Showing 264001 words to 267000 words out of 288345 words

Chapter 89 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

695

mu da kayan mu har da rara ma su Hafsatu kamar zasu yi kuka suna Dagamana Hannu Hajiyar su Raliya tace sai gobe zata taho Abujan tana taro yau Abba har da shi a masu rakiya ya yi min kuma dukkan nasihan da Uba zai yi ma yarsa.
Shi da su Baba Ati da Inno tunda tun Daurin auren suke min har kuma da zamu tafi sai ga shi ina sharan kwallah Rayuwa kenan kana naka Allah na nashi kuma na shi Tsarin shine daidai.
Da yake motar Sabuwa ne ga Lafiya karfe biyu muna garin Abuja,Direban baisan wajen ba,na kuma ta kara kiran Engr lambarsa bata shiga muna cikin Tararradi ne sai Kafaya ta kirani ita ta agaza tayi ma Direba kwatancen gidan su na gwarimpa tunda daman nan zamu fara sauka kafin Su rakamu gidansa na Abuja mu kwana kafin gobe mu wuce Benue din.
Gidan su Engr wani katon gida ne Aljannar Duniya har ta Hajiyar Dala mai takama da suna da shi sai ta ce"Kai kun ga gida kamar a turai"
Komai ba hayaniya cikin aji da kudi,Gida ne mai girma daga su sai ma'aikata acikin wannan wargajejen gidan Hajiya Shukra da kannenta mata su suka tarbemu tare da su kafayatu,munga karamci irin karamcin da bamu taba zaton suma sun iya ba,ko don ita Hajiya Shukran Bahaushiya ce..?
Wani shashe mai falo biyu suka saukemu ashe shashen Engr ne Sharifatu ke fad'a,babu abunda babu a shashen na kayan more rayuwa,abinci ko kala kala da ababen sha ga su nan nama ko harda na Dawisu sai wanda kake jin ci.
Sallah muka farayi kafin zaman cin abinci ni dai na kasa ci saboda rashin jin Engr,nasan kuma nasan shima bai Sameni ba ne shiyasa ban jisa ba.
Direban da ya kawomu shima an sauke shi a daki na musamman an bashi abinci da abun sha ya huta zuwa Gobe tunda Har Benue da shi zamu je.
Dakyar na iya tsakuran abinci shima sai da Ammi ta matsamin sai bayan mun gama cin abincin sannan Hajiya Shukra ta shigo sanye cikin wata shadda Doguwar riga taji aiki,ta ci Daurinta daga ganinta kinga bahaushiya mai ilimi da wayewa da sanin ya kamata ga ta da fara'a,haka hakoranta duk a waje ita da Sister dinta suna mana maraba da zuwa da tambayan Hanya.
Su kafayatu ma basa kama da Engr sai dai kama ta jini ammh yanayin Fatan su iri daya ne,tsawon kuma ma Hajiya Shukra suka Dauko dukkansu zabga zabga ne masha Allah.
Tana ganin su Anum ta kirasu tana tambayan su sunayen su dayake sun san juna da Ammi suna ta Hira tace"Wannan jikata ce ko..?
Tafad'a tana kallona ni daman Tunda ta shigo kaina ma kasa tun kafin ma Anmi tayi mgana Hajiyar Dala tayi karaf tace"Eh ita ce ma ta biyu. ai akwai ma yayanta da kannensu biyu,Kunsan ai auran zumunci ne da shi tsohon mijin nata"
Ammi sai hararanta take yi fadi ba'a tambayeta ba sai Hajiya Shukra ta bata mamaki da cewa"Ai Babatunde ya fad'amin Allah Sarki ya sunanki..?
Ta tambayi Anun ni kuma ina jin tace Babatunde nasan Engr take nufi tunda shi ya fad'amin sunan datake kiransa.
Anum da Falaq suka fada mata sunanyensu cikin Mirmishin ta tace zasu zo mata hutu sai suka juya suna kallon mu tayi dariya kafin tace"Suna tambayan ku ne ku ce eh"
Gababaya sai akayi dariya,ni kuma har inda nake ta kariso ta dagoni ta Rumgumeni kafin ta dago kaina Tana Fadin"'Sannu da zuwa Faa'iza.."
