Showing 162001 words to 165000 words out of 288345 words

Chapter 55 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

718

maido da shi bayan wata biyu Saboda Yaya Abdul'ahad zai tafi kasar waje karo karatu kuma da matarsa zai tafi.
Mama dai kam kamar bata gidan ko motsinta ba'aji ta daina shiga duka Hurumina,sai dai bansan tsakaninta da Da'nta ba,Anty Binta kuma tana ta Hidiman auran Halisa ba'a cika ganinta ba,Mganar aiki kuma shuru kake ji sannan har Abujan Mahaifin zainab ya kirasa ya koma ammh ba wani Labari.
Sai daga baya na Fahimci Saboda kawai ya rika zuwa yana zama da zainab ne,ammh tuni sun san akin bazai samu ba,tuni har ma'aikatan da aka dauka sun fara aikin su.






*Janafty*
[7/17, 7:33 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2014*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Zukata tuni sun kwanta,gabbai sun samu natsuwa hankula sunyi ruku'u sun rusuna.
Ta kowani bangare na juya na irin shafukan kaddara da kan bud'e ma bawa to ta kowani tsanani daman Allah yayi alkwarin sauki,hakan ce ta kasance dani duk lokacin da naga rayuwa ta chude'min ko tamin zafi da ikon Allah sai wata kaddara ta bude ma rayuwata sabon shafi da zai zama bango ko majingina gareni
Bayyanar Abba garemu daga Allah ne, sannan zamowarsa makwafin Uba garemu shine jin dadin mu,Sannan har makwafin uwa ya Dauke mana Ahalinsa kuma sun Dauke mana makwafin yan'uwa da Dangi,sai alokacin muka san muma ya'ya ne,Abba ko tari bai yarda mu yi?ba tare da yasan Dalilin yin sa ba,Yace duk abunda muke bukata kiransa kawai zamu yi a waya mu gayamasa,to mu saka aran mu komai muke so mun samu,Yaya Asiya tuni har ta je gidan su Ammi a kano tasha karamci ta tabbatar mana da cewa Duka Ahalin Abba masu karamci ne,Tace sai nuna ta ake yi ana fadin"Diyar yar'uwan Baban Nana ne na kaduna"Ko'ina aka kaita sai an karramata duk da Ammi bata garin tana kaduna,Direba aka saka yakai ta har gida,Sannan sun karbi lambar wayarta da alkawarin zasu rika zuwa suma. Ammi suna da yawa a gidan su matan Mahaifinta hudu ne kuma duka sun haiyayyafa,Sannan tana da kanne maza sosai wasu duk suna garuruwan da suke aiki da matansu kamar mijin Laila Uncle Junaid Staff ne a kasu Kaduna State University. yana chan sai dai lokaci bayan Lokaci suna zuwa ganin gida shi da ita.
Azumi ne ke kara gabato mu ma wannan karon,Zainab saboda ban samu zama ba bamu kara mgana a waya ba tunda na gaisheta kwanaki da jiki,shi kuma Gogan bai min zencenta ba.? Ni ma kuma ban cika Tusa kaina inda ba'a sakani ba, tunda muka yi alkawarin da shi ya daina matsamin ammh fa bai daina Takurani da kallo ba,ko kuma ya rika shigemin jikinsa na gogan jikina bana son haka nayi mai mgana sai kawai ya kalleni yace"Ba kyau Fa'iza wlh ba kyau. Ki bari kada Allah yayi fushi da Da ke"
da naji haka sai ban kara mai mgana ba,sanin gaskiya ya fada,Tunda bai sakeni ba har yanzu yana da Hakki a kaina kuma shi Allah ba ruwansa da wannan,mganar jinginan auran mu kuma wannan wani zama ne mai zaman kansa.
Sai na rabu da shi tunda na samu ya daina sakani gyaran Shimfid'a yana Rutsani sai na gode ma Allah,Abba Dubu Dari uku ya kara turo ma kowannemu mu yi siyayyan azumi har da su Goggo suma bai kyalesu ba,bakina yaki rufuwa Kana naka daman Allah ya gama nashi kuma nashi Tsarin shine daidai na zata Yaya Ishaq zai yi fad'a sai naga bai ce komai ba ya dai ce"Abban nan naku naji da ku Fa'iza"Sai na samu kaina da yin kayattacen mirmishi,Hajiya ma ta aiko mana da kayan abinci,Domin ita a di'ya ta daukeni ba kowa ba,Alherin Hajiya gareni mai girma ne da bazan taba iya mantawa da ita ba.
