Showing 267001 words to 270000 words out of 288345 words

Chapter 90 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

753

sai ta bimu a raina nace Anum ta girma bazata daina shagwaba ba.
Mun dauki hanyar Edo cike da kewa na tuna Maa yadda ta rika sakamana albarka da fatan zaman lafiya itama tace duk abunda nake so na kirata ita uwa take gareni.
Hawaye haka suke bulbulomin Duk Dauriyan Engr haka ya rumgumoni yana Lallashina kamar karamar yarinya fad'i yake"Shii..am sorry matata..Ko mu koma ne kawai mayi shagalin mu achan..?
Wata uwar harara na Dago ina hawaye na makamai sai ya yi Dariya yana Fadin"To ba ke bace kina ta kuka ina kike so na saka raina don Allah..?
Hawayen ya fara sharemin?yana Fadin"Kin yi bamkwana da kuka har Abada sai dai na farinciki.
Ki bari kawai mu sha kara'in mu ba gani ba..?ko ni ne baki son gani kike kuka saboda mun baro su..?
Sai na kasa mgana na sunne kaina a saman kirjisa ina mirmishi kamar yadda na yace bayason kuka dole na shanye hawayena ina ji ya saka hannayensa duka biyu ya rumgumoni.
Kaina na saman kirjinsa yana lallashina kamar wata karamar yarinya ni ko na lafe ina samun natsuwa Lokaci d'aya da natsuwar zuciya.
Sai kuma na fara tunani had'e da? kuma Fargaban wata irin kuma rayuwa zan fara gudanawar tare da Engr..?
Shin wani irin bambamci zan samu a zaman aure na?da shi..?
Fatan farinciki nake yi ma kaina ko ya ya ne. Fargabata har da yadda nayi aure abunda ban taba tunanin yinsa nan kusa ba.




*Janafty*
[8/1, 5:16 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3018*

*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Sai Dare muka isa garin Edo,gidan Engr na garin karamin gida ne gaskiya.
Saboda Falo d'aya ne sai bedroom guda biyu sai Kitchen haraban gidan ma karami ne bai wuce wajen ajiyan motoci biyu ba.
Sai Dakin megadi sai daga ciki kad'an D'akin waje muhallin da Direba kan kwana in suna gari.
Mun iso da daddare sannan ga gajiya a tare damu tunda tun da muka zo Benue ban yi wani barcin kirki ba,Shi ya sake fita ya siyo mana abincin kayana ma duka shiya shigomin da shi,ni ko sallalolin dake kaina na fara saukewa bayan ya nuna min Tiolet shi kuma da ya fita ina ga ya yi nasa a chan.
Koda ya dawo har na fara barci shi ya tasheni muka ci abinci rabin ma abincin a baki ya bani,muna gama ci na bingire sai barci ko kayan jikina na kasa ragewa shi ya kwashe sauran abincin yakai kitchen ya dawo ina jinsa yana tashina, na bude ido a kasalance ina kallonsa cikin yanayin mganarsa yace"Ki tashi ki yi wanka ko zaki ji dad'in jikin ki"
Luu nayi da ido na zan koma saboda na jini ne gabadaya gabbaina sun saki kamar wacce akayi ma dukan tsiya.
Ganin na sake komawa yasa ya kyaleni ya shiga tiolet din ya yi wanka Saboda baya so ya takuramin.
Nidai bansan yadda akayi ba naji ya gyaramin kwanciya sannan ya yi ta matsamin kafa alamun Tausa naji yana mgana ammh barci yaci idona, bansan me yake fad'i ba ammh dai nasan ya jima ya na min Tausa da ya yi sanadiyar sawa na kara lafewa samman makeken gadonsa ina kara jin Dadin barcina.
