Showing 183001 words to 186000 words out of 288345 words

Chapter 62 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

769

ba,Dagani har Mama muna ta zullumi ni kuma kunya ta saka na kasa kiran Abba ko Yaya Abdul'Ahad kada suga kamar na damesu shiyasa na daure Ammh ko Mama bayan mintina sai ta leko d'akina tana fadin"Fa'iza shuru Ishaq bai kiraki ba ko..?
Ni kuma sai nace mata"Mama in ya kirani ai zan gaya miki. kuma nasan in sha Allahu zai kiramu"
Daganan sai muka koma muka Nad'e hannaye,muna jiran tsammani sai wajen karfe goma sha d'aya saura,ya kirani lokacin yara har sun kwanta Hafsah ce kadai a falo tana karatu,saboda sun fara jarabawa,ni kuma ina dakina sai dai ko da na Dauka bana jinsa har sau biyu,daga baya sai ya kira Wayar mama da ita suka fara mgana kafin ta leko da kanta ta kawo min waya bayan mun gaisa sai kawai ya bige da cemin"Wato Fa'iza ki ji tsoron Gwamnati da kuma in kana da Kafa a Gwamnati. kinsan? 24hrs ya yi yawa Efcc ta saka an kamo Mr James tun jiya kuma yayi mgana. Dalilin dayasa ma aka kirani kenan ma"
Cikin son jin ya aka haihu a ragaya nace"To ya kuka yi da su yanzu..?
Cikin Farinciki yace"Ya amsa laifinsa Alhamdulillah an wankeni daga wannan zargin. ashe da wani suka had'a baki,kinsan kana zaune da mutum bakasan ya tsaneka ba ni wlh lafiya nake zaune da kowa,Yanzu haka dai an yi cike ciken Takardu an tura chan ma'aikatanmu,kuma Efcc ta bani Hakuri tare da alkawarin zata maidamin da kudina da ta karb'a sun rike Mr james a hannunsu suna kara Bincikensa. ammh ni nace na yafe masa Har abada"
Cikin jin dadi nace"masha Allah. Alhandulillah gwara daka yafe masa, ammh shi miye riban abunda ya aikata..?
Kai Tsaye yace"Matsayina ya ke so. Kuma ya samu tunda bayan Dakatar dani shi aka d'aura akan kujerata"
Cikin mamaki nace"Ikon Allah daman ai abun duniya fararre ne kararre ga shi yanzu komai ya kare masa"Cikin jimami yace"Wlh kuwa. Muna chan har karfe Takwas na dare da ni da Abba da Daddy da Abdul'Ahad,da wasu cikin ma"aikatan mu, sai shi chairman na Efcc din da Sauran ma'aikatan su da wanda suka ja Ragamar case dina a hannunsu.Wh Fa'iza Abba yayi min kokari ke kinga yadda Chairman din nan ya dinga bama Abba hakuri.?gaskiya mutumin nan yasan karamci kuma ba fa ba Bahaushe ba ne, Fa'iza Bayarbe ne. abunda na Lura dashi Megidan Abba da yake kira Engr na ji da Abba sosai. tsakani ga Allah cikin gaggawa akayi komai aka gama,kuma Engr ma ba shi a wajen,naji Abba yace yana Edo ki tayani godiya Don Allah"
Ajiyar rai na sauke kafin nace"Alhamdulillah Allah ya kara Tsarewa yanzu kana ina ne.?ko kuna tare da su Abba ne..?
Da sauri yace''Ina wajen zainab nan zan kwana zuwa gobe. Abba daganan jirgi ya hau zuwa warri suna da taro gobe Abdul'Ahad kuma ya hau jirgin kano"
kai na tsaye nace"Ba damuwa ai kana gida kayi zaman ka mu nan ba mu da matsala"Shima kai Tsayen yace min"Aa zan dawo ai ba wajenta nazo ba, itama"
Ban tsaya jan mgana ba tunda ba Hurumina ba ne,in ba wajenta yaje ba, me ya hana yabi yo? Ya Abdul'Ahad su dawo tare ya tsaya nan zai kwana?shine zai zo yana min wata mganar banza jin nayi masa shuru yasa ya kira sunana sai na amsa sai kuma ya kasa mgana sai kawai ya bige da Fadin"Sai dai na dawon"
Yara ya tambaya nace sun kwanta yaso yajani da mgana nace mai barci nake ji duk nagaji cikin Dariya yace"Ai ina samun wani babban aiki duk zaki daina sana'ar nan ta wahala Fa'iza"
Sai ya bani dariya har sai da na Dara kafin nace"To ai ko ni ce da kaina na samu babban aikin ban ji zan dakatar da wannan sana'ann tawa, domin tamin komai a Rayuwa sai dai na nemi Hanyar ingantata kawai'
Da sauri yace"Eh hakane kam.."ina ji sama sama ana mgana ta gefensa ban Tsaya ji ba na kashe wayata na yi kwanciyata sai dai har ga Allah na tayasa murna sai naji kamar komai dake faruwa Mafitan da na Roki Ubangiji ne ya sama min ne.
