Showing 171001 words to 174000 words out of 288345 words

Chapter 58 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

716

nayi masa mgana Tattara yaran nayi zuwa Dakin Mama harda Hafsah saboda chan yafi kusa da tsakar gida yafi iska,Kayan sa da na wanke masa na ninke masa basu kawo wuta ba,ballatana na goge masa,Sai na Tattara na kai masa Dakinsa tun da ya shigo ya shige ciki sannu da zuwa ma dakyar ya amsamin Abincin sa Anum na bama ta kai masa ko da na shiga yana wanka domin naji karan saukan Ruwa a makewayi.
Sai na sauke kayan Hannuna saman katifarsa na zauna gefen katifar ina jiransa bai jima ba ya fito da Dogon wando a jikinsa,Kansa na digan ruwa yana gogewa da karamin Towel,Sai da ya tsaya yana kallona alamun yayi mamakin ganina ni kuma ganinsa ba kaya yasa na mike ina fadin"in ka shirya sai na dawo'
Ban jira cewarsa ba na fice shima bai Dakatar dani ba,Na koma Falo ina yan kaye kaye yara dai ba'a rabasu da Lalata waje ko sau goma zaka gyara shi kuwa,ba jimawa sai ga shi ya fito da jallabiya da farantin abincinsa a nan falon ya zauna ya ci abincin ya sha ruwa,sai ya koma ya kishingid'a yana Hamdala ni kuma falon na Tattara domin ina taka datti Musty ne yayi sharan,ba domin ya share dakyau ba.
Ina ta jira ko zai ce me nake son fadamai sai naji yayi kamar bai ma ganni a falon ba,Sai na samu gefen kafafunsa na zauna ina fadin"Mgana fa nake so mu yi"
Kai Tsaye yace"kunne ke ji ai"
Sai na bude baki zan yi mgana sai na Rufe saboda ina tunanin bazai karb'i mganata ba Sai ya dago yana kallona kafin yace"Uhm ina jin ki"
Sai na dukar da kai ina Fadin"Tsakani ga Allah baka kyautawa abunda kake yi"kai tsaye yace"Da na yi me kuma..?
Ina gyara mganata nace"Kan mganar Zainab mana ka barni ina mata karya. Haba don Allah baka je bafa tun zuwan nan da kayi kafin azumi,Itama ai tana da Hakki a kan ka, kuma Allah zai tambayeka akan hakan ka dauki waya ka kirata ku yi mgana don Allah"
Kamar bazai ce komai ba har sai da nace"Kaji.."
Sai ya gyara zama kafin ya mike ya zauna dakyau yana fad'in"Kina bani mamaki Fa'iza wai wani hakki kike mgana..?ke sau nawa ina zuwa wajenta na tare kuma tasan hakkin ki na shiga ammh bata taba min mganar naki Hakkin da ke kaina ba, sai ke ki bi ki dameni Haba."
Ya karishe fad'a yana Tsareni da idanuwansa da suka fara shigewa Ciki,sai na sunkuyar da kai ina Fadin"ni ba ruwana da wannan. Abunda na sani ne nake gayamaka kai ma nasan ka sani,Tunasar dakai nake yi ciki fa gareta tana Bukatar kulawarka"
Kai Tsaye yace"ke ciki nawa kika Dauka kika haifeshi batare da kulawata ba..?
Sai na kasa mgana kafin nayi mirmishin takaici nace"Ni sunana Fa'iza ni ba yar kowa ba ce. sannan ni ba yar gata bace Fa'iza ba Turanci komai nata zero ne Zainab kuma mai kyau ce yar gata yar Dangi tana da ilimi tana jin Turanci sannan kowa na sonta, kaga kenan Tsakanina da ita akwai Tarin bambamcin da ko a wajen Daidaito na miji bazamu zo Tsara d'aya ba".
Ina kallon cikin Idanuwansa na fadamai haka sai kawai ya rausayar dakai yana fadin"Ashe bazaki bar wannan mganar ba Fa'iza..?baki manta komai ba kenan..?
Ko daman kin fad'ane kawai baki yafe min ba..?
