Showing 120001 words to 123000 words out of 288345 words

Chapter 41 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

700

sai nayi mata gyaran jiki ina ta Murna daman ta wannan bangaran ita kan kawo min Costumer,sau daya na hada Turaren Rushi da na Humra da muka dawo gidan nan shima na riga na karbi kudin aikin su ne tuni yana hannuna.
Da Daddare naje kai ma Mama abinci sai da tambayeni a wulakance wai a ina nasan Hajiyar Raliya..?
Kai tsaye nace mata"Su ne shugabannin kungiyar da suka bamu tallafi bayan sun koya mana sana'o'in hannu domin Dogara da kanmu"
Sai ta tabe baki kafin tace"Ina ce sanadin Badariya kika santa?
Sai na daga mata kai sai kawai tayi tsaki kafin tace"Aikin mur in ji tusa."
Ban tanka ta na fice washegari sai ga Direba da kayan abinci shake da Mota Ishaq na gida Lokacin nayi mai bayani sai kawai ya kalleni yana fadin"ina fatan ba rokon ta kika yi ba ko..?
Sai abun ya bani haushi na wuce sa na shige daki ina fadin"To ba dole fa a fada masa ya juya da kayan kawai"
Daganan ko kara bi ta kansu ban yi ba, sai naga ana shigowa da kayan a raina nace abun ma iskanci ne sai da na natsa na kirata nayi mata godiya tace bakomai indai ina bukatar wani abu na kirata kamar uwa take gareni nace mata in sha Allahu.
Muna da wattani biyu da kwanaki a sabon gidan da muke ciki,Yaya Ishaq ya tafi Abuja ranar wata asabar shima din Mahaifin zainab ya kira sa akan yazo yana nemansa ba shi ko da kudin Mota Mama ta kira Anty Binta ta bashi ya kama hanya sai da ya bar gidan nan Hankalin Mama ya kwanta.
Kamar yau ya tafi washegari Goggo tazo ganin wajen da muka koma Yaya Isa ya kawota,shima Hafsah ya kira tayi mai kwatance Dakin Mama ta fara shiga suka gaisa anan Mama wai ke Tambayan Goggo ina Hajiyar Dala..?
Goggo tace"Baki sani ba ta tafi raka mijinta kasar awaje a duba lafiyrsa"
Sai Mama ta kasa mgana tunda da Yaya ishaq ya fito daga hannun jam'an tsaro Mama bata kara jinta ba tun tana kiranta ta na bata uzuri har dai ta daina samunta goggo mamaki ya cika ta? daman ana jin kan Saudatu da Fatima ne..?
Da mamakin ta baro dakinta zuwa shashena ta iskemu muna ta Dura zobo a gorina,Goggo na zolayata fad'i take yi"A'a kaga Hajiya fa'i mai zobo da kunin Aya"
Amir da Hafsah suka kwashe da Dariya Yaya isa na gefe yana taya su, shi sauran na jiya da yammah mai sanyi nace Hafsat ta kawo masa yana sha yana fadin"Goggo gaskiya Fa'iza ta iya hada zobo sosai yake da dad'i"
Goggo ta kalleni kafin tace"Ke fa'i taso ki saka ma yayan ki waigi ya fara santi"
Gabadayanmu muka fashe da Dariyan mganarta, shima Dariyan yake yi yana gyad'a kai kamar wani kadangare.




*INGANTACCEN ZANCE*.

*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.
*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*
*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*
*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.
*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*
*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.*
*Kawai ki tuntu'bi
Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*
*08032773332.*

'?.



*Janafty*



[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2004*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Itama cire hijabi tayi ta shige cikin mu. tana tayamu zuba zobon a sabbin Gorunan da na siya,muna yi muna hira cikin Annushuwa lokaci d'aya muna darawa in abun dariyan yazo,Yaya Ishaq ne bayan ya gama shan na shi zobon zai shiga cikin gari ya mike yana fadin"Fa'iza zan dawo daukan Goggo dole na tafin ma da Madam zobon nan domin itama tana min labarin sa"
Hafsah na gefe tace"Yaya isa har da kunin Aya.."