Hankalina kwance Allah sarki bawan Allah shima fa a gajiyan yake ammh bai duba kansa ba yafi ji dani tukunnah
Ckin Dare na farka na ganni nannade acikin kirjinsa ba haske acikin Dakin ammh ta window labulen na dagawa Hasken wata daran goma sha Biyar ya haskemin Fuskar sa.? ko yana barci Mirmishinsa bai barin Fuskarsa yana Sanye da kayan barci ruwan toka masu Taushi,yana rumgume dani kamar wani zai kwace masa ni sai na shiga wani yanayi yanayin da ban taba sanin akwai sa ba, na miji ya Rungume matarsa su yi barci tunda na auri Ishaq bamu taba kwana waje daya daga farkon Dare har karshe ba. koma wani abu yake bukata yana samun natsuwa zai tsallakeni ya barni wani lokacin ko na koma Daki ko kuma shi ya koma Falo ya kwana ammh sai ga shi bingiren rayuwata ya kawoni inda ban sani ba.
Ina yin motsi ya kara saurin rikoni ya maida kaina saman kirjinsa yana Fadin"Nima nagaji Faa'izaa ki barmu mu yi barci"
Yafad'a cikin wata irin murya ashe yaji motsin tashina,sai kawai na bi Umarninsa na koma na lafe saman kirjinsa ina sauke numfashi nayi barci cikin salama barcin da na jima ban yi kamarsa ba.
Da asuba shi ya jamana jam'i bayan mun idar muka zauna ya yi ta mana addu'an zaman lafiya,bayan nan kuma yace na dauko Qur'ani daman nazo da shi,shima yana da nashi ya fito da shi,shi ya fara jawomin aya daga cikin suratul bakara na dauka sai da na karanta masa shafi biyar sannan ya yi kabbara yace na Dakata yayi min tambayoyi kan abunda ya shafi sallah,alwala da Tsarki ba domin ban iya ba yasan na iya domin cike wani bangaran sunnan ma'aiki.
Muna gamawa shi ya karbi Qur'ani ya ijiye saman Side drower din gadon yana juyowa nayi saurin cewa"Ina kwana"
Mirmishi ya yi min irin mirmishinsa mai narkan da zuciyata.
Kafad'a ya noke min kamar karamin yaro kafin yace"Bana son wannan kalan gaisuwan Tife bana so.
kada mu fara haka da ke"
Cikin kallonsa nace"To wata iri kake so..?
Tsam ya mike ya iso gabana ya saka Hannuwannsa ya Dagoni ya rumgumeni kam na wani Lokaci kafin ya sakeni ya dago kaina ya sumbaci Goshina kafin ya tsaya yana kallona nima ina kallonsa gira ya dagamin kafin yace"Ki rama ma kura aniyarta mana"
Kunya ta kamani na Sadda kaina saman kirjinsa da sauri ya Dagoni yana Fadin"A'ah Faa'iza ni bana son haka sam kunyar me..?ni fa mijin ki me Sirrin ki wanda iyayen ki da yan'uwanki suka damka amanarki a Hannuna ni kuma na karb'a da alkawarin zan iya yi na wajen ganin na rike wannan amanar sai ki bari kunya ta shigo zamantakewar mu ta Cutar dani..?A'ah Faa'izaa..!
Bana so..bana son kunyar nan fa"
Ya fad'a har cikin zuciyarsa sai naji jikina ya yi sanyi na Dago ina kallonsa sai ya lakuci hancina yana Fadin"Nayi miki afuwa na yau ammh daga gobe? zaki fara Duty"
Sai na gyada masa kai sake Rumgumeni ya yi ina jin wata natsuwa acikin raina da gangar jikina.
Hijabin da nayi sallah ya ciremin yana Fadin"Jiya kika yi min wayau kika yi barci kika barni ko..?
Ina sunne kaina nace"Nagaji ne"
Shima kai tsayen yace"Nima ai na gajin Faa'izaa sati nawa nayi ina bin Hanya ba kuma tafiyar Jirgi ba"
Sai na kasa mgana Tabbas gaskiya ya fada ya fini gajiya da Sauri nace"To kayi hakuri"
Ina rufe baki ya amsani da fadin"Waya fad'a miki laifi kika yi..?
Sai na rausayar da kaina kafin nace"Nayi laifi mana. muje ka kwanta nayi maka Tausa"
Dariya ya saka lokaci daya yana rike hannuwana ja na yayi muka koma kan gado muka kwanta ya Dora kaina saman kirjinsa yana shafawa kafin yace"Menene na sauri..?
