi Abba da Ammi suka rakasa har chan sai da aka gama komai sannan suka Dawo kaduna.
Ya tafi ba jimawa ko wata bai rufe ba Raliya ta haihu haihuwar kuma tazo da gaddama C.S akayi mata Sai da ta kusa sati a asibiti sannan aka sallameta kanwar Hajiya Aisha taje ta zauna da ita sannan ga Ammi itama tana Tsaye a kanta shiyasa ma da akace ko zata koma gida ne tace nan zatayi zamanta haka suka yi da mijinta.
A ka shirya suna Sati biyu tsakani Yaro daman yaci sunan Abba wato Usman,kuma abun jin dadi sunan yazo min a daidai na had'a Haddata izifi sittin ni na fara hadawa sai akace???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? na bari sauran su hada mu kai goma sai a yi mana Sauka da karban shahada,Islamiya kuma daman da Sauki Sauki tunda wasu littafan maimaici muke yi shiyasa na shirya zuwa kaduna ga shi daman Hajiya ta sakani gaba kan girkin suna da Turarukan Amarya shiyasa ana gobe suna muka tafi da Yaya mariya da Anty Nasara sai Aminan ya isa da Goggo aiki kuma na bar ma su jummala nace mu rika mgana ta waya.
Ya Asiya ma tazo Badariya kuma sai ranar suna ta iso,gida ya cika da yayyin Raliya ana ta Hidima,Ammi ma tayi taronta a gida walima ta shirya na Usman Abdul'ahad Usman karaye(Walid),ita da Abba soyayyar Abdul'ahad ya shafi walid har su Nana Fatima na fadin suna kishi. suma dukkansu duk sun zo akayi suna Lafiya aka ci aka sha akayi Hotuna,kusan dukkansu sun koma sai ni kadai Ammi tace sai nayi wata zan koma ina Dariya nace daman nazo da niyar nayi musu hutu.
Wajen kwana biyar nayi gidan Raliya Tafiyar Badariya yasa na koma gidan Abba,yayi murna sosai kuma yana son zuwana kawai dai bai taba mgana ba ne,Muka samu Lokaci mai tsawo muna Hira ni da shi na fad,'amasa na had'a Haddata saura karban Shahada kawai sai saka albarka yake yi har mganan Ishaq sai da mukayi yana Fadamin duk bayan kwana biyu sai ya kirasa sun gaisa na Fahimci Abba yana Fad'amin yadda Ishaq yayi Laushi ne kila ko zan koma ne,ni ko baisan komai ya fita raina ba. ganin nima ban bada Fuska ba shiyasa shima bai Takuramin ba.
Tunda naje kaduna shikenan su Abba suka rikeni musamman Ammi daga wata sai ga shi na share wata biyu,ina nace zan tafi sai Ammi tace ban isa ba in nace aiki sai tace ga shi nan ina waya da su komai na tafiya daidai,sai nayi Shuru sannan tunda ga Goggo ban damu ba,nasan zata kula da komai kuma ko aiki ne ya samu in aka kirani sai na kira jummala ko goggo mu yi mgana komai zasu kamallah kudin kuma in a hannu ne Goggo ta karba ta sallame su in kuma ta banki ne Yaya isa nake turamawa ya kai ma Goggo to anan din ma ban zauna ba ina taba Hada Taruruka,har zaria mun je da Ammi siyan kayan hadi'n su kawayenta kaf daman sun sanni ta fanni kayan kamshi zamana kuma a garin sai kowa yace yana so. nan din ma harka samun kudice ta Bud'emin sai godiyar Allah sannan tunda nazo ni nake yin girki Ammi ta sakarmin komai su Hafsah suna zuwa makaranta har weekend wani Lokacin.
Abba kuma na Office in kuma tafiya ta kamasa sai kiga yafi sati baya garin,suna yawan zuwa abuja da Parthercourt,to wannan karon dai naji Ammi na tad'in zasu yi warkshop gabadaya ma'aikansu na warri da porthercourt a nan Kaduna na tsawon wata daya har? ma'aikatan su na Edo.
Kuma naji Ammi na ambatan har da Ogan Abba wato Engr shima yana cikin Warkshop din.