A satin za'a fara azumi yara sun yi Hutun makaranta suna gida da Safe muna waje ni da Anum da Amir muna wanke wanke Ahmad da Musty na fad'a kan shara nagaji da yi musu mgana ne na kyalesu sun ki bari ina jira na tashi ne yaro yaji a jikinsa,Hafsah na makaranta jarabawa suke yi ta kosa su gama ta gudu kaduna,Badariya na kano ammh suna chan suna ta shirin Biki ita da Raliya ta waya.
Daga Daki ya fito kamar an jehosa Fadi yake yi"Bazai yuyu ba. Wlh bazai yuyu ba in kika bari aka cire cikin nan na rantse da Allah Zainab aure na dake ya karem Bazan iya ba Nagaji haba.."
Yake fad'a cikin Tsawa da Daga muryan da sai da Mama ta fito daga Daki zani a hannu cikin wani yanayi ni kaina sai da na saki aikin da nake yi na mike gabana na faduwa.
Mgana yake a waya kamar kuma da Zainab yake mgana sai kara shan wallahi yake in aka cire cikin nan sai ya rabu da ita cikin bacin rai yace"Me kuka maidani daga ke har mahaifin naki.?sakarai shashasha ko sai yadda akayi da shi ko.?to wannan karon ba Kotu ba Allah yasa majalisar Dinkin Duniya zai kaini wlh sai kin yi zawarci ni bazan iya wannan auran naku ba da kuka fifita yahudanci Fiye da Islama acikin lamuran ku"
Kokarin yi mai bayani take ya Daka Tsaki ya katse wayar yana Huci,Mama ta kallesa tana fadin"Meke faruwa ne Ishaq.?
Sai ya kalleta Har idanuwansa sun cika da kwallah cikin wani yanayi yace"Mama ki duba fa ki gani,wai cikin yarinyar nan babanta yake so a zubar..'"
Sai ya kasa karisawa saboda yadda ransa ke Tukuki,Mama tace a zabure"Cire ciki kuma Saboda mene. ?Kamar zai yi kuka yace"Saboda Hujjar su na banza wai yana wahalar da ita, hala ciwo take ko kuma wani abun ne ya sameta ana raba mai ciki da laulayi ne mganar banza kawai,Mama ne Zainab da Mahaifinta suka maidani jani talau..?wannan wani irin kaddararren aure ne..?
Mama zatayi mgana kenan wayarsa ta fara kuka yana dubawa yace"Babanta ne"Yau ko arzikin Daddyn bai samu ba,kamar bazai Dauka ba Mama tace ya Dauka mu dai mun ga yana mgana Yaya Ishaq na cika ya bude baki yace"Daddy.."
Kamar katsesa ya yi yana mgana kamar kiftawan ido sai ji mukayi K'aras,ashe wayarsa ce ya buga da bango sai da ta dargargaje,A firgice muka yi baya har da yara da suka yi Tsuru tsuru basu saba ganin haka ba. Mama ta firgita ta rikesa da karfi tana fadin"Kai Ishaq ka natsu mana"
Haki yake yi kamar wanda yayi gudun mutuwa cikin hakin yake fadin"Shi ke auranta ko ni Mama.? A shari'an ce na fi shi iko da ita meyasa komai shi zai zartar da shi.?Rabon da wasu suke nema da kudin su,mu mun samu shine zai yi sanadiyar zubarwa saboda bai da Hankali yana Uba ammh uban banza wanda baisan ya kamata ba..?
Mama ta kara rikesa tana fadin"Kwantar da hankalinka ka natsu."
Cikin Hargagi yace"Wani? iri na natsu mama..?Har ce min yake sai an zubar nayi abunda zan yi, wai akan ya'yansa zai yi iya yin komai wlh Mama indai aka zubda min jinina ba shege ba,d'an sunna wlh sai Zainab sai tayi zawarci aurena da ita ya kare har Abada,in ya'yana ne zan karbo kayana Fa'iza ta had'a da su Amir ta rike min su"
Mama ta yi saurin tareshi tana fadin"Abi komai a sannu Ishaq"
Ni dai nayi tsuru ina kallon ikon Allah Amir yaje ya tattaro wayar baban nashi ya had'ata ya miko min yana Fadin"Umma ga wayar Daada"
Sai na saka Hannu na karba ban kallesa ba nace ya had'a kan kannensa su shiga Daki,Anum sai da yayi mata jan ido ta tafi ta tsaya tana Kura ido da Daukan komai sai anjuma kaji tana maimaitawa.
