Showing 153001 words to 156000 words out of 288345 words

Chapter 52 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

761

sa gaba suna mgana da juna,ammh sama sama.
Raliya kuma kaduna aka ijiyeta,Sai ta zauna gida kawar Hajiya gidan su Laila kenan.
Tafiyar Badariya ba jimawa sai ga waya daga Abuja akan wani kamfanin Sarrafa fattu da Mahaifin zainab ya taba kai takardunsa sun nemesa,Dole ni nayi murd'a murd'a na basa kudin mota ya tafi,bayan tafiyar sa mun yi mgana da shi sau d'aya ya samu sun yi interviuw sai jiran kiran su bai dawo ba ne saboda baya so bayan ya koma su sake kiransa,To yana zaman jiran kiran nasu ne,Zainab ta fara rashin Lafiya har da kwanciya a asibiti,Ashe ciki gareta da sauran rabo a Tsakaninsu.
Daya kirani ya fad'amin ne bayan suna asibitin da ita nace in ta farka ya bata waya na gaisheta sai dare ya samu ya Had'amu na gaisheta bai fadaminciki gareta ba, ita ce tace min"Maman Amir bakin ki dai ya amsu,zai zo miki da Farhan ki yaye min shi tunda Honey yaki bari na huta hakanan"
Daganan sai na d'ago mganarta nayi murna sosai da Fatan alheri da ta basa wayan nayi masa murnan karuwa sai kawai sai yayi yar? murya yana fad'in"Saura ke. kema na kusa har ba miki alluran.."
Da Sauri na katse wayar ina mamakin a gaban matarsa yake fadin hakan?a fili na murmusa,sannan acikin raina nace haihuwa ai na bar ma, matan so ba irin mu da rabo kan rantse ba.
Kamar cikin na bata wahala ne an dawo da ita gida kwana biyu jikin ya rikice sai da aka kara maidata ita asibitin shiyasa bai dawo ba,Kuma har yanzu basu kirasa ba kuma yace an kira Mutane biyun da suka je interview tare,ni dai na lallashe da cewa Allah ne mai yi kuma shi ke ba da aiki in alheri ne Allah ya basa in kuma ba alheri ba ne, Allah ya musanya masa da wanda yafi alheri.
Ya shafe kusan wata a Abuja ba yara ba ni kaina ina kewarsa kaji Fa'iza da Samun waje wai ina kewar mijin aro.?da Sauri na cire tunaninsa a raina na cigaba da Sabgan gabana ni nake rike da karfin gidan duk da muna da sauran kayan abinci, sannan daga Gidan Hajiya ma ta aiko mana da shi,Sannan na samu aikin yin Humra da kwallacha da kudin nake ta riritawa muna cefane da Hidiman yara..

******

Wata ranar asabar data kama kwanan Yaya Ishaq Talatin da hud'u da tafiya Abuja mun yi waya da shi a daran jiya har da yara suka gaishe da Antyn nasu tana gida an bata Bedrest,Da gaske yake da yace yayi kuskure kuma yayi nadama zai gyara kuskuransa,yana kokarin kirana in dai baya garin sannan zai ji ya gidan yake tafiya mganarsa kenan"Nagode Fa'iza Allah yayi miki albarka"
Safiyar ranar sai da na zane Musty sannan yaje Tahfezz da shirin sa bazai je ba,ya zauna yana min rigima na shiga jikinsa da Bulala,Daman tun jiya nake jin jikina ba dadi,da Safe kuma sai fama da sanyin jiki Hafsah ta shiga makaranta zasu su yi wani aiki ita da Sauran yan ajinsu tunda ta fita ina kwance afalo ban yi komai ba sai dai in masu siyan kunin aya da zobo sun yi sallama na mike na basu, Tunda jiya nayi da yammah shiyasa yau da Safe nace bazan yi ba sai da yammah.
Wayata na cikin Dakina na baro ta ana ta kirana ban ji ba,barci ne ya kwasheni nan saman kujera acikin barci sai na ganni a gari Dabam ba karofi ba kuma ba katsina ba,bakon wajen da mutanen da ban sani ba,Kamar kuma acikin barci naji ana kiran sunana a firgice na mike ina Salati sai naga Mama a saman kaina, na mike zaune ina raruman da'nkwalina da ya fad'i saboda barci lokaci d'aya? ina fadin"Mama.."
Kallona tayi cikin nazarina kafin tace"lafiyarki kuwa.?Isa tun dazu yazo yana? ta sallama baki ji ba..?