Da Sauri nace"Wlh na yafe maka duniya da Lahira"
Da Sauri ya Tareni da fadin"To me kike son nayi ne ki daina damuna da wad'anan mganganun ne"
Kai tsaye nima nace"ka Saurari zainab sannan kaje ka dubata tana bukatar kulawarka"
Sai ya kankance ido ya mike yana fadin"To bazani ba. Nace bazani ba,Sai ki sani naje dole..Haba mata kin bi kin dameni..?zaman ki nake yi a gidan da zaki rika min kora da Hali.?na riga nayi rantsuwan da bazan kara bin Zainab ba, in tana so na tasan inda nake zata Biyo ni. kuma kin ji ma na rantse bazaki sakani yin kaffara ba. Ba ruwanki in ta kara kiranki kada ki sake d'aga wayarta Umarni ne na baki ba Shawaran ki nake nema ba Fa'iza"
Ya karishe fad'a yana kureni da ido,na bude baki zan yi mgana ya saka min yatsa a saman bakina yana fadin"Shii..Mu rufe babin wata zainab mu yi mganar mu Fa'iza ina mganar mu ta kwana..?baki ga duk na galaibata ba ne saboda rashin ki..?
Kai Tsaye nace"Shiyasa nake so kaje inda zaka samu abunda kake muradi"
Sai kawai ya mike tsaye yana Nuna ni da yatsa cikin bacin rai yace"Rashin kunya zaki yi min Fa'iza don kinga ina Lallaba ki ko..?ko karfi na saka miki Bani da laifi Saboda ke Halaliyata ce. ina binki a Hankali ne Saboda nayi miki laifi ba domin kin fini iko da kanki ba"
Mamaki ya kamani kamar zan yi mgana sai na fasa sai kuma ya Saussauto ya koma ya Duka gabana ya Riko Habana ya dago fuskata yana Fadin"Don Allah Fa'iza ki manta komai mu bama auran mu wata Dama nayi miki alkawarin bazaki kara kuka dani ba don Allah. Wlh na wahala na fara susucewa"
Ya fada lokaci d'aya yana langwabe min kai kamar karamin yaro,sai nayi wuf na kwace fuskata na mike shima sai ya mike zan gudu ya rikoni kafin nayi wani motsi ya kamkameni a jikinsa duk mutsu mutsu na na kasa kwace kaina sai na Saduda kaina ya Dago yana kallon cikin Idanuwana yace"Saboda kin ga ina kyale ki ko..?ni kuma sai na bude baki zan yi mgana, sai kawai naji ya Had'e bakina da nasa waje daya ya fara sumbatata lokaci daya yana kara kaina da Hannayensa a cikin jikina. duk iya kokarina na kwace kaina na kasa tun muna Tsaye har muka zube saman kujera yana Jagwalgwalani fargabana D'aya kada wani cikin yaran nan ya shigo gashi yaki barin bakina ballatana na yi masa magiya sai da ya maidani Tubus ko yatsana ban iya dagawa, Saboda yadda Hannayensa suka Ladaftar dani,Mganar Ahmad muka ji daga kofar daki yana kiran"Umma.."Umma"
Shi ya ceceni zaraf ya tashi daga kaina Daman doguwar rigace ajikina ya Dagemin ita har wuya,saboda bala'i shi ya saukar min da rigan yana kallona takaici da bakinciki suka tasomin,Kallona yayi cikin yar dariya kafin yace"mganin ki kenan. na lura ni nake kyaleki"
Daga haka ya wuce dakinsa yana Dariya sai hawaye suka zubomin nayi Saurin sharewa,saboda shigowan Ahmad yana fadin"Umma barci nake ji"Cikin kasala ina share hawayena nace"je kayi fitsari ka kwanta"
Daga haka na mike na shige Dakina ina share kwallah kamar wacce aka daka kan gado na fada ina cigaba da kukana abu d'aya ya tsayamin a rai in ya cigaba da min haka watarana zai karyamin lagona kuma faruwar haka kamar rug??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ujewar Burina ne.
Kuma ni bazan bari hakan ya faru ba,Wannan kudirin nawa ya Dade a raina cika shi tamkar wajibi ne.
Bansan adadin da na dauka ina kuka ba sai da naji shigowar su Hafsah naje na wanko Fuskata,nazo na kwanta Na rufe ido da suka shigo sai suka yi tsammanin nayi barci nan ko idona Biyu,Har suka yi shirin kwanciya suka kwanta,ni kuma na kasa barci ina Tunanin yaushe ne mafitan da na Dad'e da neman ma kaina zai cika..?
Shin zan iya yin abunda nake hasashe ko ba zan iya ba..?