Da sauri yace"Eh har da kunin Aya a had'amin dashi"
Gabad'ayanmu muka kara kwashewa da Dariya yana sosa kunnensa da key din motar dake hannunsa yace"Goggo kin jamin yara na min dariya ko.?
Goggo tace"Kayi abun dariyan ne.Ke Hafsah bisa ya kwaso min tsaraban Fa'iza kafin ya tafi"
Har zai fice daidai lokacin yaji Goggo na tambaya ta Yaya Ishaq sai nace mata ya tafi Abuja sai ya koma ya zauna cikin mamaki yana fadin"Daman bai daina zuwan Abujan nan ba..?
Goggo tace"Kaji wata mgana shi da yake da mata da ya'ya kake fadin bai daina zuwa ba"
Yaya isa yace"Haba Goggo.In a baya ya je yana aiki ne yanzu kuwa ba ya aiki ga wahalan rayuwa in a baya yana da motar kansa, yanzu ko babu ko na motar da zai rika zirga zirga ai wani abu ne mai zaman kansa shima ya kamata ya zauna yayi ma kansa Tunani haba.."
Ni da goggo kamar had'in baki ba wacce ta tankansa ya cigaba da fadin"In har tana son shi ta baro chan ta dawo nan, ai gidan nan shima ban ga laifinsa ba inda rayuwa ta juya dakai sai ka juya kai ma ka fuskanceta"
Goggo tace"Ya za'ayi ta dawo bayan achan take aikinta a kace"
Yaya isa yayi tsaki yana fadin"Mganar banza ne Goggo in dai tana son shi kuma ya isa da ita duk inda yake zata bisa.ammh gaskiya wannan tsarin bai yi ba, duk wanda yaji haka sai ya raina ma wayaun Ishaq. baisan zama ba aikin yi ba ne, yana ganin kamar abun wasa ne sai rayuwa ta fara kwallo da shi zai Fahimci Shayi ruwa ne"
Dariya ta kusa subucemin da mganarsa ta karshe ya mike yana fadin"Ita Fa'izan ba mutum ba ce, ba ga ta nan ta biyo sa inda yake a kuma yadda yake ta zauna da shi ba, sai ita yar gwal wahala ce bata ishesa ba Allah ya ba da sa'a"
Daga haka ya mike bayan yace Hafsah tazo ta shigo da kayan ni kuma sai nace Amir ya bita ya tayata bayan fitan su ni da Goggo bamu tada zencen ba sai muka shiga wata Hiran na Dabam Goggo ta kalli falon ta kara kallo kafin tace"Nan din ma ba laifi sai ku lallaba kafin muga Abunda zai yi"
Na gyad'a ma Goggo kai ina fadin"Ai anguwan nan tayi Goggo sosai nake samun Ciniki"
Goggo na dariya tace"Dakyau Allah yasa albarka Allah ya tunkud'o ciniki Fa'i ta biyamin hajji da kudin zobo da kunin Aya"
Ina dariya na rika fadin Ameen Ameen Goggo har da Umra ma goggo na Dariyan jin dadi tace'"Allah ya ida nufi Fa'iza"
Hafsah ne suka dawo da kaya Nasan Goggo da Dawainiya bata zuwa Hannu Rabbana tace su garin kuni ne mu lallaba ina ta godiya har da Taliyar yar muji garin Danwake garin Tuwo da tsakin masara kubewa danya,kuka daaddawa,da bushashiyar Zogala da rama sai gyada mai bawo da Mai gishiri da ta kawo ma yara Tsaraba Dadi ya cikani sai cewa nake yi"Allah ya saka da alheri Goggo na zama yar gatan ki"
Goggo tace"Daman ke yar gata na ne tuni zaman ki ne kawai bai yuyu a Hannuna ba"
Nasan haka domin duk wata kauna Goggo ta nuna mana barin ma ni,Su Hafsah tuni sun ja gyad'a gefe suna ci ita da Amir na balla musu Harara ina warce ledan Lokaci d'aya ina fadin"Wannan na sauran yara na ne yan makaranta"
Amir yace"Umma wannan yayi musu yawa fa..?