Tausa ai sai kin gaji da yi yanzu dai ki gama Hutawa ni zan kula dake ammh ki sani bashi ne zaki biyani kayana"
Ina mirmishi nace"Kada ka damu Tife zata biya Tosin bashin sa"
Dariya ya saka yana kara rikeni a jikinsa da karfi har sai naji zafi nayi yar kara sai ya sausasauta rikon da yayi min yana Fadin"Ina ji kamar in nayi miki karamin riko zaki iya kubcemin ni kuma bana so nayi rauni wajen rike amanarki Tife na"
Kai tsaye nace"Nasan ai zaka iya.Zaka iya"
Shuru ya yi na wani lokaci ammh bai sakeni ba,har sai na dago kaina ina kalllonsa sai naga shima ni yake kallo maida kaina yayi saman kirjinsa kafin ya kira sunana.

"Faa'izaa..'"

Cikin wata kasalalliyar murya nima a kasalancen na amsa masa,da Na'am sai kuma ya yi shuru har sai da nace"Umh menene..?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Wata alfarma zan roke ki Faa'izaa..?
Kai tsaye nace"Wata irin alfarma ce wannan..?
Kai tsaye yace"Rokon ki zan yi. Don Allah Faa'izan a zaman da zamu yi in nayi miki wani abu wanda ba daidai ba ki yi gaggawan sanar da ni na baki Hakuri,kada kice zaki yi fushi da ni ko? ki yi min horan kusantar in da kike,Zan fi jin zafin hakan fiye da Laifin da na aikata miki.
Ina so komai nayi miki ki tareni ki fad'amin ba kunya ba tsoro ni mijin ki mai sonki da kaunarki ba bautar juna zamu yi ba,bautar Ubangiji zamu yi
Ni dake ladan mu na wajen Ubangiji,kada mu zama bakin juna mu dora zamantakewarmu kan tafarkin koyarwa sunna da addini.? nima in kika min ba daidai ba zan fad'a miki Domin ki gyara nima don Allah ki ankarar dani a inda na kuskure ba iya amanar kan ki ba Faa'iza Amanar junan mu dukkanmu zamu rike don Allah"
Ko kafin ya gama mgana Hawaye sun cika idona yana gama mganarsa suka kwaranyomin ashe akwai ranar da wani namiji zai daukeni nima kamar Sauran mata masu daraja da kima..?
Yana ji na fashe da kuka,kukan dake fitowa daga kasan raina jikinsa na rawa ya mike zaune ya tarairayoni ya Rumgume yana fadin"Kuka kuma..?
Ko na fadi mganar da bata yi miki Dad'i ba ne..?
Yafad'a yana kara rikeni acikin jikinsa ammh na kasa daina kuka saboda abun daga kasan zuciyata yake fitowa,gani nayi ya rude yasa na kara rumgumesa kamkam cikin shesshekan kuka nace"Kukana? na farinciki ne. Ina kukan samun abokin rayuwa irin ka,sannan ina kukan da na rasaka ni ko wani irin asara na Tafka a rayuwata..?
Sai da ya Dagoni muna kallon cikin Idanuwan juna sannan yace"Ni ne da na rasaki da nayi babban asara Faa'iza ina sonki. Soyayya ta gaskiya"
Runtse ido nayi sai ga hawaye sharr,kafin na bude su akansa yana kallona da kaunata acikin idanuwansa sannan ga mirmishin nan nasa mai tsuma zuciyata.
Cikin muryan kuka nace"Me ka gani a tare dani..? Kyau.?kudi.?ilimi..?
Bani da komai fa. Bani da komai anya na chanchanci wannan kaunar daga gareka..?kana da komai,ko ta ko'ina bamu dace da juna ba..ban chanchanta ba..ban.."
Bai barni na karisa ba ya kariso ya hade space din dake tsakanin mu lokaci daya yana sumbar bakina na bude baki zan yi mgana ya tura harshensa cikin bakina da ya yi sanadiyar Daukewar mganata Lokaci daya da wani yanayi da ya zirgamin.
Tun ina rawan jiki sai ga shi na saki jikina har ina rumgumesa cikin samun natsuwa da na samu tun a ranar da auren Engr ya sauka akaina.