Zuwa washegari mgana ta watsu a Dangi Mutanen karofi dai Hafsah ta Fada musu su jamal kuma duk mama ta kira su ta fad'a musu abunda ke Faruwa. sannan sai ta kara da fadin wlh duk sanadin Kanin mahaifiyar Fa'iza shi ya tsaya har aka wanke Ishaaq,Har daki mama ta biyoni Tana min godiya ta kuma saka na kira Abba ta kwararamai godiya.
Abba yace"Hajiya kada ki damu.Da Fa'iza da Ishaq duk d'aya suke a wajena duk abunda nayi kamar nayi ma Abdul"Ahad ne"sai kimar sa ta karu a idon Mama,sai da yaya Ishaq ya kwana Biyu sannan ya dawo ranar kuma Anty Binta tazo ita da Anty mahma,sun zo yi ma Mama barka da arziki,Shima din yana samun wayoyin yan'uwa da abokan arzuka harda abokan aikinsa da suka Dad'e ma basu yi mgana, suma labarai yakai headquater din su tunda EFCC ta tura Takardan wanke Ishaq din daga dukkan zargi.
Su Goggo duk sun kirani hatta ko da Yaya mariya,ta kirani su Nana Fatima ma duk sun kirani tace Abba yace su kira su yimin barka da arziki,Har da Ammi kuma naji dadi sosai masoyin ka ne Zaka yi rashi ya janjanta maka sannan in kasamu shima ya tayaka Murna,su Amir nata murna domin ce musu yayi da kansa kud'in Daada ya Dawo ya'yan Umma nan suka Biye masa suna ta tsallen Murna.
Allah shi ke ba? da samu da rashi kuma shi ke da Daukaka da Nasara shu kuma ke da Fad'uwa da Tashi,kwana Biyar Tsakani da EFCC ta wanke Yaya Ishaq ya samu kiran gaggawa daga Headquater dinsu na Abuja aranar ya tafi sai dai mota yabi,bai kirani ba ina ta neman wayarsa a daran a kashe sai da asuba kawai zainab ta kirani ina Dauka tace"Congratulation to us Maman Amir kinga Kuduran Allah ko..?.
Mamaki ya kamani bansan kan mganar ba,ina shirin tambayanta sai kawai ta zarce da fadin"Jiya da Honey yaje ma'aikantan su upper ce suka basa ta maida shi aiki da matsayi mai girma,sun mai da shi office din su na Lagos zai fara aiki nan da wata D'aya"
Karfaffan ajiyar zuciya na sauke a Fili na furta"Alhamdulillah!
Cikin Farinciki tace"Wlh ai tun jiya nayi ta neman wayarki ni da shi bamu samu ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, yanzu haka ya tafi masallaci ne,shi nace bari na kiraki na fara yi miki albishir"
Ciki?jin dadi nace"Masha Allah. Allah ya sanya albarka,ya sa alheri a cikin aikinsa damu gabad'aya"
Ta amsa min da ameen ameen bamu jima,muna mgana ba muka yi sallama,Daganan sai na tashi na shiga Dakin Mama na isketa tana azkar bayan mun gaisa na fada'mata abunda Zainab ta fad'amin Mama ta washe baki tana Hamdala ta daga hannu sama tana yi ma Allah godiya.
Daganan dakin yaran na koma na iske sun idar da salla,Amir da Musty suka hada baki wajen fadin"ina kwana Umma"ina mirmishi na amsa ina fadin"Daada ku ya samu aiki a lagos"Sai suka fara murna har da tsalle Ahmad kenan.
Fita nayi na koma falo sai ga Hafsah ta fito na gayamata, Anum na bayanta ta Daka tsalle tana fadin"Eyyee zamu koma Lagos ehyee.."