Sai da suka shige ne na kallesa Mama ta Dake sai faman bashi Hakuri take yi,tana ya kwantar da Hankalinsa shi kuma yana kara rantsuwar Wlh matukar Zainab ta yarda Mahaifinta yasa aka cire cikin nan auran su ya kare.
Kai Tsaye nace"Saboda me zaka ce zaka Saketa..?
Sai duka suka dago suna kallona, ni ko na gyara tsayuwa a raina nace yau ce ranar maida martani Mama ce tace"Haba Fa'iza ai suma abun nasu ba su saka Tunani aciki ba"
Kai Tsaye nace"Zainab ce fa Mama. Zainab matar so yar Dangi,yar gata masu kudi da nasaba"
Sai ta kasa mgana ta Tsaya tana kallo na,Shi ma haka sai ko na kara fadin"Eh ai Zainab ce mai kyau ce ba Mummuna ba, sannan yar asali mai ilimin zamani yar gata yar masu kudi yar dangi mai cikakken gata,matar nuna wa duniya,wacce zata haifa maka ya'ya farare masu kyau ba irin ya'yan Fa'iza ba,matar da kuka zabeta sama da kowa matar da kuka fifita ta fiye da kowa matar da kuke so da kauna. Meyasa saboda wannan matsalan kace zaka saketa ke kuma Mama baki Tsawarta masa ba..?
Na karishe fad'a ina tsareta da ido kunya ya kamata sai ta kasa mgana shiko Tsawa ya dakamin bai so na kara mgana na warware komai ban kulasa ba na cigaba da fadin"Ita fa ka zaba sama da ni. Ka fifita ta sama da ni,Ka fifita zuru'arta sama da tawa zuru'ar, sannan ka fifita ya'yanta sama da nawa ya'yan,to ta ina kake Tunanin zaka hanata abunda take so.?ai tun farko a haka ka ganta, kuma ka ji ka gani kana sonta.."
Cikin hargagi yace"Ya isheki Fa'iza..Ya isheki haka nace"
Ya karishe fad'a kamar zai Dakeni sai nayi baya na tsorata kada yakaimun duka,Cikin wata murya yace"Ki bari Fa'iza ba kyau irin haka. don Allah ki bari kada ki kara Tunzarani"
Sai da na tabbatar da nayi baya sannan nace"To ka daina mganar Sakin nan? bai dace ba gaskiya, ai ku ba yara ba ne, kun fara tara kyakyawan zuru'a a tsakanin ku"
Sai kawai ya Dafe kansa ya koma kasa ya zauna Dirshan yana kara Dafe kansa,Mama na gefe jikinta yayi sanyi da kunya yasa ta kasa mgana,ni ko sai naji zuciyata wasai ko banza na gasa musu mgana sannan na maida musu martani.
Yana girgiza kansa yake fadin"Nayi Nadama Fa'iza nayi nadama ba tun yau ba.wannan auran bai amfaneni da komai ba sai bacin rai da Nasani,ban bi Turban Annabi ba wajen auran nan sai Allah ya barni da zabina,ya bani mace tagari ban gode masaa ba,na rika Hange hange ina ganin na wuce da ajin Fa'iza,Sai ga shi na bi auran kyau da nasaba da ilimi daga karshe hakan bai amfaneni da komai ba.."
Da Sauri nace"Ya amfaneka mana Zainab na sonka sannan kuma ta fara tara maka irin zuru'ar daka ke so"
Idanuwansa Jajir ya d'ago yana kallona kafin yace"Bata so na, in da tana so na,da bata fifita ta mganar mahaifinta akan nawa ba. Tana ganin tana da kyau alfarma tamin data aureni,Tana ganin tana da ilimin da Taimakona tayi ta aure ni,tana ganin tana da Gatan da ban isa da ita ba. kaico na da nabi Rudin duniya da Rudin Shed'an,ga shi yanzu ina Nadama Shiyasa duk wanda bai bi Turban Annabi ba, tun a duniya zai Tabe Annabi ya fad'ama mu auri mai addini domin itace mafi kyawun cikin su"
Dagani Har Mama ba wacce tayi mgana ita kunya da Sanyi ni kuma na shiga wani yanayi mara Dadi a lokacin.
