Showing 123001 words to 126000 words out of 288345 words

Chapter 42 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

742

na dauko kudin na basa ya karba Jikinsa a sanyaye lokaci daya yana fadin"Ki rika Rubutawa Fa'iza zan biya ki kudin ki da zarar na samu aiki in sha Allahu"
Ko kulasa ban yi ba sai dai na dago na kallesa kamar bazan yi mgana ba sai kuma nace"Kai dai baka na lissafe da abunda ka karba ba?ai shikenan."
Daganan sai bai kara mgana ba ya saka takalmi ya fita yaje ya tura ma Jamal kudin,ya dawo Yaya Ishaq na bani mamaki ko irin ya dan fita waje ya zauna bai iya ba yana gida koda yaushe dole damuwa tayi masa yawa,kamar zan yi masa mgana sai wata zuciya ta kwabeni na kama kaina.
Zainab na kiransa ko da yaushe ni ban san Halin da suke ciki ba sai wataranar asabar da Safe na shiga kai masa abun karyawansa naji yana waya ya daga murya sai fada yake yi Cikin kaukkausan murya yake fadin"Zeey na fada miki bazai yuyu nazo abuja na tare ba,bani da aikin yi ba wajen zuwa ke ba zaman gida ba ki fice tun safe ki barni da mai aiki, Fadil ma ki bar mun shi ya Debemin kewa gida kike tafiya da shi gwara na Dawo gida na zauna nan din ma ina da uwa da wata matar da kuma yara"
Ni dai daga haka na sauke abun hannuna na fice yayi nisa a mganarsa bai ma san na shigo ba.
Da na fita acikin raina sai abun ya fadomin sai naga Zainab na da gaskiya abunda ya zabar mata tun farko ne meyasa yanzu zai sauya..?ai yasan da akwai rashi da samu akwai rayuwa akwai mutuwa kuma ya zabi hakan duk wanda ya siyi rariya yasan zata zubda ruwa yadda ba wanda ya sani cikin mganar nima nayi kamar ban ji komai ba, na cigaba da Sabgan gabana.
Ina ta buga bugan? yadda zan had'a kudin makarantar Amir saboda su Anum sun kusa hutu sannan ga kudin makarantar Tahfez din su yanzu sun ciresa a kudun makaranta Daban za'a biya hakuri na bada wanchan Team din ba'a biya ba yanzu kuma baamai karban uzurin mu,Shiyasa nake aiki ba rana ba Dare rana na Dafa zobo sai Uku,saboda zafi da nake tunkara da Wahala yasa kaina ya fara ciwo da ganin Jiri ina jin haka nasan jinina ne ta haye sama bana samun Hutu ga amfani da Hutu nasan in ya kwantar dani abubuwa ba zasu tsaya sai naje kemist aka auna ni aka ga jinina ya Hau sai aka bani mganguna,Dalilin haka yasa kwana Biyu nayi baya da Wutar Sai dai Hafsah ta Dafamin kafin tatafi makaranta sai ta barmun na hada,kunin Aya bai da matsala da kaina nake yin ta tadawo da wuri sai ta sake Dafa na yammah ni kadai araina ina fadama kaina Fa'iza bi sannu Sannu zafin nema baya kawo samu.
Allah maji rokon bayinsa domin ban daina rokon mafita daga garesa ba,kawai sai ga kiran Hajiya tana fadamin bikin da ta fadamin na kaduna saura sati biyu,In na samu Lokaci nazo gida na sameta ina jin haka ko ban yi wasa ba,Allah yasa Ranar Hafsah na gida sai na bar mata komai Yaya Ishaq na dakin Mama da na shiga ciki na shiga na gayamai zan fita Hajiyar su Raliya ta kirani kan wani aikin Turaren wuta bai ce komai ba yace a dawo lafiya Mama kuwa sai da ta tofa kallona tayi tana fadin"Da zaki kwashi kafafu ki fita abinci wa kika bari ya dafa ya bamu..?