Sai da ya yi har ya gaji yana ganin zai rasa control dinsa ya sakeni ni kuma na koma na lafe ina runtse idanuwana Saboda kunyar data Lullubeni.
Rumgumeni ya karayi kam kafin yace"Na rufe wannan mganar. Kada na karajin kin ce baki chanchanta ba. Bana so, raina na kuna,in kuma kina so raina ya rika kuna ne shikenan ki cigaba da fad'a"
Yafad'a har a muryansa ina jin ransa na kuna nasan na ji kalmar bana so din da yasa nayi saurin cewa"Na bari bazan kara ba"
Saman kaina ya sumbata idanuwansa na lumshe yace"Yauwa Tife na"
Mun jima rumgume da juna yana zayyanamin kalaman kauna da Soyayya,yana kuma rarrashi na domin yana yi yana shafa kaina zuwa bayana bansan Lokacin da barci ya kwasheni ba shima dai kusa dani ya koma ya kwanta muka kamkame juna sai Sha d'aya na rana muka tashi ina ta mamakin barcin da na sha.
Yana dariya yace"To kin samu jikin Tosin mana ga Taushi dole ki yi barci baki sani ba"
Dariya nayi masa ban ce komai ba Tunda nasan gaskiya ya fada,Wanka muka fara yi dagani har shi sannan ya fita ya siyo mana abinci nikan sai da nace"Ka siyo cefane na fara girki baka yi ta siyan abinci a waje ba"
Yana dariya yace"Sai yadda kika ce Hajiyata. Siyan abinci kuma daman an saba ganina."
Kai tsaye nima nace"Eh lokacin baka da mata yanzu kuma kana da mata"
Cikin dagemin gira yace"Ehyee! ya sunan matar tawa..?
Nasan zolayarsa yasa na masa fari kafin nace"Tife mana. Tife sunanta"
Dariya ya kwashemin dashi kafin yace"Ah'a su Tife an waye an zama yan gari"
Dariya nayi masa ban biye masa ba tare muka ci abincin yana bani a baki ni da naji kunya nace zan basa sai yace'"Miye na sauri kuma..?
Ai har wanka zaki yi min gama zama dai yar gari. duk ina yi ne na bashi zaki rama ma kura aniyarta"
Ban ce masa komai ba sai dai na sunne kai nayi mirmishi.
Ranar yini ya yi bai fita ba sai da yammah ya fita siyo mana abinci bayan ya tayani mun gyara gidan mun gogesa na saka turaran wuta na da na had'a mai kamshi tunda duk Ammi ta sako min su kamar tasan ko zasu yi amfani.
A burner na saka turaran tunda nazo da kananun abubuwan da nasan zan nema da Engr ya shaki kamshin sai da yayi mgana cikin yanayin mganarsa yace"Kai Turaren nan akwai kamshi"
Ina gyada kai ban ce komai ba sai shine yace"Ke kika had'a..?
Na kara gyadamai kai sai yace"Tab. Masha Allah Zuwa zamu yi mu bud'e gidan Turarukan wuta nan da wani Lokaci sai kiji mun fi Dangote kudi"
Kai kawai na girgiza ina dariya nasan Halin Engr in ya fara zolayarsa sai cikina ya nemi ya kulle saboda Dariya.
Ranar ma tare muka kwana,bai nemi wani abu ba,Sannan shi ya karamin Tausa har nayi barci,abinci ma in ya siyo a baki yake bani gatan duniya dai ba wanda bana gani tun ina Tunanin zai nemi wani abu ina jin kunya har na saki jikina da shi na koya irin gaisuwansa komai kuma yace yana so shi nake yi masa,Sai da muka kwana uku da zuwa na bude wayata na kira su Ammi muka gaisa nayi musu bangajiya nan take gayamin a Abuja suka kwana gidan surukaina sai washegari suka koma kaduna.
Bayan Ammi na kira su Badariya,Anty Fadila da tace min jiya suka dawo Lagos ga Anum ma bata riga ta koma ba har ta bani muka yi mgana.
Dukkansu ba wanda ban kira nayi musu bangajiya ba. Nana fatima sai shakiyanci take min,wai ina cin amarci na kashe waya.