Allah ya sanya alheri ya baku zaman lafiya"
Gabadaya aka amsa da Ameen cikin yanayin fara'arta tace"Papa din su na hanya. bari ya kariso ku gaisa sai muje chan gidan ko..?
Kaina na kasa na kasa mgana sai ta Dafa kaina tana fadin"ki saki jikin ki kin ji ko..?nan din ma duk gidan ki ne kina jina ko.?
Sai na daga mata kai sakin Hannuna tayi kafin tace"Baku yi mgana Da Babatunde ba ko..?
Meeting garesu nima tun safe da mukayi mgana ban kara jinsa ba"
Sai naji Hankalina ya kwanta jin yana Lafiya sauran yan'uwanta ma suna ta saka albarka kamar zasu lasheni.
Bayan fitan su su Kafaya suka shigo dukkansu kaya iri da'ya suka saka Atamfa riga da sikat har da Murjanin su,Rumgumeni suma suka yi suna murnan ganina Yan biyu ne masu kama daya baka iya bambamce su.
Harda Mirmishin su iri daya ne.
Suna kallo na suna min mirmishi sai na Tsargu naga kamar sun ganni ba yadda suka yi Tsammani ba ammh basu nuna ba.
Kafaya tafi yawan mgana ita tace min"Anty Fa'iza u are welcome..'"
Ita kuma Sharifa ce min tayi"Bro Tosin na son ki sosai ya bamu Amanarki yace mu kula dake sosai kiji abinci kada ki zauna da yunwa"
Dariya kawai nayi nasan zai aika su Ammi na gefen mu suna ta kallon mu gwanin ban sha'awa zama suka yi dani suna min hiran Engr ina dariya ashe har a gida haka yake na Dauka yana rage wasu abubuwan ashe ma ni banga komai ba.
Sai da akayi la'sar suka fita suka barmu muma muka yi sallah Ammi da su Anty Nasara sai fad'i suke nayi dacen suruka da dangin miji Hajiyar Dala dai ba baki sai dai nazarin abubuwa da take gani,sai bayan mun yi sallah ne aka aiko cewa mu shirya zamu tafi chan gidan daman bamu fito da kayan mu ba,sai muka natsa sannan Maa tazo ta tafi dani wajen Paapa dake falonsa.
Dattijon ne mai kamala,yana zaune yana karatun Jarida da siririn gilashinsa mai karamai karfin gani,har kusa da kafafunsa Maa ta kaini ta zaunar tana fad'amai ga ni nan ya sakamin albarka.
Ba ruwan shi kaina ya dafa yana ta sakamin albarka daga karshe yace"Allah ya sa ku zauna lafiya ki yi hakuri kin ji ko..?Oluwatosin God Boy ne ammh in bai yi miki daidai ba. juzt call me nima papa din ki ne kin ji ko?
Sai na gyada mai kai ina Godiya ya bani kyautar kudi cheque Maa ta amsamin,nayi masa sallama muka fice bayan yace bazai samu zuwa Beneu ba. saboda aiki sai dai akwai brothers dinsa da Danginsa yasan i will Enjoy it.
Bayan ni ma har su Ammi sun je sun gaisa sannan muka tafi gidan Engr Dake Apo,a motar Papa direba ya tukamu ni da Maa da Ammi sauran kuma suka Biyomu daga baya,su da yake basu da wani al'adu kamar namu na Hausawa Nakiya kawai da alkaki Ammi tayi musu aka raba biyu aka bamasu Maa sauran kuma Ammi tace sun munje Benue tunda iya abunda muke da shi zamu yi.
Gidan Engr dake Apo Abuja karamin gidane ammh ya hadu falo biyu Bedroom hudu sai compaund akwai kitchen da bayika sai ta chan baya akwai tsakar gida da Famfo.
Ammh gidan ya had'u yaji kayan alatun rayuwa har da wajen shakawatawa da wajen lilo,Akwai megadin dake tsaren gidan,Kowa sai santin gidan yake masha Allah.
Hajiyar Dala fad'i take yi"Allah mai kyauta da kari yanzu Fa'iza ne a wannan gidsn..?
Tana tunanin ko yayanta da suka auri masu da shi ba wacce ta samu gida kamar nawa,daganan ta sare tasan na riga na sha kwana daman ai abunda ya baka dariya watarana shi zai baka Tsoro.