*Janafty*



[7/28, 5:55 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3009*

*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

A satin suka fara workshop din,
A nan babban ma'aikantansu na NNPC da ke kaduna. in Abba ya fita tun safe sai dare Direba ke dawo da shi gida a gajiye. wanka kawai yake yi yaci abinci ya kwanta,kwana uku da Farawarsu ranar da daddare bayan ya dawo yana cin abincin da na Dafa na shigo ni kuma mu gaisa.
Ina zaune gefensa na Hagu Ammi na barayin Dama ganin ya share Mulmulen tuwon shinkafa guda uku da Ammi ta sakamai ammh kuma yana mganar ta karamai,jin haka yasa muka kallesa a tare ni da ita cikin mamaki tace"Na hudu fa kenan Baban Nana.."
Cikin ka'da kai yace"yunwa nake ji ne Maman Nana. rabo na da abinci tun karin da nayi na Safe fa."
Cikin mamaki tace"Tun Safe fa Baban Nana?baka ce min akwai restaurant guda da aka dauko suna baku abinci a wajen ba..?
Kai tsaye Abba ya kalleni kafin yace"D'iyata k'aramin tuwon?nan kin ji,in na biye ta tambayoyin wannan uwar taku yunwar sai ta kara jigatani"
Ina Dariya kafin nayi mgana,Ammi ta zubamai ta karamai hade da miyar Ogun din da nayi wacce taji Bushasshen kifi da Kashin Rago.
Sai da ya fara ci sannan ya Dago yana Fadin"Wato maman Nana Allah ya yi ma Diyar nan taki albarka ta shagwabani da girke girkenta duk inda naje naci abinci in ba Dandanon Abincin ki ko nata ba,wlh baya kosar dani sam ga masu abincin sai ma abunda ka zaba ni dai wlh kada'n nake ci sai naji duk ba Dadi na gwammace in na dawo sai naci gabad'aya"
Ammi tace"Gaskiya to bari ka Hakuri kana ci zama da yunwa ina yaga amfani in wani cutar ta kama ka fa..?
Abun wanke hannu yace ta tara masa sai da ya wanke hannu da bakinsa sannan ya koma ya kishingida yana Hamdala ni na kwashe kayan zuwa Kitchen ban koma Falon Abba ba,sai na wuce dakin da na sauka nayi shirin kwanciya ban san kuma ya Abba suka karkare mganar ba da Ammi sai washegari Ammi ke kara min mganar cikin wasa tace"Jiya kin ji Baban ku da rigima. Kamar wani yaro yana zama da yunwa sai kaci abunda ke hannunka in ya dawo sai yaci na gida ba shikenan ba"
Nima cikin Dariyan nace"Ba matsala fa Ammi za'a iya yi masa abincin sai Direba ya rika zuwa yana karban masa'"
Ammi ta kalleni kafin tace"Ko..?duk wahala ce Fa'i bar rigiman Baban ku kin ji"
Ni kuma na Dage sai a rika yin haka Ammi ta tabe baki tana fadin"Ke mai Uba ko..?Allah ya ba da sa"a
Abba na dawowa ta fad'amai sai ya Daga waya ya kirani Lokacin ina waya da Badariya sai da muka gama naga kiransa sai na saka Hijabi zuwa Falonsa,a chan na iske Hafsah da Nana khadija suna ganina suka fara Rige rigen tashi Ammi ta kallesu tana Fadin"Daga gani baku da gaskiya ko..?
Ina Dariya nace"Ammi Wainar Fulawa na soya nafa saka musu nasu. daga shigata wanka suka zagayo suka Kwashe wanda na bari zan ci"
Ammi tace"mugaye shiyasa zasu gudu"
Dariya suka saka Nana Khadija tace"Bani bace fa Hafsi ce"
Hafsatu tayi saurin cewa"Wlh bani ba ce ni da bana cin wainar fulawa ma"
Hararanta nayi kafin nayi mgana ta kama kanta Abba waya yake yi shiyasa bai sakamana baki ba sai da ya gama su kuma Lokacin sun fice suna Dariya su san abunda suka aikata.
Zama nayi gefen Abba muka gaisa ya amsa cikin Sakewa kafin yace"Mamarku ta fad'amin kin ce bazaki bar babanki da yunwa ba ko.?
Ina mirmishi na Daga kaina kafin nace"To Abba kana damu meyasa zaka zauna da yunwa?
Abunda kake so shi za'ayi maka."
Jinjina kai ya yi Lokaci daya yana fadin"Nagode sosai Allah ya yi miki albarka yasa ya'yanki su rama miki.
Ammi ta amsa da Ameen kafin tace"Ba ka ce Allah ya bata miji nagari ba..?
Ina jin Haka na mike ina fadin"Abba mu kwana lafiya"
Ammi ta bini da Dariya tana Fadin"Diyar taka Baban Nana sai kayi da gaske ko wani gwaskan muka samu sai ta bamu kunya na lura da take takenta"
Abba ya murmusa kafin yace"kyaleta ba mai yi mata Dole. in ma bazata kara yin auren ba ina bayanta"
Ammi ta karkace baki kafin tace"Haba da kuruciyarta Baban Nana..?Allah zai kawo mata wani wanda zai kaunace ta saboda Allah ya rud'ata ta zo da kanta tana fadin Abba na amince masa"
Ta karishe fad'a tana Dariya Abba ya jinjina kai yana Fadin"Allah yasa ni dai a nawa shawaran ta daidaita da Baban yaran nan ishaq ya yi nadama sosai wlh in da zata koma da ni kaina naso hakan'"
Yana mgana Ammi na tabe baki sai da ya gama sannan tace"Nafi yi ma Fa'iza sha'awar sabuwar rayuwa akan ta koma Rayuwarta ta baya kwata kwata ishaq bai chanchanci a basa wani Dama ba, gwara haka dai kowa da nashi Kaddaran"
Kai kawai Abba ya kada kafin yace"Tunda baki son sa ai komai zaki ce, ammh duk in da zata je bai kai inda ta fara gina Zuru'arta ba azizat. da sabon yabe duk lalacewar tsoho wlh gwara tsohon yaben nan ni a ganina"
Ammi ta kada kai kafin tace"Wlh wani Sabon Yaben yafi tsohon sau Duhu"
Kyaleta yayi sanin Halinta ita ko taki Hakura tacigaba da fadin"kuma in kana mganar ya'ya ne ai sun saba da Rashinta,suna zaune gidan uban su in da ya dace da su ita kuma Allah ya bata wani mijin taje tayi auranta ta Huta taji dadinta"
Abba ya gyara zama yana fadin"Allah ya bata Azizat"
Dariya tayi kafin tace"Ameen Baban Nanas d'ina"
Girgiza kai yayi yana mirmishi kafin yace"'Allah ya shirya Maman Abdul'ahad'
Da Ameen ta amsa mai tana Dariya mganar Fa'iza suka rufe su ka kama na Raliya da mganar sai Walid ya yi kwari za'a shiryamata tafiya wajen mijinta.

