Showing 195001 words to 198000 words out of 288345 words

Chapter 66 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

721

ya Daga sama sosai sannan ga maleria"
Cikin mamaki Ishaq yace"Hawan jini Abba?Fa'iza ke da Hawan jini?
Cikin mamaki Abba yace"Eh baka sani ba?Goggon su tace an yi shekaru fa"
Sai ya kasa mgana kunya ya kamasa,To yaushe ya san Laluran Fa'iza ballatana yasan Halin data ke ciki Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un bazai raba dayan biyu ba,Dalilinsa Fa'iza ta kamu da wannan cutar nauyi da yadda ya fara fallasa kansa yasa bai kara ce ma Abba komai ba suka yi sallama Ya bar Abba da kara auna Tambayarsa kan mizani girgiza kai yayi a fili ya furta"Allah yasa ba abunda nake zargi ba ne. Domin in zargina ya tabbata bazan ragama kowa a kan wanda ya nemi kashemin y'a ba"
Abba ya fada yana kokarin daidaita kansa shi mutum ne mai zafi baya son ka wulakantasa ko kaci zarafinsa alhalin shi bai ci naka zarafin ba,Sannan ya'yansa ba abun wulakantarwa ba ne,shiyasa yake tsaya musu tsayin daka ga duk wanda ya nemi tozartasu ta kowacce siga.
Sai Dare na Farfado kuma Alhamdulillah na farfado cikin Hankalina sai dai tun da naga Abba sai kuka,alluran barci akayi min na koma barci kamar mattaciya sannan har da rashin samun hutu da bana yi sukace. shiyasa sukace zasu rikeni na Tsawon kwanaki anan.
Sai da su Anty Nasara da su Yaya Mariya sukazo Yaya isa ya tafi da Abba gida yaje ya huta yaci abinci,Goggo kuma bata koma gida ba su Hafsatu suka zo mata da abubuwan da zata bukata,nan ta kwana tare dani kafin kuma wayewar gari ciwo na ya shiga kunne kowa ana ta kiran wayata bata hannuna tana wajen Yaya mariya,da Safe na tashi Lafiya sai dai idanuwana sun yi luhu luhu sai ciwon kai da bai sakeni ba,ammh bana ma kowa mgana in an gaisheni sai na amsa dakai.
Zuwan Abba ya rikitani yana cemin"Fa'i ya jikin naki.?
Sai kawai na Fashe mai da kuka sai ya zauna gefen gadon yana Lallashina fadi yake yi"Kinga bar wannan kukan kin ji ko..?ba mai kara takura miki Fa'iza har sai kin samu lafiya"
Jin haka yasa na tsaigaita da kukana Daman Fargabata kada Abba ya ce na koma ma Ishaq abu na farko da zai Umarceni naji na kasa cika umarninsa ammh jin haka yasa sai naji nauyin kirjina ya kwanta,Kaina kawai na Dafe nayi kasa da kaina ina ji Abba nata waya ciki har da Nana Fadila na kasa kunnena sai naji ana mganar su Amir da sauri na Dago ina kallon Abba tun kafin in yi mgana yace"In ta kara jin sauki zuwa yammah sai a had'ata da yaran su ji muryanta ko zasu samu natsuwa"
Sai? na kurama Abba ido har ya gama wayar ya kariso gareni yana kallon yadda na rame da bai taba Lura ba sai yau cikin son kwantar min da Hankali yace"Kada ki damu su Amir na wajen Nana Fadila tace suna ta kiran sunanki ne, sai nace ta bari in kin kara jin sauki zaki yi mgana da su ko..?
Kai tsaye na girgizama Abba kai karo na farko da nayi mgana nace"Ku kyalesu Abba. gwara su saba da rashina"
Na karishe fada muryata a shake,Gabadaya sai suka bi ni da kallo ganin haka yasa na koma na kwanta na kauda kai ina tsiyayan Hawaye ni kadai nasan yadda nake azbatuwa da rashin su Amir ammh bani da mafita kila tamu kaddaran kenan dagani har su.
