Showing 201001 words to 204000 words out of 288345 words

Chapter 68 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

728

sannu kaji ko"
Kai Tsaye yace"In sha Allahu Inno"
Daga shashem Inno Dakinsa ya wuce yana neman Fadila a waya bayan ya sameta ta Dauka sun gaisa cikin Dakushewar murya yace"Fadila ki kira mijin Fa'iza ki tambayesa asibitin da suke kije ki Dubamin Ahmad dan wajen Fa'iza. in da yuyuwa ki saka ayi masa Transfer zuwa in da kike aiki "
Cikin Ladabi tace"To shikenan Abba"
Daganan ya katse wayar saboda Haushin Ishaq din yasa bai kirasa ba,ransa kawai yaji yana Tafasa a Fili ya furta"in dai ko hakane Zan tabbatar masa da Fa'iza na da Gata"
Ko Ammi da taga yanayinsa ta tambayesa,sai yace mata bakomai gajiyan aiki ne kawai shi kadai ya zauna yana auna wasu abubuwa sai yaji ya zaku a zauna ma domin yaji inda bakin zaren ya fara
Ya kira wayar Fa'iza bata Dauka ba,sai ya kyaleta Tunda Sun sake mgana da su Goggo sun tabbatar masa sun hanata tafiya ta shige Daki tana ta kuka,sai ya bari sai zuwa anjuma zai sake kira ya lallasheta.
Har ma ya fita yana Office Nana Fadila ta kirasa ta fadamai jikin Ahmad da Sauki,zazzabi ne ya rikita jikin yaron,sannan kuma ta maida shi asibitin da take aiki Abba yaji Dadin jin haka cikin Murna yace"Dakyau Allah ya yi miki albarka Nana Fadila"
Ta amsa da Ameen Abba kafin tacigaba da fadin"Ammh Abba Laluran Ahmad har da rashin Uwa a kusa. Sai kuka yake yana kiran sunan Umma sai da muka saka alluran barci cikin Drip dinsa sannan muka samu ya kwanta yana barci"
Shuru Abba ya yi kafin yace"Bakomai Fadila ina shi Ishaaq din..?
Fadila tace"Yatafi wajen aiki sai dai Mahaifiyarsa na nan,tare da amaryansa suka tafi inaga ita gida ta koma tazo da wasu kayan"
Abba ya jinjina kai yana fadin"Bari zan kiraki ina office ne"
Daga haka suka yi sallama Ranar gabadaya ransa a bace ya yini a office duk wanda ya gansa sai yace yau waya bata ma Eng,rai an riga an san shi Mutum ne,mai barkwanci da Wasa da Dariya shi ko Bacin ransa irin Labarin da ya samu ne Ishaq ya basa,kunya sosai shiyasa yaga kiransa yaki Dauka sai dare da ya koma gida yayi wanka ya na Hutawa ya kira Fa'iza domin yaga kiranta Daga baya.
? Sanda wayar Abba ta shigomin na Idar da Sallar isha'i kenan,ina ta kuka tun Safe da Mallam ya hanani Tafiya nake kuka sannan ban ko kara lekawa ko Falo ba, da Farko Kin amincewa nayi da Goggo taso tsaidani sai da Mallam ya fito da kansa ya rika lallashina sannan na Hakura bayan yace Abba yace kada na tafi na Dakata,Tunanina Ya'yana sai a lokacin na Fahimci nayi Wauta,kada na zo na rasa ya'yana Saboda su na zauna shekaru ina kunsan bakinciki yanzu in na rasasu wake da asara? kamar an rufe zuciyata na daina Hango duk abunda ya Shude a baya ya'yana kawai nake tunawa da kuma Halin da Ahmad yake ciki nayi ta kiran Ishaq naji ya jikin nasa Ammh bai Dauki wayata ba, sai na sakama raina na rasa Ahmad shikenan ya rasu Goggo kuma banza dani tayi bata kara kulani ba Har Yaya Mariya tazo tayi ta aikin Lallashina ban saurareta ba.
Sanda naga kiran Abba kukana sai yaci karfina a raina nace rasuwar ya kirani ya fad'amin Shiyasa sai da ta kusa katsewa Sannan na Daga ina kuka nace"Ahmad ya rasu ko Abba..?