Shuru yayi yana sauke Numfashi kafin yace"Mahaifinta bai Daukeni a bakin komai ba,gani yake taimakona yayi alfarma ya yi min don ya bani auran yarsa shiyasa yake takani yadda yaga dama har cikin gidan nan ya tako ya ci zarafina na, kasa komai ammh wannan karon wlh bai isa ba. sai na nuna masa na fisa cikakken iko da yar tashi ta zubar da cikin ta gani Sai dai kuma a bi wani Sarkin"
Da haka ya shuru takalmansa yayi waje Mama na kiransa bai ko Juyo ba,Ni dai nace Allah ya kyauta na koma ina cigaba da wanke wanke na, Mama na Tsaye ta kasa gaba ballatana baya har ga Allah ba wai dadi naji ba ammh raina bai baci ba,Gwara su fara gani Tun yanzu ban ga laifin su ba,Irin Rariyan da ya siya ne kuma don tayi zubar ruwa shatata bai kamata yayi korafi ba.
Ina gama aikina na shige Daki abuna,Na fara wata Hidiman yaran kuma karatu na iske su suna yi,Duk da nasan suna jin tashin mganar Baban nasu daga falon,tsakar gida na fito zan Dafa zobo na,Sai naga Mama an kwashi kafafun da sanyin jiki ta koma Daki Ranar sai dare ya shigo gidan ajaran majaran a falo ya fadi kan kujera yana sauke Nunfashi ina mai sannu da zuwa ya amsani a Dake kafin yace na sama mai ruwan wanka.
Sai da ya rarrafa ya shiga Dakinsa na bisa na kai masa wayarsa da ya fasa da tawa ina fad'in"Ga shi matarka nata kira, tana son mgana dakai"
Domin tun bayan La'asar Zainab ke kirana tana tambayansa nace mata ya fita ta Dameni ta kira yafi sau goma Daga gani bata cikin natsuwarta ne.
Yana cire rigan jikinsa ya d'ago yana kallona ina shirin ficewa yace"Dawo ki Dauki wayarki"
A kausashe nako ki dawowa na fice ina jinsa yana fadin"Lalle itama ko zan fasata wlh" a fili na furta"Kana fasamin waya zaka biyani kayana"
Daganan na fita zuwa kitchen sai da ruwan yayi zafi sannan na juye mai na ba ma Amir ya kai mai ban koma Dakin ba, abinci ma Anum ta shigar mai da shi yaran suna falo suna karatu ni kuma ina Daki,Hafsah na gefe na muna mgana sai ga shi ya shigo daga gani yanzu ya fito wanka ga kansa nan na digar da ruwa yana shigowa yace"Hafsah jeki falo wajen yara zan yi mgana da yayarki"
Ba musu ta fice ya kariso gabana yana fadin"Ki ka bama Amir ruwan zafi in ya kona sa fa..?
Sai na kallesa kafin nace"Ba yau ya saba dauka ba, zai iya ne"
Sai ya kuramin ido kafin yace"Ba kyau Fa'iza na horu fa don Allah ki yi hakuri".ganin ya fara sauya mganar yasa na mike na fice,na bar masa Dakin jiki a sanyaye ya koma Dakinsa ya shirya abincin ma afalo ya fito ya ci,Ina gefe sai kallona yake yi ni ko nayi kamar ban gansa ba.
Wayata sai washgari ya aiko Anum da ita, ban ko Duba? ko sun yi mgana ba. ammh naga an kirani Hafsah ta Dubamin tace Abba ne da Nana Fatima daman sune rana bata fitowa ta fadi basu kirani sun ji lafiyata ni da yara na ba,Har ga Allah ina kaunar Nana Fatima kamar yadda take kaunata,Sai da na natsa sannan na kirata muka gaisa sai tace measurement din yara da nawa take so na Rubuto mata sai nace ta bari sai Hafsah ta dawo zata turo mata,mun cigaba da mgana duk akan Bikin Yaya Abdul'Ahad ne da Raliya bayan sallah Tana fadamin Nana Fadila ta fitar mana da anko imu imu gabadayanmu,Na lura suna ji da Bikin nan ko don shine na farkon da zasu fara na Namiji, barin ma Ammi kamar Abdul'Ahad ba yaron ta na fari ba,ba ruwanta da kawaici da ita ake shiryawa komai.? Abba kuma daman ba mazauni ne ba ne tafiya na yawan kamasa Ammi ce akan komai.