Wasa wasa sai da na Shafe kwana Biyar kwance a gadon asibiti,ranar da na kwana Biyu Ammi ta zo Dubani ita Nana khadija da Yaya Abdul'Ahad da Raliya,aranar kuma Abba ya koma tare da su da Hafsah da zata fara karatunta a Kasu Kaduna State University,Abba ya tafi da Dokar kada wanda ya karamin wata mgana a kyaleni sai nasamu lafiya tunda likita yace jinina ya yi sama a guji tadomin da abunda zai rika tadamin Hankali. da wannan Abba yace a rabu dani mganar Ishaq ko ta yarana kada a sake Daukomin ita,a kyaleni sanda na samu Cikakkiyar Lafiya sai a zauna a samu mafita shi kuma Ishaq din Abba ya masa mgana da kakkausan murya akan kada ya baro aikinsa ya taho in yana so ya shiga mganar in kuma baya so shikenan ya taho Dole ya Hakura ya zauna su Anty Binta kwana Hudu sukayi suka biyo mota ita da Anty Hure,suka bar Mama agida ita kad'ai tunda yaran sunki zama kamar ma basu san su ba har Shi kanshi Baban ya kasa Lallashin su,Anty Binta ita kanta tasan rabuwar Fa'iza da Ishaq wani abu ne wanda kowa ba zai so faruwansa ba,Da ka gansa kasan yana cikin damuwa duk ya fita Hayyacinsa,Abinci siya yake yi Mama bazata iya wani girki ba. Anty Binta a ranta ta saka cewa in suka koma zata je ta samu Fa'iza ta mata mgana ta roketa ko zata koma ko saboda yaran dake tsakanin su.
Zainab kuma daman tace sai ta gama shirinta,Ishaq din tun a washegarin tahowarsu Lagos?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya fada mata Halin da ake ciki itama hankalinta ya tashi tace zata kirani to kuma tun ranar take kirana bana Dauka bata san ina Gadon asibiti ba,sai daga baya Yaya Mariya ta Dauka ta fadamata ga Halin da nake ciki, sai jikinta ya karayin sanyi itama ta kuduri niyar cewa kafin ta wuce Lagos zata zo ta sameni mu yi mgana domin har ga Allah kamar yadda na bata gummuwa a auranta da Honey itama bazata zo aurammu ya samu matsala ba.
Tunda ya fad'amata cikin damuwa cewa Saki nake nema batayi mamaki ba,tunda ai zuwanta tasan wasu abubuwan dake faruwa tsakani ga Allah abunda Honey da su Mama suka aikata,ma Maman Amir bai kyautu ba.








*Janafty*
*24/07/2023*




[7/24, 11:17 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3002*

Kimanin kwanaki takwas kenan da sallamoni daga asibiti bayan na shafe kwana bakwai sati d'aya kenan karkashin kulaawar likitoci.
Na dawo gida da Tud'in mganguna tare da Dokokin likita kan na kiyaye shiga Damuwa da tsananta ma kaina Dogon Tunani,duk jinsu kawai nake yi ana iya raba bawa da Tunani ne..?ballata ni da tunani ya zame min dole ba ma sai na gayyace shi ba.
Tun ina asibiti ina amsa wayoyin yan'uwa masu min sannu sama sama,da kuma muka dawo gida na karajin sauki Tiryan tiryan nake mgana da mutane,sai dai kamar yadda Abba yayi gargad'i ba wanda ya karamin mganar Ishaq dasu Amir duk da suna raina nima nayi kokarin yakice tunanin acikin raina,Kud'in da aka kashe a asibiti na Dawainiyata duk Abba ya dauki nauyin komai da komai bayan na koma gida kuma Goggo ta mike tsaye ta cigaba da kula dani kamar yadda ta saba itama kamar yadda Abba yace bata kara tada wata mganar ba.
Mun yi waya da Anty Fadila ta gaisheni bata min mganar komai ba nima ban mata ba,Haka zalika Badariya ma ta kirani tamin sannu itama a bakinta nake jin jamal sun gama Jarabawa zasu yi graduation dinsu sannan ya taho gida,to shima a daran ranar da ta fadamin haka ya kirani ya gaisheni da farko na zata ba su san ina Karofi ba sai da naji yana tambayata ya su Goggo? sannan nasan sun ji Labari ammh yadda basu nuna min komai ba nima ban nuna musu ba.