A haka har barci ya kwasheni,Sai chan wajen ukun dare na tashi nayi alwala na fara Nafila bayan na idar na Daga Hannuna ina addu'ar Allah ya bani juriya da kwarin gwiwa sannan kada yasa ya'yana su zama raunin da zai sa su shiga Tsakanina da Burina.
Washegari Fuskata a Had'e na tashi shi kanshi ya ganni ko gaishe shi ban yi ba shine yace"Ina kwana Anty Fa'iza"
Kallonsa nayi na basar na cigaba da aikin gabana sai ya kwashe da Dariya yana fadin"Wai fushi kika yi..?zaki yi ma mai Dalili yarinya"
Ina jinsa nayi masa banza Da rana Zainab nata kirana sai na rasa ya zan yi da ita.?Sai kawai na dauki wayar na tafi Dakin Mama yana ko kwance kan kujera Mama na zaune a kasa suna Hira yanayin yadda na shigo yasa Mama ta kalleni tana fadin"Fa'iza lafiya..?
Shima sai ya sakamin ido yana nazarina Gabanta na duka na ijiyemata wayar ina fadin"Mama ki masa mgana kila ke yaji mganarki"
Matarsa ke damuna da kira shi kuma in na kai masa sai yak'i mgana da ita. Har ga Allah mama bana so Zainab taga laifina,sai taga kamar ina mata Tsakani da mijinta ne"
Mama sai ta kallesa tana fadin"Shi ina wayarsa ne..?
Kai tsaye nace"Bai gyara ba kuma yaki siyan wata. saboda yasa matarsa ta rika jin Haushi na"
Sai Mama ta Rausayar dakai kafin tace"ka kyauta. Tashi kije Fa'iza zan yi mai mgana"
Na ko mike na ficewata ban ko kallesa ba,inaga Mama tayi mai fad'a yasa ya dauki wayar suka yi mgana,washegari kuma da Safe wajen sha daya sai gata Direba ya kawosu ita da yara,Na karbeta hannu biyu kamar yadda na saba kai Tsaye wannan karon Dakin mijinta ta sauka yana dakin tana zuwa ya shuru Takalminsa ya fice ya'yansa kawai ya Kula ga cikinta har ya fitio ta kara kiba kamar ba ita ba.
Bayan na gama abincin rana munci muka zauna zaman Hira a manganunta na fahimci ita kaddaranta Soyayyan Yaya Ishaq ne shine Rauninta Kuma mahaifinta na kaunarta bazai so abunda zai sosa mata rai ba.
Kai Tsaye ta kalleni tana fadin"Maman Amir Honey yaki ya yafemin laifin da ban ma aikata ba. Daddy mu kad'ai ya Haifa Dagani sai zuzu komai muke so a duniyan nan yana bamu shi baya so yaga muna wahala ganin yadda kwanakin chan nayi ta fama da Laulayi ne yasa yace a cire ciki ammh da nuna bana so ai bai kara mganar ba. meyasa shi Honey bazai sauko ba Har Daddy fa ya so yaje chan su yi mgana yaki ya Saurareni,yanzu haka Daddy na chan ya kafa kwamitin Bincike a ma'aikatarsu kan Case dinsa ammh duk bai gani ba yanzu nazo ko kulani bai yi ba"
Sai Hawaye sharr sai ta bani Tausayi,Ashe an fara binciken ni bama mu yi mganar da Abba ba. Tunda yace min bai samu sun yi mgana da Engr din ba har yanzu saboda baya kasar bai dawo ba,Ina kallonta tana kuka,sai a raina nace ita kuma nata kaddaran kenan..?tana son shi Kuma Dole Mahaifinta ya barta ta biyo abunta take so in har shima yana son abunda yarsa ke so.
Lallashinta na dinga yi ina bata baki ta kara kallona tana fadin"Wlh maman Amir ina cikin wani Hali Cikin nan sani Son kasance da shi yake yi. ammh yaki Saurarena a kwanakin baya kamar zan yi hauka haka nakeji,saboda yanayin jikina yasa sai da na samu sauki na taho"
Na Tausaya mata saboda haka nayi fama da wannan sha'awan Lokacin cikin Ahmad ammh ban samu ba,Domin Yaya ishaq bai saurareni ba akwai ranar da har kuka nayi masa yace shi baya cikin mood din ya gajiye ya Dawo bazai iya min wani amfani ba, ranar kamar zan yi hauka naji kamar na Mutu da addu'a da Taimakon Allah sai da cikin yayi kwari komai ya lafa tsakani ga Allah na Tausaya mata matuka shiyasa na Rike mata Hannu ina fadin"kada ki damu zai sauko in sha Allahu"
Tana sharan kwallah tace"Yaushe zai sauko..?ko fa kallona bai yi ba..?