Cikin Muryan Lallashi yace"In ji wa..?Ahmad na nan da ransa kuma jikinsa da Sauki, yana asibitin da Fadila ke aiki Ita ke kula da shi"
Fadin haka yasa ajiyar rai ya kwacemin har sai da Abba yaji cikin Dariya da kuka nace"Da gaske Abba..?Da gaske Ahmad yaji sauki"?
Kamar yana ganina ya gyad'a min kai kafin yace"In sha Allahu ki kirata kiji yanayin jikin nasa. in baki yarda dani ba"
Da Sauri nace"Na yarda Abba wlh na yarda"
Sai yace"To ki daina kuka mana Fa'i Share hawayen ki kin ji ko..?Ahmad ya samu sauki sosai har yana mganarsa ma"
Kamar yana ganina na ko share Hawayena Hankalina ya kwanta Cikin Sanyin murya nace"Na share Abba. Na bar kukan wlh"
Abba ya gyara zama yana fadin"Dazu ni nace Goggon ku su tsaidake saboda barinki ki tafi Lagos ke kadai Fa'i hatsari ne ga shi baki da ishashen Lafiya,kuma baki san w???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aje ba wahala zaki sha ki bari in kina son zuwa zan zo sai mu tafi ta jirgi yadda bazaki wahala ba"
Da Sauri nace"Na hakura Abba daman da naji jikin Ahmad din ne ammh tunda ga Anty Fadila ga su Zainab basai naje ba"
Abba yayi mirmishin su na manya kafin yace"Shikenan to ki kwantar da Hankali ki kira Fadilan sai ta baki Ahmad din kiji muryansa ko..?.
Kunya ta kamani na noke fuska ina yar Dariya mun dade muna Hira da Abba yana ta jana da wasa domin ya kwantar min da Hankali,daga karshe ya bama Ammi itama ta rika Lallashina nan da man naji zuciyata tayi sanyi Hankalina ya fara kwanciya kunya da nauyi yasa na kasa kiran Anty Fadila kamar na kira zainab sai na rasa me zan ce mata ganin itama bata nemeni ba.
Zama na gyara waya a hannuna ina jiran kiran Anty Fadila har goma ta gota bata kira ba,Duk kuma sai na Damu kamar na kira wata zuciyar sai ta Hanani,goma da minti shidda sai ga Kiranta da Rawan jiki na Daga,cikin sanyin murya na gaisheta ta amsa Lokaci daya tana fadin"Ya jikin ki Fa'in mu..?
Kai tsaye nace"Naji sauki Anty Fadila"
Ina so na tamnayeta jikin Ahmad kunya ta hanani kamar ta sani sai tace"Ina asibiti,dayake aikin Dare gareni ga Ahmad yau ya kira Umma yafi sau dubu"
Murna ta kwace min na kasa mgana har sai da naji Muryan Ahmad yana Fadin"Umma."Umma..ni zan dawo wajen ki"
Sai kuka na rud'e na mike har hijabin jikina na neman kadani Cikin rawan murya nace"Ahmad din Umma..Daina kuka kaji ko..?
Kamar yana ganina ya fara goge hawayensa yana fadin"Umma ina ta kuka ina kiran sunan ki baki zo ba Umma yaushe zaki dawo..?
Ina sharan hawaye nima nace"Kayi hakuri Ahmad din Umma zan zo in dai ka sake kirana ya jikin ka..?ka warke ko..?
Da kai ya amsa min cikin muryan Kuka yace"na ji sauki Umma Anty Fadila tamin allura,Anty Zainab da Daada sun kawo min nama Umma"
Cikin jin dadi nace"Sun kyauta kaci abinci sosai sannan ka rika shan mgani kaji ko Ahmad di'n Umma..?
Da sauri yace"Umma yaushe zaki zo..?mu kadai ne a gida daga Daada sai Anty sai Mama ke baki zo ba"
Cikin karfin hali nace"Ka rika shan mgani ka warke da wuri in dai kana so nazo na ganka"
Da Sauri yace"To Umma zan warke da wuri"
Cikin jin dadi nace"Yauwa Yaro na ina sauran yan'uwan ka..?
Ina yaya Amir ina Yaya Anum?