Abun mamaki hatta da Mama sai da ta kirani kuma ina da tabbacin shi gogan ya fad'a musu banda Lafiya ta,ni banganeta da farko ba saboda ban da lambarta,sai da tamin bayani sannan na gane bayan mun gaisa tamin sannu,sai naji tana ta kame kamen mgana ammh ta kasa fad:a sai kawai ta bige da fadin"Kiyi hakuri Fa'iza ki yi hakuri don Allah"
Toh kawai nace mata saboda na kashe mganar,Kuma muna mgana da mama yau gobe Ishaq ya dosa kirana a waya na ki dauka Saboda so nake na yanke alaqa da shi a yanzu tukunnah ko zam samu natsuwa inaga shine sai ya kira Abba ya fad'amai ya kirani ya gaisheni ban amsa ba,Damn kuma Abba a rana mukan yi waya sau uku sau hud'u shi da Ammi da sauran yan'uwana Hatta Hajiyar su raliya ta kirani ta gaisheni ita da sauran yayyin su Raliya tace a bakin Raliya taji bani da lafiya,Abba ne ya yi fadan meyasa ban Dauki wayar Ishaq ba..?
Sai na kasa mgana cikin Umarni Abba yace in ya kira na dauka mu gaisa Dalilin da yasa daya sake kira na Dauka muka gaisa kenan bazan taba iyama Abba gardama ba daman ba Halina ba ne.
Mun gaisa kamar bakin juna ya gaisheni na amsa a Tunkushe,kamar bana so,ina jinsa ya dade yana Auna mganganunsa kafin ya fara fadin"Fa"iza kin gani ko.?Dukkanmu bamu da natsuwa yaranmu ma basu da natsuwa basa tare dani suna wajen Fadila,ki dawo Fa'iza mu rumgumi ya'yan mu kamar yadda muka saba"
Ina jinsa yana kuma kai aya na katse kiran ina,jin wani takaici ya kara kumeni.
na kara tabbatarma kaina Ishaq bazai taba sona ba, zai yi kokarin maidani ne Saboda inganta gidansa da wani Muradinsa,Zainab ai mun yi mgana da ita ammh itama ban bata damar min wata mgana ba,Ranar ina tare da baki Yaya Asiya da yan gidan su Ammi Mota guda suka zo dubani sai nace mata ta bari zan kirata nayi baki Daganan kuma na manta ban nemeta ba.
Nana Fatima duk ta waya muke mgana da su ammh ta min alkawarin zata zo har karofi ta Dubani,ina Dakin Goggo bana aikin komai daga ci sai shan mgani sai kwanciya,na rame sosai duk nayi zuru zuru in na kwanta ban da tunanin su Amir ba abunda nake yi ina sharan kwallah Ko Goggo ta ganni ina kuka ci kanki bata cemin Ita da Yaya Mariya ke Dawainiya dani tunda koda yaushe tana gidan,haka ma su Anty Nasara Suma gidan suke yini da matan su Yaya isa wani Lokacin sai in Dare yayi ne,Mallam mijin Goggo ya tarkata kowacce zuwa gidan mijinta,Ni daman ina Daki daidai da Falon Goggo bana lekewa.
Na maida kaina wata Shuru shurun karfi da yaji lura da yanayina yasa suke kyaleni kawai da kuma dokar Abba.
Kabarin komawata Karofi ya shiga kunnen dangi da Dadama,har Hajiyar Dala ita kuma daman iyalan Anty Binta zasu fad'a mata tunda ga ma Halisa a kusa da su,bata zo ba sai dai ta kira Goggo ni ban ma sani ba sai da Yaya mariya ta shigo dubani Goggo na dakin tana bani mgani suke mganar naji ashe bayan ta kira Goggo sun gaisa sai ce mata tayi"Aisha yanzu da girmanki da komai zaki yarda yarinyar nan Fa'iza ta ce zata kashe auranta ta zauna a gidan ki..?