******

Kamar yadda nayi alkwari ban sauya ba tunda ina nan ba ranar Tafiya. Goggo ma bata damu ba tasan daman Ammi nata korafin rashin zuwana,aranta daman tasan sai an ganni kawai,daman ni nake yin girkin Rana sai nake dib'arma Abba Ammi ta kirasa ya turo Direba ya Daukan masa ya kai masa watarana ma in ya makara sai dai a basket yake tafiya da abun karin nasa ya yi achan ba'a Rufe Sati ba Ranar Abba ya dawo yace yunwa yake ji sosai.
Ammi ta kallesa yana ragema Tie din wuyansa tsukewa tace"a'ah ina abincin da direba yakai maka..?
Kai ya girgiza kafin yace"Wani abinci..?ai ina gaya miki tun rana na biyu da Ashuru ya fara karbo'min abincin su Engr Bashir suka sakamin ido. wlh tun suna su biyu har sukamin gayya suna min tsiyan ina musu wayau ina barin su da abincin kedaran maza ga mai dadi da Dadin dand'ano,da nakan samu naci ko ba da yawa ba,ai yau ko a bakina ina gaya miki Engr ya ga Shigar Ashiru Office d'i na da kwandon abincin bai yi mgana ba sai da aka tashi sallah da cin abinci yaga mun zame jiki mun shige Office dina ya Rutsamu Maman nana"
Ammi ta zaro ido tana Fadin"Allah yasa ba laifi kuka yi ba?
Abba yace"Wani laifi..?ai shima cewa yayi an munafuncensa barin ma ni ban taba gayyatansa shima yazo aci abincin da shi ba,karshen ta dai wanda zan ci na bar mai ni da yunwa na yini wlh sai santi suke suna fadin muna jiran na gobe Engr Usman"
Ammi na Dariya tace"To sai kace musu me..?
Abba yace"Nace ba mai gajiyarmin da D'iya kunyar Engr naji domin da kansa yace a fada miki a sawo da nashi Gobe ba Baban Nana kadai ke kaduna ba"
Ya karishe fada yana Dariya Ammi ma Mirmishinta take yi kafin tace"Allah Sarki kada ya damu zan fad'ama Fa'i ta kara sanwa Hannunta ya yi albarka"
Abba yace"Ban so a rika wahalar da ita ba domin Engr ya yi mgana ba, har ni hakura zan yi mu rika cin wanda ma'aikata ta bamu"
Ammi tace"A'a bazai ayi haka ba. bazai gagara ba in sha Allahu"
Da farko Abba bai amimce ba Darajan Engr da ba abunda bazai iya masa ba yasa ya amince,ammh sai da ya kirani yamin mgana har da bani Hakuri ina Son Halin Abba mutum nagari mai sanin Darajan dan Adam
Ni ko nace masa bakomai na saba ba aikin da zai gagareni nan duniya.
Abba nata min godiya kamar bai isa dani ba.
Tunda ga ranar na kara sanwa a babban Tukunya nake yin girkin,a cika manyan kololi direba ya kai musu bayan abinci kullum da kalan lenukan da nake hada musu kala kala wadanda muka koya a katsina da kuma daman wadanda na iya tun a baya abinci ko kala kala nau'ika Dabam Dabam,ko wata rana da kalan Godiyan da Abba zai ce sun ce ayi min in ya dawo da farko sun zata Ammi ce ke yin girki daga baya ya fada musu Diyarsa ce to sun zata ko cikin ma yaran da ya Haifa ne.
Abba da kansa ya fad'amin wani cikin abokan aikinsa yace a jinjina min tabbas a gaisheni bai taba cin girki mai Dadin girki ma ba har ko na matarsa Ranar ma Dubu Ashirin Abba ya kawo min Sabbin yan Dubu Dubu yace gashi in ji Engr yace a kai ma yar Baiwa.
Ammi nata Dariya da naki karban Abba ya min tsawa yace maza na karba ai kyauta suka bani na wahalan da nake yi sai na karba,Itama Ammi da nace ta ciri wani abu ki tayi haka takemin ko Aikin Hada Turare na samu in na bata wani abu bata karba,Sai dai na bama su Hafsah kowacce dubu uku suna ta Murna.
Inno ma na bata Dubu ukun ta karba tana ta saka albarka tana nan idonta ya tashi tana ta fama da shi Baba Ati na Korafi bata dawo ba.
Yau da gobe bata bar komai ba,Har ga shi su Abba sun kamallah warkshop din su cikin nasara,Ranar da suka gama washegari bayan Abba ya fita ya kira Ammi a waya yace ayi girki na Mutum goma haka su Engr sun ce zasu zo godiya anjuma da Daddare.