Bai yi mgana ba sai naji ana mgana kafin naji muryan Zainab tana Fadin"Maman Amir"
Nima sai na maida mata da fadin"Maman Fadil mutanen ikko"
Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Ba kin ki mu ba Maman Amir..? Ga Ahmad rigima duk ya rikitamu baya yarda da kowa sai Amir ko Anum har Honey baya yarda da shi yanzu shi dai Umma Umma. Don Allah Umma ta Dawo wlh gidan ba Dadi da baki nan"
Sai nayi mirmishi Lokaci d'aya ina sharan kwallah kafin nace"Daman gidan bai taba karban bakuncina ba to bakomai ba ne in bana nan Maman Fadil ba ga ki ba?nasan zaki kula da su"
Cikin Jimami tace"Nima kinsan ba iyawa zan yi ba.
Allah yasa ma nazo da Yarinyar nan dake min Reno. ita ke tayani Dawainiya da yara"
Cikin Tausayawa nace"Wlh ga shi kin yi nauyi,Allah dai ya raba lafiya"
Ta amsa min da Ameem kafin tace min ga Amir ta mikamai wayar ban san ko Ishaq na dakin ba,Domin banji Ko Tarin sa ba
Amir bai yi kuka ba sai dai shima Muryansa a sanyaye ya gaisheni na amsa ina fadin"Amir kana kula da Sauran kannen ka ko..?
Kai Tsaye yace"Eh Umma. Ahmad ke kuka kullum Mutsy ma nayi. Umma yaushe zaki zo ki Daukemu mu wajen ki zan koma?
Tausayin yaran ya kamani Cikin Dauriya nace"Zan zo watarana Amir..Ya mganar makarantar Boko kun fara zuwa?
Cikin sanyin murya yace"Sai Ranar Monday zamu fara zuwa makarantar su Fahad din Anty Fadila Daada ya sakamu"
Cikin murna ta nace"Eyee yan gatan Daada islamiya fa..?
Kai tsaye yace"Ba'a sakamu ba Umma"
Sai na jinjina kai kafin nace"To kace ma Daadan ku ya saka ku kaji ko..?.ya amsamin da toh sannan na sake gyara zama ina fadin"Amir kai ne Babba ka Kula da sauran kannen ka,Ka rika musu Bitar karatun Qur'ani kai da Anum Tunda kin yi nisa ku rika karanta azkar Safe da yammah,ban da abokan banza Amir ban da wasa na rashin gan gado,ka rika taimakon kannenka bangaran karatun Boko da na islamiya,kuma ku zama yaran kirki ban da damun su Daada kada ku ki jin mganar Antyn ku,duk abunda tace ku yi ko ku bari ku ji mganarta,kun samu bambamcin Muhalli ba kamar katsina bace Lagos Amir don Allah ka kula da kanka da kannenka, ku rika sallah akan Lokaci kuna yimin addu'a kuna yi ma kan ku kaji ko.?
Cikin Sanyinsa yace"In sha Allahu Umma"
Cikin jin dadi na sakamai albarka sai ya bama Anum wayar itako kuka ta sakamin tana cewa itama waje na zata Dawo sai da na Lallasheta da zan zo sannan tayi shuru itama fad'a na rika mata ina Fadin"Anum ke macece kin sani ban da waasa da maza a makaranta ban da kawayen banza Anum,azkar Safe da maraici kun iya karatun Qur'ani ku rika yi in da kika karkare yayan ku ya Tadake,ki kula da kannen ki gabad'ayan su Anum ban da rashin ji ko Rashin kunya ku ji mganar Daada Data Antyn ku in wani abu ya shige miki Dubu ga Antynku ga Mama ga Babanku duk zaki iya tambayan su kin ji ko?
Ta amsa min da naji Umma,mganarta tasa jikina yin sanyi da nace ta mika ma Musty wayar kafin ta basa sai tace"Shikenan Umma bazaki dawo nan da zama ba..?
Sai na kasa mgana na Dauke Hawayena ina fadin"In Allah ya yi zan dawo Anum"
Daga haka bata kara mgana ba ta bama Musty wayar shima duk yan Rigiman ne sai da nace zan zo gobe sannan ya koma yana bani Labarin agidan Anty Fadila an siya musu wannan an siya musu wannan yana gayamin Ahmad bai da lafiya suna ta kuka,Sai da Fadil ya kwace wayar shima duk labarin kuruciyar ne,Mun jima muna mgana da su wayar daga kunnen wannan zuwa wannan sai da naji kamar Muryan Yaya ishaq na Fad'in tafiya za su yi sai naji mgana dai sama sama kafin wayar ta katse na samu natsuwa da nayi mgana da ya'yana sannan na kuma Tabbatar da Ahmad na nan da ransa bai mutu, kamar yadda nake Hashashe ba.