A babban bedroom din? gidan Maa ta saukeni tana min addu'a su kafaya ne suka rika zagayawa da mutane suna ganin gidan da suka dawo suka baje suna labarin gidan Yaya Mariya tace"Faa'iza mutumin nan kudi garesa kenan"
Ashe bamu ga kudi ba sai da Maa ta saka aka bude dayan bedroom d'in shake da akwatina bakwai babu abunda babu aciki harda zinare sai makulin mota kamfanin Peageua,ashe itace muka gani a haraban gidan,tab ashe kudin da yabani na kayan cin bikin ya hada lefensa ba tare da ya gayamin ba.
Kayan ciki kuma masu tsada ne da yarari,bakin dangina ya kasa rufuwa dai masha Allah ke tashi,Hajiyar Dala da Anty Nasara ke fadin darajan kayan da Tsadan su, tuni ta saki ta san duk hassadann mai hassada Faa'iza dai ta dace da gidan kima da arziki.
Yaya mariya da Yaya Asiya fadi suke"Fa'iza. yanzu ke ce da wannan kayan alfarman harda mota..?
Allah mai hikima in yaso sai ya fidda matacce acikin rayayye in kuma ya so sai ya fidda rayayye acikin mattacce"
Daman haka Allah yake lamarinsa ga Faa'iza ta hau wani mataki na rayuwa,ahalin kuma bata da ilimin boko kuma bata da kyau sannan ba fara bace sannan ita ba kowan kowa ba. Allah ta rike shi kuma ya bata Engr a matsayin miji domin ribar Hakurinta.
Ni ko ina gefe bana mgana sai mirmishi zuciyata da gangan jikina sun cika da kewar Engr da Tunaninsa na kara gwada kiransa ban samu ba. kamar ya kashe wayarsa ni duk wannan kayan basa gabana na samu kwanciyar Hankali da salama shine abunda nafi kwad'ayi.
Ammi bakinta har kunne itace kiran Abba tana fad'a mishi har Goggo sai da ta kira Badariya ko Fadi take"Masha Allah Anty Fa'iza ta tako wlh.."
Nana Fatima sai faman daukan Video take saboda su Hafsah daman sun ce ta Dauki musu duk abunda ya wakana su Anun ko tuni sun fice suna chan wajen Lilo suna wasa
Sai yammah su Maa suka koma gida da Daddare Direba da su kafaya suka kawomana abinci kala kala da ababen sha,Daman Maa ta fad'ama Ammi karfe takwas zamu tafi tunda tafiyar Mota ce in muka isa za'ayi taron gabatarwa bayan la'asar na chan garin haka suke yi in bako ya shigo cikin su,anayi masa taron Introduction kowa ya san shi,shima yasan kowa.
Sai dare Engr ya kirani ina Dauka sai na sakamai shagwaban da bansan na iya ba ina fad'in"Tosin yau ka sakani cikin Damuwa.."
Duk yau fa ban ji muryan ka ba.?
Shima cikin damuwa yace"Tife na Meeting muka yini yi fa. kema kinsan ban samu dama ba ne da sai na kiraki..To yaya..?kun isa tun dazu ko..?kuna gidan Papa ko gidan ki.?
Kinsan fa Saboda zumudin nafara jin muryan ki ko naji sanyi yasa ko Sweethear ban kira ba"
Ni na zayyane masa abunda ya faru sai naji ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Alhandulillah. Gobe sai da rana zan kariso benue lokacin kun iso kuma ko..?
Sai na dagamai kai kafin nace"Maa ta karbeni sosai ita da su kafaya harda Paapa shima yana yi ma addu'a"
Cikin jin dadi yace"Haka suke ba su da damuwa ballatana su san ina son ki, so suna Daraja duk abunda nake so ne"
Na aminta da mganarsa cikin gamsuwa nace"Naga wasu kayan kuma har da mota fa?ka manta ka bani kudi na siya wasu a kaduna..?
Kai tsaye yace"me kika gani..?
wai wad'anan yan kayan..?me kika sani akan Abdulbasit Faa'iza..?
Ai baki san komai ba sai zama yayi zama sannan kila zaki kara sanina sai kuma in nayi wani abun zaki ce daman Haka kake Tosin"
Sai da dai ya sakani Dariya mun jima muna hira kafin yace naje na kwanta Saboda tafiyan gobe.