To in ta kashe auran uban wa zai rike mata ya'yan..?ya kamata fa kuyi Tunani shima dan'uwan mahaifiyar nasu naji ance mganar na hannunsa bai ce komai ba. gwara dai ku maida ta bata da inda yafi nan Ishaq ne Rufin asirinta,kuma ya rufa mata tun a baya bama yanzu ba"
Inajin sun manta ina Dakin ne sai da sukaji nace"In har Ishaq ne Rufin asirina, to na yarda na rabu da shi. In yaso sai asirina ya fallasu a duniya gabad'aya"
Na fad'a ina kokarin maida hawayen da suka cikomin ido ko don ganin Aurena da Ishaq alfarma ne ya zama Dole na nuna musu Allah ne kadai ya isa ya yi ma bayinsa alfarma ba Mutum ba,Goggo da yaya mariya suka kalli juna ganin haka ma yasa na tashi na shige Tiolet na rufe na fashe da kuka,Ina jin su Goggo na mgana a Cikin Dakin ban jin dai me suke fadi daga karshe suka fice sai da nayi kuka na ya isheni sannan na wanke fuskata na Fito ina kara ma kaina karfin gwiwa ba kaina Farau mutuwar aure ba, Sannan ba a kaina aka fara zama zawarci ba kuma ba kaina za'a kareta ba,sai dai nayi alkwarin zawarcina ba irin na kowa ba ne.
ban rabu da Ishaq Saboda na koma makaranta domin na samu Ilimin da yake min gori ba a'a na yanke rabuwa da shi ne,saboda baya sona sannan yana zama dani ne Saboda Kalaman Baba da kuma alfarma. tunda ya auri zabinsa sannan ya Jingine aurena da shi addini ya bani Damar iyayena ko shari'a ta shiga ciki ta raba auranmu.
Ranar kamar an yi min fami Yini nayi ina kuka,ni ko sai na nuna ma masu Tunanin Ishaq rufin asiri na ne da cewa ba shi ya Rufamin asiri ba. Allah ne sannan shi ke rufama bayinsa asirin su na Duniya har da na Lahira. naji kwata kwata ko ina da burin komawa Saboda ya'yana na cire wannan Tunanin ina da yakinin tunda ga Zainab ga Anty Fadila yarana baza su yi maraici a Lagos ba.

*****

Ina da Kwana ashirin da Biyu da jinya a asibiti ranar wata asabar Nana Fatima ta Diro,bata zo da yaram ba. daga ita sai Direba tace kuma zata kwana min Daya sannan ta koma,tazo min da katan katan din lemuka da kayan karin jini,sai pepe Chicken da yawan shi,gefe daya ga Yam ball,sai Faten wake da yaji hanta da allayahu,Naji dadin zuwanta sosai daman kuma ni na fada mata bakina bayamin dad'i sosai ba kasafai nake son cin abinci ba,kuma naci Faten waken sosai ya kuma saka bakina yayi dadi.
Mun kule a daki muna ta Hira na saki jiki da ita saboda Nana Fatima ta Dabam ce gaskiya ina kaunarta don Alah kamar yadda take kaunata,Ba ta sako min mganar Ishaq ba kwata kwata. sai dai tana ja na da Labaran da suka saka na saki jiki muna ta Hira kowa yazo dubani Ranar sai yayi mganar sakin jikina sai an ga Nana Fatima sai ace Lalle jinina ya hadu da ita.
Mun tsinke da hira ko kiran wayata ban ji ba,muna ta hiran ginin Abba da aka gama komai Fenti kadai ya rage Nana fatima ke cemin"Kila har da Inno zata dawo nan"
Ni kuma sai nace mata"Anya..?Abba ban ji yana mganar ba"
Sai tace min"To ai naga Inno ta saba da Baba Ati ne dakyar ta yarda Abba ya Dauketa zuwa nan sai dai su dawo tare"Kai tsaye nace"Ita kuma Ammi ai bazata ji dadi ba in dai Inno ta dawo nan da zama"
Muna cikin Hiran ne Abba ya kira wayar Nana Fatima bayan ta Dauka sun gaisa tace gata ta ga Fa'inzan sa Cikin Dariya yace"Au madallah ashe ke Fa'iza ta samu yau ba'a ji kiran Abba ba"Dayake ta saka ta a amsa kuwwa ina ji.
Cikin Dariya na karbi wayar ina gaisheshi ya amsa yana fadin"Fa'in Fatima shikenan yau ina ta kira baki Dauka ba ashe Fati ce tazo ta sha gaban Abba"bakina na rufe da Hannuwana ina yar Dariya nace"Abba wayar na nesa ne ban ji kiran ka ba kayi hakuri"
Da Sauri yace"Bakomai Fa'iza daman naji ya jikin ki ne..?na kuma jiki Lafiya lau ga Nana nan ta wakileni ki kula da shan mganin ki kin ji ko..?
Na gyada mai kai Lokaci daya ina fadin"Toh Abba"
Sallama muka yi gabadaya ya kashe wayarsa bayan yace min zai zo da zaran aiki yayi masa sauki.