Sai alokacin naji yunwa ta taso min na zare Hijabin jikina na fita Falo ba kowa kila Goggo na Dakin mallam Kitchen na shiga ina neman abinci sai ga Goggo ta shige muna Had'a ido tace"Kin gama kukan ne kuma kika Fito neman abinci..?
Sai na kasa mgana itama bata kara mgana ba sai da ta Dauki abunda zata Dauka sannan ta fice tana Fadin"Ki duba flalks din nan akwai ruwan zafi ki sha sai ya warware miki ciki yadda kika yini baki ci komai ba"
Naji dadin shawaran Goggo tea na Hada mai kauri na sha sai zufa nan da nan naji na fara dawowa Daidai sannan na Dora da doya da miyan da Goggo ta Dafa a cikin kitchen din naci na koshi na kora da ruwa sannan naji ni na dawo cikim Hayyacina.
Ranar barci nayi har da makara Washegari tunda Goggo taga na tashi Garas ina walwalata sai ta kalleni tace"Hala kun yi mgana da yaran ne..?.
Kai tsaye nace"Eh Umma jiya nayi mgana da su har Ahmad din yaji ma Sauki"
Sai Goggo ta gyada,kai kafin tace"Dakyau! Allah ya kara lafiya"
Ta Fahimci farinciki a Fuskata.
A ranar aka sallame su suka koma gida Anty Fadila na kira ta fad'amin sai na Kira wayar Zainab bayan mun gaisa da Tambayam mai jiki sai ta bani Ahmad da Sauran yaran muka yi mgana suma na Lura sun fara walwala da jin muryata.
Da nace bazan nemesu ba sai sun saba da Rashina ammh ban san nayi Fatali da wannan Tunanin ba sai da naga kullum Safiya sai na kira mun yi mgana da su,Ranar da zasu fara zuwa makaranta Zainab ta kira da Safe ta fad'amin harda Ahmad Tunda ya warware tace babansu zai rika kaisu tunda ya siya mota in an tashi Direban gidan Anty Fadila in ya Dauko su Fahad zai rika sauke su agida an basu waya,mun yi mgana nayi ta musu nasihan kada su manta da karanta addu'an fita gida da azkar tare da natsuwa suka tabbatarmin da bazasu manta ba.
Naji dadi hankalina ya kwanta Tunda Ahmad ya samu sauki sannan ya Daina Rigima,kuma Yaran hankalinsu ya kwanta tunda suna mgana dani,Jamal ashe sanda Ahmad yayi ciwo yana kano yazo kamallah Takardunsa sai daga baya ya koma sai naji Dadi da Amir ya fadamin yana yi musu Lesson agida kafin ya samu Tafiya bautar kasa ko bakomai shi yana gidan zai kula da wasu abubuwan sai na samu natsuwa Hankalina ya kwanta ammh fa ko? ban kira su ba zasu dauki wayar Antynsu ko ta Mama su kirani Amir da Anum tuni sun haddace Lambata.
Sati uku Tsakani Abba ya yi min waya cewa gobe suna tafe shi da su Inno yadda bai cemin komai ba nima ban kawo ba sai a daran Anum ta saci Wayar Mama ta kirani tana murna tana Fadamin gobe zasu zo wajena In ji Daada, sai Hankalina ya tashi na rasa ta ina zan kama mganar Cikin Tashin Hankali nace"Ke Saudatu bana son karya"
Da Sauri tace"Wlh Tallahi Umma har da ma Mama fa zamu zo Anty kad'ai zamu bari a gida"
Sai na yarda da ita domin tasan ai rantsuwa in kayi karya na shafa Fada musu ba kyau,Da Sauri na katse wayar sai na rasa wazan tambaya tuna Goggo yasa na kwashi gudu na Fita bata afalo tana Dakinta ina shiga na isketa tana zaune tana jan Cashaba ina Tsaye a kanta nace"Goggo Abba yace min zasu zo gobe..?akwai abunda zasu zo yi ne"
Kallomta tayi da mamaki kafin tace"Eh nima mun yi mgana da shi Inno ne da Baba ati zaso zo dubaki wani abu ne?
Kai Tsaye nace"Anum ta kirani da wayar Mama tace gobe Babansu yace zasu zo wajena, har da Mama itama"
Goggo tace"To ni ban san wannan ba kira Baban naki kiji"
Goggo ta fad'a tana kauda kai ni ko hankalima ne ya tashi bana so ya kwasomin yaran nan ban kuma san yadda zan yi da su ba.