Na bude ledan ina gani sai naga da yawa sai na debo a hannu na zube a gabansu na boye sauran ina fadin"yara kun ci rabon ku"
Goggo na mana Dariya naji Dadin wannan zuwan na goggo muka yini muna Hira,Hafsah tayi abincin rana bayan ta gama nace ta dibar mama da Badariya da taje kai mata sai tace sai yanzu aka ga daman bata abincin..?
Ita dai Hafsah bata tanka ta ba sai da ta Dawo daki take gayamin Ban ce komai ba Goggo tace"Sai kin kara Hakuri daman fa'iza yanzu Saudatu zatayi ta tsiro da abubuwa saboda ta kuntata miki, to kada ki biye mata Har a gobe uwa take gareki"
Kai na jinjina ina fadin"Goggo ni ban da Lokacin wannan kina ganin bama zaune nake ba"
Goggo tace"Ba shakka Sana'a ai mganin Damuwa ne da sha'anin Duniya,"
Sai da muka yi sallar la'asar sannan Goggo ta yi shirin tafiya daman da La'asar Ya Isa yace zai dawo shima daga ma'aikatar su ta nepa dake Dutsemah ne aka turo su meeting babban Headquater su na katsina da ya gayama Goggo tace zata Biyosa.
Aiko sai ga shi hudu da wani abu sai faman hon yake yi ma Goggo tunda yaki shigowa na zuba ma Goggo kunin Aya da zobo mai yawa shima Yaya isa na bashi na shi Goggo sai fada take yi tana fadin"bai yi yawa ba Fa'iza? kada mu karya fa jarin"
Ina Dariya nace"Cikin Riba ne fa Goggo"
Sai ta karba tana fadin"To Allah ya yi albarka Allah ya sanya miki nasibi da karama acikin Kasuwancin ki da sana'arki"
Na dinga amsa mata da Ameen na rakata Dakin Mama tayi mata sallama ni da Hafsah da Amir har kofar gida muka rakasu Yaya isa ya zaro dubu biyu ya bani naki karba sai ya harareni yana fadin"Kyauta na baki ni ba kudin zobo ba ne"
Jin haka yasa nayi dariya na karb'a ina masa Godiya Hafsah na ganin haka tace"Yaya isa kada ka manta yar makaranta marainiyar Allah"
Dagowa yayi yana fadin"Data zaki saka ko..?
Da Sauri tace"Eh Yaya ai muna Browsing sosai"
Sai ya yi dariya ya zaro dubu ya bata yace a saka data ayi ta browsing ta karba tana godiya sai kuma ya bama Amir dari biyar yana fadin"Kai baka fara zuwa makarantar ba ne..?
Da Sauri nace"Bai fara ba sai zangon karatu na biyu Yaya isa"
Sai ya jinjina kai har Goggo ta shiga mota sai ta leko ta window tana fadin"Kinga na manta Maman isuhu tazo da kanta ta kawo min goro da mintin biki Isuhunta zai yi aure tace kada a yada zumunci don Allah"
Fatan alheri nayi kafin nace"Da wahala zuwa na Goggo kinga ga Mama ina fita sai kiji ance ban kyauta ba"
Goggo tace"Hakane ki yi zaman ki ni da mariya sai mu leka"
Da haka muka yi sallama suka tafi muna Daga musu hannu sannan muka koma cikin gida,Danwake nayi mana da Daddare Hafsah kuma sai ta hada kunin Aya zobo ma bamu yi na yammah ba nagaji nace ta bari da Safe yan sari ma basu samu ba duk a gida ya kare.
Aiko Mama tayi ta fad'a wai danwake ne abinci da daddare kamar a gidan yari..?yarda aka kai mata haka Hafsah ta Dauko kulan da safe da zatayi wanke wanke, Badariya bata dawo ba kila gidan Anty Binta ta kwana,haka na cigaba da Hakuri da Mama ammh Allah ke da kullum da Sabon korafin da take tashi da shi sai dai bana biye mata,Yaya Ishaq tunda ya tafi bai kirani ba nima ban damu ba sai dai nasan suna waya da Mama.