Sai gabana ya fad'i na zare ido ina fad'in"Wani Isan.?Yaya isa."
Kafin na karisa ya d'ago labule ya shigo a gaggauce yana fad'in"Fa'iza maza dauko hijabin ki Karofi zamu tafi yanzu"
Gabana ya fad'i ras! Cikin Dafe kirji nace"karofi..?me ya faru ne..?
Na fad'a ina wuce Mama zuwa gaban Yaya Isa itama Mama sai tabi bayana tana fadin"Isa lafiya kuwa.?
Cikin natsuwa yace"Lafiya lau kada ku damu.Goggo tace na dauko su ita da Hafsah akawai wanda zai gan su ne"
Dagani har Mama sai muka bisa da kallo zan yi mgana da sauri ya tare ni da cewa"Ki sako hijabi muje sauri ake yi Fa'iza"
Jikina na rawa na ruga daki na Dauko Hijabi na fito ina fad'in"Mama su Amir"
Da mamakina sai kawai tace"kuje ko taliya zan dafa musu,tunda akwai komai kafin ki dawo"
Sai kawai nabi bayan Yaya isa da gudu daya riga ya fice gabana na fad'i jikina na rawa a raina nace kodai Goggo ce..?da sauri nace"Aa ba haka ba ne"
A mota na same shi na bud'e gidan gaba na zauna cikin Sauri yace"na kira hafsa tana makaranta zamu biyu mu dauketa"
Sai kawai na Sadakar Mun rasa goggo,kawai sai ji yayi na fashe da kuka cikin kukan nake fadin"Allah Sarki Goggo"
Tsawa ya dakamin yana fadin"Wayace miki wani abu ya samu Goggon.?
Cikin hawaye nace"To me zai saka kazo da gaggawa ka daukemu zuwa karofi..?
Hankalinsa na wajen tuki yace"To ba mutuwa ba ne abun farinciki ne, Dan'uwan mahaifiyarku ce ya bayyana, shi da mahaifiyarsa yau a karofi"
Na ji dai kalmar dan'uwan mahaifiyarku a kunnena sai na Dafe kirji ina fadin"Ta madina..?
Kai ya gyad'amin yana fadin"Shifa..Sauri suke yi shiyasa Goggo ta tasoni daga gun aiki tace na dauko ki keda Hafsah"
Daganan ban kara bi ta kansa ba farinciki da wani irin zumud'i ya sarkeni hannuwana na da'ga sama ina fadin"Alhamdulillah..Allah abun godiya"
Har muka isa makarantan su Hafsah bakina yaki rufuwa a waya ya kirata ta fito a gaggauce itama kamar ni duk ta Rud'e sai da yayi mata bayanin da yayi min sannan itama ta rud'e da Murna tana fad'in"Yaya Isa ya ka gansa? yana kama da Tamadina..?
Mirmishi yayi yana fadin"Tsammanin abunda baku yi tsammanin ba. muje dai zaku gansa labari bazai gamsheku ba."




*Janafty*

[7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2012*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Har muka isa karofi ban sani ba, na lula cikin wani irin farinciki da zakwad'i abun da ka dade kana hasashensa bai faru da wuri ba sai yanzu.
Wani irin farinciki ne ace yau ga wani naka daka jima kana jin labarinsa baka taba ganinsa ba, kafin isar mu gidan Goggo a cikin zuciyata na wasaafa yadda zan ga Dan'uwan Tamadina bansan iyaka ba nadai san bakina yaki zama waje d'aya na kasa natsuwa har Hafsah tafini mallakan kanta.
Tunda Muka iso kofar gidan Goggo sai kuma jikina yayi sanyi maimakon na zama ta farkon shiga gidan sai na kasance ni ce ta karshe na koma na rab'e bayan Hafsah kamar wacce tayi karya, gabad'aya sai naji gabbaina sun saki na fara tunanin wani irin tarba ko maraba zai yi damu alhalin bai taba ganin mu ba? sannan meyasa ya kai wad'anan shekarun batare da ya waiwayemu ba?har sai da Allah ya Dauki ran Tamadina basu gana ba?
Ya ya zamu gansa..?mu ma ya ya zai gan mu..?yadda ya zata ko ba yadda yayi tsammani ba?