Sai tsalle take yi ina kallonta ina mirmishi,sai da gari yayi shaa Yaya Ishaq ya kirani cikin Tsananin murna yace"Fa'iza albishirinki"
Ba da niyyar gwasale shi ba nace"Zainab ta riga ka. Har na shaida ma Mama da yara"Sai naji kamar gwaiwarsa tayi sanyi duk da haka bai nuna ba nan take na tayasa murna ya amsa yana fadin"Wlh ban taba saka rai aiki nan zai dawo gareni ba,Ammh sai ga shi sun kirani sun bani takarda har da karin girma da kuma sauyin wajen aiki"sai na tare sa da fadin"Haka Allah ke lamarinsa. Sai ya baka ya kwace in kuma yaga dama sai ya maida maka mafiyinsa"
Cikin gamsuwa ya gyada kai yana fadin"Hakane wlh. Allah ya datar mu"
Na amsa mai da Amen mun yi sallama yace zuwa anjuma zai kamo hanya ina shirin nace sun yi mgana da Abba?sai na sha'afa sai ga shi ma Abban ya kirani da kansa ina Dauka yace"Congratulation Dougther yanzu na samu labari wajen Dr.Lawal"
Cikin mirmishi nace"Daman yanzu nake shirin kiran ka Abba"
Kai tsaye yace"Gashi ni na rigaki,Duk na kira sauran yan'uwaki na shaida musu. Allah ya tayasa riko Zaki koma kusa da yar'uwanki Fadila tana ta jin dad'i da na shaida mata"
Sai mirmishi na ya Dauke da yake da cijewa muka gama wayar nan,yinin ranar sai amsa waya nake yi har mamakin yarda mganan ta Je, kunnen kowa nake yi,Yaya Asiya tace min Goggo ta fad'amata sai ban yi mamaki bam Saboda ni na kira ta da kaina na fad'a mata.
Ranar ya dawo da Daddare,yana shigowa ni ya fara cin karo dani a Tsakar gida ina kaye kayen kaya sai ji nayi ya Daukeni Caraf ya dagani sama yana juyi dani cikin Firgita nace"Innalillahi ka sauke ni don girman Allah"bai saukenin ba sai da yaji muryan Mama sannan ya saukeni Tana fitowa ya sakeni ya nufeta yana Fadin"Mama.."
Cikin jin dadi tace"Na'am Ishaq naji abun arziki Allah ya sanya alheri"
Ya amsa mata cikin fara'a ta dafa kansa tana sakamai albarka,mganarsa yaran sukaji suka firfito suna masa oyoyo d'aya bayan d'aya ya dinga dagasu yana saukewa Anum sarkin mgana tace"Daada yanzu Lagos zamu koma..?cikin shafa kumatunta yace"Sosai chan zamu koma."
Musty yace"Daada dukkan mu?
Ya gyad'a masa kai Lokaci d'aya yana fadin"Dukkan mu mustapha.."
Amir ne ya kalleni yana fadin"har da Umma da Mama..?
Kai tsaye ya bashi amsa da"Eh har da Anynku dasu Farhan"
Sai suka saka Ihu,yana biye musu da Dariya ni dai sau daya muka hada ido na kauda kaina,Daki na koma shi kuma da yaransa suka shiga Dakin Mama sai chan ya fito Hafsah tayi mai Fatan alheri ya amsa bakin nan har har kunne.
Garin ana d'an zafi zafi da ruwan Sanyi yayi wanka na kai masa abinci yana ci yana bani labarin abubuwan da suka faru cikin hirar nasa ne yake ce min"Sai zuwa gobe zamu yi shawara Fa'iza. nan da wata d'aya suka ce zan fara shiga office bana so na kara raba iyalaina Waje d'aya zan had'eku bari kudi su shigo kawai"
Ina kallonsa nace"Yaushe su sukace zasu maida maka kudaden na ka..?
Yana lomar shinkafa yace"Ko wani Lokaci zan iya gani suka ce"
Ni dai ina jinsa yana ta Tsara abubuwansa nayi masa gum sai in ya sako sunana ne zan daga kai nace tom ko Umh,naja bakina na tsuke ni dai gajiya nayi naje na kwanta shi da yaran sa falo suka Dawo suna ta Shagalinsu tun ina jinsu sama sama har barci ya Dsukeni.
Tun daga washegari muka yi samun bakin Taya murna wad'anda basa kusa sun yi mana ta waya Goggo tazo Yaya isa ya kawota tayi mishi Murna,Anty Binta baki har kunne,ita da Mama,Jamal yana makaranta suna Jarabawa Badariya dai sai ta zo gida ta kwana Biyu,ranar da ta dawo zuwa tayi ta Rumgumeni tana fadin"Ina murna matar yaya. Allah ya sanya alheri"
Na amsa mata da mirmishi sai ta fara zolayata da fadin"Har mun fara kewa Anty Fa'iza yanzu chan ikkon zaku koma.?