Ai ban kwanta ba na Dauro alwala na fara jera salollin godiya ga Allah har sai da na gaji. washegari ma Daga gidan su Engr aka kawo mana abinci Direba ne ya kawo mana wannan karon da wuri muka shirya Maa da su kafayat suka Biyo ma Dauke da katuwar BMW din Papa da Direba aciki aka sakani sai Ammi ta dawo nan su kafayatu kuma suka koma wacce muka zo da ita.
Tun safe daman mukayi waya da Engr yace shi sai 12pm zai baro Edo zamu hadu achan to muna Hanya sai yayi ta kirana kunyar Maa yasa ba na Dauka sai ya koma yana kiranta bini bini sai yace"How is Faa'iza? Is she?ok.?
Ita bata damu ba sanin Halinsa da naci kan abunda yake so.
Tafiya tsakanin Abuja zuwa Benue akwai nisa,mun ma yi gudu sai 2pm na rana muka isa asalin Babban gidansu muka sauka wato gidan Sheik Abdulbasit Abdulfattah.
Ya'ya da jikoki cike da gida gabadaya kannen Paapa da yayyensa sun zo da iyalansu,gida ya cika da mutane gasu nan kowannen kalansa Dabam Dabam sai dai sun yi shigan su na yaren su musamman ma mazan.
Dakin Hajiya Kudirat aka saukeni su Ammi kuma sauran dakunan haka ta rikeni tana yaren su ni ba ji nake yi ba. tsohuwa ce fa ta tsufa gaskiya sai dai Hutu da jin dadi.
Daman Hijabi na saka har kasa,sai wata farar amtafa super mai baki da Fari shiyasa ma Hijabin jikina Fari ne,sauran matan kannen Papa da yayyensa ma suka yayyemeni suna ta yare hatta Maa naji itama ta juya yare su kafayatu ko muna zuwa sun shige cikin Dangi.
Ankawo abinci su amala da miyar kuka taji ganda da nama sai jallop d'in shinkafa da kaza abinci dai cima kala kala suma su Ammi suna chan ana karrama su.
Bayan mun yi sallah ne muka natsa ni daman ina tare da Anum da Falaq ne. Maa tayi musu bayanin yanayin taron kayan da zan saka tace matar Uncle din Engr Tobi. Bimpo kenan zata kawo nawa kayan,ni kuma sai daga baya su Ammi suka zo dakin suka sameni Anty Nasara na juya baki tana fadin"Jama'a kun ji yadda yare ke tashi.?
Yaya Mariya tace"Komai sai da sanadi ga shi Sanadin Fa'iza nazo tsakiyar abun naci kuma amala kamar cikina zai fashe"
Dariya aka saka mata Anty Fadila tace"Kai dangin sun burgeni. komai tsab gasu wayayyi kamar ba yarbawa ba."
Hajiyar Dala tace"Uhm ai naga abun mamaki ayi ta cewa yarbawa kazamai masu kashi a leda kaza kaza ni ko da muka zo ban ga haka ba ga su nan Tsab da su kamar ma mu hausawan"
Ammi tace"Ai in kin lura sun surka kowani yare a cikin su, ba kabilanci ko jin kyamar wani yaren".
Haka dai suka yi ta hira suna Tattaunawa ni dai bana saka musu bayan la'asar Maa tace daman za'a fara tarom muna idar da sallah Wata yar matashiya tazo shiryani Wanka ma sake na fesa turaruka sannan aka bani wani less baki da Fari na saka Riga da zani ciki da alaku har Daurin zanin matar ta dauramin ta min Daurin Kallabi irin na su,sai dan kunne da sarka ga murjani da ya saukomin har Cikina hannayena ma ta sakamin su da yawa,Takami baki ta bani mai tsini yana da igiya sai karamar Jaka pos ligth makeup tayi min sai nayi kyau kamar bani? ce uwar yara Hud'u ba.
Suma su Anty Nasara sun shirya,abun dariya har da ciki da alakun suma suka yi suna fadin suma fa duk an zama daya,Har su Anum suma an shirya su da kayan yarbawa su kafayane da wannan aikin yara sai suka saje kamar anan muka same su.