Don Allah ki yi masa mgana ki tayani basa Hakuri"Sai na kasa mgana kawai ina kallonta ina zan kara mgana nima ta kwabemin Saboda na lura da yadda nake masa mganarta alokacin yake kokarin nuna min nima ai matarsa ce.
Ni dai ina ta bata baki ina fad'amata zai sauko cikin hakane yasa nace"To kiyi masa abunda yake so ki bar aikin nan Maman Fadil sai ya sama miki anan ki dai dawo kusa da shi hakan zai fi"Sai tayi shuru kafin tace"Daddy ne ya hana fa. Ammh wlh naso haka tun da na Fahimci bazan iya zama nesa da shi ba"
Ni ko sai naga na samu damar da zan gayamata gaskiya sai na gyara zama ina fadin"Mahaifa suna da iko a kanmu ne idan muna gabansu. ammh da zarar sun aurar damu mun bar karkashin ikon su mun koma karkashin ikon Mazajen mu,Ki gane wani abu shifa miji ba abun wasa ba ne yana da cikakken iko akan ki Zainab. Yafi mahaifinki iko akan ki, in yace kada kiyi abu kika yi Allah zai yi Fushi dake in ransa ya baci,ko da mahaifinki kika sabamawa dalilin Umarnin mijinki Allah bazai kamaki da laifi ba,a ko'ina Umarninsa na saman na kowa in dai a kanki ne"
Sai tayi shuru tana kallona alamin bata san haka ba ni ko sai na cigaba da Fadin"Annabi muhammad Salallahu alaihi wasallam ya fad'amana in da Allah zai wajabta Sujudda Tsakanin mutane da ya wajabta Sujuda ga mata zuwa ga mijinta.Saboda a nuna Daraja da girman miji ga matarsa"Sai ta waro ido tana fadin"Yanzu duk ina cikin Fushin Allah ne Maman Amir..?
Sai na girgiza mata kai ina fadin"Cikin Rashin sani ne. Shi kuma Allah bai kama mutum da laifin da bai sani ba,Ni dai shawaran da zan baki ki yi kokari ki gyara zamantakewar dake Tsakanin ku,Sannan ki daina Fifita mganar Mahaifinki saman tasa baki kyauta ba ki bashi hakuri ki nuna masa zaki bi Umarninsa sannan zaki Girmama duka muradansa akanki sai a zauna Lafiya"Sai ta damke hannuwana Tana fadin"Nagode sosai Maman Amir.Ban taba ganin kishiya mai kyakyawan zuciya kamarki ba"
Sai kawai nayi mata mirmishi sai gashi na zake ina gayamata yadda zatayi ya sauko,ni nace ta sake wanka ta d'au gayu yau a sha soyayya. Sai Dariyan jin dadi take yi,Mama na Dakinta tana jin mu bata ko leko ba naga yanzu ta daina ma Zainab din Rawan jiki,yara suna dawowa makaranta suka fara Murnan ga Anty ga su Farhan,ko Dakin nasa ma ni na shiga na gyara shi Saboda bata iya ba. Da Daddare tuwon shinkafa nayi mana miyar ganye,da gyad'a sai Dare ya Dawo ina ta mamakin shi ko ina yaje haka?
Ruwan wanka ma da yace na sakamai yana zafi na juye na bama Zainab nace ta bisa Dakin dashi ta karba ta wuce to bansan ya suka kare ba,Saboda afalo muka hadu muka ci abinci gabad'aya. ina kallo sai kallonsa take yi shi kuma yana basarwa kamar an matsi bakina nace"Wai ina kaje yau tun Safe ne.?
Kamar yana Jirana kawai sai ya harareni kafin yace"masallaci naje na zauna ina kai kararki wajen Allah. Ki nemi yafiya ta.
wlh in ban yafe miki ba, bazaki yi albarka ba Fa'iza"
Sai na saki baki ina kallonsa kuma agaban yara ga Hafsah. zaraf Anum tace"Umma me kika yi ma Daada..?
Kafin nayi mgana yace"Tambayeta dai Anum.."
Zainab na gefe tace"Kema fushi yake yi dake Maman Amir..?
