Showing 159001 words to 162000 words out of 288345 words

Chapter 54 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

758

ya karishe da fadin"Duka wad'anan kannenka ne nauyi ya kara hawa kanka Babban yaya.kamar yadda kake tafiyar su da Nana Fadila haka zaka tafiyar da su ya'yan yar'uwata da na baku Labarin bamu had'u ba har Allah ya Dauki ranta wad'anan sune iyalan data bari"
Cikin gamsuwa yace"In sha Allahu zaka sameni mai kulawa da kannena kamar ko yaushe"
Jinjina kai yayi kafin ya Kallemu yana fadin"Fa'iza Asiya,Mariya da Auta ga yayan ku nan sunan sa Abdul'Ahad zai yi muku Jagoranci kamar yadda zan jagorance ku, ku gaisa da shi"
Daya bayan d'aya muka rika gaishe shi yana amsaawa cikin Sakewa kafin Abba ya yafito Nana Fadila ta matso kusa da shi Tana fadin"Na'am Abba."
Cikin Dattakonsa ya nuna mu yana fadin"Ga yan'uwanki nan.Kinga Asiya itace kamar age mate din ki to ki riketa Amana ku zama kamar yadda kike da Nana Fatima"
Cikin gamsuwa tace"In sha Allahu Abba"Nan itama muka gaisa ya yafito Nana fatima ya gabatar mana da ita yana fadin"Ga age mate din ki nan Fa'iza ki kula da ita kamar yadda zaki kula da Nana khadija tana da raunin ji Hallita ne haka aka haifeta ki kula da ita"Da sauri ta rike Hannuna tana fadin"Ni daman Abba ina ganinta naji ina sonta"gabadaya sai akayi Dariya Abba ya Kira Nana khadija da Hafsah ta Dawo rakata Tiolet ya had'a su da Hafsah sai Yaya mariya taga an wareta Cikin damuwa tace"Abba ni wa zaka damka ma Amanata?
Yana dariya yace"Amanarki tana hannu nagari D'iyata. Maman Nana ga wata amanar na kara miki Dukkansu ya'yanki ne kamar su Nana fadila ki zama uwa tagari garesu kamar yadda na sanki kada ki kara bari suyi kukan maraicin rasa uwa"
Da Sauri ta Gyada kai Lokaci d'aya tana jawo Yaya mariya ta Rumgume tana fadin"In sha Allahu Baban Nana,Mari babban kifi rabu da wad'anan yaran ke da uwa kika samu sukutum ga Abdul'Ahad da zan saka yafi shagwabaki"
Yana dannan wayar sa yace"Itace fv sister di'na ma daga yau Ammi"
Nana Khadija ta shagwabe fuska tana fadin"Kai yaya ni din fa..?.
Yana tabe baki yace"Kin zama tsohon yayi"Sai dariya gabadayanmu Farinciki ya samu muhalli a zukatanmu Abba ya gabatar da su Baba ati ne a matsayin Goggon su kad'ai data rage mu su sannan ya gabatar da Maman Nana a matsayin matarsa uwar su Fadila sai su Goggo a matsayin Dangin mahaifin mu.
Badariya ya gani ya nunata yana fadin"Wannan fa ban ganeta ba..?
Da Sauri nace"Kanwar mijina ne Badariya Abba"
Cikin gamsuwa yace"Itama ya'ta ce sannu Badariya"kanta na kasa ta amsa tana gaishesa sai lokacin Abdul'ahad ya lura da ita ammh shi karon farko ya gane ta,har Hoton wayarsa ya Dauko yana gani to ai dolensa ya ganeta duk kan Hoton Raly dake wayarsa rabin sa tare da wannan kawar nan tata take yi, in bai manta ba sunan? kamar Badar sunan ta, in suna tare wani Lokacin har gaisawa suna yi ta kalleshi shima ya kalleta ammh ganin kamar bata ganesa ba sai shima ya basar.