Bana gida ma Lokacin ina gidan Raliya ni da su Hafsah Ammi tamin waya,daga gidan Raliya Ashiru Direba? ya wuce damu kasuwa nayo cefane,a hanya ma muna ta waya da su Anum sun samu wayar Mama,Amir ne kadai bamu yi mgana ba shi bai cika karamniya ba. sai mu yi waya da sauran yaran sau nawa shi bamu yi ba ko yana daki ko yana karatu baya son damuwa sai dai mun yi waya da shi ta wayar Jamal in yana gari zai saki jiki mu sha Hira da shi na lura Shirgin yaran ne baya son shiga gudun reni.
Tare da su Hafsah muka yi aikin Tuwon Shinkafa mukayi da miyar Allayahu wacce taji kashin Rago da manshanu sai Ferfesun kayan ciki da priderice,sai Fruit salat sai nayi musu kunin Aya ga zobo,sai lemun kankana,sai yammah muka gama muna gamawa ana kiran sallar mangariba Ammi bata da ko yar aiki komai ita ke yi da kanta,su hafsah na bar ma gyaran kitchen din ni kuma na tafi yin wanka nayi sallah ba Karya nagaji sosai shiyasa ina fitowa daga wanka nayi sallah na kishigida ina azkar barci barawo nata son sace ni karar wayata yasa na zabura Jummala ce ta kirani kan mganar gidan Alhaji Bukar na cikin gari sun turo da kaji talatin za'ayi musu Dambun kaji na girgiza kai ina fadin"Kai aikin ya yi yawa jummala..?zaku iya kuwa..?
Jummala tace"Zamu iya maman Amir ga Zainabu ta dawo ma, sai nayi ma su laure mgana su Auwalu sai su tayamu Matsewa"
Kai na jinjina kafin nace"Sun hado da kayan yi ne..?
Kai tsaye tace"Ban duba ba tukunna"
Ban damu ba nace"Duba bari na kira Goggo mu yi mgana"
Goggo na kira bayan mun gaisa na fadamata yadda muka yi da jummala Goggo tace"Sai su yi ga su Auwalu ba komai zasu iya, da? kina nan ai kun sha yin masu yawan su"
Jin haka yasa sai nace to shikenan bayam gama wayarmu da Goggo ashe ma matan gidan Alhaji Bukar ta kirani sai na kirata daga baya mukayi mgana tace an ce bana nan,ammh sun kai ma Jummala nace ta fadamin kada su damu za'ayi ammh sai nan da kwana Biyar zasu samu tace bakomai sun san ka'ida na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login