Kawai sai ya kai mata Harara yana Fadin"Ina ruwanki..?
Sai ta kalleni nima na kalleta nayi mata signa da ido sai ta mike nima na mike ina fadin"Amir ka kwashe kwanukan nan ka kai kitchen.
Anum ki share falo Hafsah ki yi ma yaran shirin kwanciya Fadil dina taho muje mu kwanta"Yaro ko ya taso daga wajen Uban ya nufoni na Daukesa na kalli Zainab ina fadin"Ki shiga ki gyara masa shimfid'a. Sai da Safe"
Sai ta amsamin da Toh,ta wuce nima na wuce da kallon mamaki ya bimu da shi kuma muka ki basa damar mun Fahimcesa yaran kuma suka rika fad'in"Umma sai da Safe,Anty Sai da Safe"
ni dai tunda na shige Daki kamar Allah ya aikomin da barci ina Kwantar da Fadil nima nabi gefensa na kwanta sai barci sai asuba na tashi,Da Safe basu ma fito da wuri ba. Sai chan rana tunda naga ta fito tana Annushuwa na kalleta ina fadin"Ya ya.?
Sai ta bani Hannu muka tafa Lokaci daya tana fadin"Komai ya daidaita.
Ammh fa yace sai na ijiye aikina na Dawo nan sannan zai san ina son sa"
Kai Tsaye nace"Sai ki nema wani anan ba Shikenan ba"
Kai ta gyada min kafin tace"Haka za'ayi. Nasan zamu sha rigima da Daddy ne"
Ina shirin mgana kawai daga bayanmu mukaji muryansa yana Fadin"Fa'iza wlh kiji Tsoron Allah. Ki kuma Tubar masa saboda abunda kike yi sam bai dace ba."
Kafin nayi mgana tayi zaraf tace"Honey laifin me Maman Amir tayi ita kuma..?
Sai ya harareni yana fadin"Tambayeta ita ai tasan komai"
Sai ta juya tana kallona kafin tayi mgana na tare ta da fadin"Kada ki biye masa bansan abunda yake mgana ba"Saboda kada ya kara mgana na yi wuf na fice ina sauke Numfashi,shikenan ma'auratan suka Daidaita kansu,Sati daya tayi mana sannan ta koma ta kuma ta tabbatar min zata yi kokarin ta ijiye aiki sannan ta Lallabi Daddy ko gida ya siya mata a nan ni ko araina nasan Yaya Ishaq bazai yarda ba. kuma Tsakani ga Allah wannan gidan yayi mana kad'an ace mata Biyu da yara ga Mama shima ai sai ya Duba ammh yadda bai sakoni aciki ba nima ban Tusa kaina ba..
Maganar auran Halisa ya taso Anty Binta ana ta shirye shirye ni dai nace zan gyara amarya ta bangaran jiki da kamshi,kuma Anty binta na fad'amawa sai gashi tana min godiya sannan tamin mganar zatayi Zobo da kunin aya ranar walima tana so nayi mata,girki ma in ba damuwa na shige gaba ban nuna mata komai nace duk zan yi,mun yi waya da Badariya tace bazata dawo ba,ni na bata baki tace zata dawo ana gobe Daurin aure tunda kano za'a kawo amarya sai ta biyo su ta dawo abunta nace shikenan kuwa.
Da kudina na siyo kayan hadin Turaruka na had'ama Halisa da na Rushi da Humra da kwallacha sun kai na Dubu ashirin,sannan ga na gyaran jiki tun ana saura sati daya biki take zuwa kullum da yammah ina mata Gyaran jikin.
Ranar da muka kwana uku muna yi sai dare na gama mata,ita da wata kawarta suka zo,kuma tare suka tafi a dakin Mama nake yi mata ita tunda ta gidace,Mama sai mamaki take yi tana fadin"Ikon Allah.."
Ranar na gaji,ko zobon yammah ban Dafa ba Hafsah na makaranta,bata dawo da wuri ba,Ban iya ko yin abincin Dare ba saboda bayana ya rike sai nayi wanka na gasa jikina da Ruwan zafi nayi sallar mangariba ina zaune ina lazumi Hafsah ta shigo ina ta mata fadan ina ta Tsaya sai tace min bata samu abun hawa ba ne da wuri, sai na Sassauta nace in ta huta ta Dafamana ko Cousscouss ne.
Tace to bari tayi sallah Yaran kuma suna Falo Yaya Amir na biya musu karatu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login