Yaran duka Abba yasa muka yi masa bayaninsu,muma muka tara su wajen shi muna fada musu Abba ne su gaisheshi Amir ya karisa ya gaishe shi ya Dagosa yana fadin"An ya Fa'iza bazaki bani abokin nan nawa ba yaron ya burgeni akwai natsuwa sosai'
Ina dariya ban yi mgana ba Da Sauri yace"Kada ki damu in dai bangaran megidan? ne ke da shi Duka ya'ya ne ina da iko a kanku da ya'yan ku gabadaya"Nana Fatima na gefe tace"Allah ya bar mana Abba"
Nana Fadila da Inno na tayata Dariya shi bai ma jinsu ba Hankalinsa na wajen Anum kuke tana faman tambayansa"Kai ne Abban Umman mu.?ya gyad'a mata kawai sai ta kalleni tana fadin"Umma ba kin ce Baban ki ya rasu ba har muna addu"a ba?
kafin na samu amsar bata ya amsata da cewa"Wani Sabon Abba ta samu ke kuma kin samu sabon megida ko bakya so na..?.sai su Anum aka noke kai ana dariya kafin tace"Ina sonka mana ammh sai na girma zamu yi aurre"Gabadayanmu muka saka Dariya Ammi tace"Kaji min yarinya Daga haduwa sai fashin miji"Abba ya Dora t saman cinya yana fadin"Maman Nana dai ana ta kishi"Sai dariyan barkwancin su muke yi, Sai yarinyar da suka fara shigowa naji Nana Fadila na kiranta Falaq,ita tayi ma mamanta Rad'a a,kunne sai ta Dago tana kallon Anum kafin ta kalli Ammi tana fadin"Ammi Kin ji Falaq tace Anum tazo bikin uncle Junaid ta ganta a gidan Anty Laila"
Sai kallo ya koma kan Anum tana jin haka jikinta na rawa tace"Nima na ganta"Sai mamaki ya kamani Ammi tace"Haba ni fa ina ta yi ma yarinyar nan kallon Sani sai da Falaq ta fad'a na tuna kunga yara da rashin mantuwa ko..?
Nana Fadila tace"Ko ita ce Anum d'in da kika Dameni da zencenta da kika koma gida.?sai yarinyar ta Daga kai sai mamaki gabadaya ya kamamu Abba yayi mirmishi kafin yace"To yara dai sun san juna sai aji ta ina aka haihu a ragaya"
Ammi ta kalleni tana fadin"Fa'iza ko har dake aka zo bikin Lailan ne bamu hadu ba.?Laila ta kaduna..?
Sai alokacin na tuna bayan Amir yayi zaraf yace"Umma Anty Laila da take zuwa ita da Anty Raliya"
Da Sauri nace"Laila..Oh na tuna ta Aa Anum kad'ai taje bikin ita ta roki babanta ya barta suka tafi da ita"Sai da ake mgana Badariya ta tuna inda tasan Abdul'ahad da Sauri ta kallesa tana fadin"Abdul'Ahad right.?
Sai ya jinjina mata kai yana fadin"Yes Badar ko..?
Sai ta fara Dariya kallo ya koma kansu ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza kinsan waye..?wanda zai auri Raly ne fa."sai na bude baki ina fadin"Raliyar ki.?sai ta gyada min kai sai na kasa mgana Ammi tace"ikon Allah kusan Raliyar da Abdul'ahad zai aura kenan..?kusan Hajiya Aisha Saulawa kenan?
Kai tsaye nace"Nasan ta sosai akwai zumunci a tsakanina da ita da ahalinta. Raliya kuma yar gidana ce Aminiyar badariya ce, kanwar mijina"
Sai mamaki ya kama kowa,Ammi ta bude baki kafin tace"Ke Fa'iza ba dai ke bace mai Turaran kamshi na Katsina ba..?
Sai ta bani dariya na gyad'a mata kai lokaci daya sai na Tuna da Sauri nace"Ba dai ke ce yayar mijin Laila da na hada turare humra da Kwallacha wajen ki ba..?
Sai ta fara Dariya tana fadin"Baban Nana diyar taka fa sananniya ce.
Ba shakka ina turaren da nace maka naga Amaryan junaid dasu masu kamshi na tambayi inda akayi mata tace Daga katsina kawar mamanta Hajiya Aisha ta bada akayi mata?ka manta har kana min tsiya shegen son kanshi bazan iya siya a kaduna ba sai na lula har katsina..?
Sai ya daga mata kai yana fadin"Duk na tuna"Da sauri tace"To ai di'yar kace mai hadawan Allah mai iko sannu Fa'iza"
Sai kallo ya koma kaina Nana Fatima tace"Ammi wai turaran da na sace din nan da nazo duba Inno..?
Dakuwa tayi mata tana fadin"Asirin ki ya Tonu kaga barauniyar gidan ka Baban Naana ina fad'an an dauke min Turare kace baka da barawo a gidanka to wannan fa..?
Gabadaya dariya muke cikin Had:e rai yace"Yayi mata kamshi ne ta ara ko Nana Fatima..?