Kai Tsaye nace"Za dai ku koma Badariya"
Cikin jimami tace"Ni ina kano kin manta,ban gama hidimar kasa ba"
gyada kai nayi ina fadin"Duk da haka dai. in kika gama chan zaki koma indai ba aure kika yi ba"
Daganan muka cigaba da Hira duk akan mganar aikin ne,ni da kaina na Kira Hajiya na sanar da ita,tace zata zo taya murna abun mamaki har da kawayen Mama da suka gujeta a baya har da su a masu taya murna. Hajiyar Dala bata zo ba ta dai kira mama a waya da dashi da Uban gayyar ta masa murna nima su Nana Fadila duk sun kirani ita har ta fara murnan zan dawo kusa da ita. ban ce mata komai ba sai yake a raina ko nace kiyi hakuri Fadila hakan bazai tabbata ba.
Baki muka yi ta samu ta ko'ina abun har mamaki yake bani,shi kan shi yace wasu wlh sun manta ma dashi Lokacin da ya rasa ammh sai ga shi har da su a sahun masu murna,mganar da yace zamu yi duk bamu samu mun yi ba. nasan kan mganar tafiya lagos ne tuni mutane har sun gama daukan zencen Lagos zamu koma gabad'ayanmu har da yara.
Yaya mariya bata zo ba. A waya ta kira ni bayan mun gaisa tace"Ashe kuma abun alherin da ya samu kenan..?
To Allah ya sanya albarka.Goggo ke tad'in Lagos zaku koma daa ke da yaran gabad'aya"sai kawai na ce mata haka yace,yaya mariya bazata sauya ba sai ta karkace baki tana fadin"itama yar abujan fa?ina fatan chan zai barta domin Lagos ke kad'ai zaki zauna kamar yadda ki ka bar mata Abujan ita kad'ai"
Sai nayi dariya kafin nace"Ya ce gabad'ayanmu zamu koma har da Mama"sai ta tabe baki kafin tace"A na nan dai jiya iyau"
Ban biye mata ba shiyasa bamu dad'e muna mgana ba muka yi sallama.
Bamu samu zama ba sai da mutane suka Tsagaita,Ranar ma da daddare,Dariyan Musty muka sha wai har yayi ma yan ajinsu sallama su zasu koma Lagos gabad'aya.ina Dariya nace"kaji yaro da zakewa. "
Yaya Ishaq na gefe yace"Ba wani zakewa ya fad'a musu gaskiya da ya tafi ba sallama fa..?
Amir yace"Umma da Anum na zuwa makaranta da tuni kowa ya sani"
Ita muka kallah yadda tayi yasa muka kwashe da Dariya,kowa yasan zata aika da bakinta kamar na aku,har fa gidan da muke kai nika da taje sai da tace lagos zamu koma zamu tashi Daga gidan nan kamar an tambayeta,Amir ke fadin da yaje kai nika suka tambayesa,kallonta nayi ina fadin"To wa ya aike ki gwana..?
Cikin Shagwaba tace"Umma sallama nayi musu kada suga min daina kai nika"Sai ko muka kara saka Dariya sai ta fara kokarin kuka Ya jawota jikinsa yana fadin"manta da su mamana ki fad'a ma kowa lagos zaku koma sannan ki kara da fad'a musu a jirgi zaku tafi"Da sauri ta waro ido tana fadin"Daada jirgi fa mai tashi sama..?
Ya daga mata kai kawai sai ta fara Tsalle tana murnan zasu hau jirgi Ahmad da Musty na tayata,Amir dai na zaune yana bin su da kallo.
Yaro shi yana son sauyin muhalli,Amir ne yayi hankalin cewa'Daada in muka koma chan wata makarantar zaka sakamu?
Yana dariya yace"Amir d'an makaranta. Kada ka damu makaranta mai kyau zan saka ku in sha Allahu"
Daganan ya cigaba da biye ma yaran suna masa tambayana yana amsawa.
Ni har zan shige daki yace yana son mgana dani,dole na hakura sai da yaran suka yi mana Sai da Safe suka shige Dakin su,sanin in yace muje Dakinsa bazani ba yasa muka zauna afalo ya fara da gayamin EFCC ta dawo mai da kud'insa kimanin Naira miliyan Sitti,Tunda ba lalle kudin mutum su dawo duka ba.