Sai biyar akace su Ammi su fito dani Ita da Hajiyar Dala a haraban gidan an shirya kujeru da kuma in da zamu Zauna sai da muka fito naga ashe Engr ya iso ban sani ba,domin bai kirani ba shima irin less din jikina ne da shi yaci hulansu na ashoke har da karyata gefe sai alokacin na hango kamarsa da yarbawan gefensa aka zaunar dani ina zama ya ramkwafo yana Fadin"Eh Tife..Tife.."
Idanuwana na kan mu shiyasa na kasa juyawa sai dai mirmishi masu Hotuna nata aikin su,sai gani na fito ba mayafi Cikin mutane sai faman kunya nake ji na kasa sakewa shima daya Fahinci haka sai yace"Ki yi hakuri yanzu za'a gama
Nima fa ina jin kishin yadda wasu mazan ke kallemin halalina"
Tokarinsa nayi da gwiwan hannu na ya koma gefe yana dariya, an yi jawabi Maa ita ta gabatar dani ga Hajiya Kudirat itace head of the family,sai kuma suma suka min jawabin maraba da Yarbanci da Turanci Engr yace a fasaara da Hausa,dole a ka samu wani ya yi mgana da Hausa kuma nasan saboda ni ya yi sai naji na kara son shi.
haka aka rika min layi ana gabatar min da su Daya bayan d'aya Engr ya koyamin irin gaisuwan su kamar na indiyawa kayi kamar zaka Duka sai a dafa kanka a saka maka albarka sunaye ko wlh na kasa rikewa ga sunan birjit suna da yawa sosai wlh kamar tsaki.
An ci an sha kuma an yi rawa Engr yaso yajani muyi rawa naki sai yaja su Anum da daman suna tare da shi. suna ta rawa an zubda kudi kamar ba'a son ranar su ba Anty Nasara da su Nana Fatima sun shiga sun sha rawan su,ko ajikinsu ina gefe ina Dariya,sai mangriba aka tashi na samu kudi tunda duk wanda za'a gayamin sunan shi in na gaishe shi sai ya bani kudi sakamakon gajiya yasa ina sallar isha'i sai barci ko Engr ban nema ba,su Anum ko na Tare da shi bama Daki daya muka kwana da su ba Wajen Maa suka kwana.
Da safe kuma akayi walima,gabadaya aka taru afalon gidan manya da yara aka yi karatun Qur'ani izifi Ashirin,naga ranar ilimi naga kuma gidan ilimi ni na fara Bude karatun Daga suratul Muhammad muka fara,Engr kuma shi ya Rufe karatun ashe shima haka yake da kira'a an rarraba charbi da Dardumai sai da yammah kuma akayi party shi a Hall akayi na cikin gari shima an ci an sha kuma an chase,sai washegari ni da Engr zamu wuce Edo su kuma su Ammi zasu koma kaduna.
Mu muka fara tafiya gabadaya kaya na daman suna hade ne waje d'aya. Ammi ta yi ta jadaddamin na rike kamshi da Tsabta biyayya da sanin kan miji sannan bata jina ta bangaran girki,Mun rumgumeni ni da Anum har sai da nayi kwallah tace zata bini nace zan je da ita Engr ma yace da ita zamu tafi Ammi ce tace ba inda zataje.
Sai da naga rabuwan da gaske na fara kuka suna ta min nasiha na rumgume yaya mariya da Yaya Asiya suna ta fadin Fatan alheri Fa'iza.
Haka ni da Badariya kamar wasu yara A babbar Prad??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????o din Engr fara zamu tafi dagani sai shi sai Direba.
An kai ni wajen Hajiya kudirat ta sakamana albarka sannan ta bani kyautan warwaro da ashoben su da murjanai,sai duka kannen Papa da yayyensa suma na samu kyatuttukan na kudi da kaya tare da addu'a daga garesu.
Gabadaya kuma suka rakomu har bakin mota,Abaya na saka maroon mai zanen baki sai Nana Fatima tamin nadin mayafin baki nayi kyau sosai duk da ina kin sakawa sai gashi na saka takalmin kafata ma baki ne,mai Tudu duka kayan jikina ba na kudi kad'an cikin ma wanda muka siyo ne da Ammi ne.
Ina ji ina gani Ammi ta sakani a mota suna d'agamin hannu Engr ma ya shigo Direba ya rufe shi ya tsayama Lallashin Anum ammh tana ta kukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login