Da sauri ta daga kai Lokaci daya tana fadin"Fa'izata zata sake had'amin nawa Ammi na dibar miki"
Dakuwa ta sake yi mata tana Dariya AbdulAhad na dariya nace"Nana Fatima kamar itace mujaheed d'an sandan farin kayan wajen Lauya mgana"
Abba yace"To Za'ayi mata taron dangin abun kuma ma nasu ne.daman haka abun yake ba gashi da aka had'u ba yara suka fara shaida da juna ba"
Nan fa falo ya ka?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
ure da Hira suma basu da bakunta sun saki jiki suna ta Hira damu,Ammi ko ta shige cikin mu ba ruwanta Inno dai Goggo tajata Daki don ta Huta Mama ba baka sai ido ta zama kamar mujiya afalon da na gabatar da ita a matsayin uwar miji na, cikin girmamawa Abba ya gaisheta sau taga ba ma raina gorin asalin datake yi min sai da ta raina kanta da taga Abba da Ahalinsa.
Abdul'Ahad kuma na gefe ya Kira Raliya sun yi mgana da yace ga wata su gaisa sai ya bata Badariya tayi matukar mamakin inda suka Hadu sai Badariya ta bata labari tuni ta bazama Dakin Hajiya tana gayamata yadda komai ya wakana Daman tun a satin Abdul ya gayamata zasu zo katsina wajen dangin mahaifinsa tana ta mamakin daman su ba yan kano ba ne..?sai yace eh asalin Babansa haifaffan garin karofin katsina ne.
Abba da shi da yara aka barsu suna ta Budiri da kuma mazan su Yaya Ishaq kowannen ya gabatar da kansa garesa,Duk rashin sakin jikin Yaya Ishaq ya saki jiki da Abba Saboda yana da Dadin zama sallar la'asar ya fitar da mazan zuwa masallaci mu kuma muka yi namu acikin gidan yaran kuma tuni sun hade kansu suna wasa.
Bayan an dawo sallah ne aka zauna zaman cin abinci,su Abba a kofar gida suka baza musu tabarma suka zauna mu kuma muna cikin gida,Girkina aka ci daga karshe zobo da kunin Aya har ana Fada da Nana Fatima da Nana Khadija Goggo na Dariya tace"sai kun gaji da sha duk sana'ar yar'uwan ku ce gatan? nan Fa'iza"
Ammi ta saka salati tana fadin"Allah mai Hikima sannu Fa'iza kai masha Allah"tana sha itama tana santi hakama abinci da akace ni nayi ta kalleni Lokaci d'aya ta kalli goggo tana fadin"Goggo Fa'iza yar baiwa ce gaba da baya fa ba'a sani ba"
Nana Fadila ne ta kara mata jaka a baya da sunan waigi ta ko mako mata Dakuwa suka koma gefe suna Dariya,ashe suma mazan sun yi santi sai da Daddare bayan an sake Taruwa a tsakar gida ciki zafi ga ba wuta ana Hira Abba yace"wacce cikin ya'yana tayi shinkafar nan mai dan karen dadi?
Da sauri Nana Fatima tace"Abba Fa'iza ta ce"Nana fadila tace"Ji bakinta Fa'izan mu dai malama ai bataki ke kad'ai ba ce"
Sai suka fara gaddama muko murna da Farinciki yaki barin mu,Abba ya? raba rigiman da fadin"Naji fa'izan kowa da kowa ne shikenan"
Daganan sai ya kashe mganar ya kalleni yace"Fa'iza komai da ruwan ki kenan..?masha Allah Allah yasa albarka"
Aka amsa da Ameen sai ya kalli Ishaq dake dauke da Ahmad Lokaci da'ya yana fadin"Ishaq ka yi dace gaskiya zaka karamin Sadaki saboda wannan girkin da zobon data kware akwai cikon Sadaki"
muka saka dariya gabadaya Ammi tace"Baban Nana zaka zama surukin zamani ne..?
Da Sauri yace"Daman nace miki ni surukin da ne..?
Yadda yayi mganar ne ma Dole sai da mukayi Dariya Allah Sarki Rayuwa daman haka Allah ya kan shirya lamuran bawa, sai kusan sha Biyu su Abba suka tafi masauki bangaran da aka? gyara musu ,Mijin Yaya mariya gida ya koma ya kwana kuma shi ya sauki su Yaya ishaq a gidan iyayansa Dakin kaninsa shi da mijin Yaya Asiya muko duka nan gidan goggo muka kwana har da Mama da Badariya mu da yan'uwan mu raba Dare mukayi muna Hira kamar mun shekara tare Nana Fatima na zama Fa"izanta abu kad'an sai kiji tace"Fa'ina kaza kaza"
Ita ya'yanta Biyu,Jidda da jalil kanana ne,Saboda sai da tagama Service dinta tayi aure Nana Fadila ke da uku FalaqFahad,Da Fairuz,Yadda kuka san mun dade da sanin juna saboda yadda muka shaku daga Dare zuwa Safe suma suna da Tarbiya daidai gwargwado Ammi ta basu tarbiya itama irin Abba ne akwai barkwanci.