Duk wad'anan tunanin suka taimaka wajen da dakushe murnanta a fili har Yaya Isa yayi sallama kofar falon Goggo Ya shige Hafsah tabi bayansa nice karshen shiga falon, sannan sallamata ma a saman bakina ta makale idanuwana suka fara wurgawa cikin falon ina neman bakon fuska naga Goggo da megidanta,Sai Baba Ati da wasu Tsofaffi maza daga gidan su Tamadina ne,Sai wata Dattijuwa mai natsuwa da Haiba zaune kan kujera cikin shigar alfarma kallo d'aya zaka yi mata kasan ta samu dukkan gatan duniyan da suka Boye shekarunta.
Gefenta a kasa wajen kafafunta wani kamilin megidanci ne baki sai dai bakinsa ya hade da hutu da jin dad'i da Fatarsa ta sauya,yana Sanye da Shadda Mai ruwan kasa har da babban Riga tana maiko kansa da Hula zanna na mutanen maiduguri,yana duke ne ammh ina iya ganin yadda yake saka karamin farin kyale yana Tsane ruwan Hawayensa,Yaya mariya na gabansa itama a duke kamar kukan take yi, Dattijuwan nan ta rike mata hannu alamun lallashi.
Daga sama naji murya Goggo tana fadin"Alhamdulillah ga Fa'iza nan da Hafsatu nan sun iso.."
Kamar an zabure sa haka ya mike cikin Haibarsa da muryansa da ta dakeni yace"Ku matso nan ya'ya na ku matso naji dumin ku..Ku zo ga Abban ku"
Yake fad'a cikin nuna tsananin murnansa sai alokacin na kara kallonsa ba shakka jini ba karya ba ne ina ganin kama ta jini Tsakaninsa da Tamadina Hafsat ne ta nufesa zata duka ta gaishesa sai kawai ya Rumgumeta,hawayensa na zuba ni kuma ya miko min hannu sai na sulale kasa a gabansa idanuwana sun ciko da kwalla,Dattijuwan nan ta kallemu ta kara kallon mu musamman ma ni sai kawai ta fashe da kuka tana fadin"Allahu akbar daga ganin wannan na shaida jinin Lauratu ne"
Sai kawai ta rikice tana rusa kuka Goggo ta matso tana????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
fadin"Haba Hajiya zuwaira ashe kukan naki bazai isa hakan nan ba..?.
Cikin kukan take fadin"Dole nayi kuka, Dole na koka na yi sanadiyar da na yanke ganawa Tsakanin yan'uwan juna.?kaico na.."
Tafad'a cikin wani yanayi da sauri ya tareta da fadin"Inno ni ne kika yi ma wannan laifin kuma nace na yafe miki ba shikenan ba..? Ni dai naji ciwon rashin ganawa da yar'uwata guda d'aya da nake da shi,Ammh nayi murna daya kasance ta barmun zuru'an da bazan jima ina kuka ba, in na kallesa zan tuna yar'uwata ta bar min su ne domin kada in na zo nayi kukan rashinta"
Gabad'aya kalamansa sai suka sakani rauni bansan Lokacin da na fashe da kuka ba ganin haka yasa sai Hafsah ta d'auka Yaya mariya ma daman mun sameta tana kukan ta ne.Wacce aka kira da Inno ta sauko kasa tana neman Durkusa mana cikin kuka tace"Ku yi hakuri ku yafe min ya'yan nan na zalunce ku na yanke ganawa tsakanin mahaifyarku da dan'uwanta"
Da Sauri ya saki Hafsa bayan ya zaunar da ita ya karisa gareta ya rikota ya maida ta saman kujera yana fadin"Inno ki daina wannan kukan don girman Allah"
Sai ta ji mganarsa ta koma tayi shuru tana sharan kwallah kasa ya zauna a gabanta yana kallonmu d'aya bayan d'aya kamar yadda muke kallonsa. Lokaci da'ya yana Dauke Hawayensa da Farin hanky din dake hannunsa.
Cikin Kayattaciyar Muryansa ya dago yana kallon su Goggo kafin yace"Cikin su wacece tafi kama da yar'uwata..?
Har Baba ati da goggo suna had'a bakin wajen fad'in"Gata nan a gabanka Fa'iza kamar Tamadina ta tsaga kara yadda ka ganta haka mahaifiyarta take. sai dai ita bambamcin Tamadina bebiya ce ita kuma Fa'iza jinta ne yake da rauni"
Kawai sai ya kuramin ido Lokaci d'aya yana fadin"Naji dadi da akwai fuskar da zan rika ganin yar'uwata a ciki, baku da Hoton yar'uwata ku nuna min ya'yana..?.