Da Hafsah ta dawo na saka ta tura mata har da na takalmaa,Ban san cewa Yaya Ishaq bai yi mgana da Zainab ba, sai da ta kara kirana bayan na Dauka mun gaisa sai ta sakamin kuka na rud'e na zata ma ko wani abun ne ya faru cikin Kid'ima nace"Lafiya Maman Fadil..?.
Cikin kuka tace"Maman Amir ki saka baki Honey ya daina fushi dani wlh ba laifina ba ne. Daddy ne ya matsa kuma ni nace mai bana so tunda Honey baya so kuma ba'a cire cikin ba. wlh nayi ta kiran sa wayarsa a kashe bana samun sa"
Sai shesshekan kukan ta, na fara lallashinta kafin nace"Daman jiya baku yi mgana?ba ne da na kai masa wayar ..?
Da Sauri tace"kashewa ya dinga yi Maman Amir yaki ya saurareni ma, Daddy fa har fushi yake yi dani saboda naki amincewa da mganarsa Maman Amir don Allah ki basa hakuri wlh ban cire cikin ba, yana nan kada yace zai sakeni wlh ina son mijina"
Sai ta bani Tausayi cikin sanyi na nace"Kiyi hakuri ki daina kuka in ya Shigo zan mai mgana"
Da haka muka rabu sai mganarta ta Tsayamin arai, tana son mijinta har ga Allah nice shaida,ammh Mahaifinta ne ya riga ya saba da juya al'amarin ya'yansa,Ni kuma na kudiri niyar daidaita Tsakaninsu saboda itace Dahir dinsa,Da ya shigo Dakin Mama ya tsaya,sai da ya jima sannan ya shigo Dakina yara suka mike suna mai Sannu da zuwa Dakinsa ya shige Saboda ina da mgana dashi da kaina na tafi kai masa abinci,yana zaune ya yi Tagumi ammh yana ganina sai ya cire Tagumi,sannu da zuwa nayi masa na sauke mai abincin a gabansa ya jawo yana fadin"Me muka samu ne..?
Ina zama nesa da shi nace"dambun Shinkafa ne da zogale"
Cikin yanayin sa yace"Salon ya shake mu Fa'iza"ina Dariya nace"Tuwo naso nayi ban samu gyad'a ba,sai yara sukace Umma ki yi mana Dambu"
Bai ce komai ba sai da ya tashi ya wanko hannunsa ya fara ci sannan yace"Ko bakomai zamu dora da zobo mai sanyi"
Yafad'a yana kashe min ido sai nayi dariya yana ci muna hira,Sai da ya gama ya kuma dora zobo mai sanyi kamar yadda yace sannan na sako mai mganar Zainab kici kici yayi da Fuska kafin yace"Ina ruwanki da wannan mganar Fa'iza..?
Na rausayar dakai nace"Da ruwana mana ai yar'uwata ce musulma kuma shi ai sulhu alheri ne"
Sai kawai ya mike yana fadin"To ki cire bakin ki a ciki ba ruwanki ahto.."
Sai naga daga taimako kawai sai na tattara kwanukan daya bata na fice ina fadin"Allah ya kyauta"
Da gatse ya amsamin da Ameen sai abun ya bani Dariya a raina nace mata da miji sai Allah sai su shirya ma ban sani ba.
Kuma saboda Zainab din yaki kai wayarsa ya gyara. ya gwammace ya zauna ba waya nidai tunda yace ba ruwana na cire bakina data kara kirana,sai nace mata nayi mgana yace zai kirata in ya gyara wayarsa Da dai taga ba Nemanta zai yi ba an fara azumi Takwas sai gata ta iso,ita kadai ko Farhan bata zo da shi ba, ta yayesa yana gidan su Tace ko Daddy bai son ta taho ba Shari'a har Falon Mama ammh Gogan ka yace shi fa ya gaji kowa yayi ta kansa baiwar Allah sai kuka take yi a raina nace ita kuma nata Jarabawar kenan na soyayya Allah yasa mu dace.
Yadda yake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login