Na kira Abba mun gaisa yanata tambayana ya bakon waje..?
Nace lafiya lau,Tunda dai ba fita nake yi ba ina gida Engr yace duk makotan mu yare ne da wad'anda ba musulmai ba,Har Goggo na kira mun gaisa da Sauran yan'uwa kowa mukayi mgana sai yace na dace sai fatan zaman Hakuri da juna.
Engr bai koma aiki ba yace sai ya yi sati zai koma,ranar da muka kwana Biyar nace ya bar siyan abinci yayo cefane zan rika Dafawa sai da ya kalleni yace"Kin tabbata..?bana so ki na wahala fa"
Kai tsaye nace"Hakki na ne fa na girka na baka ko wanda kaga ina barin ka kana siya na bakunta ne,ni dai kayo cefane zan fara girki"
To kasuwan ma tare muka je muka siyo komai na cefane da kayan abinci naga garin Edo cike da yaruka kala kala da mabambantan al'ummah.
Da muka dawo tare muka shirya kitchen din nayi nayi ya tafi yaje ya Huta sai ya noke kafada har ce min ya yi "Kin manta nace miki sunana makale mata manne mata"
Ai ko naga makale mata girkin ma da nayi na Doya da miyar kwai tare muka yi yana mikomin abubuwa sannan yana tayani Hirarrakinsa masu dadi da ban Dariya.
Da na gama girkin nace masa megadi da Direba kai tsaye yace"Ni kad'ai ne Dolen ki Faa'iza su ko ba Dolen ki ba ne ki kyalesu ina basu kudin abinci"
Tunda ya nuna haka sai ban ja ba,aammh nace masa in ya ragu gudun kada ya lalace zan rika basu sai yace shikenan in ba Takura.
Tundaga ranar na nake yi mana abincin yaci kuma yana Santi yana sakamin albarka wani lokacin har hawaye nake Daukewa a boye ashe ashe nima zanga wannan ranar..?.
Ranar da zakayi ma miji abun alheri yaci da godiya yana saka maka albarka.
Cakarewa ta nake yi a gida ina cin gayuna ban cika dai kwalliya ba tunda ban saba ba,ammh ina saka kaya masu kyau ina gyara kaina.
Tunda Engr yana yabamin ko wani irin shiga nayi ko na burgeshi ko ban burgeshi ba,sai yace"Tife na kin yi kyau"
Wannan yabawar tasa ke karamin kaimi ina jin wani karsashi a kasan raina.
kuma Engr bai taba min korafin rashin kwalliyata ta yan matan zamani ba,zai gani kuma zai yabamin shiyasa ban ma san Lokacin da nake cin masa gayun ba saboda bakinsa da idanuwansa suna nuna Darajata sannan suna yabamin shiyasa nima nake yin wasu abubuwan ban sani ba.
Zuciya tana son mai sonta sannan tana Daraja mai yaba mata.
Ranar da muka cika sati na kira Maa muka gaisa na tambayi Kafaya tace suna makaranta tunda University of Abuja suke yi,bayan mun gaisa sai tace"Kuna nan dai lafiya dai ko..?
Ba wata matsala shi Babatunden d'in bai yi miki komai ba ko..?
Sai nace mata lafiya lau muke haka fa da mukayi waya da Paapa shima haka yace min ko oluwatosin din na bani matsala nace musu komai lafiya muka rabu suna sakamin albarka.
Yafara zuwa aiki ranar yana ta kirana ina waya sai da na gama na kirasa da ya tambayeni da wa nake waya nace ma su Paapa ne.
Kai tsaye yace"Uhm lalle kin kwace gwammati na. Nifa basu kirani ba yau kwata kwata."
Ya fad'a kamar zai yi kuka.
Ina Dariya nace"ko kana kishi dani ne..?
Da sauri yace"Name..?zan famshe a wajenki ni dai in dai zaki gatan tani ai shikenan''Dariya nayi masa ban ce komai ba sai da ya dawo muna cin abinci ya kalleni kafin yace"Wai Hajiya baki gama Hutun naki ba ne..?
Ban gane mganarsa ba nace"Hutun me..?
Sai da ya kashemin ido kafin yace"To ina so na fara kara'i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login