Mun cigaba da Hirarmu da Nana Fatima sai taba kashin wuyana take yi tana Fadin"Haba Fa'in mu wad'anan kasusuwan fa..?
Ina Dariya nace"Daman ina da kashin wuya. Bani da kiba tun asalina"
Nana Fatima tace"Har da ta damuwa da kuma yanayin rayuwa Fa'i"
Kai Tsaye nace mata"To bawa ai ba'a rabasa da Tunani ballatana mata ire irena da suka samu nakasu ta bangarori da dama"
Sai a alokacin ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Fa'iza daman fa zuwana ba na duba ki ba ne. Harda cire miki wannan tunanin a ranki"
Sai nayi dariya ina kokarin mantar da ita mganar nace"Shine kika k'i zuwa da su Jalil.."?
Hararata tayi kafin tayi mgana mukaji Goggo na faman maraba da bakuwa afalo,Muna dakin bamu fito ba Goggo ta lekomu tana fadin"Ke fa kin yi bakuwa. abokiyar zaman ki ce ta zo yanzu"
Ido na zaro kafin nace"Zainab..?
Ban gama rufe baki ba sai gata ta shigo,da cikinta na fara cin karo har ya Fito dayake mayafi ta sanya ta kara Kiba ta zama katuwa,cikin Mirmishinta na yan gayu tace"Ni ce Maman Amir kin yi mamaki ko..?
Ni da Nana Fatima muka kalli juna kafin ni na yunkura na mike naje na Tarbota rumgumeni tayi tana fadin"Sannu Maman Amir kin sha jinya"
Na amsa mata ina kokarin karban karamin akwatin hannunta da jaka na jata gefen gado ta zauna ina fadin"Sannu..ai sannu na wajen ki maman yan uku da nauyin jiki haka kika Dauko hanya..?
Kai Tsaye tace"Ya zama Dole tunda kin Hana Honey sukuni dole nazo nayi masa biko"
Ban ce mata komai ba na fita falo na barsu suna gaisawa da Nana Fatima Ruwa na Dauko mata da lemu na kawo mata,ruwan kawai tasha tace min tana so tayi wanka sai na nuna mata Tiolet ta shiga ni da Nana Fatima sai muka fita falo mu bata waje ta natsa kan kujerun falon Goggo muka yada zango nan Goggo ta same mu ta kallemu tana fadin"Daman kinsan zaki yi bakuwa baki yi mgana ba Fa'iza..?
Cikin girgiza kai nace"Wlh ban sani ba Goggo ni bamu yi mgana da ita ba"
Goggo ta kada kai tana fadin"To me za'a dafa mata..?
Kai tsaye nace"Abunda ya sauwaka Goggo kada ki matsa ma kanki".
Goggo ta wuce tana fadin"Ke dai bari. ai bakon ka Annabin ka Fa'iza"
Sai da ta bar falon Nana Fatima ta kalleni tana fadin"Wannan ita ce abokiyar zaman naki..?
Na gyada mata kai sai kawai itama ta tabemin baki tana fadin"Lalle to me tazo yi..?daga Lagos din take kenan..?
Da sauri nace"A'a ita bata bisa ba..Tace sai ta gama kintsawa inajin bata riga ta tafin ba ne"
Daganan Nana Fatima bata kara mgana ba,sai muka sauya hirar muka Shiga wata mganan muna nan zaune sai ga Anty Nasara tazo sai muka hade muna Hirar gabadaya,Abinci da tazo da shi aka dibar ma zainab Farar shinkafa da miyar allayahu,da Nama taci kadan sai ta kishigida hutawa sai da aka kira mangariba na tada ita tayi sallah muma muka yi.
Sai bayan mun idar muka zauna muna kara gaisawa ina tambayanta yara tace suna gida wahala ce tazo dasu tana fama da kanta.
Na gabatar mata da Nana Fatima sai ta kalleni kafin tace"Ok..nagane Daddy ya bani Labarin Kanin mamanku friend dinsa ne yarsa ce ko..?
Sai na gyada mata kai itama Nana Fatima na gabatar mata da Zainab suka gaisa sama sama na wayayyin yan Boko daganan kowacce ta Dauke kanta.
Ni ce muka cigaba da mgana da ita,ban tambayeta ba tace min"Gobe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login