Sai na kada kai na koma Daki Goggo ta bini da kallo kafin tace a fili"Ya Allah in da sauran zama Tsakanin yaranan Allah ya Daidaita su. in babu kuma Allah ya warware mana al'amuran"
Taki fad'amin abunda zai kawo su Abba saboda jin nima bai Fadamin ba,Abunda bata sani ba ina komawa Daki na kasa Hakuri sai na Kira Yaya Ishaq har sau uku bai Dauka ba,Dare ne nasan yana gida sai na Kira Zainab tana Dauka ta fara fad'in"Maman Amir"
Muryata a shake nace"Yana kusa..?basa wayar"
Tasan wanda nake nufi tunda ai a gabanta nake kira yaki Dagawa so yake yayi amfani da yarana ya sake Cutar dani tana bashi ko mganarsa ban jira ba na fara fadi'n"Kada kace zaka yi amfani da yarana domin ka sake Kuntatama rayuwata Ishaq.."
Kada mu yi haka dakai.
Ka bar su, su zauna in da ya zame musu Dole.
Naji Labarin kana shirin kwaso su ka kawomin su nasan manufarka wlh karka fara na riga nayi rantsuwan Wallahi Tallahi NAGAMA aure dakai. ya rage naka ka kyalesu ko kazo da su, ka kara Rikita su yadda kaima din zasu Gagareka"
Ina gama fad'in haka na yanke kiran ina Huci duk da Abba bai Fito Fili ya fad'amin ba ammh na Fahimci zama Abba ya Shiryamana kamar yadda yaso yayi tun farko na tuna mganar mu da Nana Fatima jiya har ce min tayi in Abba yazo yana tambayata kada naji nauyin gayamasa komai Abba zai kwatar min yancina to sai yanzu na Fahimci mganar ta gefen gado na zauna gabana na Faduwa ni bazan taba iya mgana ba. sai in har Ishaq ya warware mafarin komai da bakinsa.
Washegari ma yadda Goggo ta tashi da Shirye shirye na tabbatar da Zargina sannan da Safe mun yi mgana da Hafsah tace Har da Ammi da Yaya Abdul'Ahad a babbar Jeep din Abba zasu taho,Kuma naji Goggo na waya da Yaya mariya ita zatayi girkin bakin,Tunda Tafi kusa akan Anty Nasara ina Daki sai na Lafe wanka kawai nayi na koma na kwanta Ina Tunanin yadda komai zai gudana yau sai dai na samu mutuwar jiki da Faduwar gaba Ishaq da Mama suka Fara isowa tunda su tafiyar Jirgi ce,Ina Daki naji muryoyinsu suna gaisawa da su Goggo,naki Fitowa nima kuma ban ji an yi mganata ba Duk da Raunin jina nima na Koyi na kasa raunanun kunnuwana ina Jiyo mgana daga Falon Goggo.
Su Abba sai wajen sha Biyu suka iso,zuwan su yasa na fito bazan ji zuwan Abba da su Inno naki Fitowa ba,sanda na fito su Abba na kofar gida sai su Inno na duka na gaishesu Inno tace"Yar nan haka kika sha jinya..?jiki sai kashi..?
Baba Ati tace"Daman ai duk sauran sun fita kumari sannan ga rashin Lafiya kuma"
Sai mamakin Ramata suke yi wajen Mama na isa tana Falo na gaisheta sai naga bata son kallona kanta na kasa ni dai ban bi ta kanta ba. araina nace yaji barazana kenan bai Daukomin yaran ba wajen Ammi naje muka gaisa ita kan sai da ta taba wuyana Tana Fadin"Na shige su ni Aziza..Fa"i kin ji kasusuwa..?bari Baban Nana yazo tafiya dake zan yi na cike miki wannan kasusuwa da ba su da kyan gani"
Inno tace"ke ana shirin Daidaita komai tabi megidanta kina wata mgana"
Sai Ammi tayi shuru batayi mgana ba,Abba basu shigo gidan ba sai bayan azahar yaje duba ginin gida sai da kuma suka Tsaya suka yi sallar azahar sannan suka shigo nan ma cikin gida su Ammi sun yi salla sun ci abinci Inno da Baba Ati da Goggo sun kule sai Tattaunawa suke ni ko muna tare da Ammi tana ta ja na da Hirarta na barkwanci,su dai sun ci abimci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login