Kai tsaye nace"Hafsah zata dafa ai ba jimawa zan yi ba zan dawo"
Baki ta tabe kafin tace"Wanki na ya taru wannan satin naga baki zo kin kwashe kin wanke ba ko kin gaji ne..?
Yadda tayi mganar kamar wata baiwar ta ko yar aikinta Tunda muka Dawo gidan nan ni nake kwashe kayan Mama in sun yi Datti na wanke mata.
? kuma na zauna na goge mata,ba kayan Mama ba Har na Yaya Ishaq ni nake wanke masa wani lokacin saboda bai saba ba,Sai dai in aiki yayi min yawa sai nace yakai wanki da guga zan ba da kudin.
wannan satin da ban ji dadi ba ne ko na yaran Hafsah ta rage musu nasu ammh ji yadda take min mgana kamar tana biyana.
Kaina na kasa nace"Banjin dadi ne wannan satin ban yi wanki ba, ammh za'a wanke in sha Allahu"
Yaya Ishaq mamaki ya kamasa cikin mamakin yace"Mama bata jin dadi yanzu ko Badar baza ki saka ta wanke miki kayan ki ba..?baki ga ayyuka sun mata yawa ba ne..?
Sai Mama ta fara bala'i tana fadim"Kaga Badar din ne a gidan..?da makaranta zataji ko da aikin gida ba zaune take ballatana kace"
Kai tsaye yace"Ai ba kullum ake makaranta ba Mama ita Hafsah ai karatun take yi kuma bai hanata ta taya yayarta aiki ba."
Mama ta cika tayi fam ta faara fadin"Na lura ai yanzu yarinyar nan tafini Daraja a idon ka saboda tana Dauke maka wasu laluron,har Abada bazan so Dangin jaraba da cin Amana ba'"
Naga cin mutumci zai yi yawa sai na tashi na fice sai yi take yi ban bi ta kanta ba, na dauki pos dina da na siya da kudi aciki nayi tafiya ta, adaidaita na hau har anguwan su Hajiya kusa da jami'ar alkalam.
Nasameta a gida da tana shirin fita ne ma sai gani,sai ta fasa bayan mun gaisa tamin bayanin komai zan had'a Turaren rushi da na Humra sai kwallacha sai zan yi ma Amaryan gyaran jiki,duka zasu bani dubu dari biyu,Naji kudi sai na rude cikin Firgici nace"Hajiya duka nawa..?
Hajiya na dariya tace"Eh kudin aikin ki da ladan ki ba'
Sai na hau mata Godiya sai ta bata rai tana fadin bata so na koma na zauna araina ina Hamdala,Nan take ta bani dubu dari a hannuna sauran tace zata Turamin ta banki ta karishe da fadin"Sati mai shiga amaryan zata zo nan zaki zo ki yi mata ko sai dai ta biyo ki gida..?
Cikin Ladabina nace"Hajiya sai dai gida kinga ga yara sannan ga Mama bazai yuyu na rika Dadewa a waje ba"
Hajiya tace"Eh hakane shiyasa da suka yi mganar girki nace su dauki wata kawai zuwan ki kaduna da wahala"
Na jinjina mata kai sai tace ba Damuwa fita zatayi duk abunda ake ciki sai mun yi waya,tare muka fita da ita bayan ta bani kyautar atamfa da Mayafi,sai turare da lotion mai kyau,tare muka taho Direban ta ya Daukoni sai da suka saukeni a gida sannan ya wuce da ita in da zataje.
Bakina kamar gonar auduga haka na shiga gidan cikin murna naja Hafsah Daki na zayyana mata komai na nuna mata kudin cikin Farinciki tace"yaya Fa'iza Hajiya tana da kirki tana son ki da arziki"
Ina jinjina kudin hannuna nace"Bari Hafsatu Allah dai ya biya ta kawai"
Aranar bamu je kasuwa ba sai washegari mukaje da Hafsah ta tayani na sissiyo abunda zan bukata ina Dawowa na Dukufa na fara aikin Hada Turaruka,araina ina jin duka matsalolina zan kauda su in na samu wannan riban aikin,Aikin zobo sai ya koma sau daya a rana kunin Aya ma sai da yammah Lokaci na bada kacokan kan hada Turarukan nan ban rufe kwana hudu ba, na gama su duka,Kwallachan ne ma ta bani wahala ita sai da nayi kwanaki ban gama ba,inagamawa na kira Hajiya sai tace na ijiye komai a Hannuna in su Laila sun gama gyaran jiki in zasu tafi sai su tafi dashi.