Ni dai na kasa mgana Hafsah ce tayi karfin Halin cewa"Yaya Asiya na da shi a wajenta"da alamun karin bayani ya ke kallon mu Yaya mariya ta jinjina kai tana fadin"Itace babbarmu wacce su Goggo suka ce tana kano tana aure"
Sai ya jinjina kai yana fad'in"Rashin sani ne ai kano gida ce a wajena chan na girma nayi karatuna kuma chan nayi aure,kafin chanjin aiki ya Dawo dani nan kaduna,yanzu komai ya kare tunda Allah yasa nazo kuma na ganku nayi alkwarin bazan kara sakacin da zaku rasani ba"
Sai ya fara sharan kwallah ya cigaba da fadin"Yau yau din nan Inno ta fad'amin ina da yar'uwa bayan ta sanar dani inda dangin Babana suke,a gaggauce na taho ko iyalaina ban zo da su ba suna kano ana auran kanin Mai dakina,yaran duka suna chan,ni kaina Tafiya gareni zuwa porthercourt gobe akwai Taron da muke dashi daga wajen aikin mu aka turamu,ammh nace bazan zauna ba sai nazo na ga ahalina ina zuwa kuma sai na samu labarin dangi duk sun kare itama yar'uwan nawa Allah ya yanke ganawa tsakanin mu da ita"
Inno na sharan kwallah tace"Allah ya jikan Hafsatu ina kallon fuskarta ranar da zan bar garin Lokacin bata wuce shekara Biyar ba"
Aka amsa da Ameen Ameen mu dai sai kuka muke yi muna sharban hawaye Shi ma kukan yake tayamu ammh nasa bamai sauti ba ne,yana dai yi yana tsane hawayensa,da farin Hanky din dake Hannunsa..
Baba ati ta gyara zama tana fadin"Zuwaira wani dalili ne yasa tunda kika tafi baki kara waiwayomu ba sai yau.?Sannan wannan yaron baki taba sanar da shi komai game da mahaifinsa da Danginsa ba..?
Inno ta fara kuka kasa kasa tana fadin"Ba laifin Usman duka acikin abun da ya faru kada ku manta na bar garin nan yana da kananun shekarun da bazai iya tuna komai ba!
Duka abunda ya faru laifina ne shiyasa nace ku yafemin"
Hannayenta ya rike cikin Lallashi yana fadin"Inno ashe kukan nan ban ce ya isa haka ba..?
Da jajayen idanuwanta tace" USMAN rashin kuka na ba zai sa laifina yaki bayyana ba,da gaske na zalunceka na tafi dakai na raba ka da Dangin mahaifinka gashi karshen karshen sai da na kawo ka gare su"
Sai ya kasa mgana Saboda bata kiran sunansa sai dai tace mai BABAN Nana kamar yadda matarsa ke kiransa.
Gyara zama tayi tana kara gyara zaman mayafin dake kanta tace"Bani da wani kwakwaran Dalilin aikata abunda na aikata Sai dai nace rashin son da ban yi ma mahaifin Usman ba aka aura min shi,alokacin ina da wanda nake so ammh Mahaifina yayi min Dole,ya aura min shi aka kawo ni wannan garin kada ku manta tun Lokacin da aka kawo ni,ban yi zaman Dad'i da kowa hatta da kakarku da ta haifi mahaifiyarku Lauratu,Sannan ban saki jiki da kowa ba,bani da aiki sai kuka sai zama cikin Damuwa Ko Usman Rabo ne ya rantse tsakanina da mahaifinsa? aka same shi,ko da zama ya kare tsakanimu da shi bayan rasuwarsu zuciyata bata Rusuna ba. gani nake yi in na barsa a wajen ku bazaku barsa ya zauna dani ba, shiyasa tunda kuka amince na tafi da shi a raina nakudiri niyyar zan Nisanta shi da abunda ya shafi wannan nahiyar,Tsakaninsa da mahaifiyarku bai fi shekaru uku ba yana gabanta domin neman irin haihuwan yakai mallam ga aurena sai bayan na haifi Usman sannan Lauratu ta Haifi Hafsatu tabbas nasan an haifeta da laluran rashin ji da mgana,Sai dai bamu zauna da lauratu ba,Duk da mun yi zaman kishi na mutanen na wanchan lokacin,Ni ba kishi nayi da ita ba, ni tsanar duk abunda ya shafi mallan nayi shiyasa itama ban yi mu'amala mai kyau da ita ba,Ita kuma tayi kishi dani a matsayin wacce ta auran mata miji duka duka zamana ko shekara goma ban yi ba na bar karofi na koma karaye gidan mahaifina ba jimawa shima ya rasu.sai yayana ya Daukeni zuwa cikin Hukumar Dala ta kano inda yake zaune da iyalansa yana kasuwanci.