Shine? ya ke ce min yanzu ya yanke shawaran zai fara yin gaba yaga yanayin garin da komai,zuwa ya sama mana inda zamu zauna tunda Abba yace zai had'asa da mijin Nana Fadila.
Ban yi mai musu ba nace shawaran shi tayi sai ya cigaba da fadin"gida nake son siya babba wanda zai wadace mu. In bai samu yanzu ba, sai na kama Haya zuwa gaba in na samu a hankali a hankali sai na siya na kaina"
Kai Tsaye nace"Gwara ka mallaki naka zai fi. Kuma mganar ka siya babba kada ka yi asaran kudin ka,ka siya daidai zaman mata d'aya da Dakunan yara,kana da maza sannan mace Daya gareka Anum,Ga mama ga su Badariya duk da ita tace sai ta gama hidiman kasa tukunnah"
Cikin mamaki yace"Bangane wajen mace da'ya ba.?ina miki bayanin itama Zeey na gayamata ta fara shiri,kila ku zaku fara yin gaba ita sai daga baya zata same mu achan"
Mirmishi nayi kafin nace"Ka gane mganata mana. ni fa bazan bika Lagos ba"
Sai ya yi karamin Tsaki kafin yace"To sai ki zauna a ina.?kai tsaye nace"A nan mana"harara ya sakar min kafin yace"kina Hauka ne.?ina wata Duniya kina nan?wazai barki di'n? kafata kafarki, kafar yarana Fa'iza"
Sai ban ce komai ba na kauda kai bai Damu ba ya cigaba da fadin"Abba yace na siya mota saboda zirgan zirgan? zuwa wajen aiki da sauran dai Bukatu"jin sa kawai nake yi ina tunanin ya dauka wasa nake yi sai na kara gyara zama nace"Da gaske nake yi. ni bazan bika Lagos ba"
Sai kawai ya mike yana fadin"Bina ko kamar kin gama shi Fa'iza meyasa zan barki.?ba mai kara rabamun hankalina yanzu iyalaina duka waje d'aya zan had'asu"
Kai Tsaye nace"Yanzu kuma.? Ni fa kada ka manta na saba zama ni kad'ai a baya ma kana Abuja ina katsina, kuma na zauna lafiya sai don ka koma Lagos..?
Kallon sai ki yi yayi min ya shige Dakinsa ya bugo kofa sai ya bani Dariya ya Dauka wasa ne?lalle ko zai ga wasa alokacin da bai yi tsammani ba.
Ya samu mun fara tattara kayanmu,ni daman ma na had'e nawa na yara ne ba'a gama had'awan ba,yace bazai saki gidan ba sai in ya siya wani inda zamu rika sauka inda munzo,tunda dagamu sai kayan sawa zamu tafi sauran kayan gida Sabbi za'a siya kawai,har sun yi mgana da megidan ma ya bashi kudin Shekara,Hafsah kuma daman bata da matsala Transfer dinta ya samu kaduna zata koma,ranar muna tattara kayan kitchen waje daya Anum tace"Umma shikenan kin daina zobo da kunin aya..?
Kai tsaye nace"In ji wa..?zobo da kunin aya yanzu na fara"
Na?tuna ko ranar da Hajiya tazo min murna na fad'a mata lagos aka kaisa tun kafin na yi mata bayani tace duk inda naje kada na saki sana'ata domin sana'ar hannu abu ne mai kyau da amfani kuma na aminta da mganarta na Jaraba kuma naga riba,kuma dayake nima baama Lagos din zani ba ballatana ya dameni, inda zan koma da zama na tabbata zan rika yin ciniki sosai.
Kuma ko da muke tattara kayan ina sana'ata ban fasa ba,Mama ma nata shiri tunda yace in yaje ya dawo har da su Anty binta za'a tafi saboda suga waje,Sati hudu Tsakani ya tattara ya tafi,jirgi ya bi daga kano zuwa Abuja,bayan ya isa headquater din su ya saka hannu sun bashi accepted letter,Daman yana zuwa ya kira mijin Nana Fadila shi Costume ne,gidanta ma ya sauka yaci abinci ya huta sannan suka fita duba gida,sun duba inda yafi kusa da ma'aikatan su anguwan Apapa lagos,ya siya apartmemt,gida ne mai girma ba sosai ba,Falo hud'u mai Dauke da bedroom da Tiolet guda takwas,yana da girma gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login