Sana'ata na maida hankali bani da wani Hutu sai dare ya tsala wani Lokacin Saboda kada ayyuka su Chudemin karfe uku na Dare nake tashi na Dafa Zobo a tsakar gida tunda na koma amfani da gas na kasa 4kg,Sai na siya babban murhun gawayi ina amfani da shi wajen Dafa zobo,har girki ina yi akai saboda gas din ya rika yi mana auki sosai.
In na tashi ukun nan kafin asuba na Dafa zobon,sai naji da saka ruwan wanka. wani Lokacin Hafsah ke abun karin Safe in zata fita da wuri in kuma tana gida sai nayi in ta tashi sai ta Hada zobon ta kuma share gidan da Dakunan in kuma bata gidan duk ni nake had'awa nayi kunin Aya saboda yana Saurin Lalacewa nafi hadasa da yammah saboda an fi samun Wutar Dare kafin safe yayi sanyi.
Hakan ma bai burge Mama ba, duk yadda nake taka tsantsan sai da ta fito tace min wai warin ganyen zobo na tayar mata da zuciya ni ko sai nace sai dai ko ki yi ta sheka amai bazan daina wannan sana'ar ba,kuma duk kushen mai kushe da Hassada ta Allah ba tashi ba.
Duk yadda nayi sai tace kaza kaza ita dai kada ta ganni cikin ni'imar Allah sai dai na zauna ta rika tusamin Haushi da tozarcinta nan kuwa bata isa ba,yanzu ba irin da ba ne an samu Sauye sauye da dama. daman haka Rayuwa ta gada Kifi na ruwan sanyi sai ya iya juyawa ya gansa ana zafi kamar yadda ya faru da ita.
Na toshe jina da ganina na cigaba da sana'ata ina rufa ma kaina da ya'yana asiri,har da ita kanta Mama muna da kayan abinci ammh bamu da Cefane da Riban sana'ata nake mana komai Dawainiyar yara na makaranta na yau da kullum Badariya ma ina bata na mota har da wata matsalan in ta taso in dai tamin mgana ina da shi zan Dauka na bata.
In da na biye mata na koma na zauna yadda ta matsa Yaya Ishaq ya tafi Abuja da ta gane bata da wayau.Anty Binta take takama da ita itama bata da komai yanzu sai karya da Girman kai da tijara fal cikinta domin ban ga abun arzikin da take kawoma Maman ba,Da farko da Mama tace Ucler ya kamata kayan Tea ta siyan mata da suka kare bata kara siyan ba na Tabbata bayan Yaya ishaq ba mai iyawa da Dawainiyar Mama.
Sai da ya shafe fin sati biyu a cikin na uku ya dawo na zata zan gansa da abun arziki ne niki niki yadda Mama ke fadin sun musu komai babu abunda yazo da shi daga shi sai kayansa kamar ma a kidime yake ba wani kwanciyar hankali sai ramar da ya karayi, ashe wai takardunsa yasa yaje mai da shi ko za'a dace yasaka shi yayi zama ba wani labari mai Dadi gajiya yayi da zaman ya dawo ina Tsakar gida ina shara naji Mama nata mai fad'an meyasa bai jira ba ya Dawo dayake Mama ta iya mgana a sama sama.
Yayi mgana sai dai nashi ne yayi kasa ban ji abunda yace ba, ni dai ba gulma ba na cigaba da aikina,Yadda bai ce min kanzil ba nima ban ce mai ba sai na tambayesa ya ya baro su Farhan..?
Sai yace min Farhan ya fara zuwa makaranta Fadil kuma gidan su zainab ke kaisa in zata fita aiki Daganan bai kara mgana ba, nima na kama bakina fadan da ba ruwan ka ai Dadin kallo ne da shi.