Shi ya rikeni ya rike Usman har ya zama abunda ya zama,A baya shi ba mai arziki ba ne,d'an kasuwa ne mai karamin karfi ammh daga baya ya samu arziki har mun koma cikin garin kano a anguwar mandawari da zama,A hannunsa Usman yayi karatu,tun bayan dawowarmu kano Usman na yawan son ya tuna yar'uwansa da Dangin mahaifinsa,Sai dai ina kokarin shafe Tunanin acikin ransa a hankali a hankali sai abun ya shafe a ransa,Da kuma girma ya kamasai sai dangina suka zame masa komai yaya na shi ya bashi auran Diyarsa Azizatu ya aura a shekarun baya har sun tara zuru'a a tsakanin su,Daga baya Usman ya so ya san wani abu kan Dangin mahaifinsa ni nayi masa iyaka da hakan nayi masa Kaushin muryan cewa in ya kara tambayata garin mahaifinsa ko abunda ya Dangance shi sai na Dagamai Nono, daga Lokacin Bai karamin mganar ba.sai naji dadin haka ammh a raina ina jin ba dadi kamar wani abu mai nauyi ya zauna a kirjina,har ga Allah kiyayyar mallam ce da na sakama raina ta Haifarmin da haka na dad'e ina mafarkai marasa kyau har barci bana samu a Lokacin Dalilin haka yasa na zauna sai nayi Tunanin wannan shine babban laifin dana aikata wanda Allah bazai yafe min ba,nayi mafarki da mallam yana fad'amin na ki had'a kan ya'yansa Allah bazai barni ba.yau da Safe na kira Usman na fad'amai komai a kansa sannan na shaida masa yana da yar'uwa a garin Korafi inda na Haifesa"
Ta karishe fad'a cikin kuka Lokaci daya tana fadin"Ku yafe min ya'yan nan wlh sharrin dokin zuciya"
Ba wanda ya iya mgana sai ajiyar zuciya na mutanen dake falon Mu ko sai kuka muke kamar yanzu akace Tamadina ta rasu,Baba ati ta gyara zama tana fadin"Ashhha.Shiyasa dokin zuciya ba dadi..Yanzu ina amfanin wannan..?lauratu dai da mallam Hashimu sun bar duniya itama Tamadina Allah ya karbi abunsa ba domin wad'anan yaran data bari ba da yau kin jefa d'anki cikin Damuwa saboda bazai ga wani abu daya Danganci yar'uwansa ba"
Goggo tace"Koma dai menene yanzu ya wuce daman chan Allah bai kaddara saduwa tsakaninshi da Tamadina ba,Mu yi hamdala tunda muna da sauran rayuwa.Ga ya'yanta nan data bari shiyasa nace a dauko su su ganka kaima ka gansu Asiya ce kadai bata nan saboda tana nesa"
Yana duke a gabanmu kansa na kasa yana sharan kwallah cikin Raunin murya ya dago yana fadin"Naji dad'i da na iske zuru'ar yar'uwata.ku kalleni nan daga yau ku masu gata ne.Bazaku kara kukan maraici ba"
Yaya mariya ta dago tana sharan kwallah Lokaci d'aya tana fadin"Kawu.."
Da Sauri yace"Ba sunana kawu ba. ABBA zaku rik'a kirana kamar yadda y'yana ke kirana.nayi shekaru da nauyin kirji ina tunanin akwai wani abun da ban isa garesa ba acikin wadanan shekarun ba,na samu wadatar Rayuwa da cigaba nayi karatun addini nayi na boko har matakin Masters,na fara aiki da Hukumar wutar lantarki na jahar kano. kafinMakotan su Baffa sanadiyar gidan kakanin megidana shi chairman ne na babban Headquater refinering and petrochemical,Limited Edo state,Sanadinsa na samu aiki a Nageria National petroleum corporation NNPC,na kaduna wato Kaduna Refinaring and petrochemical company,Nayi auri da Diyar Baffa Azizat,mun haifi yara Hudu babban su shine Abdul'Ahad ma'aikaci ne hukumar sadarwa ta layin Mtn,zai yi aure wattani kad'an masu zuwa sai Nana Fadila tana Lagos tana aure sai Nana Fatima tana Dutse tana aure,Sai Nana khadija dake gabanmu yanzu tana aji daya ajami'ar kaduna ina zaune a anguwan NDC kaduna ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login