Haka ko akayi satin bikin Amaryan Laila mai kyau da ita yar gayu ga ilimi ga nasaba ga kudi,ma'aikaciyar banki ne a kaduna suke Raliya ta dinga rakota kullumn da yammah muke farawa sai shida,A tsakar gida nake bazamana Tabarmana a rumfar nan Ishaq na Daki baya fitowa ga Hafsah wani Lokacin harda Badariya sai abun ya kara armashi,Laila ba ruwanta ga sakin fuska Anty Fa'iza kasa da sama take kirana kamar yadda Raliya ke Kirana,Sannan jininta ya shaku ita da Anun ta dinga rokona in bar ta su Tafi Bikin ta kaduna da ita Amana Hajiya zasu dawo da ita ban yi mgana ba sanin Halin Babansu da Mama ba lalle su bari ba.
Sati daya nayi ina mata sai ga shi ta fito shar da ita abunka ga farar fata,ga jiki lawai lawai sai tashin kamshi take yi,Da naga ta matsa da mganar Tafiya da Anum sai nayi ma Yaya Ishaq mgana da kaina nayi mamaki da ya barta ammh yace kada ta Dad'e a dawo masa da yarsa. ranar Litini Laila taji Dadi tana ta Godiya Direba yazo ya kwashe su ranar karshe da kayan su aranar kuma Hajiya ta Turomin sauran kudina, na daka tsalle ina murna nayi sujuda na gode ma Allah.
Batare da sanin Yaya Ishaq ba,naje na yi ma Amir komai har Uniform an basa na Biya musu kudin Tahfeez sannan na shiga kasuwa na siyo mai takalmin makaranta da jaka da littafai,yanzu nima sana'a ta Budemin ido nasan sirrin shiga kasuwa lungu da sako.


*INGANTACCEN ZANCE*.

*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.
*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*
*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*
*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.
*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*
*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 dasu.*
*Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*
*08032773332.*

'?.



*Janafty*
[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2005*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Ranar monday da safe bayan yaran sun shirya Hafsah tayi musu abun karyawa,Musty sai tura baki yake yi shi bazai je makaranta ba yau.
Na kallesa ina kokarin saka masa safa yana Turje kafa cikin haushi na mangarar da kansa ina fadin"Zaka tsaya ko sai na dake ka..?
Sai ya fara kokarin sakin mun kuka na ko zare mai ido ina fadin"Na dake ka ne da zaka min kuka..?
Amir na gefe da ya shirya Tsaf yau zai fara zuwa makaranta yace"Umma cewa yayi bazai je ba, saboda Anum bata nan yau"
Na kallesa da mamaki sai abun nasa ma ya bani dariya na jawosa jikina na Rumgume ina fadin"Haba babban mutum na Umma.Anum din ai yau zata dawo yi hakuri ka saki ranka kaji"
Cikin muryan kuka yace"Da gaske yau zata dawo..?
Da sauri na amsa mai da Insha Allahu sai ya saki ihu Ahmad na tayasa Amir na gefe an saka hannuwa aljihun wandonsa kamar wani babba na kallesa ina Dariya Hafsah ta fito daga Daki tana fadin"A'a yan jss ba zama ne yau..?a tsaye zamu tsaya..?
Fuska yayi bai yi mgana ya Dauki Sabuwar Jakarsa ya rataya yana fadin"Umma yaran nan su zo mu tafi"
Na bisu da Allah ya kiyaye hanya bayan na rike ma Ahmad jaka zan rakasu kofar gida Hafsah ta daga murya tana fadin"Amir shine ba mgana..?zaka zo ka same ni ne.."