Da Safe ni suka yi ma chaa na shiga kitchen nayi musu abun karyawa da su Yaya isa suka jifgo cefane,ko wajen karyawan har sai da akayi santi Tunda nan mazan suka zo gidan Goggo aka had'u aka karya gabadaya.
Yaya Abdul'Ahad na shan ferfesun kayan ciki da nayi musu ya kalleni yana fadin"Ina fatan kina koya ma Raly irin wannan girke girken ko?
Sai Falon ya kaure da Dariya Ammi tace"Baban Nana saka ma d'anka waigi shima Cikin Dariya yace"Ammi ba fa santi nake yi ba"
Abba na gefensa yace"My son yi santin ka dadi'n abun ba kai kad'ai ba ne har da Baban Nana shima yayi santin"Kai Abba akwai ban dariya Ammi tace"Baban Nana kasan wa na ke tunawa in na samu abinci mai dadi haka..?
Yana shan tea ya zuka ya dawo da mug din yana fadin"Engr.mana"
Cikin gyad'a kai tace"Wlh shi ke fad'omin rai kasan shi da son abincin Hausawa na gargajiya da na zamani."
Abba yace"Ki bari musamman ace ya samu zobon nan na Fa'iza da shi da Maltina ko coke har abada,kinsan ya tsani lemukan ba gwamgwani ko da yaushe korafinsa Baban Nana duk kayan basir ne zakin su ya yi yawa"
Ammi tace"Allah sarki Engr kamar ba Jinin yarbawa"
Abba yace"To ai kinsan ya sirka ta bangaran Hajiya Shukra shiyasa zaki ga rabin sa bahaushe rabinsa bayarbe ba, ba domin ma ya tashi cikinsu ba sai in akace miki ya had'a iri da yarbawa sai ki karyata"Ammi tace"Nima ka manta ganin farko da nayi masa sai da na karyata"
Abdul'Ahad na gefe yace"Abba kana ji da Engr nan Sosai"
Abba yace"Mutum ne har da rabin mutum..Ya yi min abunda bazan taba mantawa ba yayansu.Engr ya goya mutane Dabam dabam irina da yazama madubin su kirkinsa nake fada'maka sai ka zauna da shi zaka san hakan"
Abdul'Ahad ya jinjina kai bai ce komai ba,Abba da Ammi suka cigaba da mganganunsa kan Engrn da su,suka? san shi.
Haka dai muka gama karyawa cikin Nishad'antarwa da Annshuwa,ranar a gida muka yini ana ta hira sai yammah muka fita Lokacin Yaya Ishaq ya koma gida shi da Mama da yara wanda Dakyar na samu Anum tabisa da ta saka rigiman bazata ba nace bata isa ba makaranta,Badariya na tare dani sai gobe zamu koma katsina Tunda suma Jibi zasu tafi saboda ayyukan su Abba su, suNana Fadila kuma zasu koma gidan mazajen su.
Da yammah Karofi muka zaga har gidan su Tamadina da yazama duk ya rushe Abba yace zai saka a bige shi a gyara zai zama nan zasu rika sauka in suka zo,Baba Ati kuma da ita zasu tafi zata zauna tare da Inno a gidan Yaya mariya muka kai wajen goman Dare,Muna ta Hira,
washegari kafin mu wuce Katsina sai da muka biya Dutsemah gidan da Tamadina tayi aure har da Abba akaje sun gaisa da mutan gidan da shi kanshi megidan suna ta fadin irin Hallayar ta madina Abba ya cika su da kudi muka bar su,suna kwallah muma muna yi Daganan muka rabu da Abba,ya koma karofi,mu kuma
Direban Abba ya kaimu har katsina da Abdul'ahad shi ya rigamu yin gaba wajen Raliya yaje ,Gidana muka sauka Nasan ko ban fad'a ba sun ga yanayin gidan susan muna da karamin karfi,Nan muka ci abinci mukayi sallah mun iske Anty Binta a gidan sai kallon su Nana Fadila take da ya'yansu taga ba ma raina a wajen su,sai la'asar na rakasu gidan Hajiyar Raliya har da Ammi,inno na gidan goggo tace bata iyawa kafa ciwo Hajiya taji Dadi ta karbemu hannu goma kamar yadda ta saba.