Sai ranar da yayi kwana Biyu da Dawowa yana zaune afalo ni kuma ina safa da marwa aiki ya had'e min Hafsah da wuri ta shiga makaranta ga aikin zobo ga girki,Amir ne ya taimaka yayi min sharan Dakuna da Tsakar gida,gajiya yayi da ina wucesa ko barayinsa bana kallah yasa ya kirani nazo gefensa na tsaya yana kwance ne ya mike yana fadin"Nagode bisa Dawainiyar da kika yi da yara da su Mama bayan ba na nan"
Sai kawai na wuce ina fadin"Ba damuwa daman kasan kula da yara aikina ne Mama kuma itama kamar uwa take gareni, kada ka godemin domin na yi mata Hidima"
Daga haka na wuce kitchen na Dauki Abunda zandauka nayi waje achan nake girki gas ya kare Hafsah nace taje ayi Refiling bata samu zama ba ne.
Har na fice yana bina da kallo nasan a ransa yana mamakin yadda na sauya ne bakina ya bude fiye da yadda yayi tsammani,Haka muka cigaba da Rayuuwa yau dadi gobe Tsumma,ahakan ma ni nake tallafe da kananun Lalurorin gidan nan ammh Mama bata gani take yi komai nake yi alfarman da suka yi min ne nake rama musu.
Ni ko Don Allah nayi abunda take yi bai Taba Damunaa ba,Ba inda Yaya Ishaq yake zuwa yana gida sai dai in masallaci in ya gaji da barci ya fito falo ya kunna kallo in yagaji ya kwanta,ko ya shiga Shashen Mama,duk yadda baya so damuwa ta samu zama a jikinsa sai da ta samu duk yayi baki ya rame hatta na katin waya gagaransa yake yi,kuma yana da girman kai da Fafa bazai yi tambayata ba ni ko bani da masaniya kananun matsalolin da na gani ne nake mgancen su.
Ana cikin Haka jamal ya yo masa waya Kudin hannunsa ya kare sannan kayan abincin sa ma sun kare Bai fadamin ba sai ya shiga bangaran Mama ya fadamata kai tsaye mama tace"Sai kayi ma matarka mgana nasan bazata rasa ba,gidan nan yini ake shiga da fita saboda sana'arta"
Kai tsaye yace"Mama ni bazan iya taba tambaya Fa'iza kud'i ba"
Mama tayi karamin Tsaki kafin tace"Kiramin ita ni zan gayamata"
Amir ya kwalama ya kira da ya shigo sai yace ya kirani ni kuma ina Falo na Dukufa da littafin, ina ta lissafin kudi so nake wannan karon daga rabin Solon Ganyen zobo na siya Solon buhun ina tattara Riban hannuna sannan Aya ma tiya goma nake so na siya,da yawa da Dabino na ijiye kwakwa kuma tana lalacewa kadan zan siya sanda Amir yazo ya kirani shine a raina so nake nayi kokarin na biyasa masa kudin makaranta ya fara zuwa zamansa ya fara Damuna,so nake na fara ji da Hidimarsa kafin su kuma a fara mganar na su Anum
Ijiye komai nayi na saka Hijabi na tafi Dakin Mama da na shiga a kasa na duka ina gaisheta da lafiya ta amsa kafin ta daga murya tana fadin"Jamal ne yayo waya bai da kudi a hannunsa nasan kina da kudi ki bada ko dubu ashirin ne sai a sakamai ya lallaba"
Sai mamakin Mama ya kamani kamar ita ta tarfamin jarin cikin sanyina nace"Sai dai Dubu goma baza'a samu ashirin ba"
Mama ta saki baki kafin tace"Wlh karya kike yi ba za dai ki bada ba ne, meye amfanin samun naki in dai bazaki taimaki mijinki naki ba"
Ina jinta ban yi mgana ba shi ya katse mganar da cewa na tashi na tafi haka na koma Dakina ina jinjina karfin Halin mama shikenan lissafina ya Sauya daman yan riban da su nake Hidiman yau da kullun kudi fa ana zaran su basa zama,Sai na cire dubu goma na ware kayan da nace zan siyo na ijiye bazai samu ba saboda kudin sun yi gibi,ko da ya dawo dakin bai tada mganar ba sai ni da kaina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login