Muna gabda fita daga falon naji muryan Yaya Ishaq a sama yana fadin"Yaushe Amir ya fara zuwa makaranta ban sani ba..?
Su sun riga sun fice sai na mikama Hafsah jakar Ahmad tabi bayan su ni kuma sai na Dawo tsakiyar falon, yana daga kofar Dakinsa alamun yanzu ya fito sanda zamu fita daga falon zuwa waje.
Cikin sanyi na, na gaishesa ya amsa a gajarce yana sake fadin'Ko ba shi ba ne nagani da kayan makaranta ya fita da su Ahmad ba.?
Kai tsaye nace"Shine ni naje nayi biya komai ranar jumma'a yau suka ce ya fara zuwa tunda karatu yayi nisa"
Sai kawai ya tsaya yana kallo na Fa'iza ta sauya sauyin dake basa mamaki bai isa in zata yi abu ta nemi shawaransa ba, ance mai hali baya fasa halinsa kawai sai ya fara fada yana fadin"Meyasa kika raina ni ne Fa'iza kin ware ni kan sha'anin ya'ya na ban isa ki fadamin Amir zai fara zuwa makaranta ba sai dai ki rika yin komai kanki tsaye..?sai yanzu na yarda da mganar Mama, kina ganin yanzu kina samun kudi kina Dauke laluran kanki da na gida shine kike ganin zaki iya yanke hukuncyi kan ya'yana to baki isa ba,ba na so.."
Ya karishe fad'a har yana nuna min yatsa kawai sai na saki baki ina kallonsa na kwaso gauron numfashi zan tare sa da mganar ya wuceni Fuu kamar kabubuwa ya fice sai Dakin Mama na bisa da kallo hannuna sabe da Haba na a fili na furta"Yau naji karfin hali ko na gani zencen ni Fa'iza"
To in ba karfin hali ba sai yanzu kasan da ya'yan ka ne?a baya da kake banzar ta dasu ka zabi wasu akan su ba'ayi maka mgana ba sai yanzu ne kake da bakin mgana..?
Kawai sai nayi tsaki na cigaba da Harkan gabana abun karyawansa ma sai Hafsah ya ma mgana ta basa, ni Daki na shige na kwanta a raina nace bazan sake yarda ka rika sakani Damuwa ba.
Daman da kullatan fad'an safe ya shiga kuma Dakin Mama ta kara ma Wutar fetir, da yammah sai ga Direban Hajiya ya kawo Anum da sha tara na arziki kaya akwati guda nata ga kayan wasa har da karamar Ipad na game din yara,da Sabuwar jakar makaranta da littafai da kayan biki cike da Jakar bikin ga Hoton Amarya da ango nan sannan ga kudi dubu goma Sabbin yan Hamsim Hamsin a Cikin wata farar takarda,Harda takalma masu kyau sai sweet da chaculate na su musty,Anum da shigem kaud'i sai murna take yi bakinta ya tsinke da Labari har Yaya Ishaq dake ciki sai da ya fito,Yana kallon kayan Anum na ganinsa ta nufesa ta rikesa bakinta yaki yin shuru an bata kaza sun je kaza sun je kaza.
Fuskarsa ba fara'a ko kad'an,kamar ta Fahimta ne yasa ta bar ta batunsa ta kwashe kayan taje ta nuna ma Mama Hafsah taso ta hanata nace ta kyaleta ta shiga ba dad'ewa sai gata tazo kiransa in ji Mama, ya tashi ya tafi ba jimawa sai ga shi ya shigo ina faman tattara sauran kayan da Anum ta watsar ya daga murya yana fadin"Daga yau ya'ta bazata kara zuwa wani gida kwadayi ba"
Sai na Dago ina kallonsa ni yanzu ya Daina bani mamaki a baya sai nake ganin Rayuwa tasa yayi sanyi ammh daga Safiyar yau na Fahimci lambo yayi.
Kamar zan yi mai mgana sai na fasa na zata shikenan kawai sai naji yana fadin"In ke zaki je kije, ammh kada ki kara tura ya'ata wani gida da sunan kwaad'ayi."