Ammi ta kalleta tana fadin"Hajiya ashe ya'ta ce ma ke turarukan kamshi bansani ba..?
Hajiya na dariya tace"To ba gashi yanzu kin sani ba!
Ammi tace"Wlh ai naji dadi kamshi har karkashinn Gadon Baban Nana insha Allahu"
Gabadayamu sai da muka Dara Raliya nata kunyana nace"Ni daman ai Antyn Raliya ce, ba kunya Tsakanimu Hajiya nata mamakin lamarin na zauna nayi mata bayani atakaice tace ikon Allah kenan itama Raliyan a bikin Laila suka had'u da Abdul'ahad duk da daman an san suna sanadin Iyayan Laila.sai dare muka baro gidan Hajiya da Sha tara na arzikin da ta hada mana, adaran suka koma karofi Washegari kuma suka koma gida Saboda a ranar Nana Fadila da Nana Fatima zasu koma gidajensu.
Kafin rabuwar mu Abba ya Tattauna damu kan abunda muke bukata sai muka kasa mgna sai yace bakomai Ko mazajen namu da bai samu zama Sosai da su ba, saboda ba Lokaci ammh zai gayyace su har gida su Tattauna mun raba ma junanmu Lambar wayanmu,Kwana uku muka yi tare kamar mun shekara tare Basu kyamace ni ba, duk rashin son mutane na, na shaku da su Nana fatima mutane ne masu karamci ilimi waye kudi da nasaba da sanin ya kamata.yaya Asiya ita yar gida ne Ammi yar kano ce Haifaffiyaa Dala ta kano,kuma daman ga bikin Raliya dake gabatowa mun zama iyalai D'aya kaduna zata yi diban manyan baki.
Badariya da Raliya sun fi kowa murnan wannan al"amarin,Ko Yaya ishaq sai da ya yabi kirkin Ahalin Abba gabadayansu.
Kuma kowa ya gansu yasan suna da kudi kuma sun taki gwamnati,Abba kamar yadda ya fada tare da Baba Ati suka koma Inno nata jin Dadi ta samu abokiyar zama tuni har Abba ya damka ma su Yaya Isa kwangilan gini an fara baje gidan ana sake sabon Faundation.
Sai da nafi sati ban koma da sana'a akan zobo da kunin aya na ba,Saboda rashin zamana waje d'aya,Muna yi da waya su sosai barin ma Nana Fatima har megidanta data koma sai da ta bani muka gaisa,Kowa ya ganni yasan na samu natsuwar zuciya da kwanciyar Hankali muma mun zama yan gata abu kad'an Abba yace me muke so..?Hafsah ta zama auta kowa ita yake riritawa yanzu haka ta kosa su samu Hutu ta gudu kaduna gidan Abba tayi Hutun ta achan.
Sati daya tsakani da zuwan su Abba ranar da Daddare muna zaune Yaya Ishaq yakalleni yana fadin"Abban ku aikin me yake yi?
Tunani nayi kafin nace"Na manta kamar ko a NN Me naji su Yaya Asiya na mgana?
Sai Yace"NNPC dai ko..?
Sai nace"To kila nan din ne".kai ya jinjina kafin yace"Akwai kudi gaskiya babban ma'aikatan matatar mai ne fa"
Ni dai ban ce mai komai ba, ammh kowa yaga Abba ai yasan ba karamin mutum ba ne.
Acikin watan Abba ya kira kowannen mu a waya kowa ta fadi abunda take so ni dai jari nace ya karamin yana Dariya yace"To Fa'iza aammh ai ni burin gina miki katon gidan abinci nake da shi, tare da shagon gyaran jiki da kayan kamshi"Sai na Bushe da Dariya ina fadin"Allah ya amsa Abba"
Dubu dari biyu ya turamin yace na rike a hannuna kafin yaga abunda Allah zai yi Dukkammu haka yabimu ya bamu kuma yace zai kira duka mazajemmu ammh sai yaje warri ya Dawo? warkshop din da zasu je suyi na wattani biyu in ya Dawo zai nemesu,Sannan ya aiko mana da kayan sawa dukkanmu mu da yaranmu da mazajen mu,abun sai wanda ya gani da wad'anan kudin na cigaba da Rufamana asiri,sannan gefe daya muna waya da su Nana Fatima muna tsara shiryen shiryen Bikin Raliya da aka matso da shi kusa,Da sai bayan wata hudu za'ayi yanzu kuma an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login