Sai na sake dagowa ina kallonsa ban yi nauyin baki ba nace"to ai in dai kace naje kamar kace itama taje ne.Saboda ni ya'yana na zaba akan ka.Kai kuma ka manta ka zabi Zainab da iyalanta a kaina da ya'yanka..?
Tsuramin ido yayi nasan yana mamakin kalamai na ne ni kuma ganin yaji mganata yasa na juya nayi shigewata Daki na barsa nan bansa ya yakare ba, Anum ta dawo da kayan ba jimawa su Amir suka dawo da ga makaranta sai Ihu ya tashi Anum ta Dawo labarai ta rika basu na abunda ya faru a chan har da abunda taci ta kwaso musu kayan suka yi min Baja baja da falo sai da na fito nayi musu fad'a Amir ya hau taya Anum tattara kayan yana fadin"Kiyi hakuri Umma zamu kwashe"
Sai na Sassauta ina fadin"Lokacin sallah yayi ayi alwala ku tafi masallaci Anum tazo muyi namu a gida"
Da haka suka kwashe kayan suka maida Dakinsu mazan suka fita alwala Babansu na dakin Mama ya tarasu suka tafi masallaci mu kuma mukayi namu agida ba abinci sai Hafsah tayi Taliya jallop,ta sa ka kazan da Anum tazo da shi na biki aciki,ita muka ci da Daddare kafin mu kwanta na raba ma yaran kayan Fulawan da Anum tazo da shi na Bikin harda lemuka na kuma aika ma Mama nata,ta kuma karb'e ko kunya, sai da safe na Kira Hajiya nayi mata godiya.
Daga wannan lokacin sai ya Dawo sak Yaya Ishaq din da na sani mara ragowa sannan mai tsanani sai na Fahinmci,wani abu har da zafin Talauci ya sake firgitasa sai dai bai min tijaran da ya saba da agaban mama ko mutane, saboda yaga bakina ya bude yanzu zan maidasa mganar da bazai so ta fita wani yajita ba.
Duk nayi biris da shi domin har ga Allah ba ina zaune saboda ina son sa ba ne,babu wani birbishin so a cikin zuciyata in a baya na so shi Saboda yana Uban ya'yana yanzu ko wannan Darajan bana dubawa,abu d'aya na sani ina zaune ne saboda ya'yana ba saboda shi ko jiginannen auransa ba. Shiyasa nake kama kaina ina chan ina Hidimar sana'ata da ga shi Har maman bana ta kansu,Anty Binta ma ta rage zuwa akai akai su Anty Mahma ma sai dai su leko mu ni kuma ban fasa abunda na yi niyya ba,Kananun lalurori har manyan ma ina Daukan su da sana'ar da nake yi,wannan zafin ran da na Talauci ban yarda na zauna ya saukemin ba,Ya saba in ya gama min Tijara na rika basa Hakuri ammh yanzu da ya fara in bana jin mgana zan bama banza ajiyarsa ko na bar masa wajen.
A cikin wannan takun sakan da muke yi ne, kayan abinci suka kare dole ni na fidda kudi na siya Mama da gadara duk abunda take bukata zatace na bata kaza kamar ita nake yi ma wahalan,sai dai ban taba biye mata ba, ina ganin ta a matsayin uwa shiyasa ban taba Daga kai akanta ba. shi kuma komai nayi sai yace na rubuta in ya samu aiki zai Biyani ni ko nace shi ya Lissafa da kansa mana
Muna cikin haka zazzabi ya Sarke sa kamar wasa ya kwantar da shi Ranar kwance ya yini Dakin mama,Yadda bai fad'amin ba shi da lafiya ba, nima ina da Miskilanci ko lekawa Dakin Maman ban yi ba ballatana nayi mai sannu Abakin su Amir naji Daada bai da lafiya, Mama ce ta leko da kanta Dakina da bata taba shigowa ba, sai dai ta tsaya daga bakin kofa tana ce min na bada kudi Amir ya raka Ishaq kemis? bai jin dadi,kamar nace bani da shi sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login